Page 12.
by @zeeykumurya
*BARA A KUFAI*
12.
Da fara'a Uncle Aminu ya juya ya dube ta ya ce. "Mun ƙaraso, ki shiga ciki, ga ƙofar entrance ɗin can, ni zan sake fita na ɗauko ƙannenki, na riga na faɗa wa Auntyn naki tare nake da baƙuwa, so da kin shiga za ta gane." Yalwataccen murmushi Hasina ta yi tana jin kamar ta ce su fita tare saboda sanyin AC da ƙamshi sassanya da yake ratsa ta, ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Tom shikenan Uncle na gode sosai, sai ka dawo Allah ya kiyaye hanya." Ya amsa da Amin cikin jin daɗin ɗabi'unta na ladabin da take yi masa, a ransa yana ayyana ba za su samu matsala da Laila ba don tana da tarbiyya, da ma ya san ƴaƴan Amma ba za su kasance saɓanin haka ba.
A hankali take tafiya tana ba wa na mujiyarta abinci, tana ganin Maigadi ya buɗe masa mota ya fita ta doka tsalle tare da juyin rawa cikin murna, a fili ta furta. "Alhamdulillah! Mafarkina ya fara tabbata, yau ni ce a irin wannan gidan? Zan yi rayuwa na kwana a cikinsa? Allah ka kawo mini wanda zai kai ni irin wannan gidan ni ma, na huta da gwaɓa maganar mutane da suke ganin kamar ba zan samu irin mijin da nake so ba." Ta yi shiru tana tuna masu cewa suna son ta da ba ta kula su, yan unguwarsu da masu zuwa siyan ƙosai gurin Amma, tsaki ta ja da ta tuna wasu ko cikakkiyar suturar arziƙi ba su da shi. Sai da ta saisaita nutsuwarta sannan ta nufi part ɗin da ya nuna mata, wanda shi ne babba a cikin Apartment uku da ta gani a gidan, cike da zumuɗi ta fara knocking.
Farha na zaune a kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin ƙasaita tana latsa waya, Laila kuma tana ta zaryar kawo mata abubuwan motsa baki.
"Wai ba yanzu muka gama ciye-ciye ba shi ne za ki zo kina jibge mini wannan tulin kayan?"
Murmushi Laila ta yi ta ce. "To ai wancan daban wannan kuma na gidana ne." Taɓe baki Farha ta yi wanda ya zame mata jiki ta ce. "I'm full, ki zauna kawai mu yi abin da ya kawo mu, ko ba ki san dauriya kawai nake yi ba? Wuni guda ba na tare da mijina, kuma tun ɗazu ya sanar mini ya koma gida." Ƙaramar dariya Laila ta yi ta ce. "Wannan miji naki yana shan gata da kulawa da tattali, na rasa irin wannan ƙauna, ga shi ku ba sabon aure ba bare a ce, Allah ya dai ya kawo mana yara masu albarka ƴaƴan soyayya."
"Ba za ki gane ba ne." Farha ta faɗa tana bin gidan da kallo sannan ta ce. "Kina da Housemaid me?" Kai Laila ta girgiza tare da faɗin. "Ba zan iya bari mijina ya dinga ganin gilmawar wata mace bayan ni a gidansa ba, shi ya sa nake daurewa na yi ayyukana da kaina." Jinjina kai Farha ta yi, daidai nan suka ji bugun ƙofar Hasina. Da mamaki Laila ta tambayi waye bayan ta tashi ta ƙarasa bakin ƙofar, Hasina ta ce. "Ni ce."
"Ke ce wa?"
"Niece ɗin Uncle Aminu." Ta faɗa cikin azarɓaɓi.
"Niece?" Laila ta maimaita tare da buɗe ƙofar.
Da rawar jiki Hasina ta janyo ledarta za ta shiga tana murmusawa, kallon sama da ƙasa Laila ta yi mata a wulaƙance, tana yatsina fuska kamar ta ga kashi ta ce. "Baiwar Allah daga ina? Ban gane ki ba."
"Uncle Aminu ne ya sauke ni, ya ce ya sanar mini ma tare muke."
"Ok." Kawai Laila ta ce ta ba ta hanya ta wuce cikin danne ɓacin ranta, wannan kucakar ce ta shigo mota tare da mijinta har suka shaƙi numfashi ɗaya?
Hasina za ta zauna a kan kujera ta yi saurin katse ta a tsawace. "A'a'a'a! Kar ki zauna mini akan kujera, ga hanyar kitchen can, ki shiga za ki ga towel ki goge ƙafarki sai ki zo ki zauna a kan carpet." Cikin ladabi Hasina ta ce. "To Aunty." Tare da rakuɓa jakar hannunta a jikin kujera.
"Tafi da ita ki ajiye a can bangon." Ta faɗa a ƙyamace.
Farha dai bin su kawai take da ido, Hasina kam ko a jikinta abubuwan da Laila ta yi mata, ita dai indai za ta bar ta ta yi rayuwa a cikin gidan ai ta gama yi mata komai, saboda ko ita ce aka ce nan gidanta ne za ta iya fiye da hakan ba.
Tsabar ɓacin rai har huci Laila take yi, wani murmushi Farha ta saki tare da faɗin. "Mu je daga ciki tunda kin yi baƙuwa." A ƙule Laila ta ce. "Ya dai yi, ni me zai haɗa ni da wancan abar kamar mai wanka da kalwa? Ba ki ji har falon ya sauya ba."
Ba su daɗe da shiga ba suka fito jikin Laila duk a sanyaye da jin bayanan Farha, don abu ne da ba ta taɓa tsammani ba wanda ya matuƙar ɗaure mata kai ya kuma caza mata ƙwaƙwalwa.
Hasinah na zaune a inda aka umarce ta, ta saki baki da hanci ta tasa TV a gaba da kallo kamar wata shashasha.
"Ke!" Laila ta kira ta cikin Faɗa.
Cikin kwantar da murya Hasina ta ce. "Na'am Aunty."
