Chapter 12
by @maidambu41
Dakinsu ta wuce kai tsaye, ta zauna sallah take son yi amma hayaniyar da yake kusanto bangaren yasa ta kara shigewa cikin gadonta. Tare da haɗe kai da gwiwa, tana jin Hajiya Atikah tana zagin Maamah. Can muryan Uban kowa ya ratsa cikin gidan. Haka yasa suka watse basu shirya ba. Shima bata ji muryanshi ba.
Sai da Yan uwanta suka shigo ta mike zuwa banɗaki, tana fitowa kamar munafuka sallah tayi tana idarwa Mairoh ta ce mata. "Me yasa ba zaki tsaya ki kwaci kanki ba? Kina nufin haka zaki rayu kina guje-guje a tsakaninsu? Didih." Komawa gadon tayi ta kwanta bata fito ba. Muryan Maamah da ta ji a kanta yasa ta bude idanu. "Bani sarkan da Mustapha ya saya miki?" Tashi tayi ta cire bakiɗaya ta mika mata. Ita kuma Maamah ta fita zuwa bangaren Hajiya. Bayan ta shiga ta samu yadda kannen Mijinta suke wani huci ta ajiye sarkan ta ce mata. "Gashi nan ku yi hakuri, idan na san zai bata wani abu zan hana in sha Allah ba zai kara kashe mata kudi ba, har na makarantar ma duk Allah zai bada abinda za a yi." Tana fadin haka ta juya zata fita ta hango Uban kowa bakin kofar parlourn. Takawa yayi ya dauki sarkan ya ce musu. "Akwai shegen da ya bashi kudi ya saya ne? Ko akwai wacce take iya ɗaukar wani abu ta bashi? Yayi niyya saya mata wai ku me yasa idan baki hada fada baku jin daɗi ne? Maamah kai mata abinta. Duk abinda Ni Adam ko Mustapha, Fuad, Amin zamu yiwa Asma'u mun yi ne don muna da raayin haka, na kara jin wata yar iskar yarinya tayi wani motsi sai na ɗaye fatar jikinta da wuka na bawa Ranbow ya cinye danye don Ubanta." Ya nufi gaban Hajiya ya zauna ya ɓalla mata harara yana faɗin. "A cikinsu wacece take miki hidimar da Maamah take miki? Ba na gaya miki ki daina biye musu ba? Hajiya kina son mu shirya kuwa? Ni da ke nace ki fita harkan kowa, wannan watan nayi niyyar biya miki amma wallahi na fasa tunda ba zaki daina shiga harkokin Asma da Maamah ba, zaki sani ai waye yake miki wanki da guga a cikin su ? Ke da kanki kike fadar tunda ta tafi makaranta hatta kitson kanki waye yake miki idan ba ita ba. Hajiya yaushe zaki daina biye musu? Hajiya ina rokonki ko bakya son Naanah Asma'u da Mahaifiyarta ki ji a ranta wata rana idan bana raye ko so ta ko da na kwana daya ne zaki fahimci girma da soyayya da kake yiwa wanda baka taɓa so ba.. "
" Haba Uban kowa ya zaka kira mutuwa a wannan maganar ko yau kace na sota zan so ta ba sai ka kira mutuwa ba!" Naɗe hannunsa yayi a kirji ya ce mata. " To kori Yaranki kowacce ta koma gidanta kada a sake wani taro a gidan nan, domin Naanah Asma'u tafi su iko da gidan sama da su da Yaransu ko koma gidansu." Ya fada yana turmune fuska. " Kowacce ta koma gidanta, bana son ganinku idan ba alkhairi ba ne ya kawo ku!" "Amma Adam kasan!" " Hajiya kin ji su ko?" "Kaniyarki Atikah marayan zaki takurawa?" Yadda ya gama nunawa Hajiya kauna a duniya bata jin akwai wani jika mafi soyuwa a ranta. Shi bai shiga rigimar don Naanah Asma'u ba, alkhairin Maamah yake tunawa Yana yaro ba zai iya fadar girman kyautatawarta a gare ta ba. Shi yasa yake jin zafi idan aka mata wani abu.
