SHI SO DABAN YAKE

Babi na goma sha biyar

by @dijensy

  

15




 Yau ƙarfe goma a  gidansu ta mata Jidda ,wuni guda tayi a gida sai yamma ta tashi tafiya Anty Baby na tambayarta ba da Hassan zasu tafi ba tace yau ba zai zo ɗaukanta ba.


 "Daman ai wahala shi kike har sai ya zo nan duk nisan wajen aikinsa".Cewar Anty baby ita dai bata ce komai ba amma yau karo na farko sai da ta ji ba daɗi ta saba yana zuwa ya taho da keke napep su tafi tare.Kafin maghriba ta ƙaraso gida ta ciro makulli ta buɗe gidan ta shiga ,ƙofar parlour ta tarar a buɗe alamar ya dawo gidan bata samesa a parlour ba ta shiga ɗakin ta tsaya da mamaki take kallon akwatunan da ke jere a ɗakin masu kyau ruwan pink kala uku ta kalli Hassan daga zaune ya ɗago ido yana kallonta da murmushi ,jakarta ta sauke ƙasa tana cire mayafin "Mene kuma wannan?"Ta fara tambaya "Duk naki ne"Ya amsata a sanyaye ta ƙarasa tana kallar kayan ta shiga buɗe akwatunan ɗaya bayan ɗaya tana kallon kayan ciki taff a cike guda ɗaya kayan sawa ne kama daga atampopi lace da dogayen riguna ɗaya akwatin hijabai mayafai da kayan bacci da under wears ta buɗe daya kowaanne da mamaki take ɗagashi wani list da ta taɓa bass tun farkon aurensu har ya ce mata bashida kudi sai dai ya rage mata kaf abubuwan da ta bukata a list din sai da ya sa mata ciki ya ƙara da kayan yari da sarƙa da awarwaro ya ga tana don sawa Jidda ta ɗago ta kallesa da wani yanayi mai nuni da damuwa "Meyasa ka siyo wannan kayan?"


 "Sabida yakamata,na daɗe ina buri na samu wata yar dama kowacce mace a aladarmu da muke ana mata lefe aamma ke ban maki ba sabida yanayi kuma na samu faraga nayi ai ba laifi ko Amiraty?kin cancanta fiya da haka ne".Da wani irin sanyin jiki maganganun na ratsata ta zauna gefe "Kuɗi fa dayawa ka sa ka saya ? Ina ka samu kuɗi ko salary ba kai ba fa masu tsada ne kayakinnan Hassan meyasa ni dai Allah ban saka ka ba".Ta faɗa tamkar tayi laifi yana murmushi ya taso ya matso kusa da ita "Kamar yadda na faɗa maki faraga na samu,akwai wani kamfanin solar haka wani aboki na ya bar wajen aikinmu da dadewa tohm a can yake yanzu sai ya faɗa min akwai haka harkan da suke idan ka kawo musu customer irin in bulk aka siya panels na solar a guda ashirin da biyar daya zai zama naka kamar dai marketing tohm na samu haka dai na haɗa mutane sha bakwai tohm idan kina da kudi zaki iya juyawa ki cikake 25 ɗin abokin nawa ya juya min na ne samun 1 free idan kika siyar  benefit naki ne ,akwai alkairi sosai da na samu ciki kusan dubu dari shida da shi nayi amfani da 500k  na siya maki  wannan kayan, kai ta girgiza Jidda  tun kafin ya ƙarashe maganar "Dukda haka kana buƙatar kuɗin ai kaima"Jidda ta faɗa yayi Murmushi "Kuɗina amfaninsu na kashe miki Amiraty komai nawa naki ne".


"Nagode Allah ya ƙara buɗi"Ta iya faɗa har lokacin jikinta a sanyaye don ba karamin mamaki ya bata ba ta ga bil hakki don taji daɗi yake  irin wannan sadaukarwar?kiran sallar magrib da aka yi ya tashi ya fita jidda ta sake kallon kayan karo na biyu kafin ta rufe akwatin tana jinginewa a gefe,koda ta idar da sallah ta shiga kitchen ta ga ya tafasa mata naman da ya siyo gas ta kunna tana ɗora musu jollop taliya wanda zai fi sauƙi bata sani ba ko yana jin yunwa yanzu.Koda ya shigo gida sai da ya taho mata da kankana da abarba ya yanka musu a plate ta kammala abincin ta zauna suka ci tare shi ya wanke kawanukan bayan sun gama yace ta huta.