"A gidan Uwar wa na zama auntyn taki? Wai ke ƴar wacece ɗinsa ma tukunna? Ban fa gane ki ba, ban ma taɓa ganin ki ba."
Labarin zuwan Uncle Aminu da yadda aka yi ta biyo shi ta ba ta in brief.
Kallon juna suka yi ita Farha sannan ta ce. "Saboda jaraba daga ganin sai ki kama ki biyo shi? Ku wai matsiyatan nan me ya sa ba kwa iya riƙe zalama da kwaɗayinku ne?" Ta ƙarashe maganar tare da jan tsaki.
Murmushi Farha da ta ƙure Hasina da ido ƙur ta saki ta ce. "Haba Ƙawata, menene a ciki don ta yi zumunci? Ni har ta burge ni ma, ina son mutum mai son nasa." Washe baki Hasina ta yi amma ba ta ce komai.
"Saka mini numbernki a nan, ni na samu ƙanwa, yanayinki ya nuna ke mai tarbiyya ce, ni kuma ina son yara masu hankali."
Mamaki ne ya kusa hallaka su, ita Hasina har da farinciki, wannan zuƙeƙiyar matar da tun ɗazu take satar kallon ta saboda kyan fatarta da gayun da ta sha ita ce take cewa ta burge ta? Har ta buƙaci numbernta? Lallai yau ta tashi da sa'a ta shigo wannan gida da ƙafar dama, irin mutanen da ta daɗe tana fatan mu'amala ta haɗa ta da su, ashe dai lokacin zai zo, kamar ta taka rawa tsabar murna, da rawar jiki ta karɓi tsaleliyar wayar Farha da take ta tashin ƙamshi ta saka numbernta ta mayar mata.
Laila kuma sanin halin ƙawar tata na ƙyamar talaka da raina mutane ne ya sa mamaki ya cika ta, har Farha ta karɓi wayarta ta kira Hasina ta ga tata lambar ba ta farfaɗo daga sandarewar da ta yi ba, girgiza kai ta yi a ranta ta ce. 'Ruwa ba ya tsami banza, dole akwai dalilin da ya saka ta yi haka.
***** ****** ******
Sai wajen uku na dare Ahayan ta farka, lokacin su Ummi sun dawo sun ƙara komawa gida saboda ba za a bari su kwana da yawa ba, sai Umma kaɗai ta gani tana gyangyaɗi a ƙasa, kanta ya yi mata wasai, amma fayau take jin ta babu ƙwari jikinta, ga cikinta kamar an yi mata yasa har hanji saboda yunwa.
Kulawar da Umma ta dinga ba ta ba ƙaramin ɗaure mata kai ya yi ba, tana yi mata sannu tare da yi mata duk abin da ya dace. Ta haɗa mata tea ta sha sannan doctor ya zo ya ƙara duba ta, bayan ta sha magunguna ta ƙara komawa bacci.
Washegari tunda safe su Ummi suka zo musu da abincin kari, bayan sun gaisa sun yi mata ya jiki Raudah ta dubi Amma ta ce. "Baba yana ta faɗa, wai sai kin dawo, da ƙyar Yaya Saif ya taushe shi bayan ya ba shi toshiyar bakin biredi da ƙwai da safen nan, Inno kuma tana zuga shi, da Yaya Saif yana ba shi haƙuri ma zagin shi ta yi ta yi." Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Umma ta sauke ta ce. "Ki ce da na shiga tara yau ba da ban Saif ba?" Yadda ta yi maganar a gigice ya saka Ummi faɗin. "Wallahi wannan tsoron na Baba da kike yi shi ya sa yake ƙara raina ki, Umma Lantana da ba ta yi masa haka ai ya fi shakkar ta a kanki, ko a jiyan ma fa sai da muka koma ta dawo, amma faɗa kaɗan ya yi mata ya ƙyale ta." Numfashi Umma ta sauke ta ce. "Yaro man kaza, a yi sha'ani kawai don ba gane abin da nake gudu za ku yi ba." Ahayan dai tana kwance idonta a lumshe tana sauraren su, ji take da ma ta dawwama a asibitin akan ta koma gida saboda matsin da take fuskanta da rayuwar ƙuncin da take. Su Ummi ba su daɗe ba suka tafi saboda zuwa makaranta, a nan suka bar Sabira suka ce idan suka dawo sai su koma da ita, kuɗin da Kamal ya ba su a jiya da shi suka yi amfani wajen yin breakfast ɗin da suka kawo su ma suka ci.
Wajen shaɗaya Saif ya zo. Bayan sun gaisa da Umma ta fita wanko kayan da Ahayan ta sauya ta bar su shi da Sabira.
A hankali ya ja kujerar da ke gaban gadon ya matsa kusa da ita ya fuskance ta, cikin tausasa murya ya ce. "Ahlove!" Kanta ta ɗaga a hankali ta kalle shi.
"Ya jikin naki?"
"Da sauƙi Alhamdulillah, sun ce ma zuwa anjima za su iya sallamar mu."
"Ma sha Allah, Allah ya ƙara sauƙi ya ba ki lafiya, duk na damu sosai, ga Inno ta kafa ta tsare da ƙyar na samu na sato hanya na zo." Ya ƙarashe maganar yana miƙa mata ayabar da ya ɓare mata a cikin kayan fruit ɗin da ya zo da shi. Murmushi ta yi ta karɓa ta ce. "Na gode sosai Yaya Saif Allah ya saka da alkhairi ya biya ka da aljanna."
"Amin ya rabb, amma ki daina yi mini godiya, don dole ne miji ya kula da matarsa, kuma ko ma ba wannan yayata ce ta yi sanadin w...."
"A'a Yaya Saif, don Allah kar ka ce haka, Allah ne ya ƙaddaro mini, kuma a nan ma Ulcer suka ce tana damu na sai kuma stress, ka ga ba shi da alaƙa da Aunty Laure kamar yadda kake zato."
