MATAR GUDA PAGE 43
MATAR GIDA 043
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P43
Karfe ɗaya na rana Ɗalha da Unaisa suka sauko Kaduna,tun sanda aka yi bikinta da Ɗalha sai yau ta fara zuwa gidansa na Kaduna,tun sanda suka tashi daga Kano Ɗalha ya kira cleaning sarvice ya tura masu address ɗin gidansa,Muhsin ya kira ya kai masu makullen gidan kasancewar akwai spere key a wajensa,gidan bai yi wani datti ba hakan yasa cikin kankanin lokaci masu sharan sun gama share ko ina haɗe da morping bayan isowarsu sosai tsarin ginin gidan ya yi mata kyau ga fulawa da aka yiwa gidan ado da shi daga waje,bayan Ɗalha ya yi parking mota Unaisa ce ta fara fita tsayawa ta yi jikin motar tana miƙa,Ɗalha ya fito daga bangarensa tare da buɗe bayan mota yana fito da akwatunan lefen Unaisa,sai da ya buɗe kofar entrance kafin ya dawo ya shiga daukan akwatunan ɗaya bayan ɗaya,nan babban parlour Unaisa ta tsaya tana jiransa tana ƙarewa parlourn kallo,unique set ɗin furniture sun yiwa Unaisa kyau sosai deco ɗin da aka zuba a parlour Unaisa ta shiga bin kowanne da kallo komai na parlour is unique babu wani ado a parlour amma hakan ya yi mata kyau,ba a tara kayan ado masu yawa ba cikin parlour,tana nan tsaye har Ɗalha ya gama shigar da akwatuna har nasa,ita dai sai binsa take da ido wata ƙofa taga ya buɗe wanda tana da tabbacin kofar bangarenta ne,tana nan tsaye har ya gama shigo da akwatunan ɗakinta kafin ta tashi ta bi bayansa,wow Unaisa ta faɗa a hankali bayan shigarta bangarenta parlour ne da ɗakuna huɗu sai kitchen, parlourn yana da girma dai-dai gwargwaɗo, saitin kujera kalar madara da labule kalar gold sune a parlourn Unaisa, sosai kalar ya yi mata kyau yasa parlour looks luxury and mature, dan mini daining table da kujeru baƙaƙe sun ƙarawa parlourn kyau da armashi ga deco da frames da aka yiwa parlourn ado da su,kayan furniture da iyayen Unaisa suka yi mata su aka yi mata jeri a Kano,a can ɗakin Unaisa king size bed Ɗalha ya sa mata, haka ma ɗakinsa sauran ɗakuna biyu babu komai cikin su ba kananun kuɗaɗe Ɗalha ya kashe bangaren Unaisa ba haka ma Amirah duk sabbin furniture ya zuba masu kitchen ɗin Unaisa kowa modern cookware ne non- stick granite,sai die-cast aluminum haka ya zuba mata kayan electroninc na yayi,bayan Unaisa ta gama kalle kalle tana sakin murmushi sosai gidan ya yi mata kyau da komai na cikinsa sun yi mata kyau,zama ta yi bakin gado tare da ajiye gyalen da ta ya yafa a gefe tana daukan waya,bayan Ɗalha ya gama shigar da akwatunan su shopping mall ya nufa saboda babu lokacin zuwa kasuwa jirgin karfe biyar zai bi zuwa legos,siyayyan kayan abinci Ɗalha ya yi wa Unaisa babu abinda bai siya mata ba har kayan ciye ciye sanin kansa ne bata son girki wannan dalilin yasa Ɗalha ya tara mata kayayyakin ciye ciye,Ɗalha da kansa ya shirya duk wani abinda ya kamata ya sa a firiji da kansa ya shirya su cikin firiji sauran kayayyakin ya kai su pantry ya ajiye kowanne a inda ya dace,nan cikin ɗaki ya tarar da Unaisa zaune bakin gado hannunta riƙe da waya tana chating fuskarta dauke da murmushi,waje Ɗalha ya samu ya zauna kafin ya mayar da dubansa gareta har sannan hankalinta na kan waya wannan dalilin yasa ya kira sunanta kai tsaye,a hankali Unaisa ta ɗago manyan idanunta ta zuba masa lokaci guda tana ajiye wayarta sosai take