     

    *Bayan sati uku*



      Hassan ne tsaye bakin ƙofar gate ɗin nasu yana kwankwasawa Jidda ta fito daga ɗaki tana nufar ƙofar ta buɗe ta ganshi tsaye ba tare da tace komai ba ya shigo yana sunkuceta ya ɗaga ta sama ta yi yar kara a tsorace don bata zata ba "Jiddatyyy yau da albishir nazo miki".Ya faɗa yana sauketa ta ɗaga gira "Mai ya faru ?"


  "An biya min Umrah".Ya amsa ya kasa rufe bakinsa "Haba?waye wannan?"Ta tambaya da mamaki.


"Ba min je musabaqa ba rannan da ɗalibanmu ?"


Kai ta giɗa yace "Da manyan makaratu daga wasu garuruwa sun zo haka akwai manyan mutane da suka zo gurin aka bada kyaututuka bayan an samu wanda sukai na ɗaya a makarantarmu  ashe daga baya wani mutum a wajen yace kyaututukan sunyi kadan ya ɗauki nauyin biya mana Umrah mace da namiji ɗaliban nawa su biyu sannan ya ce har da malamin ɗaliban shine shugaban makarantar ya kirani yake faɗa min.


 Murmushi tayi Jidda yadda ta ga Hassan ba ƙaramin farinciki yake ciki  ba ya saba murmushi amma na yau daban ne "Ina maka murna ,Allah ya sa ayi ibada lafiya ya cigaba da bada saa".


"Ameen Jiddatyna".Ya amsa suna shiga cikin parlour,ya faɗa mata a gobe zai je yayi katin dan kasa  don tafiyar tasu nan kusa ce.Labari ya je wa su Umma da baba suka kirasa Allah sanya alkairi baba dubu dari biyu ya basa kyauta ya ƙara a kuɗin da zai tafi dasu Jidda ba ma ta sani ba sai da Hassan ɗin ya faɗa mata ,Anty Ruƙayya ma tayi farinciki sosai har gida tazo Allah sanya alkairi.Ranar da zai tafi aka turo mata su Abdallah sai Amal ma tazo duk abinda take buƙata ya bar mata a wadace.Dukda da akwai yara gidan amma Jidda hakan bai hanata kewar Hassan ba musamman tashin asubah ga aikin gida su Abdallah sai tayi da gaske zasu tayata shima baza su mata me kyau ba ta saba da yadda Hassan yake kalkale gidan ko ita gyaranta baya mata kyawun nasa,yana kiranta sosai su gaisa kullum sai ya tambayeta wace addua zai mata dukda koyaushe yana yi mata,haka ita kaɗai zata zauna wayar ma ta kasa dannawa.Sati biyu Hassan sukai suka kammala umra suka dawo Jidda kwata kwata bata san yau zai dawo ba ya ce mata gobe ko jibi tana ta tsammanin gobe shikuwa yana so yayi surprising ɗinta ne,tana zaune parlour ta gama yiwa su Abdallah faɗa ta korasu sun fita ball daga ita sai Amal Jidda tana danna wayarta Amal kuwa tayi shiru zaune suka ji bugu a ƙofa ta sa Amal ta je ta buɗe ,Amal ta tashi ta fita tana buɗewa ta ga Uncle Hassan da murmushi a fuskarta ta shiga masa sannu da zuwa ya amsa yana dafa mata kafaɗa yana tambayarta yan uwanta fuskarsa ɗauke da fara'a Jidda ta ji muryarsa kamar daga sama ta ajje wayar tana saurin tashi ta leka baki ta buɗe da mamaki sai kuma ta tsuke fuska tana juya baya lallai tayi fushi take yayi dariya banda Amal na wajen da ya sunkuceta sai kawai ya rungumota ta gefe suna shiga parlourn ta na harararsa ya sauke jakar da ya rataya kafada da wata rike hannunsa ta kayansa.


  "Rabbatul baiti ki gafarceni nayi laifi".


  "Kace gobe ko jibi?"


   "Ina son yi miki bazata ne kin haƙura yanzu?"Ka ta girgiza tana zaunawa kujera ɗaya dashi "Ina yan tayin kwanan naki? Ko su na hango can suna ball?"


 "Sun addabeni na korasu waje,yau zasu koma".Ta faɗa hassan na kallonta yayi kewar rigimarta "A yi haka ?Umma zata ce kin kora mata yaranta".


 "Ai daman cewa tayi duk sanda zaka dawo su koma".Yayi murmushi yana kallon Amal da ta kame gefe guda "Amal baki gaji ba ko?yaushe hutun makarantar naku zai ƙare?"Ya tambaya yana maida kallonsa ga Amal da tayi shiru tana zaune gefe "Sati ɗaya ya rage"Ta amsa.