"Na zato ba ne Ahayan abin da aka tabbatar ne, ni na san tunda har Abba Adam ya saka baki a cikin lamarin nan ba ƙaramin abu ba ne."
Da mamaki Ahayan ta ce. "Ya saka baki kuma? Ban gane ba, na san dai Umma ta ce shi ya kawo mu ya biya kuɗin komai." Saif ya ce. "To har kiran Aunty Laure ya yi ya ja mata tsatstsauran gargaɗi akan kar ta sake taɓa ki, ko ɗazu da safe sun yi waya da Inno tana ta nanata maganar alamun ba ƙaramin dukan ta ta yi ba." Numfashi Ahayan ta sauke ta jingina kanta da jikin gado cikin al'ajabin maganar da aka ce Abba Adam ya yi wa Ramlah, abu ne da zaton kowa ba zai taɓa hasasowa ba, ba ta taɓa tunanin tana da wannan darajar da wani zai damu don an yi doke ta ba, hawaye ne masu zafi suka zubo mata ba tare da shirya musu ba.
"Kukan na mene kuma Ahlove?"
Numfashi ta ja da ƙarfi ta ce. "Har za a tambaye ni kukan me nake yi a wannan karkatacciyar rayuwar tawa da ni kaina ban san ina zan tsinci kaina a gobena ba? Wallahi Yaya Saif tunda na farka nake kallon mutane suna hada-hadarsu cikin nishaɗi da farinciki, su babun abin da yake damun su a rayuwa, ni kuma ni kaɗai na san me nake ji a cikin raina, ni kaɗai na san irin raɗaɗin zucin da nake kwana na tashi da shi a kullum."
Cikin matsanancin tausayin ta ya ce. "In sha Allah za ki yi farinciki za ki zama abar alfaharin da ba a taɓa tunani ba, komai zai wuce ya zama labari."
Girgiza kai kawai ta yi tare da gimtse baki ba ta ce komai ba, ta san babu mai gane abin da take ji bare ya fuskanta, babu mai gane irin hasashen da take yi da abubuwan da suke tattare da ita, rayuwa kawai take don rai da numfashi suna yawo a jikinta, amma da za a ba ta zaɓi ko jinkiri ba za ta yi ba za ta zaɓi mutuwarta.
"Na daɗe da son sanin asalinki da tahirinki amma a duk lokacin da na tambaye ki sai dai ki saka kuka kawai ba za ki ce mini komai ba, kamar yadda na faɗa maka ina tantanma akan Umma ce ta haife ki tun lokacin da aka kawo ki gidanmu, saboda a kodayaushe ina tambayar kaina me ya sa take treating ɗinsu yadda ya dace amma ke saɓanin hakan ne? Me ya sa kike kasancewa cikin tunani a lokuta da dama? Me ya sa kodayaushe kike cikin yanayin rauni da damuwa? Me ya sa komai aka yi miki kike shanyewa? Me ya sa kika zamar da rayuwarki kamar raƙumi da alakar da wasu suke ja, ba ki da wani ra'ayi ko yin wani abu naki sai abin da aka saka ki ko a ba ki umarni? Wannan ya sa nake zargin akwai lauje cikin naɗi, akwai wani abu a cikin rayuwarki da ba mu sani ba, ina son sani don Allah Ahayan!"
Murmushi ta yi mai ciwo ta ce. "Zan faɗa maka Yaya Saif, za ka san komai game da ni in sha Allah."
Dawowar Umma ce ta katse musu hirar da suke yi, sallama ya yi musu ya tafi bayan ya ajiye wa Umma kuɗi don ya san suna cikin buƙatar shi.
A ranar aka sallame su, jikin nata ya yi kyau sosai don ta samu kulawar da ta dace, sosai suka jaddada wa Umma kula da shan maganinta akan kari, da kuma barin ta tana hutawa tana samun bacci ishashshe gami da cin abinci akan kari.
Da Umma Lantana suka fara cin karo a tsakar gida, ta baje shirgin kayan tuwon dare, ga murhu ta hura har biyu. Kallo ɗaya ta yi musu ta ɗauke kai, don kamar yadda ƙawayenta suka ba ta shawara yanzu ba da ba ce, ta zama surukar mai kuɗi Umma ba ajinta ba ce ta daina kula ta, jiya da yau wunin wani ƙauye suka yi ita da ƙawayen nata, ta je gurin wani malami an kafe mata auren Zeenat gam tare da riƙe musu mijin gam a hannu yadda za su juya shi son ransu, shi ya sa ma duk a gajiye take, gefe guda kuma ga damuwar rashin samun Zeenat a waya, tun safiyar jiya take gwadawa ba ta shiga, ga Baba ta ce ya ba ta lambar mijin ya ƙi ya ce daga kai yarinya ba za a fara takura musu ba, hakan ya sa ta ƙudiri aniyar zuwa gidan gobe, ta gano ta, ta kuma ba ta wasu magunguna da za ta yi amfani da su.
"Sannu Hamshaƙiya, kin kwashi jiki raɓe-raɓe ba tare da kin sanar mini ba kin je har da kwana, don iskanci sai yara za ki aiko su faɗa mini."
Suka ji muryar Baba kamar saukar aradu da ka yana faɗin haka a fusace.
Risinawa Umma ta yi ta ce. "Ka yi haƙuri Malam, wallahi lalura ce da ba a shirya mata bare tanadi, yarinyar nan ranga-ranga haka muka ɗauke ta ko sanin inda kanta yake ba ta yi ba."
"Wannan ba abin da ya shafe ni ba ne, ni dai ga abin da na faɗa miki, idan kuma kika ƙi ji ba kya ƙi gani ba."
Haƙuri Umma ta shiga ba shi, Ahayan ta gaishe shi a ladabce, bai amsa ba ya wuce ya bar su.
