Chapter 35&36
by @deeyamerh10
đź’–đź’– SOYAYYAR ZUCI đź’–đź’–
(Love and Romantic story)
Written
By
Deeyamerh
07070647236
Page 35&36
DUBAI🔥🔥🔥
Kwanaki da dama da Sha’ayan ya yi a Dubai sun fara zama masa kamar shekaru. Duk da yawan shagaltuwa da yake yi, da manyan wuraren da yake ziyarta, da kuma duk irin nishaɗin da Dubai ke bayarwa, zuciyarsa sam ba ta cikin garin.
Suhaima ce kawai take cikin zuciyarsa.
Yana zaune a balcony ɗin ɗakin hotel ɗinsa, sanye da farar riga da wando baƙi, hannunsa riƙe da wayarsa. Ya buɗe hoton Suhaima da ya fi so,Ya dade yana kallon hoton Sai ya yi murmushi yake saki kamar tana gabansa Ya ɗaga kansa yana kallon fitulun Dubai.
“Na yi tunanin zan iya mantawa da ke idan na yi nisa... amma kullum sai na ƙara kewarki.”
Duk lokacin da ya dauki wayarsa, hotonta ne yake fara zuwa masa a rai. Idan ya ga wani abu mai kyau, sai ya yi tunanin yadda Suhaima za ta yi farin ciki da shi. Idan dare ya yi, kewarta sai ta ƙara tsanta.
Duk yadda ya kau da tunanin Suhaima abin yaci tura domin Ji yake kamar ana hura masa wutar sonta a kirjinsa,kai abun har yakai ya kawo tana masa zigo tana kuka akan yadawo gareta,mai makon ya samu sauki to abin kawaruwa yake,bashi da wani aiki sai tunaninta har wani rama yayi sai karan hancin yasake fituwa,sosai ya azabtu da rashinta,kwana 3 yayi a daddafe zunbur ya mike kamar wanda aka tsikara ya fara shin barin Dubai.
_______
Karfe 9:00 na dare, jirgin Sha’ayan ya tashi daga Dubai.
Yana zaune kusa da taga, amma tunaninsa ba ya kan jirgin,Yana tunanin idan ya sake ganinta, ko za ta yi murmush,Ko za ta yi fushi.
Ko kuma za ta yi kamar ba ta damu da dawowarsa ba.
Ya buÉ—e wayarsa yayi da zummar ya rubuta mata message sai ya tuna ai wayar tana cikin motarsa,mai da wayar aljihu yayi yasata airplane,Dan ma Allah yasa hajjiya tasan zai bar garin da yasha kira,tunawa da Ammey da yayi sai ya goge duk wani bacin rai da suhaima tai masa domin bai san wacce ba amma Allah ya dora masa sonta.
__________
JUMETA
Tunda Ammey tazo gidan take samun kulawa,sosai hajjiya da yan matan suka dage gun maganin karya asiri,tun tana doke-doke har Allah yasa ta dai na,sosai suke ganin cigaba dan yanzu tana iya magana Amma tunaninta bai dawowa ba.
Duk da tunanin ta bai dawo ba Amma haka kawai take ji kamar tana da yara har da budurwa kamar su Nihal Amma kanta yakasa tunawa idan tace zatai tunani me zurfi sai kanta ya hau ciwo sai kawai tabari,sosai take sallah da addu'ar amma tabbas tasan tayi wata rayuwa kafin wannan.
Duk abinda tace tana so shi hajjiya take mata haka masu Nihal domin idan kaga yadda suke ji da ita har mamakin zakayi a jinin jikinsu suke mata SOYAYYAR ZUCi.
___________
Bayan doguwar tafiya da yayi, jirgin sa ya sauka a Najeriya da misalin 2:00 na rana.
Yana fitowa ya shaki iskar Nigeria sai wani lumshi ido haka kawai yaji wani sanyi yana ratsa masa zuciya domin jin zuciyar ta rage gudun da take Alamu yana nuni da ko Mahadarsa tana cikin Airport ko kuma yana jin feeling din ya dawo kusa da abarsa.
