Chapter 13
by @maidambu41
Yana gama mata alluran Maamah ta mika masa kunu mai zafi. Amsa yayi ya fara kurba ya cewa Maamah. "Amma ba zata yi azumi ba fa!" Yana fadar haka ya bar dakin, "Maamah zan yi iya fa!" Ta fada kamar zata yi kuka. "To ko na. Kira shi sai ki gaya masa da bakinki!" Tasan ba zata iya ba shi yasa ta ce matata gaya mishi da bakinta, tunda ta fahimci yadda take tsoronshi.
Bayan ta gama fadar haka ta bar dakin, "Didih zaki yi wanka ne na haɗa miki ruwan?" "Eh Khamiee!" Ta fada tana kokarin mikewa, fita Mairoh tayi ta kawo mata ruwan zafin ita kuma ya hada mata. Faɗime ta rike mata hannu suka shiga ban dakin ta kalli Naanah Asma'u ta ce mata. "Didih na kira Maamah ta miki ne?" Gyada kai tayi, fita tayi can sai ga Maamah ɗinsu. Kayan wankanta aka kawo mata ta fara wanke mata kai tass sannan ta mata wanka musamman bayanta da hannunta dukka biyu. Sannan ta fita, ita kuma ta rasa wanka. Shigowa Khamilah tayi ya riko hannunta suka fito waje. "Sannu Didih mun zata zaki tafi ki bar mu ne!" Kallon yar Uwarta tayi tana fadin. "Idan lokacin yayi zan tafi." "A'a wallahi da saura in sha Allah!" Ta wuce tana ciro mata doguwar riga ta saka sannan ta shimfida mata abin sallah, "kwana na nawa?" "Biyu ne da yau?" Ta bata amsa, haka tayi sallah har da kwanakin, tana idarwa Maamah ta kawo mata tea me kauri. Tana sha tana kallonsu.
Hira suke mata sama sama har aka shiga sallah asuba, duk suka yi a dakin sannan suka yi addu'a. Bayan minti goma da fitowa sai gashi tare da Sadisu, suna zuwa ya zubawa gashin kanta idanu wanda ya zubo har bayanta. Harara ya watsa mata yana mata wani irin kallo kasa kasa. Jikinta ne ya fara rawa, da sauri ta shiga tattara gashin tana me daukar hularta ta saka. Sadisu ya duba abinda zai yi ya kara mata ruwa, saboda yadda tace bata jin karfin jikinta. Sai bayan ya gama ya fita. Kallonsu yayi cikin haɗe fuska ya ce musu. "Idan ita ba zata iya kula da kanta ba, meye amfaninku?" Ya nuna musu kanta. "Kada na kara dawowa na ga sumar nan a waje idan ba haka ba dawowa na gaba kwalkwabo zan muku wallahi!" Daga haka ya fita, duk da suna bala'in tsoronshi amma yadda yayi maganar sai da ya basu dariya wai zai musu aski.
***
Daga gidan asibiti ya wuce ganin Hajiya, lokacin da ya isa ya samu duk Yaranta sun haɗu abin mamaki har da Mustapha, ya samu Hajiya tana sharban kuka. Shan jinin jikinsa yayi yana kallon yadda ta kauda kai ta basu labarin abinda ya faru kenan. Hade rai yayi ya dauki duk takardanta yana kallon kafin ya fita ya.
"Aure zan masa, ba na son abinda yake aure zan masa na gaji da haka. Ke Atikah Makaho zai samu Abubakar da maganar Mufidah, in sha Allah." Cikin tsananin farin ciki ta ce mata. "In sha Allah, Allah ya jikan Mahaifiyarshi. Allah ya jikan Babanmu!" Ta jima sosai akan wannan haɗin.
Kallon Almu Hajiya tayi tana son cewa maganarshi da Hamidah, ganin yadda ya kafe ta da idanu yasa ta haɗiye abinda yake ranta, tasan bai da mutunci. Haka suka tsayar da maganar bayan shan ruwa zasu sami Mahaifin Yarinyar. Wato yadda Mustapha yake farin cikin wannan haɗin ba karamin dadi yake ji. Fita suka yi iyayen ya rage daga Hajiya sai shi. "Wallahi da kin sake kin yi wani motsin da xai raba ni da Naanah Asma'u da yau Yaranki kuka zasu yi ni kuma na kwana ina murna!" Shiru tayi bata ce kome ba.
Har Uban kowa ya dawo ya samu Mustapha yana dariya saboda mugunta, ita kuwa Hajiya taki kallonshi. Jikinshi ne ya bashi dariyar da Mustapha yake babu alkhairi a cikinsa. Murmushi yayi ya fita bai zame ko ina ba sai gidan Mahaifinsa. Yana shiga ya samu yana ban daki shiga dakin yayi ya tsaya yana jiranshi. Yana jiran ya fito can kuwa sai gashi ya fito. Ganin Uban kowa sai da ya sa gabanshi ya faɗi ya ce mishi.. "Haba Adam shine zaka shigo min daki idan kuma ba kaya na fito!" Zaro wayarshi yayi ya dan-danna ya yi magana ɗaya." Ku dakatar da kayan nan sai na baku umarni!"