mamakin yadda Ɗalha ya canza dare ɗaya kaman ba Ɗalha da ta sani ba,kafe sa idanunta ta yi tare da amsa kiran da ya yi mata saida ya gyara zama kafin ya ce ''zuwa anjima zan tafi legos wani aiki,insha Allah zuwa laraba zan dawo,ban sani ba ko za ki iya zama ke kaɗai,in ba za ki iya ba za ki iya kiran wata daga cikin ƴan uwanki ta taya ki kwana kafin na dawo'' ya kare magana idonsa a kanta kamar yadda ita ma tana kallonsa,Unaisa ba ta yi tunanin Ɗalha zai tafi ya barta ba, a tunaninta tare za su tafi duka duka aurensu sati biyu amma zai iya tafiya ya barta,a iya sanin Unaisa maza na daukin amarensu na tsawon watanni wasu ma har sai sun haihu amma bata ga hakan daga wajen Ɗalha ba rawar ƙafa da daukin da ya nuna a kanta bai fi kwanaki hudu zuwa biyar ba ya koma wani iri kaman sun shekara goma da aure,a hankali ta sauke ajiyar zuciya can ta ce ''ba damuwa zan iya zama ni kadai'' cike da mamaki Ɗalha ya ce za ki iya?" Unaisa ta gyaɗa kai tare da faɗin ''eh zan iya'' har cikin zuciyarsa ya ji tausayin Unaisa gani yake kamar baza ta iya zama ita kaɗai a gidan ba saboda babu laifi gidan yana da girma sannan ko mai gadi babu a gidan amma Unaisa ta ce za ta iya zama ita kadai,ya ji ina ma yana da damar tafiyar da ita amma hakan bazai yiwu ba,saboda su huɗu aka tura su training,da ya duba reservation ɗinsu ya ga ɗakuna biyu aka kama masu hakan yana nufin mutane biyu zasu zauna a ɗaki ɗaya,sanin kansa ne baza ta ji dadin zama ita kadai ba hakan yasa ya bata damar kiran wata daga ƴan uwanta amma ta ce za ta iya zama ita kadai,numfasawa ya yi tare da ɗaga kafaɗu kafin ya ce ''oky akwai komai a gidan just try as much as you could ki riƙa dafawa kanki abinci l will be away for some days,and Please in da wani abu ki kirani ki sanar da ni in time'' ta gyada kai kawai tare da fadin ''insha Allah'' kallonta ya kuma yi a karo na babu adadi kafin ya ce ''akwai take away a kitchen ki duba'' da to kawai Unaisa ta amsa masa daga haka ya tashi ya fita daga ɗakin zuwa nasa bayan fitar Ɗalha Unaisa ta faɗa tunani can dai ta tashi ta bi bayansa
Ganin sa ta yi cikin ɗakinsa yana shirya kaya cikin wata ƴar karama traveling bag waje Unaisa ta samu ta zauna tana ƙarewa dakin kallo babu wani tarkace cikin ɗakin komai daidai misali aka zuba a ɗakin kallonta Ɗalha ya yi yana zuge zip ɗin jaka ya ce ''ya aka yi me ke faruwa'' shiru Unaisa ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce ''kafin auren mu ka yi min alkawarin zuwa Poland honeymoon'' ta kare magana tana kafesa da ido Ɗalha na tsaye wajen saif ya dauki wasu saitin riga wando zai sa cikin jakar da yake shirya kaya ciki,a hankali ya waigo hannusa riƙe da kayan ya ce ''yes amma ai mun gama wannan magana'' gyara zama Unaisa ta yi ta ce ''eh na sani mun gama maganar amma ai ka faɗa min bayan biki zan iya gayyatar ƙawayena na haɗa masu liyafa'' Ɗalha ya gyada kai lokacin da ya sa kayan cikin jaka ya ce ''eh haka ne l even gave you some money'' Unaisa ta ce ''oky in Allah ya kaimu ranar talata zan gaiyato su zan haɗa masu liyafa kamar yadda ka faɗa,tun da sai Laraba za ka dawo kaga Talata sai su zo'' a natse Ɗalha ya ce ''ba komai Allah ya kaimu'' daga haka ya cigaba da shirya kayyayyakinsa karfe huɗu daidai Ɗalha ya yiwa Unaisa sallama har gate Unaisa ta yi masa rakiya tana masa Allah