Cikin karfi na kyakkyan Namiji yafito daga jirgin cikin annashuwa ya furta "Alhamdulillahya" ajiyar zuciya ya sauke.
Waya ya daga domin kiran driver domin jin ina ta ina dan ya tura masa da sako ta,bai dade da da sauka ba sai ga driver cikin sabuwar mota kirar Mercedes-Maybach S-Class —Black sai daukar ido take,bai tsaya ko ina ba sai gabansa kokarin shiga cikin motar yake kamar ance masa dago,daguwar da zai yi sai kuwa idanunsa ya sauka a kanta ita da Fatima suna yiwa Amarya bye bye domin ba a kasar zata zauna ba zabi mijinta inda Yake Aiki.
Kallonta yake kamar zai cinyeta,domin gani yayi ta ka rama kyau kamar ya dauke abarsa.
Basu kula da shi ba domin sai zance suke akan komawarsu makaranta Domin hutun da aka bata ya kare. Tafiya take jatai ta tsaya cak domin jin bugun zuciya ta ya karo domin Akan mutum Daya take jin wanna bugun ko da kuwa tunaninsa tayi SH Idanu ta fara rabawa cikin filin ko da zata ga abinda take son gani,idanun ta sosai take juyawa kamar tana neman wani da zuciyarta ta dade tana jira.
Sai kawai ta hangi wata bakar mota mai kyau ta tsaya a gefe,tana tsayar da iduwanta sai cikin na Sha’ayan da yake tsaye yana kare mata kallo,Sanye yake cikin wata farar shirt da bakar wando, agogon hannunsa yana kyalli, yayin da fuskarsa ta nuna irin nutsuwar da tagame masa jiki, Amma a wannan karon, idanunsa sun bayyana abin da bakinsa ya kasa fada.
Idanu kawai ta kafe shi da shi,wato shi kasar ya bari kenan tana neman yadda za'ai ta dame shi su War ware wanna Auran Amma shine ya gudu ko?
Shi ma tsaya wa yayi na kallonta,Na wasu dakiku babu wanda ya ce komai,Kawai idanuwan sune suka kasa rabuwa da na juna.
Juyawar da Fatima zatayi itama tai arba da inda suhaima ta kafe da ido, murmushi tayi irin an gamu kenan kafin itama ta ja ta tsaya taga yadda za'ayi.
murmushi ya saki a hankali irin me kashe zuciyar duk wata budurwa,takowa ya fara a hankali wanda hakan ya jefa Suhaima suman takin lokaci,inda take ya nufa kai tsaye domin idan bai ji dumin jikinta a kan kirjinsa ba to tabbas da matsala.
Sai da yazo gab da ita kamar zai shige cikin jikinta cikin Romantic word yace "WIfe"Kawai ya furta ya cigaba da laluben idanuwanta wanda kara suwar sa yasa ta sauke nata kasa,domin bazata iya kallon blues eye dinsa ba, yadda ya furta Wife ya sa zuciyarta ta buga da sauri.
Hannu yasa ya dawo da habarta Domin bai gaji da kallon zara zarar eyelash din ta ba,cikin Slong yace“Na dawo ne saboda na gaji da kewarki.”
Kara sunkuyar da kanta tayi, tana kokarin boye murmushin da ya bayyana a fuskarta,kokarin kara dago da fuskarta take Amma cikin sauri Fatima tace"Bross a hanya muke kyanta mushiga daga cikin mota idan yaso sai ku cinye juna"Fatima ta kalli Suhaima, sannan ta yi murmushi tana kau da kai.
Hannunta ya kama a hankali kafin ya juya da ita,motar suka nufa kai tsaye,da sauri Driver ya fito domin bude mata motar Amma SH ya dakatar da shi domin wanna aikin na sane,bude mata kofar mota yayi sannan yace "Shiga.”
Cikin kalar da ya saukar mata ta shiga, shi kuma ya zagaya ya shiga bangaren dayan,Fatima kuma ta shiga gaba.
Motar driver yaja suka hau kan kwalta.shiru ne lullube motar,domin ba wanda yace kala bare kwankwaran motsi, shiru ne mai cike da abubuwa da yawa.