Inno ce ta fito daga ɗakinta cikin ƙasaita, ta dube su a wulaƙance ta ce. "Sai ki zo ki gyara mini ɗaki tunda an dawo daga gantalin da aka fake da asibiti." Ƙasa Umma ta yi da kanta ba ta ce komai ba, a hankali Ahayan ta ajiye flaks ɗin hannunta, ta fara takawa zuwa ɗakin Inno cikin rashin ƙwarin jiki, ga baccin da yake fizgar ta, don ba ta jima da shan magani ba suka taho, ciki kuma har da na bacci, duk abin Umma Lantana sai da ta ce. "Wannan rashin imani da me ya yi kama? Kina kallon yarinya tana ɗingisawa da ƙyar saboda rashin ƙarfin jiki amma ki ce ta zo ta yi miki aikin? Alhalin ko makaho ya shafa ta ya san ba ta da lafiya."
"Ban shiga sabgar ki ba, ki fita a tawa, wawiya kawai." Inno ta faɗa tana aikawa Umma Lantana harara.
Cike da dauriya Ahayan ta tsallake steps ɗin bakin ƙofar ɗakin Inno ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ta je tsakiyar parloun ta ji wani abu ya shige mata tafin ƙafa kamar allura, da sauri ta yi gefe tare da ambaton sunan Allah, sai ta ji ta ƙara takawa a ɗayar ma, wani irin zafi da raɗaɗi ne suka ziyarce ta, ya yi saurin zama a kan kujera, tafin ƙafar ta ɗaga ta fara dubawa, sai ta ga ƴankunnaye ne, zare su ta yi a hankali tare da sakin ajiyar zuciya, har gumin azama ta fara, ga tsigar jikinta da take ta tashi, jinin da ɗan fito ta saka ƙasan rigar jikinta ta goge, sannan ta miƙe ta ajiye ɗankunnen a kan TV stand. Tattara falon ta yi ta gyara shi tsaf sannan ta fice tana ɗingisa ƙafa.
Da kallon gefen ido Inno ta bi ta, ta risina ta ce. "Na gama." Da hannu ta yi mata alamar ta tafi, sannan ta tashi ta shiga ɗakin, laluben ɗankunnen ta fara yi, don ta san Ahayan ba ta ɗaukar abu sai dai ta adana shi ko ta canza masa guri, wata irin ajiyar zuciya ta saki bayan ta gan shi, ta ɗauka da sauri tana duba gurin tsinin, danshin jini ta gani kaɗan a jiki, murmushi ta saki cikin farincikin yadda abin da ta tsara ya tafi daidai, bedroom ɗinta ta nufa da shi a hannu tana ci gaba da sakin makirin murmushi.
Umma tana ƙirga kayan wankin da aka kawo da ba sa nan ta shigo ɗakin, ta nemi guri a ƙasa ta kwanta don ko katifa ba su da ita bare gado, da fara'a sosai Umma ta ce. "Women leader ce ta kawo wannan kayan, kin san ita ba iya kuɗin wanki kawai take biya ba, wani lokacin ma sai ta ninka kuɗin sau uku ta bayar, Allah ya sa ki ƙara warwarewa kafin safiya sai mu yi wankin tare, saboda suna cewa sun fi son naki akan nawa, wai kin fi ni fitar da kaya fes." Da kai Ahayan ta amsa mata, don wani iri take jin ta, ga ƙafarta duka biyu da take yi mata zugi har yanzu.
****** ******
Hantara da kyara kala-kala Hasina ta sha su a wajen Laila, amma tana ganin Uncle Aminu ya shigo ta miƙe cikin fara'a ta ɗauki ledar kayan Hasina tana faɗin. "Ya za ki ajiye kayan a nan kuma bayan ga ɗaki can na nuna miki na ce a can za ki zauna? Ga shi na yi na yi ki hau kan kujera kin dage a ƙasa za ki zauna, sai ka ce wata baƙuwa, nan ma ai gida ne ƙanwata." Fuska a sake Uncle Aminu ya ce. "Ai da ma ke ya kamata ki kai mata kayan ki yi mata jagora, sai ta fi sakewa, don na ga kamar a takure take." Laila ta zabga mata harara a fakaice ta ce. "To bari na kai ta, ina su Suhail ɗin?" Ƙofa ya juya ya kalla ya ce. "Ga su nan, wai addu'a ake tun ɗazu kuma ba a ida ba har yanzu." Ta ƙarasa inda Hasina take ta take mata ɗanyatsa da ƙafarta cikin mutunta, da sauri Hasina ta janye ƙafar tare da sosa gurin, ba don yana yi mata ƙaiƙayi ba sai don fatan jin sauƙin azabar da ta ziyarce ta.
"Ta ci abinci kuwa?"
"Ta ci, na kawo mata." Laila ta faɗa a hanzarce..
Da mamaki Hasina ta dube ta amma ba ta ce komai ba, sai a lokacin ta yi masa sannu da zuwa, ya amsa tare da faɗin. "Ki saki jikinki Hasinatuwa, nan ma gidanku ne." Murmushin yaƙe kawai ta yi, don jikinta ya fara yin sanyi, wata irin azababbiyar yunwa take ji, ga ƙamshin abinci da ta shiga kitchen ɗazu ya ƙara hautsina ta, zaman da take jira take ko a ƙasa ne a zuba mata abincin ta ci ta mayar da mugun yawo, amma shi ne Laila za ta ce masa ta ci.
Murmushin mutunta Laila ta saki a ranta tana faɗin, da ƙafarki za ta bar gidan nan indai ni ce sai kin yabawa aya zaƙinta.
Ta miƙe ta kamo hannun yaranta sannan ta bi bayan mijinta zuwa sama, ba tare da ko kallon inda Hasina take ta yi ba, suka bar ta a rakuɓe a tsakar falon kamar alamjira.
