MASIFAFFAN NAMIJI

32

by @jamilaumarjanafty

*MASIFAFFAN NAMIJI..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty💞*


Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.


*032*



  "Cikin Tafiya a hankali ya Shigo Cikin Bedroom din,Sadaf Sadaf Saboda kada Hafsah ta Farka kan gadon ya kwanta Lokaci Daya yana Laluban gefen da Hafsah ke kwance yajita Wayam sai ya mike Zaune yayi amfani da Hasken Wayarsa ya Haske Gadon yaga Bai ganta ba sai ya Fara Waige Waige kafin ya mike Tsaye Wutar Dakin ya kunna ya Haske ya Gauraye Motsin Dayaji a Tiolet yasa ya saki ajiyar Zuciya sai yanzu Zuciyarsa ta bashi Tana Bayi ne.

Gefe Daya kuma na Ransa na Wani Tunani kodai Hafsah Tajishi yana waya ne..? Anya kuwa..? Duk sai ya Tsargu Jin Shuru bata Fito ba yasa ya karisa Kofar Toilet din yana Kiran Sunanta Jin Motsinsa da Kiran Sunanta Dayake yi yasa tayi Kokarin Dafa Bangon Bayin ta Mike Tayi Saurin kwabe Rigar Barcin Jikinta ta jefa Cikin kwandon kayan wankinsu Dake Cikin makewayin,Ta yi Sauri ta Zari Towel Dake Rataye saman Wata igiyan Dake Daure Daga sama acikin makewayin.

Taba Kofar yayi yana Fadin"Wai Hafsah me kike Cikin Toilet da wannan Daran..? Kina lafiya kuwa..? Dakyar ta iya Bude baki tayi Gyaran Murya Lokaci Daya Hawaye na kara kwaranyomata Jin Datayi yana Kokarin Bude kofar yasa ta Kamfaci Ruwa a wani karamin Kofi Daga Cikin Bambin Dake Bayin ta Watsa ma Fuskarta Saboda Kada Abdullahi ya gane tayi kuka..

Bude kofar Tailet Din yayi ya Shigo Lokaci Daya yana Bin Hafsah da wani kallo na kamar bai yarda da ita ba ita kuwa sai Tayi Tsuru Tsuru Da sadda kai kasa Saboda kada ya Fahimci Wani Abun Shi kuma mamakin ganinta Da Towel ne ya kamashi Cikin mamaki yace"Ya naganki Haka kuma..? Wai lafiyarki kuwa..? Ko baki lafiya ne muje Asibiti..?
Da Sauri Hafsah ta Girgiza kai Tana"A"a Lafiyata Kalau...Fitsari ya Tadani sai kuma naji Zafi Shine nace bari nayi wanka kila naji Dadin Barci.."Tafada tana Kauda kanta ganin irin kallon Dayake mata.

Cikin Tsareta da ido yace"A'a...Taya zaki yi wanka Awannan Lokacin..? Pass 12 fa kuma kinga bake kadai bane Hafsah Ko zaki bar wankan nan ne Na Samu Ruwa da Karamin Zani na Dinga Shafa miki Ajiki Kila kya samu Barci.."kai ta Girgiza Tana Fadin"Don Allah ka barni nayi zan fi samun natsuwa..Kaga kuma Bayin Daki ne fa.."Tafada Lokaci Daya tana Jan Botiki ta Fara Zuba Ruwa da kallo ya Bita wani Tunani na Shiga Ransa kafin ya kada kai ya Fice Lokaci Daya yana jawo mata Kofar makewayin.


Da kallo Ta Rakashi mai Cike da kunci kafin kukan Datake Rikewa ya Fito ta Sakeshi Gabadaya ammh Tanayi tana saka Hannu kada Abdullahi ya jiyota,Dakyar ta iya Wanka wanda Watsama Jikinta Ruwa kawai Tayi,sai kuma Tsarkin Fitsarin Data bata Jikinta Dashi,Alwala ta Dauro Domin Ta Tabbata Barci bazai Taba Daukan ta ba gwara ta kai kukanta ga Allah kila ya yaye mata Damuwa...!