kiyaye hanya,Unaisa ba ta koma cikin gida ba saida motar Ɗalha ya ɓacewa ganinta,da wani irin sauri ta koma ciki da shigarta ciki wayarta ta dauko ta shiga yiwa bangarenta vidoe ko wanne lungu da saƙo na gidan sai da ta yi masa vidoe har ɗakin Ɗalha bayan ta gama vidoe ne ta shiga group ɗinsu na matan gida ta tura vidoe da caption ɗin _ina Kaduna yanzu haka ko za a samu wata ƴar albarka da za ta zo gidana ta taya ni kwana oga baya nan ya tafi legos sai Laraba zai_ _dawo_ haka ta tura a group,ƙasa da mintina uku mutum kusan bakwai sun ce za su zo ta tura masu address za su kama hanya,shugabar ƙungiyar Hajiya Bilƙisu ta ce bai dace mutum bakwai su je taya Unaisa kwana ba,da kanta ta zaɓi mutum biyu ta ce suje duk a cikin group aka yi hakan,sosai Unaisa ta ji daɗi da ƴan kungiya za su taya ta kwana sanin kanta ne baza ta iya bacci a gidan ita kaɗai ba,da gayya ta cewa Ɗalha zata iya zama ita kadai saboda bata son wata daga dangi ta zo mata gida da sunan taya ta kwana ita ta fin son ƴan kungiyar su,fuskarta dauke da murmushi ta rubuta masu saƙon gayyata liyafa ta rubuta rana da kuma lokaci ta tura a group,cikin abinda bai fi sakan biyar ba Hajiya Bilƙisu ta kirata cike da murna Unaisa ta ɗaga kiran tana ƙara waya a kunneta bakinta dauke da sallama Hajiya Bilƙisu bata amsar sallamar da Unaisa ta yi mata sai ruwan masifa ya riƙa juyewa Unaisa a cewar ta ba Unaisa ya kamata ta tura saƙon gayyata ba manyan ƙungiya ya kamata ta turawa saƙon su kuma su tura a kungiya jiki babu kwari Unaisa ta shiga bawa Hajiya Bilƙisu hakuri da ƙyar dai Unaisa ta samu ta sauko ta ce Unaisa ta kira Hajiya zulfa'u ita zata tsara komai kama daga abinda za a ci da decoration komai ma ita zata tsara sannan yada ta tsara haka za a yi duk sanda suke da wata taro na kungiya ko wata ta haihu ko zata yi aure to Hajiya Zulfa'u ce ke tsara komai,Unaisa ta yi ta mamaki amma babu yadda ta iya ta kira Hajiya Zulfa'u,Hajiya Zulfa'u ce ta tsara duk wani abinda za a ci da wanda za a sha a wajen liyafa ko kaɗan Unaisa bata ji dadin hakan ba amma babu yadda ta iya,Unaisa ta so duk wani abinci su dafa da kansu ita da ƴan kungiya amma Hajiya Zulfa'u ta ce order abinci za a yi,yadda Unaisa ta tsara abinci kala biyu zuwa uku za ta yi shinkafa tuwo alale sai kunu da zoɓo, amma Hajiya Zulfa'u ta ce abinci kala biyar za a yi order farar shinkafa da miya tuwo taliya jollof ɗin macaroni cus cus,ko kaɗan abincin ba su yiwa Unaisa tsari ba amma haka ta yi shiru,su arba'in ne a kungiya Hajiya Zulfa'u ta yi lissafin kowacce zata ci abinci naira dubu sha biyar wanda ya kama naira dubu ɗari shidda sannan akwai maganar drinks da ruwa da za a siya na dubu ɗari biyu za kuma a yanka kaji sha biyar ƙudin su ya kama dubu ɗari biyu da ashirin da biyu,yadda Unaisa ta tsara cikin babban parlourn gidan za ta tara su amma Hajiya Zulfa'u ta ce decoration za a yi a compund ɗin gidan sun fi karfin a tara su parlour kudin decoration dubu ɗari huɗu haka Unaisa ta turawa Hajiya Zulfa'u naira miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu da ashirin da biyu,cikin kuɗaɗen da Ɗalha ya bawa Unaisa naira miliyan ɗaya da rabi abinda ya rage mata naira dubu saba'in da takwas ko kaɗan Unaisa bata ji dadin hakan ba sai dai babu yadda ta iya haka ta turawa Hajiya Zulfa'u ƙudaɗen
SHUUKRAN