[9/7, 11:19 AM] Bahaushiya👍🏻: Da fara'a Uncle Aminu ya juya ya dube ta ya ce. "Mun ƙaraso, ki shiga ciki, ga ƙofar entrance ɗin can, ni zan sake fita na ɗauko ƙannenki, na riga na faɗa wa Auntyn naki tare nake da baƙuwa, so da kin shiga za ta gane." Yalwataccen murmushi Hasina ta yi tana jin kamar ta ce su ƙara fitar tare saboda sanyin AC da ƙamshi sassanya da yake ratsa ta, ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Tom shikenan Uncle na gode sosai, sai ka dawo Allah ya kiyaye hanya." Ya amsa da Amin cikin jin daɗin ɗabi'unta na ladabin da take yi masa, a ransa yana ayyana ba za su samu matsala da Laila ba don tana da tarbiyya, da ma ya san ƴaƴan Amma ba za su kasance saɓanin haka ba.
A hankali take tafiya tana ba wa na mujiyarta abinci, tana ganin Maigadi ya buɗe masa mota ya fita ta doka tsalle tare da juyin rawa cikin murna, a fili ta furta. "Alhamdulillah! Mafarkina ya fara tabbata, yau ni ce a irin wannan gidan? Zan yi rayuwa na kwana a cikinsa? Allah ka kawo mini wanda zai kai ni irin wannan gidan ni ma, na huta da gwaɓa maganar mutane da suke ganin kamar ba zan samu irin mijin da nake so ba." Ta yi shiru tana tuna masu cewa suna son ta da ba ta kula su, yan unguwarsu da masu zuwa siyan ƙosai gurin Amma, tsaki ta ja da ta tuna wasu ko cikakkun suturun kirki ba su da shi. Sai da ta saisaita nutsuwarta sannan ta nufi part ɗin da ya nuna mata, wanda shi ne babba a cikin Apartments uku da ta gani a gidan, cike da zumuɗi ta fara knocking.
Farha na zaune a kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin ƙasaita tana latsa waya, Laila kuma tana ta zaryar kawo mata abubuwan motsa baki.
"Wai ba yanzu muka gama ciye-ciye ba shi ne za ki zo kina jibge mini wannan tulin kayan?"
Murmushi Laila ta yi ta ce. "To ai wancan daban wannan kuma na gidana ne." Taɓe baki Farha ta yi wanda ya zame mata jiki ta ce. "I'm full, I can't eat anything else, ki zauna kawai mu yi abin da ya kawo mu, ko ba ki san dauriya kawai nake yi ba? Wuni guda ba na tare da mijina, kuma tun ɗazu ya sanar mini ya koma gida." Ƙaramar dariya Laila ta yi ta ce. "Wannan miji naki yana shan gata da kulawa da tattali, na rasa irin wannan ƙauna, ga shi ku ba sabon aure ba bare a ce, Allah ya dai ya kawo mana yara masu albarka ƴaƴan soyayya."
"Ba za ki gane ba ne." Farha ta faɗa tana bin gidan da kallo sannan ta ce. "Kina da Housemaid me?" Kai Laila ta girgiza tare da faɗin. "Ba zan iya bari mijina ya dinga ganin gilmawar wata mace bayan ni a gidansa ba, shi ya sa nake daurewa na yi ayyukana da kaina." Jinjina kai Farha ta yi, daidai nan suka ji bugun ƙofar Hasina. Da mamaki Laila ta tambayi waye bayan ta tashi ta ƙarasa bakin ƙofar, Hasina ta ce. "Ni ce."
"Ke ce wa?"
"Niece ɗin Uncle Aminu." Ta faɗa cikin azarɓaɓi.
"Niece?" Laila ta maimaita tare da buɗe ƙofar.
Da rawar jiki Hasina ta janyo ledarta za ta shiga tana murmusawa, kallon sama da ƙasa Laila ta yi mata a wulaƙance, tana yatsina fuska kamar ta ga kashi ta ce. "Baiwar Allah daga ina? Ban gane ki ba."
"Uncle Aminu ne ya sauke ni, ya ce ya sanar miki ma tare muke."
"Ok." Kawai Laila ta ce ta ba ta hanya ta wuce cikin danne ɓacin ranta, wannan kucakar ce ta shigo mota tare da mijinta har suka shaƙi numfashi ɗaya?
Hasina za ta zauna a kan kujera ta yi saurin katse ta a tsawace. "A'a'a'a! Kar ki zauna mini a nan, ga hanyar kitchen can, ki shiga za ki ga towel ki goge ƙafarki sai ki zo ki zauna a kan carpet." Cikin ladabi Hasina ta ce. "To Aunty." Tare da rakuɓa jakar hannunta a jikin kujera.
"Tafi da ita ki ajiye a can bangon." Ta faɗa a ƙyamace tana nuna mata kusa da ƙofa.
Farha dai bin su kawai take da ido, Hasina kam ko a jikinta abubuwan da Laila ta yi mata, ita dai indai za ta bar ta ta yi rayuwa a cikin gidan ai ta gama yi mata komai, saboda ko ita ce aka ce nan gidanta ne za ta iya yin fiye da hakan ma.
Tsabar ɓacin rai har huci Laila take yi, wani murmushi Farha ta saki tare da faɗin. "Mu je daga ciki tunda kin yi baƙuwa." A ƙule Laila ta ce. "Ya dai yi, ni me zai haɗa ni da wancan abar kamar mai wanka da kalwa? Ba ki ji har ƙamshin falon ya sauya ba." Murmushi kawai Farha ta kuma yi ta miƙe, Laila ta yi gaba zuwa bedroom ɗinta tana ci gaba da mita.
Ba su daɗe da shiga ba suka fito jikin Laila duk a sanyaye da jin bayanan Farha, don abu ne da ba ta taɓa tsammani ba wanda ya matuƙar ɗaure mata kai ya kuma caza mata ƙwaƙwalwa.
Hasinah na zaune a inda aka umarce ta, ta saki baki da hanci ta tasa TV a gaba da kallo kamar wata shashasha.
"Ke!" Laila ta kira ta cikin Faɗa.
Cikin kwantar da murya Hasina ta ce. "Na'am Aunty."
"A gidan Uwar wa na zama auntyn taki? Wai ke ƴar wane ne ɗinsa ma tukunna? Ban fa gane ki ba, ban ma taɓa ganin ki ba."