"Toh zaki ƙara mana kwanaki hudu ko?kinga kina komawa sai ki shirin makaranta".Hassan ya faɗa Jidda ta hararesa "Toh ta gaji gidansu take so baka ga ko magana batayi ba".Ya murmusa Jiddan na kallon fuskarshi ta ga ya wani sake kyau tashi tayi ta dauki backpack ɗin ta kai ɗakin shikuma ya ɗauki  akwatin kayansa ya shigo da ita ya rage kayan jikinsa "Garinku zafi"Ya faɗa cikeda zolaya Jidda ta taɓe baki "Yan saudiyya har za a mana gori, kuma ai ana rana can".


"Ana yi amma akwai wani daɗi na daban biiznillah next tare zamu je ina so ki ɗanɗana wannan niimar".

  "Ameen"Ta amsa tana kallonsa wani irin ɗaukan hankali yake mata tana jin kamar ta faɗa jikinsa ta ru gumesa wani irin abu na fuzgarta ta daure kawai tana tashi ta shiga kitchen duba abinda zata dafa don wainar flour ta musu suka ci ɗazu niyyarta ta musu taliya da daddare ko indomie su kwanta amma dawowar hassan lissafinta ya sauya sai dai ta musu jollop rice akwai busashe kifi shi ta gyara ta sa bayan ta haɗa ta koma ɗaki ta ga ya fita masallaci an kira magriba har wani kosawa tayi ya dawo tana jin wani irin abu gameda hassan din da da bata ji sosai abin yake bata mamaki Su Abdallah suka shigo ta kirasu "kunyi sallah?"Yaseer kaɗai ya amsata  Abdallah kam ya hade rai "Kada ka damu yanzu zan baka kudin mota ka tafi iskanci ma wajen zama ya samu ,yaseer zaka siyo min maltina a shago me sanyi".Ta faɗa tana shiga ciki ta ɗakko masa kudin ta bashi ya sayo yana dawowa kuwa ta ɗakko musu kuɗin mota ta sa su tafi gida Hassan ya so su zauna goben  tace a a ai daman ba su da wajen kwana tunda ya dawo Amal dakin wajen zata kwana yau.


 "Zasu tafi ba a basu komai ba Jidda kayan tsaraba sai gobe zasu iso".Ya faɗa Jidda ta kallesa tana ajje masa abincin "Sai a aika musu daga baya".Ta furta ,ƙasa ƙasa yace "Kin ƙara yin wani kyau".Jidda ta yi murmushi har cikin zuciyarta take jin dadin yabon wanda da bata jin hakan.A plate ɗaya ya zuba musu ya fara ci ta tambayesa ko da yaji don tayi kokarin rage attarugu yadda bazai ji yaji baya ce mata babu da ta dandana taji akwai kadan sai da taji ba dadi a ranta daren ranar Jidda da farincikin dawowar Hassan ta kwana.A washegari kayan tsarabarsu ya iso Hassan yawanci siyayyar ta Jidda ce ya siyo mata kaya iri iri ,ya bata ta bawa su Umma da Baba ya siyo masa abin salla da jallabiya da dabino da kayan su zam zam , haka Anty Ruƙayya ma Husna ma sai da ya samu ya aika mata daga nan akwai me zuwa jos ya bayar aka kai mata sauran dalibai nasa ma bai barsu ba da abokansa malamai ba abinda ya tashi dashi duk ya kyautar da komai wasu ma yana jin kunya ya kare be basu komai ba Jidda tace daman ai ba kowa ze samu ba har haushi taji yadda bai bar wa kansa abun arziki ba jallabiya daya sai carbi da wasu litattafai da aswaki.Dawowarsa daga Umrah ba jimawa Hassan ya samu canjin aiki ,kamfanin da abokin nasa yake solar suka nemesa aiki dasu ba ƙaramin sauƙi ya samu ba yanzu baya fitar sassafe a nitse yake shiryawa sai dai yana kai dare wataran bai dawo ba amma samun ya fi na wancen aikin.Jidda kwana biyu abubuwa suka fara sauya mata a hankali take jin damuwa da hassan na shigarta ,wani irin shauqi ya fara fusgarta ko fita yayi ta dinga jin kewar rashinsa a gidan sam bata karɓi cewa soyayya bace a tunaninta kawai zaman tarene ya kawo haka.A da bata damuwa da kiran Hassan a waya amma yanzu tana zaune sai tayi ta dubawa ko zai kira idan ta ga bai kira ba da kanta zata kira ta ɓige da bashi sautu amma zahirin gaskiya muryarsa kawai take son ji da wellbeing nasa.