Suka tafi da haushin Maamah, da Ya Almu yazo bayan an gama komai. Fushi Hajiya take da shi tare da nuna mishi cewa. "An rigada an zaba maka macen da zaka aura me yasa kuma kake kula Naanah Asma'u, bayan kasan itama ba mamaki uwarta ta tsayar da wancan munafukin Yaron!" Kallon cikin idanunta yayi ya matsa gabanta ya zauna da kyau cikin bude ido ya ce mata. "Idan kika sake kika yi wani yunƙurin hana ni aure, wallahi kin ji na rantse miki da Allah zaku nimeta ku rasa zan tafi da ita na aureta. Sai ta haifa min Yara kyawawa irinta zan dawo da ita. Wannan shine kashedina da ke. Idan haka bai samu guba zan baki ki mutu kowa ya huta. Kin ga sai na auri Naanah Asma'u bayan ranki.
Yana mikawa zai juyawa Uban kowa ya kai mishi naushi da sai da ya fadi akan Center table, shima yana mikewa ya rama suka fara dambe kamar Yara, Hajiya kasa raba su tayi ta fito da sauri tana kwalawa Abba Babba kira baya nan, Maamah da Tente Hasiya suka shigo. "Mene ne haka nake gani? Ba zaku bari ba?" Ina suka san Maamah tana yi, shi Adam kishi yasa yake damben ba wai don maganar da Almu ya gayawa Hajiya ba ne, amma ya kafe akan maganar da ya gayawa Hajiya ne.. shigowarta tsaya tana kallonsu. "Ya Almu!" Dafe kirjinta tayi tana sauke numfashi da sauri da sauri. A kuwa take fadar ya ƙare, cikin jin haushi Uban kowa yana zuwa ya bangaje Almu tare da ciro inhaler ya tura mata baki ya shaka mata yana barin Parlourn. Har lokacin kirjinta yana ciwo. Rikota Khamilah tayi suka fita. Ƙarshen fadar da basu kara ba kenan.
Washi gari.
Da sassafe sai ga likita ya zo dubata daga Almu. Kunyar shiga gidan yake saboda abinda ya faru gashi duk fuskarsa ta tuje. Bayan fitar likitan Uban kowa ya shiga gidan a tsakar gidan ya samu Abba Babba yana karyawa."Barka da safiya!" Ya fada yana kallon kofar Maamah, " Da sauki jikinta! Ina Babana yake?" Watsar da hannunsa yayi alamar bai sani ba. "Adam wato baka da matsala a rayuwarka sai na fada da rigima? Adam me yasa ba zaka gane ka girma bane? Kai Yaro ne da kullum zan maka faɗa? Shima Babana ya bani mamaki da ya biye maka har kuka yi fada da abin kunya a gaban kanwarku. Nasan halinsa haka nasan naka Adam kada na kara jin ka kama wani da faɗa domin zan zuba maka ido kayi yadda kake so, da iliminka da kome amma kake abinda bai dace ba, Adam kayi aiki ka ki ka bude shagon da kullum sai anyi fada haba Adamu haba don Allah, me yasa kake haka ne?" Sunkuyar da kai yayi yana jin maganar Abba babba kamar yana zane shi da bulala. Shigowar Almu ya samu wuri ya durkusa yana gaida Abba Babba, anan shima ya amshi fadarshi. Har da karar da Hajiya ta kawo duk sai da ya musu tas, sannan ya ce musu. "Sai ku shiga ku ganta!" Nan ma fa shigar Uban kowa wani bangaje Almu yayi ya shiga, koda suka shiga sun same ta a parlourn, d'ago kai tayi ta kalli Uban kowa a hankali ta sauke kai, muryan Almu da sallamar da yayi ta amsa tana murmushin, wani irin kallo yake bin ta da shi. Takowa yayi ya zai iso gabanta. Uban kowa ya sha gabansa. Wani mugun kallon da ya watsa mata sannan ya ajiye mata wasu maganganuna.
