05
by @oumfatima33
*MEERAH*
*OUM FATIMA*
*05*
Lokacin da Ajmal ya kammala secondary school zai shiga Jami'a ne, Hajiya Na'imatu tayi yanda tayi ta lallaɓa Abby akan a sama masa makaranta a nan Abuja. Hakan kuwa aka yi ya amince da hakan don bai yi tunanin da biyu ta nemi hakan ba.
A ɓangaren Hajiya Na'imatu kuwa don ta samu damar da zata mayar da yaronta kusa da ita yasa tayi hakan. Tunda aka yi maganar Momy dasu Ya Sultan suka fara kewar rabuwa da Ajmal da za suyi.
Nice kawai ban damu ba, don ni murna ma nayi azababben dake takura min zai tafi in samu sake. Ko kaɗan bama jituwa da Ya Ajmal, kasancewarsa miskilin mutum da bashi da wasa ko kaɗan.
Kullum yana fama da ɗaurarriyar fuska wai shi ga wanda baya ɗaukar raini ko kaɗan, saɓanin ni dana kasance yarinya mai ƙiriniya da surutu sosai.
Kasancewar ni kaɗai na tashi Mace a cikinsu, da irin gata da sangartar da suke min yasa na tashi da ƙiriniya da rashin jin magana irin wanda aka san yara Maza dashi.
Duk abinda nake so shi nake yi saboda ko kaɗan Dady baya son ɓacin raina, haka ta kasance a ɓangaren Ya Sultan da sauran yayuna. Momy ce kawai ke ƙoƙarin tsawatar min idan nayi wani shirmen, ita ma kuma in a gaban Dady ne baya bari.
Sai ya zamana cewa Ya Ajmal ne kaɗai ke iya min tsawa idan nayi kuskure tun ina ƙarama, kuma idan ya saka min doka dole nabi don ko Dady baya hanawa saboda ƙaunar da yake masa shima.
Wannan dalilin ne yasa sam bana saukewa dashi kamar su Ya Sultan, ko zama nayi a wuri yana zuwa nake tashi in bar wurin.
Lokacin dana fara wayo sai na ɗauki hakan a matsayin tsana da ƙiyayya yake nuna min, wannan shine dalilin daya saka na tsane sa sosai bana son zama kusa dashi. Duk irin ƙauna da shaƙuwar dake tsakanina da Ya Sultan idan suna tare bana zuwa inda yake.
Duk lokacin da Ya Sultan ya tambaye ni a kan me yasa nake gudun Ya Ajmal na kan ce masa.
"Bana son sa ne Yaya, saboda shima ya tsane ni." Duk sanda na faɗi haka zama Ya Sultan keyi yayi ta ƙoƙarin fahimtar dani kan cewa, Ya Ajmal bai tsane ni ba. Duk abinda yake min don gyaran kaina yake yi min shin.
Duk lokacin daya faɗi hakan jinsa kawai nake ba don na fahimta ba, har duka na Momy ta taɓa yi lokacin dana furta wa Ya Ajmal cewar Na tsane sa bana ƙaunar sa a gabansa.
Hakan ya faru ne lokacin dana taɓa haɗa party na rashin dalili, na gayyato friends ɗina har da Mazan school ɗin mu, muka kunna kiɗa a garden ɗin gidanmu muna ta tiƙar rawa.
Koda ya dawo gidan ya same mu a haka yaje yayi ta min faɗa a gaban friends ɗina, sannan ya kore su ya lalata min party. Hakan ba ƙaramin ɓata min rai yayi ba don haka ina kuka na furta masa waɗan nan kalaman.
A lokacin dana furta masa waɗan nan kalaman tsare ni kawai yayi da kaifafan idanunsa da suka yi wani irin sauya launi. Bai furta komai ba ya juya ya fice daga gidan baki ɗaya.
A lokacin ne Ammy ta saka hannu ta ɗauke ni da mari, abinda bata taɓa min ba tunda ta haife ni. Kai tunda nazo duniya ma babu wanda ya taɓa duka na, don ko a school ba'a taɓa dukana ba.
Wannan dalilin yasa na ƙara jin tsanarsa matuƙa a cikin zuciyata, don karon farko an dake ni ta dalilinsa. Nasiha sosai Momy tayi min bayan nan, ta nuna min kuskuren abinda nayi. Ta kuma saka ni dole na bashi haƙuri wanda ya ƙara min nauyin tsanar dana masa.
Shi yasa lokacin da aka sanar da batun tafiyarsa Abuja karatu nafi kowa farin ciki, don har ɗan ƙaramin party sai da na shirya. Sai dai kuma abinda ya rage min armashin farin cikin nawa, shine Dady ya sanar damu cewar har Ya Sultan zasu tafi suyi karatun tare.