Labarin zuwan Uncle Aminu da yadda aka yi ta biyo shi ta ba ta in brief.
Kallon juna suka yi ita da Farha sannan ta ce. "Saboda jaraba daga ganin shi sai ki kama ki biyo shi? Ku wai matsiyatan nan me ya sa ba kwa iya riƙe zalama da kwaɗayinku ne?" Ta ƙarashe maganar tare da jan tsaki.
Murmushi Farha da ta ƙure Hasina da ido ƙur ta saki ta ce. "Haba Ƙawata, menene a ciki don ta yi zumunci? Ni har ta burge ni ma, ina son mutum mai son nasa." Washe baki Hasina ta yi amma ba ta ce komai.
"Saka mini numbernki a nan, ni na samu ƙanwa ai, yanayinki ya nuna ke mai tarbiyya ce, ni kuma ina son yara masu hankali."
Mamaki ne ya kusa hallaka su, ita Hasina har da farincikin wannan zuƙeƙiyar matar da tun ɗazu take satar kallon ta saboda kyan fatarta da gayun da ta sha ita ce take cewa ta burge ta? Har ta buƙaci numbernta? Lallai yau ta tashi da sa'a ta shigo wannan gida da ƙafar dama, irin mutanen da ta daɗe tana fatan mu'amala ta haɗa ta da su, ashe dai lokacin zai zo, kamar ta taka rawa haka take ji tsabar murna, da rawar jiki ta karɓi tsaleliyar wayar Farha da take ta tashin ƙamshi ta saka numbernta ta mayar mata.
Laila kuma sanin halin ƙawar tata na ƙyamar talaka da raina mutane ne ya sa mamaki ya cika ta, har Farha ta karɓi wayarta ta kira Hasina ta ga tata lambar ba ta farfaɗo daga sandarewar da ta yi ba, girgiza kai ta yi a ranta ta ce. 'Ruwa ba ya tsami banza, dole akwai dalilin da ya saka ta yi haka.
***** ****** ******
Sai wajen uku na dare Ahayan ta farka, lokacin su Ummi sun dawo sun ƙara komawa gida saboda ba za a bari su kwana dukkansu ba, sai Umma kaɗai ta gani tana gyangyaɗi a ƙasa, kanta ya yi mata wasai, amma fayau take jin ta babu ƙwari kwata-kwata a jikinta, ga cikinta kamar an yi mata yasa har hanji saboda yunwa.
Kulawar da Umma ta dinga ba ta ba ƙaramin ɗaure mata kai ta yi ba, tana ta yi mata sannu tare da yi mata duk abin da ya dace. Ta haɗa mata tea ta sha sannan doctor ya zo ya ƙara duba ta, bayan ta sha magunguna ta ƙara komawa bacci.
Washegari tunda safe su Ummi suka zo da abincin kari, bayan sun gaisa sun yi mata ya jiki Raudah ta dubi Umma ta ce. "Baba yana ta faɗa, wai sai kin dawo, da ƙyar Yaya Saif ya taushe shi bayan ya ba shi toshiyar bakin biredi da ƙwai da safen nan, Inno kuma tana zuga shi, da Yaya Saif yana ba shi haƙuri ma zagin shi ta yi ta yi." Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Umma ta sauke ta ce. "Ki ce da na shiga tara yau ba da ban Saif ba?" Yadda ta yi maganar a gigice ya saka Ummi faɗin. "Wallahi wannan tsoron na Baba da kike yi shi ya sa yake ƙara raina ki, Umma Lantana da ba ta yi masa haka ai ya fi shakkar ta a kanki, ko a jiyan ma fa sai da muka koma ta dawo, amma faɗa kaɗan ya yi mata ya ƙyale ta." Numfashi Umma ta sauke ta ce. "Yaro man kaza, a yi sha'ani kawai don ba gane abin da nake gudu za ku yi ba." Ahayan dai tana kwance idonta a lumshe tana sauraren su, ji take da ma ta dawwama a asibitin akan ta koma gida saboda matsin da take fuskanta da rayuwar ƙuncin da take. Su Ummi ba su jima ba suka tafi saboda zuwa makaranta, a nan suka bar Sabira suka ce idan suka dawo sai su koma da ita, kuɗin da Kamal ya ba su a jiya da shi suka yi amfani wajen yin breakfast ɗin da suka kawo su ma suka ci.
Wajen shaɗaya Saif ya zo. Bayan sun gaisa da Umma ta fita wanko kayan da Ahayan ta cire ta bar su shi da Sabira.
A hankali ya ja kujerar da ke gaban gadon ya matsa kusa da ita ya fuskance ta, cikin tausasa murya ya ce. "Ahlove!" Kanta ta ɗaga a hankali ta kalle shi.
"Ya jikin naki?"
"Da sauƙi Alhamdulillah, sun ce ma zuwa anjima za su iya sallamar mu."
"Ma sha Allah, Allah ya ƙara sauƙi ya ba ki lafiya, duk na damu sosai, ga Inno ta kafa ta tsare da ƙyar na samu na sato hanya na zo." Ya ƙarashe maganar yana miƙa mata ayabar da ya ɓare mata a cikin kayan fruit ɗin da ya zo da shi. Murmushi ta yi ta karɓa ta ce. "Na gode sosai Yaya Saif Allah ya saka da alkhairi ya biya ka da aljanna."
"Amin ya rabb, amma ki daina yi mini godiya, don dole ne miji ya kula da matarsa, kuma ko ma ba wannan yayata ce ta yi sanadin w...."
"A'a Yaya Saif, don Allah kar ka ce haka, Allah ne ya ƙaddaro mini, kuma a nan ma Ulcer suka ce tana damu na sai kuma stress, ka ga ba shi da alaƙa da Aunty Laure kamar yadda kake zato."
"Ba zato ba ne Ahayan abin da aka tabbatar ne, ni na san tunda har Abba Adam ya saka baki a cikin lamarin nan ba ƙaramin abu ba ne."
