MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 44

by @maimunabala209

MATAR GIDA 044



SHUUKRAN/022


YOTA ASSOCAITION




P44





Unaisa ce zaune parlournta inda ta rabka uban tagumi tana jinjina yawan ƙudaden da ta turawa Hajiya Zulfa'u, ko kaɗan bata yi tunanin liyafar zai ci mata ƙudi har haka ba,a lissafin da ta yi bai wuce ta kashe dubu ɗari uku zuwa huɗu ba,sauran canjin ta samu ta yi wani mai muhammanci da su,tana nan zaune har karfe shidda gidan ya yi shiru baka jin motsin komai sai kukun tsuntsaye kasancewar yamma ta yi,har an kira sallar magrib Unaisa na nan zaune da kyar dai ta samu ta tashi ta yi wanka kafin ta yi sallah,bayan ta idar da sallah ne ta ji kaman ana buga gate ɗin gidan jiki babu kwari ta tashi ta nufi hanyar fita daga bangarenta,tun bata kai ga buɗe kofar ba ta jiyu muryar Jamila da jaleela( Jamila da Jaleela zaurawa ne masu ƙananun shekarun sa'an'nin Unaisa ne basu wuce shakara ashirin da biyu zuwa da uku ba a duniya,su biyun sun kasance ƙawaye ne na kut da kut duk wacce take ƙungiyar matan gida ta san ƙawancen su,su Hajiya Bilƙisu ta tura taya Unaisa kwana)jiki babu kwari Unaisa ta buɗe masu gate Jaleela ta daƙa tsalle tare da rungumar Unaisa tana faɗin ''amarya mai lokaci'' tana washe baƙi ita dai Jamila tana tsaya gefe tana kallon Jaleela yadda ta rungume Unaisa tana ta murna fuskar Jamila dauke da murmushi ta ce ''dan Allah ki cika ta haka ya isa,haba irin wannan runguma sai ki sa ta ciwon jiki'' sakin Unaisa Jaleela ta yi tana mayar da dubanta ga Jamila ta ce ''kya ci kan ki'' ita dai Jamila bata ce komai,har sannan fuskarta dauke da murmushi,daga haka Unaisa ta ja hannun Jaleela,Jamila na biye da su,nan parlourn Unaisa Jamila da Jaleela suka ya da zango sun shiga bin gidan da ido suna yaba tsari da kyawun bangaren Unaisa da furniture ɗinta,ita dai Unaisa jin su kawai ta yi ta wuce kitchen ta dauko masu ruwa da lemo mai sanyi a firiji ta dire shi gabansu,duk suka miƙe kafa sun sha ruwa da lemo Jamila ce ta mayar da dubanta ga Unaisa take ƙokarin jona masu TV ta ce ''amarya ba ki yi girki bane? ki sa mana abinci yunwa muke ji'' Unaisa idonta kan TV ta ce ''wallahi babu abinda na dafa ɗazu fa muka dawo gaba ɗaya a gajiye nake,wata ta shiga ta dafa maku duk abinda ya sauwaƙa,ba zan iya ba gaskiya'' tun bata kai ga ida zancen ta ba Jamila ta yunƙura ta tashi ta nufi hanyar kitchen tana fadin ''ba laifi ki bane mun zo gidan ki shi yasa'' bayan shigar Jamila kitchen Jaleela ta bi bayanta nan sun shiga yaba kayan kitchen ɗin Unaisa ita dai Unaisa shiru ta yi tana jinsu daga parlour har sannan jikinta a mace,muryar Jamila ta jiyo daga kitchen inda ta ce ''ke Unaisa kin tabbata za ki iya zama cikin kungiyar mu kowa?miji irin na ki da bai rage ki da komai ba bafa zai bari ki zauna cikinmu ba duba yadda ya cika maki kitchen da kayan abinci,ga kifi ga nama ga kaji cike cikin firijin ki,mazaje irin mijin ki basu ciki ɗaga wa mace ƙafa ba,a iya fahimta ta in za ki zauna cikin mu to tabbas za ki samu matsala daga wajen mijinki har da dai ban  san halaiyarsa'' banza Unaisa ta yi mata kamar bata ji abinda ta faɗa ba jin Unaisa ta yi shiru bata amsa ba yasa Jamila tunanin ƙila Unaisa bata parlour ne,abinci mai rai da lafiya Jamila ta dafa da taimakon Jaleela ita dai Unaisa tana nan zaune cikin parlourn tana kallo harda hankalinta baya kan TV amma haka ta ƙorawa TV ido har suka dafa abinci sun sa mata a plate kamar yadda suka zubawa kansu,nan ƙasan parlourn suka zauna sun fara cin abinci sun ci kusan rabi Unaisa na nan zaune ko kallon inda Jaleela ta ajiye mata abinci ba ta yi ba ta yi nisa cikin tunanin ƴan ƙudaɗenta da ta turawa Hajiya Zulfa'u Jamila ce ta mayar da dubanta ga Unaisa can ta kalle plate abinci ta ga ko taɓa abincin Unaisa ba ta yi ba mayar da dubanta ta yi ga Unaisa ta ce ''lafiya kuwa Unaisa mai yasa ba ki ci abinci ba'' Jaleela ta yi murmushi tare da faɗin ''ko dai an gamu ne amarya'' duk suka fashe da dariya,numfasawa Unaisa ta yi kafin ta ce ''bana jin yunwa'' ta yi magana a sanyaye,baki sake Jamila ke kallon Unaisa can ta ce ''kin ƙoshi amma kin yi shiru ba ki faɗa ba kin sa mun ɓata plate'' ta ƙare magana tana tura nama a baki numfasawa Unaisa ta yi a karo na babu adadi Jamila da Jaleela na cigaba da cin abincinsu can dai Unaisa ta ce ''wace Hajiya Zulfa'u cikin ƙungiyarmu?"



