Kafin ya bar parlourn yana mai bangaje Almu a karo na uku, a tsakar gidan ya samu Mahmoud yana gaida Abba Babba, wani bakin ciki ne ya cika shi. A ransa kuwa kallon munafukai yake musu, shiga bangaren Hajiya yayi ya fara mata bori da rigima da tsaki kala kala. Ita kanta bata iyawa da rigimarshi, fita yayi ya nufi bangarenshi ya shiga dakinsu ya dauko wiwi. Ya kunna tare da fitowa baranda ya zauna yana busa hayakin. Can kuwa sai gasu tare. "Uban me kika zo yi bangaren Maza? Idan kika kara motsi sai na karya kafarki da kika d'aga." Yadda yayi maganar yasa ta tsayawa cak. Takowa yayi har inda Almu yake yana busa hayakin wiwin a fuskar. "Nan ba cikin turawa ba ne, da ake yadda ake so da su babu bismillah, wannan kazar gida ce, kuma kowacce kaza tana da zakaranta.. zaki wuce ko sai na karya wuyarki ko kunya baki ji ba kin biyo namiji a baya da shegen tsawo kamar isha!" Ba musu ta juya simi-simi ta bar bangaren. Tana barin wurin Almu ya ce mishi. "Bani da lafiya mutum irinka mara gobe!" Dariya yayi yana sake hayakin wiwin a sama, "future kike nufi? Hmmm ni Ina da shi kai ne dai nake da yakinin baka da shi." Ya bangaje shi. Daga haka ya wuce ya bar Almu a wurin.
Kwanakin da suka yi a cikin Agadaz da Naanah Asma'u yana cikin kwanaki masu tarihi, domin har Gidan kakanninta suka je, kowa sai murna yake da ganinta. Asalin jika ce da ake bala'in so. Tsakanin Mahmoud da Mustapha ba wani rashin jituwa, domin akwai mutuntata juna, amma kishin juna kan suna yi, domin Almu ya fahimci yadda bata hira da shi sosai tafi yi da Moud, yayinda shi kuma Moud yake ganin Almu yafi shi shiga jikinta. Ko suna tare da Almu Moud ya zo sai ta nuna mishi abokinsa ya zo haka zata raba hankalinta biyu tana magana da Moud amma hankalinta yana kan Almu, idan ta ga yayi shiru zata d'aga mishi kai tare da cewa.. "hmm!" Girgiza mata kai yake ya ce mata.. "Mhmmm!" Murmushi take ta cigaba da zuba surutunta don itama magannaniya ce idan ta samu Yayanta.. wannan abin sau biyu ana yinsa a gaban Uban kowa kai ranar ya gaji da wannan rashin mutuncin da suke mishi, yana ganin haka ya nufi cikin gidan wata sharbebiyar wuka ya dauko ya nufe su ya ce mata. "Idan baki tashi ba kin shiga cikin gidan wallahi sai na sare kafar dayansu tashi!" Ya nuna su da wukar, ba musu ta mike tare da nufa cikin gidan. Ya zuba musu ido cikin takaici ya ce musu. "Yan iska kawai!" Ya juya tare da nufar cikin gidan. Yasan zata kawowa Hajiya abinci. Ai kuwa tana kawowa Hajiya abincin, nuna mata hanya yayi jikinta na rawa ta shiga gaba har Parlournshi. "Ciri wata karamar wuka ya nufe ta." A haukace ya damki gashinta yana faɗin.. "wallahi zan soka miki ina wasa dake? Na. Kara ganinki da wani Shegen." Kuka take tana gyad'a kai. Sannan ya sake yayi ta fara haki, shiga daki yayi ya dauko inhale don yana. Daga cikin abinda baya rabuwa da shi a rayuwarsa. Tana zuwa ya bude bakinta ya saka mata can kuwa ta ja numfashinta kafin ta mike zata fita shima ya biyo bayanta daga shi sai gajeren wando irin iya cinyar nan, janye dankwalin kanta yayi tare da zare ribon din kanta tayi tana tsaye jikinta yana rawa ya turo ta waje. Ya fito shima daidai Almu ya zo bangaren ganin yadda take ƙoƙarin daura dankwalin tana kuka, wani irin kishi ne ya fisgi zuciyar Almu ya nufe shi da wani irin yanayi yi ya kai mishi nauyi. "Kome zaka yi ba zai taɓa sauya kome ba, lasarta nayi tare da jin yadda take tunda ai naga ku har haɗaka kuke don." Zai sake kai mishi naushin ta ce mishi. "Wai me yasa ne?" Sake shi yayi tana kuka ta ce mishi. "Kada ki yi uzuri amma ina son ka fahimci kome!" Shiru yayi yana kallonta, riko hannunta yayi suka bar wurin.