Tana Fitowa Ta iskeshi kan gado yana Jiran Fitowarta Kai Tsaye ya kalleta yana Fadin"Kin Fito..? Yake tamai Lokaci Daya tana gyadamai kai,Wardrope dinta ta Nufa ta Bude ta Dauko Wata Doguwar Riga ta saka da Hijabi Ta Dauki Darduma ta Shimfida Cikin mamaki yake Binta da kallo ganin zata kabarta Sallah yasa ya Katseta Lokaci Daya yana Fadin"Me zaki yi kuma..? Badai sallah ba..?

Kai Tsaye tace"Eh salla zanyi.."Cikin mamaki yace"Sallah..? Baki sallar Isha"i bane kafin ki kwanta..? Hafsah tace'"Nayi..Na kasa Barci ne Shine nace bari kawai nayi alwala nayi Sallah koda Raka"a Shida ne.."Abdullahi dai kallon Hafsah kawai yake kamar Wata Bakuwa ganin Tana mgana Bata son kallonsa.

Cikin Tsuramata ido yake Fadin"Yanzu fa Farkon Dare ne Hafsah...Ga Jikin ki yayi Nauyi ke baki Tsausayin kanki ne..? Allah ma ya sani Saboda haka bar zencen Sallar nan maza kizo ki kwanta..'Yafada yana nuni da bata Umarni,Kai ta Sadda tana Fadin"Bari to nayi Shafa"i da wuturi Domin banyi ba barci ya kwasheni.."Tafada Batare Data Saurareshi ba ta kabarta Sallah Da kallon mamaki kawai ya Bita acikin Ranshi yana Tunanin kodai Hafsah taji Wayarsa da Barkat ne..? Ammh in Taji ai bai ga alama ba sai dai yana Tunanin kodai bata da lafiya ne..? 

Yana nan zaune yana kallonta tayi Idar da Salla Raka"a uku ta Zauna Lokaci da mike kafarta kanta na kasa tana kokarin son maida Hawayenta kada Abdullahi ya gani,shi kuwa yana ta lura da ita da Duk wani motsinta Yana kallonta ta Daga Hannu Tana addu"a Hawaye sun Fito Daga Cikin Idanuwanta Saukowa yayi Daga kan gadon ya Tsaya agabanta yana Fadin"Hafsah..Lafiyanki kuwa..? Kina addu"a kina kuka..?


Jin Haka yasa tayi Saurin Dago kanta Lokaci Daya tana Dangwalo Hawaye tana Fadin"Kuka kuma..? A"a Digon Ruwa ne inaga Abban Amira.."Jinta kawai yayi yana Binta da kallo ganin yadda take kokari wajen Tashi yasa ya saka Hannu ya Dagata cak zuwa kan gado ya kwantar da ita ya Lullubamata Bargo bayan ya Ciremata Hijabin Jikinta Kallonsa Tayi kafin ta kakaro Mirmishi tana Fadin"Nagode.."Mirmishi yayi mata kafin ya Kashe Wutar Dakin ya koma ya kwanta Abayanta ya Zuro Hannuwansa ya Zagayeta Tsakanin Cikinta ajiyar Zuciya ta Sauke Lokaci Daya da wasu Siraran Hawaye suka Zubomata Kalaman Abdullahi nayi mata lugude acikin Ranta kasa Motsi Tayi Saboda kada ya Fahinci Halin Dayake Ciki Bata son ya Fahimci ta san komai Tunda dai bai yi Niyyar sanar da ita ba Duk da ko Tana matsayin matarsa...Ta Dade Batayi Barci ba Tana Tunanin Halayyar Da Namiji Shi kuwa Tana jin Saukar Numfashinsa akan Dokin Wuyanta alamun Barci ya kwasheshi ita kuwa sai gabanin Asuba kana Barci ya iya kwasanta Barci mai Cike da Rudani Da Damuwa.