Ba haka Hajiya Na'imatu (Mamy) taso ba, don Abby yace a gidansa Sultan da Ajmal ɗin zasu zauna suyi karatu. Taso ne ta janyo iya ɗanta ta samu lokaci da zata jashi a jiki sosai ta raba shi da kanainayar da Momy da zuri'arta suka yi wa yaronta.
Musamman ma wannan shagwaɓɓiyar tar tata mara jin magana, wacce ta lura da cewa duk yanda yaron nata ya kai ga kame wa baya iya ɗauke kansa a al'amarin yarinyar. A zahiri babu wata shaƙuwa ko jituwa a tsakaninsu, amma sai dai yana fin kowa damuwa idan wani abu ya same ta.
Ko hutu yaje mata can Abujar aka kira shi aka sanar da shi cewar wani abu ya same ta, tofa baya iya ƙara minti biyar a inda yake ba tare daya tafi ba.
Ita fa haka kawai bata son ko wace irin alaƙa ta riƙa haɗa yaronta da ita, don ita sam ba son hakan take ba.
Dole babu yanda ta iya tana ji tana gani Sultan da Ajmal suka dawo gidanta da zama da sunan karatu, don ko giyar wake ta sha bata isa ta cewa Abby Sultan ba zai zauna mata a gida ba.
****** Ya Sultan da Ya Ajmal sun tafi l Abuja inda suka fara karatun su cikin kwanciyar hankali, Ya Sultan baya damuwa da rashin sake masa fuska da Mamy keyi. Koda ya lura da yanayinta ma sai ya kame kansa.
Yayin da ni kuma na samu sake sosai a gida nake yin abinda naga dama, don ma Momy na taka min birki a kan wani abin.
A lokacin da nake wannan fitinar fa ba wasu shekaru ne dani ba, don ban fi shekara goma sha uku ba. Don a lokacin ina Js 1 ne a makaranta. Kawai tsabar rawar kai ne da nake dashi a lokacin.
Rashin ji sosai muke tafkawa nida ƙawata Zeezee wacce hali yazo ɗaya muke abota, mun haɗu da Zeezee ne a makaranta rana ɗaya aka kai mu secondary school. Gurin zama ɗaya aka bamu wanda shine silar ƙulla zumuncin namu.
Rashin Ya Ajmal a gidan ba ƙaramin sake na samu ba, duk da Momy na min faɗa idan nayi wani. Idan taga abin nawa yayi yawa sai tace zata kira sa ta faɗa masa ya bar abinda yake yi yazo ya saita mata ni.
duk lokacin data faɗin hakan ina yin sanyi na kwana biyu, don na tsani abinda zai haɗa ni wuri ɗaya dashi.
Abinda na tarka duk lokacin da suka zo hutu sai in gudu gidan Mommy Safiya (Yayar Dady). Ko ɗaya daga cikin gidajen su Uncle Abdurra'uf.
Babu mai hana ni tunda normal ne ana kai mu daman, suma kuma yaransu suna zuwa gidanmu hutu. Kasancewar haɗin kan da Familynmu ke da shi, yasa muke ɗaukar ko ina gida.
A haka su Ya Sultan suka kammala degree ɗinsu, inda babu ɓata lokaci Dady ya sama musu makaranta mai kyau a UK zasu je su ɗora master's ɗinsu a can. A lokacin su Ya Maheer ma duk suna ƙasashen waje karatu, Ya Aryan ne kawai ya kammala secondary shima ana masa shirin tafiya karatun.
A lokacin mu kuma muka zana jarabawar kammala aji uku zamu shiga Senior section, zuwa lokacin ina da shekaru sha biyar don haka ƴanmatanci ya fara bayyana a gare ni. Ita yi da rawar kai ya ƙaru nida Zeezee jin kanmu muke dai-dai da ko wace budurwa.....
--------------------
A yau ne muka shirya gagarumin party na JSSCE ɗinmu, a gidan su Zeezee muka shirya partyn saboda Ya Ajmal yana gida. Bana so na shirya a gidanmu in gama tara friends ɗina yazo ya zubar min da Class a gaban su.
Don haka muka yanke shawarar shirya wa a gidan su Zeezee da yake a nan cikin street ɗin mu ta can ƙarshe, Dady baya nan yana Abuja don haka Momy kawai na tambaya. Da farko taso hana ni sai da na saka mata rigima, na kuma tabbatar mata a cikin gidan su Zeezee ne za muyi sannan ta amince.
Duk da haka sai da tace Ya Aryan ya raka ni sai ya dawo, ban ƙi ba na amince da hakan tunda dai na samu an barni. Shirya wa nayi cikin sababbin kayan da Ya Sultan ya kawo min lokacin da suka kammala degree ɗinsu ya dawo gida.
