KARKI TAMBAYI MAMA

CHAPTER TWO : Abin da mama taki fada

by @waleedarhabbubak309

CHAPTER TWO

Amina ta zauna a gefen gadon, wayar tana hannunta amma hankalinta ya riga ya tashi daga kan screen ɗin. Kalmomin da ta karanta suna ta dawowa cikin kanta.
“Kada ki tambayi mahaifiyarki game da ni har sai kin shirya jin amsar.”
Ta ɗan lumshe ido. Me ya sa Salsabilla ta ambaci Mama?
Kuma me ya sa ta san sunanta?
Amina ta danna screen ɗin wayar, ta koma cikin Drafts ɗin, tana neman ko akwai wani saƙon da zai ba ta ƙarin bayani. Ta gungura ƙasa a hankali, amma kafin ta kai ƙarshen jerin saƙonnin, sai ta ji motsin Mama daga ɗakin waje.
Ta ɗaga kai.
“Mama?”
Babu amsa.
Ta fito daga ɗakin da sauri, wayar har yanzu a hannunta. Ta tarar da Mama a kitchen tana gyara kayan abincin dare, kamar babu abin da ya faru.
“Mama.”
Hauwa ba ta ɗago ba.
“Me kika ce?”
Amina ta tsaya bakin ƙofar kitchen. “Waccan yarinyar… Salsabilla.”
Hannun Mama ya tsaya kan abin da take yi.
Ƙaramar shiru ta sauka tsakanin su.
“Me ya sa kika tambaye ni shekarunta da ta ɓace?” Amina ta tambaya.
Mama ta ɗago mata ido, sannan ta sauke shi.
“Ki je ki kwanta, Amina.”
“Amma Mama”
“Na ce ki je ki kwanta.”
Amina ta kalle ta na ɗan lokaci. Wannan ba irin muryar Mama ba ce ta yau da kullum. Akwai wani abu a ciki, wani abu da ya fi umarni ƙarfi. Kin san ta, ko?”
Mama ta ɗan motsa leɓenta kamar za ta yi magana, amma sai ta juya ta ɗauki kwano.
“Amina, wasu abubuwa ba sa bukatar a tono su bayan shekaru.”
“Amma wannan ba amsaba ce.”
“Wata rana za ki fahimta.”
“Wace rana?”
Mama ta tsaya.
Sai ta ce a hankali, “Ranar da za ki gane cewa ba duk gaskiyar da mutum ya nema ce yake iya rayuwa da ita ba.”
Amina ta yi shiru.
Mama ta wuce kusa da ita ba tare da ta sake cewa komai ba.
Amma kafin ta bar kitchen ɗin, Amina ta lura da wani abu.
Hannun Mama yana rawa.
Amina ta koma ɗakinta ba tare da ta sake binsa ba. Ta rufe ƙofar, ta jingina da ita, sannan ta kalli wayar da ke hannunta.
Idan Mama ba ta san komai ba, me ya sa take tsoro?
Ta zauna a gefen gado, ta sake kunna wayar.
A wannan karon, wani sabon notification ya bayyana a saman screen.
1 New Draft.
Amina ta daɗe tana kallon saƙon kafin ta buɗe shi.
Saƙon bai yi tsawo ba.
“Amina, idan Mama ta ce ba ta san komai ba… kada ki yarda da ita.”
Ta daina numfashi na ɗan lokaci.
Sai ta ga layin da ke ƙasa.
“Amma kada ki tambaye ta har sai kin gano sunan mutumin da ke cikin hoton.”
Amina ta gyara zamanta.
“Wane hoto?”
Ta koma gallery.
Akwai hotuna huɗu kacal.
Na farko tsohon hoton titi ne.
Na biyu wani gida ne da ba ta taɓa gani ba.
Na uku… mutane biyu ne tsaye a bakin wata mota.
Ta ƙara haske.
Sai zuciyarta ta buga da ƙarfi.
Mutumin da ke tsaye a gefen Salsabilla ba ta san shi ba.
Amma matar da ke gefen ta…
Amina ta kusan sauke wayar daga hannunta.
Mama ce.