******

Washegari ma Tana kallonsa Tun Safe yana ta Shiri Su Amira ma Kiran mai mashin Dinsu yayi yace yazo ya kaisu Shi yana Sauri Tun 7am ya Fita ko karyawa bai yi ba yace mata Suna da Meeting a office kallonsa kawai take bata yarda Dashi ba Haka kurum acikin Ranta taji Cewa Wajen Baba wada zashi Kan Mganar Dataji yanayi Jiya,Hawayenta Ta Share kawai ta koma ta lafe kan gado Bayan Mai Mashin Dinsu Amira yazo ya Tafi Dasu kwance kawai take Ammh gabadaya tana jin kanta kamar ba ita ba in ta Tuna wai Abdullahi zai kara Aure.

Illai kuwa Abdullahi na Fita Gidan Baba wada ya nufa ya Fara zuwarmai da mganar,Shi kanshi Baba Wada yayi mamaki Karin Auran na Abdullahi sai dai kuma bai isa yace Don me zai kara Aure Tunda Allah ya Hallartamai Baba wada yace ba Damuwa in Ya tsara komai sai ya kira Mijin Goggo Habiba Su tafi gidansu Barkat din neman Auran Abdullahi yace ya bashi nan da kwana Biyu zai kirashi a waya su Karishe,Da haka suka Rabu da Baba wadan ya Karisa Gidan Mama itama ya zauna ya gayamata yana son ya kara Aure ba Mama kadai Dake zaune ba Hatta da Mariya Dake Cikin Dakinsu Tana Shirin zuwa asibiti,sai da ta Razana Mama ta maimaita Kalmar Auren Da Abdullahi yace zai kara  yafi a kirga Cikin nuna ma Abdullahi kamar yayi gaggawa ya bari zuwa Bayan Hafsah ta Haihu ammh sai Abdullahi ya nuna mata Babu komai Ba matsala,Jin haka yasa Mama taja bakinta tayi Shuru kafin ya Tafi sai yace Ma Mama ta Rufe mganar kar kowa yaji Saboda Bayaso mganar takai kunnin Hafsah Don bai gayamata ba Ya bari sai komai ya kamkama uwa uba kuma Cikin Dake Jikinta Baya so Hankalinta ya Tashi.

Bayan Fitarsa Mariya Ta Fito Daga Dakinsu Tana Fadin"Mama Aure naji ya Abdullahi na mganar zai kara ko..? Mama ta kada kai tana Fadin"Hmm Haka yace Nima Abun ya bani mamaki Aure haka Cikin gaggawa..Ni Wlh ban taba kawoma yayanku Aure yanzu ba.."Mariya tace"Tabdijam...Lallenema Toh Mama a ina zai Sakata..? Bai fa gama Gininshi ba Bikin Jidda ya Tsaida komai ga Anty Hafsah da Tsohon Ciki Mama Gaskiya Ya Abdullahi yayi gaggawa.."Tafada Cikin Jin Haushi kamar za"ayi ma kishiya.

Mama tace"Nima shi nagani...Naga Yadda yake Mganar kamar yana son Auran kusa ne ko wata yarinya ce kuma Oho Donni ko Da zence banji Labarin yana neman Aure ba.."Mariya dai ta Rike baki kawai Tana Jajantama Lamarin Haka Auwal ya Shigo ya Samesu yana Tambayan lafiya Mariya ta Koramai Jawabi ido ya Zaro yana Fadin"Aure..? Kan bala"i ita Wacce yarinyace zata kawo kanta..Nifa ina ganin mai iya zama da ya Abdullahi Bayan Anty Hafsah da Wahala Wlh..".

Mama tace"Atoh..Tazo dai ta gani..In Zasu Daidaita in batayi Hakurin Hafsah ba ko"ina bazasu jeba za"a fara jin kansu.."Nan ne dai suka Hadu Suna Ta Tattauna mganar, Karyawa sukayi Mariya ta Fice Zuwa asibiti Auwal ma wanka ya Shiga Domin yana da Class karfe 9am na Safe suka bar Mama Tana Janjanta Abun Cikin Ranta na Tsausayin Abdullahi Daya Jajibo ma kansa Aure 