SH ya dade yana kallonta ta gefen ido,domin Allah Allah yake su bashi guri domin nuna mata yayi kewarta matuka gaya.
Duk abinda yake Suhaima ta lura da shi Amma ba tace maka komai ba domin batasan ta inda zata fara masa bayani ba,dan har ga Allah kwarjini nake mata.
Bini bini ta saki murmushi cikin sauƙin da ya debesa yace mata“gani ga abinda ba dade ina kewarsa Please Wife mutafi gidan mu wllh taran bikin na gode ba sai anyi ba".
Da sauri taa kalle shi tace"muje wuce ina?Haba sai kace wanda basu da mafada kawai daga haduwa sai na bikin zungu zungu kamar wata mara kamun kai.
Ni bani da kamaunkai din shiyasa nace kawai kazo mutafi duk wani fada da Abba zaiyi to akai na zayi tunda Ni nace kuma ai umarnin mijinki zaki bi kinji Wife mika hannunsa ya kama nata a hankali.Yatsunsa suka hade da nata, sannan ya dan matse hannunta kamar yana tabbatar mata cewa ba zai sake barinta cikin sauki ba.
“Kin san me ya fi bani wahala?” ya tambaya.
“Me?”
“Ranar da ba na ganinki.”
Ta kalle shi cikin kunya.
“Hmm?” kawai tace dan Allah ka daina kaga da mutane cikin motar fa,kamar zatayi kuka.
“Me zan daina?”ya tambaya yana sake juyowa gareta baki daya.
Wannan maganar ta na bika mana.
Murmushi yayi me kayatarwa“Ba zan daina ba Na dade ina boye kewarki.”Ya daga hannunta kadan, ya kalle shi har yanzu lalla bikin yanan kafin ya sake kallonta.
“Wife, kin san duk inda na je, akwai wani bangare na zuciyata da yake nan… tare da ke.”ya dura hannunta a kirjinshi
kasa magana tayi domin wllh wani iri take ji a cikin jiki da zuci
ci gaba da kallonta yake cikin kasa da murya yace "Na kewar ki sosai har da wanna bakin me fada mun zai rungume wani".
Wannan karon Suhaima ta kasa boye murmushinta duk dauriyar da take kada tanuna masa kalamansa suna shigarta.matsa hannunta yayi kadan yadda bazataji zafi ba“Ki yi min magana mana.Ko murmushinki kawai zan dauka a matsayin amsar.”
ta yi dariya a hankali “Na ji.”
“Me kika ji?”ya jefo mata tambaya cikin sauri
“Kalaman kama, ko ba su ke so naji a cikin kalaman naka naji wanda sukayi wanna agun SECRET LOVER wanda daya yayi mun sai naji bana cikin duniyar mutane.”
Dariyar da bai shirya yi bace ta kwace masa domin wllahi lamarin Wife tana bashi dariya to Indai wanda yake mata wanna kalamane to gashi a kusa da ita to ya zatayi kenan?
Shagala tai da kallonsa domin ba karamin kyau dariyar ta masa ba.
Hura mata iskar bakinsa yayi wacce kamashin mango ya daki hancinta dan sai da ta lumshi ido,domin duk maganar da yake ba sweet a bakinsa to ya haka kenan?
“Ina son ki,dan Allah ki daina guduwa daga cikin idanuna, Duk lokacin da na kalle ki, sai na ji kamar na samu abin da na dade ina nema, idan kuwa ba haka ba zaki kashe dan Hajiya tun bata ga jikokinta ba.
Sosai taji zuciyarta ta motsa jin yana tare da mahaifiyars Ita kuwa har yanzu bulayin nemanta ake.
Kanta ta sunkuyar duk da har yanzu hannayensu a hade suke,Kuma a wannan lokacin, babu wanda ya damu da inda motar take tafiya.
Domin Sha’ayan ya riga ya samu abin da ya fi so—Suhaima a gefensa, hannunta a cikin nasa, bayan doguwar kewar da ta kusan karya masa zuciya.