Pallazo trouser ne tare da rigarsa, kasancewar kayan masu laushi ne yasa suka kwanta a kyakykyawan jikina Masha Allah.
After dress na ɗauko baƙa na ɗora a saman kayan sannan nayi rolling mayafinta, turaruƙana nabi ɗaya bayan ɗaya na bulbula saboda ina matuƙar son harkar ƙamshi.
Gaban mirror na tsaya na jujjuya na tabbatar komai yayi min yanda nake so sannan na ɗauki ƴar ƙaramar hand bag ɗina na fice.
A living room na samu Ya Aryan ya shirya yana jira na, don haka sallama kawai na yiwa momy muka wuce.
Duka da cewa babu nisa sosai tsakanin gidanmu dana su Zeezee, sai da Ya Aryan ya ɗauki mota saboda in ya ajiye ni zai wuce aiken da Momy tayi masa gidan Mamy Safiya kai mata saƙo.
A ƙofar gidan su Zeezee Ya Aryan yayi parking na fita.
"Ki jira ni zuwa 6 zan zo in ɗauke ki." Ya faɗa yana duba agogon hannunsa.
"Okay." Na faɗa ina satar kallon wayarsa ina sosa kai.
"Menene kike wani kallar min waya?." Ya faɗa yana hararata.
"Ya Aryan don Allah ka ara min wayar ka, kaga Friends ɗina fa duk suna da waya. Kuma pictures kawai zan ɗauka nima don Allah!." Na ƙare maganar ina marairaice murya sosai nayi kalar tausayi.
"Jibe ta tamkar wata mumina, wato dai in kina son Abu a wurin mutum kin iya kwantar da kai ko?." Ya faɗa yana harara ta.
"Please mana Ya Aryan." Na kuma faɗa ina haɗa hannayena. Kwaffa ya ja sannan ya ɗauko ɗayar wayarsa dake ajiye a gefensa ya miƙo min yana cewa.
"Karɓi ba don halin ki ba, Allah kuma idan kika min shirme a waya ba zan ƙara baki ba." Cike da farin ciki na karɓa ina cewa.
"Thank you My Ya Aryan."
"Eh da yake kina son Abu a wurina ba, amma idan ba haka ba ai kowa ya san nine nan marainin wayonki."
Ya Aryan ya faɗa yana hararata. Dariya na ƙyal-ƙyale da ita ina cewa.
"Allah ba haka bane Ya Aryan, kai ma ka san daga Ya Sultan ɗina sai kai." Na faɗa ina juya wa na nufi ƙofar gate ɗin, bayan na ɗaga masa hannu. Gir-giza kai kawai yayi ya tashi motar ya tafi yana murmushin halin autar tasu.
****** Ina shiga gidan su Zeezee na fara cin karo da wasu daga cikin friends ɗinmu sun fara zuwa, gaisawa muka yi da waɗan da muka haɗu a compound sannan na shige ciki. Mom ɗin Zeezee naje na fara gaisarwa sannan na tambaye ta Zeezee.
"Tana ɗakinta tana jiran ki tun ɗazu." Mom ta bani amsa.
"Bari naje na same ta." Na faɗa ina miƙewa, kai tsaye ɗakin Zeezee dake sama na nufa. Da sallama na shiga bayan nayi nocking.
A gaban mirror na same ta tana faman tsara kwalliya a fuska, kasancewarta mai son kwalliya. Saɓanin ni da bata dame ni ba ko kaɗan.
Harara ta watso min tana faɗin.
"Haba Bestie sai yanzu zaki zo partyn da kin san cewa kece ƙirjin biki?." Ta ƙare maganar cike da ƙorafi tana hararata. Murmushi nayi mata nace.
"Ki bari kawai Bestie kin san da ƙyar Momy ta bar ni na fito, shima kuma sai da ta haɗa ni da Ya Aryan ya rako ni. A hakan ma fa saboda wan can azababben baya nan ne!." Na ƙare maganar ina tsuke fuska, tuna wa dashi kawai da nayi.
Dariya Zeezee tayi tana cewa.
"Wai kina nufin Ya Ajmal?." Sanin ba amsa zata samu a wurina ba ya sata ci gaba da cewa.
"Wallahi ina mamakin rashin jituwar ki da Ya Ajmal Bestie, any way tun da dai kin ƙaraso muje kawai a kafta. Su Billy sun ƙara so tun ɗazu suna can wurin da aka yi mana decoration suna kula da sauran tsare-tsaren kafin mu ƙara so." Ta ƙare maganar tana miƙewa don ta kammala........
Barka da dare, da fatan anyi hutun weekend lafiya.
Oum Fatima
***