Abdullahi kuwa Sai da yaje Office ya Kira Nazifi yamai Bayanin komai Nazifi ya Cika da Mamakin Jin har yanzu Abdullahi bai bar mganar nan ba Cikin Rashin son yarda Nazifi yace"Kai mutumina anya Abun bai yi kusa ba..Kaga da baka gama gininka ba..Ga Hafsah nada Nauyi Duk kai kadai fa..! Ni ina ganin da kabar mganar kara Auran nan zuwa gaba.."Abdullahi yace"Karka Damu Duk na mata Bayani ta Fahimta..Ta yarda zata Zauna agidana Zan gyara Dakin Da nake ijiye Mashin Dina kafin Zuwa gaba na karisa gina na..Nidai yanzu ka Kira Salisu kai mai Bayanin komai.."Nazifi yayi ajiyar rai kafin yace"Shikenan bari na Taboshi naji.."suka rabu akan yadda sukayi zai Kira Abdullahi ya gayamai.

Nazifi ya kira Salisu Engr.Bayan sun gaisa Nazifi ya koramai Jawabin Komai Salisu bai yi mamaki ba sai ma Farinciki Daya Cikasa Dama Tun ganin Da yayi ma Abdullahi a asibiti yazo Duba Barkat yake ta addu"a aransa Allah ya Tabbatar da Zarginsa Domin Har ga Allah Zai mata Sha"awar samun Nagartattacen Miji irin Abdullahi,Sun Rabu da Nazifi kan anjuma da yammah zai je Gidansu ya samu Hajiya Da mganar ,daganan zai samu Wan Babansu yayi mai mgana Wanda Daman Bayan Rasuwar Mahaifinsu Shi ne ya zama kamar komai nashi.

Salisu ya samu Hajiya Amina Dayaje Gidan Da Daddare ya labarta mata komai nan take Shaidamai Bahiya tazo da labarin Abdullahin na zuwa Wajen Barkat a makaranta,Tayi Murna Sosai tace yaje gidan Wan Baban nasu yamai bayani bai samu ba Sai Washegari yaje yamai Bayani Shi kuma yace Abdullahi ya Turo magabantan Ammh zai Kira Barkat din yaji ta Bakinta kuma ya Kirata wanda taji Abdullahi ya kara Shiga Ranta ganin yadda ya Fada mata kuma ya aiwatar ba kunya tace ta amince Shi kuma yace yana Jiran Wakilan Abdullahi.


Salisu Nazifi ya kira ta waya ya gayamai Shi kuma yace zai kira Abdullahi Suyi mgana,Bama Kiransa yayi ba Washegarin Ranar yazo Zarian ya kawo Jidda ta Rubuta Jamb suka Hadu da Abdullahin yamai bayanin komai jin Haka yasa Abdullahi baiyi Wasa ba suka Tafi Kasuwa Dashi da Nazifi suka Siyo Goro da kwakayan Biskit da Minti da Tabarma dasu Dabino ya Rakashi Atm ya Ciro Kudi 150k Dama Kudin Albashinsa ne ya Ijiyesu ne zai ba Hafsah tayi Siyayyah Suna,toh ganin maganar tataso sai ya Kwaso kawai yana Tunanin Daukan Loan awajen aikinsa yayi Hidimar Biki da gyaran inda Amarya zata zauna Gefe Daya kuma ya Sallami Hafsah kartazo ta Haihu bai Siyan mata komai ba.

Daya ma Nazifi wannan mganar kamar yace wani Abu sai kuma ya Fasa yana Tunanin kodai Asiri Shegiyar Barkat din nan tama Abdullahi ne,Daya Birkice akanta Aransa kuma yana Ji ba Lalle su Shirya da Abdullahi ba Domin Abdullahi bazai iya zama da macen Datake da jin kai da isa kamar Barkat ba.

Gidan Mama suka Fara kai kayan Tagani ta saka albarka Lokacin Jidda na gidan Bayan ta Dawo Daga Jamb din Tabiyo gidan Mama Labarin Auran Abdullahin Har ya Shiga kunnanta Daganan Gidan Baba wada suka Kai mai ya gani ya saka albarka Abdullahi ya Damkamai kudin Hannunshi Duka yace Duk Abunda suka Nemi So yake suyi zuwa Daya ayi komai agama..Shi ya Kira Mijin Goggo Habiba yamai Bayani kuma yace zai Shigo Garin Ranar da Baba wada ya Tsara zasu neman mai Auran ita kanta Goggo Habiba Tayi ta Fada Dataji labari Tana Fadin Abdullahi bai kamata yayi Aure a irin wannan Lokacin ba..