Kallonshi Mahaifin yayi tare da cewa." Me kake nufi?" "Eh abinda nake nufin kenan. Me kuka shirya a asibiti da Hajiya?" Ya tambaye shi, tsaki Uban yayi ya ce mishi. "Akan wannan kake d'aga min hankali? Tow Maganar aurenka aka yi kai da Mufidah!" "Da alamu kana son kayi asarar dukiyarka, ni babu wanda ya isa rubuta min ƙaddarata da wata macen da bata min ba, idan kuma kana ganin haka shine dai-dai bismillah Hajiyar ma zata gamu da ni."
Daga haka ya juya zai fita ya kalli kofar dakin ya kai mata wani jahilin naushi ya ce. "Hmmm" ya fita daga dakin ya nufi waje, da Fuad ya haɗu ya ce mishi. "Na ji labari mai daɗi!" "Zan ci kai!" Ya fada a fusace tare da fadawa motarshi ya bar gidan.
La Coffee shop ya nufa ya rasa me yake mishi daɗi, wayarshi ce tayi kara ya ɗauka. "Hello!" "Ya Adam yaushe zaka zo? Me zan hada maka?" Shiru yayi tare da dauke wuta, da baya azumi yau da katuwar mandula zai naɗa ya zuka ko zai ji sanyi. Sake tambayar shi tayi bai san lokacin da ya danna mata wani irin zagi wanda ya sa ta jin kamar an buga mata guduma a tsakar kanta, ya haɗa da wani kashedi ko ya biyo ta ya mata dukar mutuwa. Jin haka yasa ta kashe wayar.
Kallon wayar yayi bai san lokacin da ya bugat da kasa ba, jinjina kai yake yana shirin abinda zai yiwa Hajiya wanda zata gane shi fa baa mishi dole. Wunin ranar har aka sha ruwa yana shagon a karon farko a rayuwarshi da ya hada fushi da hukuncin lokaci guda ya zartar. Domin ana shan ruwa gidan wannan jami'an tsaron nan ya nufa dai-dai yana masallaci, lokacin da ya isa gidan ya samu Yaransa kanana yan mata, cire harsashi yayi a cikin ƙaramin bindigar da ya zo da ita ya zuba a cikin aljuhun wandonsa. Ya ajiyewa Yaran suna wasa da shi. Matar mutumin kuwa jikinta sai rawa yake. Haka tayi ta kaiwa da komowa. Musamman da Uban kowa ya cire jacket din saman yar ƙaramar singlet din jikinsa, yanka ce kaca-kaca irin wanda kana gani kasan wuka ce tayi aiki.
Ɗaya daga cikin ƴan mata tace mishi. "A ina ka ji ciwo?" Murmushi yayi yana faɗin. "Wurin shigo da kayan aiki!" Ya fada daidai shigowar Mutumin, wanda ganin Uban kowa yasa shi saurin ɗauke yarinyar da take taɓa yanka. "Kai!" "Kada ka razana Yaran, zauna muci abincin ai iyalinka ta iya girki ashe shi yasa kake jin kai wani ne, ka hada zazzafar mace!" "Ka iya kalamanka!" Dukar table din yayi sai da kowa ya yo kansu. Kallonsu yayi ya ce musu. "Kada ku damu mun saba ai yara yi wasa da bindigar nan!" Ya fadawa yarinyar da ta dauki, a fusace Uban ya juya ya ga yarinyar ta nuna shi ta ce mishi. "Abbi na halbeka?" Wani irin tsoro ne ya saka shi kallon. "Ka razana ne? Ka zata kowa jahili ne? Ga bullet dina a cikin aljuhun. Ni ganin waɗannan halittar yasa naji na yafe maka! Amma ka sake ka ƙara shiga gonata. Musamman kuskuren da kaso kayi wallahi da yaran nan sai sun manta da kai. "
"Amma kasan gidan da ka shigo?" "Da alamu baka san aikinka ba ne, idan da ka iya aikinka da ba zaka biyo ni har gida ba. Ina da kayan da za'a fitarshi ƙasashen makota idan ka isa ka dakatar dasu. Namijin gaske mutuwa yake akan al'ummarshi da aiki domin kare ƙasarshi." Mikewa yayi ya nufi inda aka ajiye tutar kasar kamar zata fado kasa, a hankali ya d'aga ya gyara tare da gyara mishi zama. Sannan ya kalli yadda Mutumin yake tsuma, ya kai hannu ya amshi bindigarshi a hannun Yarinyar ya zaro bullet din ya saka a cikin bindigar. Nuna shi yayi ya ce. "Saboda abinda ka aikata ka saka bakiɗaya ahalina cikin tashin hankali. Wannan ya zama kuskure na ƙarshe da zaka aikata."