Tundaga ranar Adam ya samu hanyar mannawa Mustapha hauka. Shima ya daina ya daina kuka shi don ba zai iya Iskancinsa ba. Har ta gama hutun suka bar Agadaz. Basu bar Agadaz sai da Adam ya zuga Hajiya ta saka a hana Naanah Asma'u zama a gidansu Mustapha shi gani yake ba banza Mustapha yake tare da A
Naanah Asma'u ba akwai abinda yake samu a tare da ita, duk da bata karbi maganar ba amma kuma ganin irin kaunar da suke yi wanda tun suna yi a bayan idanun mutane ya fara fitowa, gashi dama Mustapha ya dawo gida ne saboda wani rashin lafiya da yake fama da shi na ciwoj baya. Haka aikuwa sai gashi sun kara wani irin shakuwa. Moud yana zuwa har Makarantar ya ganta tunda yanzu ta daina zaman gidansu Mustapha uban kowa ya hana. Haka ta samu shekara na biyu da fara karatun.
Tana zuwa huɗu duk lokacin da aka yi hutu.
A cikin shekara biyu nan duk wanda yasan abinda ake kira da alaƙar zuci, idan ya ga Mustapha da Naanah Asma'u yasan zuciyarsu a hade take da juna. A gaban kowa a ko ina maganar daya ce.
A irin wannan yanayin wani zuwanta biyu Hajiya ta kira Maamah ta zaunar da ita ta gaya mata kudirinta. "Rakiya ina son ki gayawa Yarki ta rabu da almu nayi mishi mata shida Uban kowa, bana son kara ganinta da shi. Ai naga kamar Yaron nan Mahamuda yana sonta."
"Kwarai Mahmoud yana sonta, in sha Allah haka za ayi." Duk wannan tsarin anyi shi ba tare da sanin Abba babba ba, sun shirya abinsu ne na ƙwarya ta bi ƙwarya.
Wannan yasa Maamah ta tsayar da Mahmoud a ranta kuma bata jin zata iya sauya raayinta. Bayan tafiyar Naanah Asma'u ta gaya mata ta zaba mata Mahmoud. Taso tayi gardama amma Maamah ta ce umrni ta bata ba shawara ba.. haka yasa ta hakura da nuna Almu a zahiri amma cikin ranta yana nan kamar zuciyarta.
Uban kowa da Adam basu sani ba, Amma Mahmoud yasan da haka shi yasa da karfinsa ya shiga filin daga domin babu wani da xai doke shi.
***
Mu dawo labari.
Dukkansu suna sahur, suka ji tarinta juyawa suka yi suka gan tana ƙoƙarin mikewa, da sauri suka nufeta. " Sannu Didih! " " Yawwa! " Ya furta, " Maamah ta farka." Da sauri suka shigo tare da ce mata. "Sannu!" Gyada kai tayi basu cire mata kome ba, sai dai Abba babba ya fita har bangaren Adam da yake d'aga karfe kowa yana sahur amma shi d'aga karfe yake! "Adam ta farka!" "Tow!" Ya fada cike da mamaki ajiye ƙarfen yayi ya dauki duk abinda Sadisu da likitan suka gaya masa yadda zai yi. Yana shiga ya same ta zaune abinda ya fara kashe kome sannan ya duba ta, ya gama abinda zai yi, yana lura da yadda take dan rawan jiki. "Ku bata tea ta sha kada a saka sugar!" Gyada kai suka yi ya cire mata karin ruwan da yake makale a hannunta sannan ya mike tare da tambayarta. "Ina yake miki ciwo?" A hankali ta kai hannunta gefen hagu na kirjinta tana mai lumshe idanunta. Shiru yayi kafin ya haɗa alluran da ya dace ya ce mata. "Nasan kema nan fied dinki ce, ayi miki Im ko Iv?" Yana nufin ayi mata alluran a mazauninta ko a hannunta. Mika mishi hannun tayi. Yana ganin mutane masu rashin magana ko shi mutane na yawan fada bai da magana amma Naanah Asma'u da Mustapha sune asalin kuramen. A hankali ya haɗa tare da yi mata a jijiyar hannunta. " Shiii!" Ta fada jikinta yana rawa. Duk mugunta da ya mata tana yarinya yasa take tsoronsa amma sauran mutane ai ba haka take musu ba. Yana mata alluran yana kallon fuskarta da yake zufa......