Abdullahi ya Dakatar dasu Baba wada yace gobe Shida Nazifi zasu Tafi Gusai Sai ya gayama Umman Sadiq tukunnah in ya Dawo sai su Tafi kuma Duk abunda ake Ciki Barkat na sane Domin Abdullahi na gayamata,Nazifi nan suka kwana agidansu Shida da Jidda Washegari kuma Tun Safe suka Dau Hanyar Gusai Hafsah Kuma Tuni ta Fawallama Allah komai ko afuska bata Bari Abdullahi ya Fahimci tasan Wani Abu kan karin Auransa ba Ko Zuwansa Gusai bai gayamata ba cemata yayi kaduna zashi Shida Nazifi bata kawo komai aranta ba tamusu Fatan Dawowa lafiya.

Sun Isa Gusai Lafiya da Misalin 11am na Safe Umman Sadiq tayi mamakin Zuwansu kwatsam Haka sai dai bata Nuna ba sai da suka Huta suka sha Ruwa kana Abdullahi ya Sadda kai yana karanta ma Umman Sadiq mganar karin Auransa a karkace Take kallonsa kafin tace"Aure fa kace Zaka kara Abdullahi..? Anya kana da Hankali kuwa..?

Shuru kawai yayi kansa na kasa Nazifi ma Dai baiyi mgana Ba Cikin Fada Umman Sadiq ta Cigaba Da Fadin"Ina Daukan ka mai Hankali Ashe kai Sakarai ne bansani ba kai in banda Rashin Hankali yau ko kyautar Mata aka baka sai ka amsa..? Ka manta Halin Dake ciki ne..? Ina zaka sakata awannan karamin Gidan da kuke Ciki..? Bama kokarinka na ka gama gini gidanka ka Tare kai da matarka ta Haihu achan ba kokarin kara Aure kake kai Abunka ko..? Toh ban amince ba ba kuma zan lamunta da wannan Auran ba yarinya da Tsohon Ciki kasa Hawan jini ya kamata ba.."..

Tafada Tana kokarin Tashi Da Sauri Abdullahi yace"A"a Umma karkiyi Saurin yanke Hukunci..Ita yarinyar ai Tasan ni bamai Wani kudi bane sai Rufin Asiri kuma nayi mata Bayanin komai ta Fahimci..Zata Fara zama dakin Dake kusa da Hafsah kafin na Karisa gini na mu koma Gidanmu Umma mganar Hafsah kuma Da amincewarta Umma zanyi wannan Auran.."Ya Fada suna Hada ido da Nazifi wanda yayi Kur yana kallon Abdullahi yadda ya Shararama Umma karya alhalin Suna Hanya ya tabbatarmai da bai gayama Hafsah komai ba Tukunnah.

Umman Saddiq tayi Shuru tana kallonsa kafin ta kalli Nazifi Tana Fadin"Gayamin gaskiya Nazifi Shin da sanin Hafsah kan wannan Auran.? Nazifi ya Sadda kai yana Jin kunya yin karya gefe Daya kuma yana jin Idanuwan Abdullahi masu Cike da Tsammani a kansa Cikin karfi Hali yace"Eh Umma..Inda bata amince ba kema kinsa Abokina bazai Taba rikoto Aure ba ayanzu.."Yafada yana Takama Abdullahi yatsu Cikin  Takaichin karyan Dayasa yayi ma Umma Shi kuwa Abdullahi ajiyar Zuciya Ya Sauke jin Nazifi bai Tona mai aasiri ba.

Umman Sadiq tayi Shuru kafin ta kada kai Tana Fadin"Naji..Wata yarinya ce wai ma zaka Aura..? Nazifi ne yace"Yar Tudun Wada ce...A makaratar ABU samaru suka Hadu kanwar abokinmu ne Salisu Umma.."Umman Sadiq tace"Kenan itama Digirin Take yi..? Nazifi yace"Eh Umma ammh Tana Shekaran karshe ne ta kusa Gamawa"Umman Sadiq ta Tabe baki Tana Fadin"Naji...Sai dai bazan amince da mganarku ba sai na Kira Hafsah Dakaina na Tambayeta Domin Haka kurum naji Ban yarda Daku ba.."