Daga haka ya mike tare da saka rigarshi. Ya kalli Matar mutumin ya ce mata." Na gode sosai da karramawa, amma ina son ki gayawa Mijinki ya kula da harkokinsa ba ni ba, kin san yadda zaki gaya mishi. Mutumin irina ina da kawazuci idan ya sake na cire kawazuci zan aikata komai."
Daga haka ya mike tare da cewa." Idan ni zan binciko inda kake to ya kake tsammanin zai faru. Yaran nan kawai na kalla naji ba zan iya maka kome a cikin gidanka ba, Yaranka suna da kyau bana son na haifar da kiyayya a cikin idanunsu. Na san ka fahimci yadda nake ji lokacin da ka nufi taɓa Matar nan da Yarinyar bayanta. Da ka sake ka taɓa yarinyar nan wallahi ka gama aiki a hukumar tsaron sirri, ai na samu labarin irin aikinka azabtar da wani ɓangare na wanda kake tuhuma kada ka yarda mu yi haduwa na biyu." Ya taka har gabansa ya tura bindigarshi a bayan shi ya ce mishi. "Naji labarai dayawa a kanka da irin abinda kayi wa, Hale da iyalinsa da babban yarshi.. kuma kasa yayi shiru bayan ka saka shi amsar laifin da yake cikin gidan kaso." Sosa giranshi na dama yayi. Kafin ya taka sosai ya kai bakinsa kunnenshi. "Da ka taɓa yarinyar nan, ni ba zan taɓa matarka ba, yaran nan zan yi cinikinsu zuwa Italiya kullum sai na turo maka videonsu wallahi na rantse maka abinda zan aikata kenan ba ka sanni ba ne. " Daga haka ya juya ya bar parlourn yana sha kan Yaran, faduwa yayi yana jin wani irin abu yana dukar zuciyarshi. Bai taɓa haduwa da dan ta'adda me tarin confidence kamar El Mayor, Matarshi ta ce mishi." Me ya faru? Waye shi? "
Girgiza mata kai yayi yana jin kamar an mishi wani abu, tsoro ce wannan shine asalin tsoro da ake bawa duk wanda yasan me ake kira tsoro. Idan ka hadu da shi tow shi kanshi tsorata tsoro yake domin kuwa bai ga shakka a cikin a cikin idanunsa ba. Haka ya tattara ya shiga dakinsa ya kira wayar office ɗinsu aka haɗa shi da ogan. Yana dauka ya ce. " Yallabai waye El Mayor? Waye Uban kowa? " Dariya Yallabai yayi tare da cewa. "Ka hadu da Giwa ko? Kayi karo da mugun dawa ko? Ka hadu da wanda ya saka ka faduwa ko? Ya kaji bugun zuciyarka kamar zata faso waje ko? Haka yake Adam Haris Ladan, ya kalubalence ne?" "Eh Yallabai ya ce idan na isa na dakatar da kayansa da zasu bar kasar nan ko wani lokaci."
Murmushi yayi ya ce mishi. "Ka amshi kalubalen?" "A'a Yallabai ina da Yara mata guda biyu, ya kuma min alƙawarin na kara shiga cinikinsu zai yi a nemi wani ya amshi aikin nan na rufe bincikenshi."
Ajiyar zuciya mutumin yayi ya ce mishi. "Shi kenan na fahimci abinda kake ji." Kashe wayar yayi yana girgiza kai yana faɗin." A'a ban isa ba ban isa! "
----
Uban kowa yana barin gidan kuwa can gidan Hajiya ya nufa, ya samu kofar gidan a cike saboda Abban tsakiya da yazo. Wuce su yayi don haushin kowa yake ji, a bangaren Ya samu Mustapha da Naanah Asma'u, yadda suke manne da bango kamar ƙadangaru, bai da lokacin Mustapha balle har ya san suna wurin. Kanta a sunkuye shi mamaki ma ta bashi yaushe ta warke da zata zo biyewa Mustapha? Bai bi ta kansu ba baya son karawa kanshi damuwa, amma abinda Hajiya tayi mishi ya bashi mamaki. Haka yasa shi jin wani irin haushi ma a karo na babu adadi. Bayan ya wuce daki sallah da ya baro ya sauke sannan, dauko wiwi yayi ya cika takarda da ita ya naɗe sannan ya fito baranda yana zuka.
A bangaren Almu da Naanah Asma'u kuwa, wani irin shiru ne ya shiga tsakaninsu. Amma da ka kalli fuskarsu zaka fahimci akwai wani babba al'amari. "Hmm!" Almu ya ce mata, d'ago kai tayi tana kallonshi sannan ta sunkuyar da kai tana faɗin. "Uhmm!" "Jikin da sauki?" Gyada kai tayi....