Da mamaki Ahayan ta ce. "Ya saka baki kuma? Ban gane ba, na san dai Umma ta ce shi ya kawo mu asibiti ya biya kuɗin komai." Saif ya ce. "To har kiran Aunty Laure ya yi ya ja mata tsatstsauran gargaɗi akan kar ta sake taɓa ki, ko ɗazu da safe sun yi waya da Inno tana ta nanata maganar alamun ba ƙaramin dukan ta ta yi ba." Numfashi Ahayan ta sauke ta jingina kanta da jikin gado cikin al'ajabin maganar da aka ce Abba Adam ya yi wa Ramlah, abu ne da zaton kowa ba zai taɓa hasasowa ba, ba ta taɓa tunanin tana da wannan darajar da wani zai damu don an doke ta ko an ci zarafin ta ba, hawaye ne masu zafi suka zubo mata ba tare da shirya musu ba.
"Kukan na mene kuma Ahlove?"
Numfashi ta ja da ƙarfi ta ce. "Har za a tambaye ni kukan me nake yi a wannan karkatacciyar rayuwar tawa da ni kaina ban san ina zan tsinci kaina a gobena ba? Wallahi Yaya Saif tunda na farka nake kallon mutane suna hada-hadarsu cikin nishaɗi da farinciki, su babu abin da yake damun su a rayuwa, ni kuma ni kaɗai na san me nake ji a cikin raina, ni kaɗai na san irin raɗaɗin zucin da nake kwana nake tashi da shi a kullum."
Cikin matsanancin tausayin ta ya ce. "In sha Allah za ki yi farinciki za ki zama abar alfaharin da ba a taɓa tunani ba, komai zai wuce ya zama labari, ka da ki manta a bayan kowanne duhun dare hasken rana ne."
Girgiza kai kawai ta yi tare da gimtse baki ba ta ce komai ba, ta san babu mai gane abin da take ji bare ya fuskanta, babu mai gane irin hasashen da take yi da abubuwan da suke tattare da ita, rayuwa kawai take don rai da numfashi suna yawo a jikinta, amma da za a ba ta zaɓi ko jinkiri ba za ta yi ba za ta zaɓi mutuwarta.
"Na daɗe da son sanin asalinki da tahirinki amma a duk lokacin da na tambaye ki sai dai ki saka kuka kawai ba za ki ce mini komai ba, kamar yadda na faɗa miki ina tantanma akan Umma ce ta haife ki tun lokacin da aka kawo ki gidanmu, saboda a kodayaushe ina tambayar kaina me ya sa take treating ɗin su Ummi yadda ya dace amma ke saɓanin hakan ne? Me ya sa kike kasancewa cikin tunani a lokuta da dama? Me ya sa kodayaushe kike cikin yanayin rauni da damuwa? Me ya sa komai aka yi miki kike shanyewa? Me ya sa kika zamar da rayuwarki kamar raƙumi da alakar da wasu suke ja, ba ki da wani ra'ayi ko yin wani abu naki sai abin da aka saka ki ko aka ba ki umarni? Wannan ya sa nake zargin akwai lauje cikin naɗi, akwai wani abu a cikin rayuwarki da ba mu sani ba, ina son sani don Allah Ahayan!"
Murmushi ta yi mai ciwo ta ce. "Zan faɗa maka Yaya Saif, za ka san komai game da ni in sha Allah."
Dawowar Umma ce ta katse musu hirar da suke yi, sallama ya yi musu ya tafi bayan ya ajiye wa Umma kuɗi don ya san suna cikin buƙatar shi.
A ranar aka sallame su, jikin nata ya yi kyau sosai don ta samu kulawar da ta dace, sosai suka jaddada wa Umma kula da shan magungunanta akan kari, da kuma barin ta tana hutawa tana samun bacci ishashshe gami da cin abinci akan kari.
Da Umma Lantana suka fara cin karo a tsakar gida, ta baje shirgin kayan tuwon dare, ga murhu ta hura har biyu. Kallo ɗaya ta yi musu ta ɗauke kai, don kamar yadda ƙawayenta suka ba ta shawara yanzu ba da ba ne, ta zama surukar mai kuɗi Umma ba ajinta ba ce ta daina kula ta, jiya da yau wunin wani ƙauye suka yi ita da ƙawayen nata, ta je gurin wani malami an kafe mata auren Zeenat tare da riƙe musu mijin gam a hannu yadda za su juya shi son ransu, shi ya sa ma duk a gajiye take, gefe guda kuma ga damuwar rashin samun Zeenat a waya, tun safiyar jiya take gwadawa ba ta shiga, ga shi ta ce wa Baba ya ba ta lambar mijin ya ƙi ya ce daga kai yarinya ba za a fara takura musu ba, hakan ya sa ta ƙudiri aniyar zuwa gidan gobe, ta gano ta, ta kuma ba ta wasu magunguna da za ta yi amfani da su.
"Sannu Hamshaƙiya, kin kwashi jiki raɓe-raɓe ba tare da kin sanar mini ba kin tafi yawon barbaɗa har da kwana, don iskanci sai yara za ki aiko su faɗa mini, to kin yi na farko kin yi na ƙarshe, wallahi idan irin haka ta kuma faruwa sai na ɗauki mummunan mataki a kanki."
Suka ji muryar Baba kamar saukar aradu da ka yana faɗin haka cikin ɗaga murya.
Risinawa Umma ta yi ta ce. "Ka yi haƙuri Malam, wallahi lalura ce da ba a shirya mata bare tanadi, yarinyar nan ranga-ranga haka muka ɗauke ta ko sanin inda kanta yake ba ta yi ba."
"Wannan ba abin da ya shafe ni ba ne, ni dai ga abin da na faɗa miki, idan kuma kika ƙi ji ba kya ƙi gani ba."
Haƙuri Umma ta shiga ba shi, Ahayan ta gaishe shi a ladabce, bai bi ta kansu ba ya wuce ya bar su.