Daga Abdullahi Har Nazifi sai da Gabansu ya Fadi suka kalli Juna..Umman Sadiq na Lura dasu Tatashi ta Shiga ciki ta Dauko Wayarta Tazo ta Kira Hafsah kuma ta saka wayar a Spekear kowani karan Shigan Wayar da Zuciyar Abdullahi yake Bugawa


 Hafsah kuwa Lokacin da Kiran Umman Sadiq ya Shigo Tana kwance ne kan Doguwar kujerar Falonta ta kasa komai Tun Bayan Fitan Abdullahi Wayarma an Ci sa'a tana kusa da ita ta jawota ganin Umma ke kira yasa ta yunkura ta Mike Lokaci Daya tana Daga Kiran da sallama Umma ta amsa Hafsah ta gaisheta ita kuma ta amsa Tana Tambayanta Jikinta da kuma yata tace Jiki da Sauki kuma yara na makaranta.

Umma ta gyara zama Tana Fadin"Hafsah..Tambayarki Zanyi kuma ina so ki Fadamin gaskiya.."Hafsah tace"Insha Allahu Umma.."Ta gefen ido ta kalli Abdullahi Da Nazifi wadanda suka Sadda kai kasa Sun gama Sadakarwa yau sun gama Jin kunya da Girmansu suna karya.


Umman Sadiq tace"Wata mgana Mijinki Abdullahi Suka zo min Da ita Dashi da abokinsa Nazifi gasu Zaune agabana.."Gaban Hafsah ya Fadi acikin Ranta tace Shikena mgana ta Tabbata ammh Cikin yake da nuna bata san komai ba tace"Mganar me fa Umma..? Umma tace"yazo min da Zencen yana so ya kara Aure..kuma cikin gaggawa nan da Wata Daya ko Biyu Toh na Nuna Ban amince ba Saboda ke sai kuma ya Tabbatarmin da Saninki zai kara Auran kuma da yardanki Shin Hakane..?

Hafsah Taji mamaki ya kamata Wani Abu na Zuwa Daga karkashin Ranta tayi Shuru kawai Tana Jin Ruwan Hawaye na Taruwa acikin Idanuwanta Jin Shurunta yasa Umma ta kalli Abdullahi Cikin bacin Rai tana bamkamai Harara Cikin mamaki Sukaji Hafsah na Fadin"Eh Umma gaskiya ya Fada miki..Sai da ya gayamin na kuma amince Daman Don Allah karki Hanasa Tunda dai yana so Umma kuma Daman bazai Zauna Dani ni kadai ba Yana Da Damar da zai karo uku ma ba Daya ba Umma Tunda Allah ya bashi Dama.."Hafsah ta Karishe Fada Hawaye na Wanke mata Fuska ba Umma Sadiq kadai ba Hatta su Abdullahi jikinsu yayi Sanyi barin ma Abdullahi Daya ji Wata kunyar Hafsah ya kamashi Da kuma Wani karin Tsausayinta da Sonta.

Umman Sadiq tace"Shikenan Tunda kince Haka Daman gani nayi Hidima zatamai yawa.."Hafsah Tayi Mirmishin Dayafi kuka Ciwo tace"Bakomai Umma..Allah zai Rufa Asiri.."Umma tace"Shikenan Allah Shigemana gaba ke kuma Allah ya baki Juriya ki kwantar da Hankali kinga bake kadai bace..Allah ya Saukeki lafiya..Hafsah na Kokarin Sakin kukanta Take Fadin"Ameen Umma nagode...agaida su Zahra.."Ganin kukan nata na neman kwacewa yasa ta yanke Wayar da Sauri sai kuma Dukkansu Sunji alamun a kalaman Hafsah na karshe kuka take.

Ajiye wayar Umma tayi ta mike ko kara kallonsu batayi ba ta Fita Daga Dakin Tana Fita Nazifi ya Numfasa yana Fadin"Na Dade ina baka Shawara kan yadda zaka Tafiyar da gidanka ammh wannan karon ina Bayan Hafsah..wlh samun mata irinta sai ka Tona kuma ka Rubuta Wlh Wannan Barkat Din Daka kema Rawan Jiki bazata taba maka Hakuri da Biyayyah Hafsah gareka ba ballatana ta iya da Halinka na Saurin Fushi da Korafi ba.m."Wani kallo Abdullahi ya Sakarmai kawai kafin ya Dauke kai Shima Nazifin kai ya Dauke kawai yana kunkuni wai Abdullahi ya sakashi karya yana jinsa yayi mishi Banza.

Abinci Umman Sadiq ta kawo musu Sukaci suka Koshi kana suka Fita Sukaje sukayi Sallah bayan Sun Dawo suka gaisa da Mijin Umman Da abokiyar zamanta ko Su Zahra basu Jira Sun Dawo Daga makaranta ba Sukayi musu Sallama suka Dau Hanya Bayan sun Zube musu Tsaraban su Minti da Biskit,Umma kuma ta Bada Zuma mai kyau tace akaima Hafsah Garin alkama da Garin Konu kuma tace akaima Mama suka karba suna Godiya.

Koda suka Dawo Nazifi ya kawo Abdullahi gida bai Shiga ba.Ya wuce Abunsa Domin in garin Allah ya waye gobe yake son su koma Kaduna Abdullahi kuwa da kunya ya Shiga Gidan sai dai me Hafsah ta tarbeshi Sosai ta kokarta Tayi Girki Tayi Wanka taci kwalliya Ganinta Haka sai ya kaasa mgana Daya bata Tsaraban Umma Haka take Murna tana Tambayanshi ya suka Baro Su Umman Shidai kawai yake yake mata Duk Abun kuma sai ya Dameshi sai alokacin yake ganin Rashin kyautawarsa bai iya ce mata komai ba Har Washegari da Safe kalma Daya ya gayamata Lokacin Data Rakosu Shi da su Amira zai kai su makaranta Dagachan ya wuce Wajen aiki.

Ya kalleta yana Karban Karamar Jakarsa Dake Hannunta yace"Don Allah Hafsatuna kiyi Hakuri kinji..? Banso haka ba bani da wani ZABI NE don Allah ki yafemin kar Allah ya kamani Da Fushinki.."Mirmiahi Dayafi kuka Ciwo ta Sakarmai kafin tace"Waya gayamaka kayi laifin a wajen Hafsah..? Karka Damu...Ko ka gayamin ko baka gayamin ban isa in ja da Hukuncin Allah ba Abban Amira.."Kallonta yayi gani Hawaye sun Cikamata ido kai Tsaye yace"Ban gaya miki bane Saboda Bana so Hankalinki ya Tashi..Ga kuma Ciki Tare Dake ina Tsoron ki Shiga wani Hali.."

Dariya kawai Hafsah tayi kafin tace"Haba dai..Kamar ban yarda da Allah da kaddara ba..Kuma wacece ni da zan Hanaka Kara Abunda Allah ya Hallatarmaka..?Ban isa ba..Ina Fatan Allah ya kaimu Lokacin ya kuma Sanya alheri.."Tana Gama Fadar haka ta juya ta koma Daki Tana Share Hawayen Idanuwanta da kallon Tsausayi Abdullahi ya Bita yana Jin Hafsah ta gama Samun wani Wawakeken Fili acikin Zuciyarsa Jiki a Sanyaye ya Gungura mashin Din zuwa Waje ya Tada ya Hau,Amira ta Hau baya Amira kuma ya sakashi gaba suka Dau Hanya.