Inno ce ta fito daga ɗakinta cikin ƙasaita, ta dube su a wulaƙance ta ce. "Sai ki zo ki gyara mini ɗaki tunda an dawo daga gantalin da aka fake da asibiti." Ƙasa Umma ta yi da kanta ba ta ce komai ba, a hankali Ahayan ta ajiye flaks ɗin hannunta, ta fara takawa zuwa ɗakin Inno cikin rashin ƙwarin jiki, ga baccin da yake fizgar ta, don ba ta jima da shan magani ba suka taho, ciki kuma har da na bacci, duk abun Umma Lantana sai da ta ce. "Wannan rashin imani da me ya yi kama? Kina kallon yarinya tana ɗingisawa da ƙyar saboda rashin ƙarfin jiki amma ki ce ta zo ta yi miki aiki? Alhalin ko makaho ya shafa ta ya san ba ta da lafiya."
"Ban shiga sabgar ki ba, ki fita a tawa, wawiya kawai." Inno ta faɗa tana aikawa Umma Lantana harara.
Cike da dauriya Ahayan ta tsallake steps ɗin bakin ƙofar ɗakin Inno ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ta je tsakiyar parloun ta ji wani abu ya shige mata tafin ƙafa kamar allura, da sauri ta yi gefe tare da ambaton sunan Allah, sai ta ji ta ƙara takawa a ɗayar ƙafar, wani irin zafi da raɗaɗi ne suka ziyarce ta, ya yi saurin zama a kan kujera, tafin ƙafar ta ɗaga ta fara dubawa, sai ta ga ƴankunnaye ne, zare su ta yi a hankali tare da sakin ajiyar zuciya, har gumin azaba ta fara haɗawa, ga tsigar jikinta da take ta tashi, jinin da ya ɗan fito ta saka ƙasan rigar jikinta ta goge, sannan ta miƙe ta ajiye ɗankunnen a kan TV stand. Tattara falon ta yi ta gyara shi tsaf sannan ta fice tana ɗingisa ƙafa.
Da kallon gefen ido Inno ta bi ta, ta risina da ƙyar ta ce. "Na gama." Da hannu ta yi mata alamar ta tafi, sannan ta tashi ta shiga ɗakin, laluben ɗankunnen ta fara yi, don ta san Ahayan ba ta ɗaukar abu sai dai ta adana shi ko ta canza masa guri, wata irin ajiyar zuciya ta saki bayan ta gan shi, ta ɗauka da sauri tana duba gurin tsinin, danshin jini ta gani kaɗan a jiki, murmushi ta saki cikin farincikin yadda abin da ta tsara ya tafi daidai, bedroom ɗinta ta nufa da shi a hannu tana ci gaba da sakin makirin murmushi.
Umma tana ƙirga kayan wankin da aka kawo da ba sa nan ta shigo ɗakin, ta nemi guri a ƙasa ta kwanta don ko katifa ba su da ita bare gado, da fara'a sosai Umma ta dube ta, ta ce. "Women leader ce ta kawo wannan kayan, kin san ita ba iya kuɗin wanki kawai take biya ba, wani lokacin ma sai ta ninka kuɗin sau uku take bayarwa, Allah ya sa ki ƙara warwarewa kafin safiya sai mu yi wankin tare, saboda suna cewa sun fi son naki akan nawa, wai kin fi ni fitar da kaya fes." Da kai Ahayan ta amsa mata, don wani iri take jin ta, ga ƙafafuwanta da suke yi mata zugi har yanzu.
****** ******
Hantara da kyara kala-kala Hasina ta sha su a wajen Laila, amma tana ganin Uncle Aminu ya shigo ta miƙe cikin fara'a ta ɗauki ledar kayan Hasina tana faɗin. "Ya za ki ajiye kayan a nan kuma bayan ga ɗaki can na nuna miki na ce a can za ki zauna? Ga shi na yi na yi ki hau kan kujera kin dage ke a ƙasa za ki zauna, sai ka ce wata baƙuwa, nan ma ai gida ne ƙanwata." Fuska a sake Uncle Aminu ya ce. "Ai da ma ke ya kamata ki kai mata kayan ki yi mata jagora, sai ta fi sakewa, don na ga kamar a takure take." Laila ta zabga mata harara a fakaice ta ce. "To bari na kai ta, ina su Suhail ɗin?" Ƙofa ya juya ya kalla ya ce. "Ga su nan, wai addu'a ake tun ɗazu kuma ba a ida ba har yanzu." Ta ƙarasa inda Hasina take zauna ta take mata ɗanyatsa da ƙafarta cikin mugunta, da sauri Hasina ta janye ƙafar tare da sosa gurin, ba don yana yi mata ƙaiƙayi ba sai don fatan jin sauƙin azabar da ta ziyarce ta.
"Ta ci abinci kuwa?"
"Ta ci, na kawo mata." Laila ta faɗa a hanzarce..
Da mamaki Hasina ta dube ta amma ba ta ce komai ba, sai a lokacin ta yi masa sannu da zuwa, ya amsa tare da faɗin. "Ki saki jikinki Hasinatuwa, nan ma gidanku ne fa." Murmushin yaƙe kawai ta yi, don jikinta ya fara yin sanyi, wata irin azababbiyar yunwa take ji, ga ƙamshin abinci da ta shiga kitchen ɗazu ta ji ya ƙara hautsina ta, zaman da take jira take ko a ƙasa ne a zuba mata abincin ta ci ta mayar da mugun yawu, amma shi ne Laila za ta ce masa ta ci.
Murmushin mugunta Laila ta saki a ranta tana faɗin, da ƙafarki za ki bar gidan nan indai ni ce sai kin yabawa aya zaƙinta.
Ta miƙe ta kamo hannun yaranta sannan ta bi bayan mijinta zuwa sama, ba tare da ko kallon inda Hasina take ta sake yi ba, suka bar ta a rakuɓe a tsakar falon kamar alamjira.
*#Zeey Kumurya*
*#****