Kwana Biyu Tsakani Su Baba wada da Mijin goggo Habiba da Nazifi sukaje gidan Wan Babansu Salisu Dake Sabon gari chan suka iske Salisu Dayake yasan da Zuwansu sun Samu Tarba Sosai Sunci sunsha kafin su gabatar da Abunda ya kawosu ganin sunce suna Shiryeni basu son Jeka ka Dawo yasa nan da nan aka Fadi Sadaki da Dukiyar Aure baba wada ya zaro ya Bada Duka 150k Sdaki da Dukiyar Aure suka kama sun Gabatar da kayan sa Ranarsu suka kuma Bukaci Saka Ranar kar ya Dau Lokaci kamar yadda Abdullahi yace toh anyi dai komai Cikin Girma an saka Ranar Kwana 50 cif masu zuwa da Wannan albishir din suka koma ma Abdullahi Duk da bai so Haka ba bai da yarda zai yi Hakanan ya Hakura Shi ya ma Kira Barkat din ya gayamata sai ta mai na yan Duniya zuwan bata sani ba Nan kuwa Daganan Sabon garin Salisu gida ya wuce ya gayama Hajiya Amina komai ya kuma kai mata Sadakin a Hannunta Shine Bahiya da Bahijjat suka Kirata suna Ihun Murna Suka gayamata Bahiya tana Makaranta ammh Tunda Taji Labari ta Gudo ta bar Barkat din achan tace gida zata koma ta kwana.

Bangaren Su Zannira da Subai"atu kuwa Abakin Mariya sukaji labari Subai  Zannira kuma Bakin Jidda Data je Gidanta Take gayamata Sunyi mamaki kwarai ainin Barin ma Subai washegari sai gata Gidan Mama Tana Tambayaa Mama tace kwarai an saka Rana Daganan Subai bata Tsaya ba sai gidan Hafsah ta Isketa Sai karfin Hali Domin Duk Ta Rame ganin Subai sai Rauninta ya Bayyana ta Fada Jikinta tana kuka Subai tana lallashinta Sai da tayi ya isheta kana tayi Shuru.

Subai ta kalleta tana Fadin"Kinga yadda kika Rame kuwa... ?;badai mganar Auran ya Abdullahi ne zai saka Kije ki kashe kanki ba..Kinga yadda kafafuwanki suka kumbura kuwa.."?Hafsah ta Kada kai Tana fadin"Haba ko Daya..Kawai Tausa ne kadai na yau da basu samu ba..Ammh gobezan je awo zan musu Complain naji..Mganar Auran Abdullahi kuma bai gabana Subai'atu Abu Dayane agaba na Sauka Lafiya.."

Subai tace"In bai gabanki..Meyasa naga kin Rame kuma nazo kin ganni kin kama kuka.."Hafsah tace"Kukam Dacin Rai ne Subai...Abu Daya ne ya batamin Rai game da wannan Auran Subai ko da bani da wani matsayi wajen Abban Amira bai kamata na Fara ji  wannan mganar Daga bakinsa ba..? Kana kuma bai kyautamana ba Da bai bari ya kamallah Gidanshi ba kuma bai bari na Sauka lafiya ba ammh yaja jibo Aure."Tafada Hawaye na Kawo mata.

Hannunta Subai ta Rike kawai Tana lallashinta Domin bata da ta cewa nan ta Dade sai yammah ta koma Gida kowa yaji labarin Auran Abdullahi sai yayi mamaki ya kuma Kira Hafsah yace kar ta Tada Hankalinta Su Ammi kuwa da kanshi yaje ya gayamusu sai ganin Kiran Ammi Tayi Hafsah tana Gayamata kar ta Tada Hankalinta Sai kawai ta sakama Ammin kuka ita tayi ta lallashinta da ban baki da Nasiha Musamman Daddy yace taje yana son ganinta Abdullahin yakai ta Shima yayi mata Nasiha Sosai wanda yasa Taji Zuciyarta ya yi sanyi ...


Ita ko Anty Hadiza Dataji Fada ta kamayi da Abdullahin tana Fadama Ammi ya cika zalama ina yaga karfin Rike mata Biyu,ga gininsa bai gamaba ya Dauko Aure Ammi ta Takamata Burki ta kuma Haneta da kiran Hafsah ta Raunana mata Rai Fadan Ammi yasa Data Kira Hafsah batayi Korafin baa ammh tace karta Damu Duk Abunda Take Bukata ta Kirata ta gayamata Fatanta karta Damu ta Cigaba da addu"an Allah ya Sauketa lafiya.


Littafin Masifaffan Namiji  free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai Completed document  1k ne biya ta wannan acct ɗin 5040273639 Moniepoint Jamila Umar.
Ko tuntuɓa ta wannan lambar ***


*Janafty...*