Kafe Unaisa Jaleela da Jamila suka yi na wasu ƴan sakanni can dai Jamila ta gyara zama ta ce ''me ya faru ki ke tambayar matsayin Hajiya Zulfa'u?" shiru Unaisa yi na wasu ƴan sakanni kafin ta shiga yi masu bayani yadda suka yi da Hajiya Bilƙisu da kuma abubuwan Hajiya Zulfa'u ta ce za a yi ranar taro bayan Unaisa ta idah zancen ta ne Jamila da Jaleela sun shiga yi mata dariya sai da suka yi mai isarsu kafin Jaleela ta gyara zama tana mayar da dubanta ga Unaisa ta ce ''Hajiya Zulfa'u ita da Hajiya Bilƙisu su suka kafa kungiyar matan gida sun ɗin ƴan uwan juna ne uwa ɗaya uba ɗaya suke mahaifinsu babban ɗan kasuwa ne,Hajiya Bilƙisu da Hajiya Zulfa'u sun tashi cikin gata da so da kauna daga mahaifinsu lokacin da sun isa aure mahaifinsu ya aurar da su ga yaran gidansa,da fari mazajensu sun riƙesu tsakani da Allah hakan yasa mahaifinsu raba dukiyarsa gida uku kashi ɗaya ya bawa mijin Hijiya Bilƙisu ɗaya ya bawa mijin Hajiya Zulfa'u kashi ɗaya shi kuma ya riƙe ya cigaba da juyawa,cikin ikon Allah dukiyar da mahaifinsu ya bawa mazajen su sun ɓunƙasa daga nan matsalar ta fara mijin Hajiya Bilƙisu ya mata saki biyu saboda ya ce zai ƙara aure ta ce bata amince ba,Allah bai bata haihuwa ba sun yi aure tsawon shekaru bakwai bata haihu ba wannan dalilin yasa ya ce zai ƙara aure ita kuma ta ce bata amince ba ta yi ta masa rashin mutunci bayan ya yi mata saki biyu ta dawo gidan mahaifinta ya je ya yi biƙu ta dawo, bayan ya yi aure amarya ta tare,amarya bata tsallake watan aurenta ba ta dauki ciki nan hankalin Hajiya Bilƙisu ya ƙasa kwanciya ta hana amaryar sukuni harda ba ta yi mata komai ba hasilama tsoron Hajiya Bilƙisu take,dalilin da ya sa Hajiya Bilƙisu ta sa amaryarta gaba shi ne tun sanda amarya ta dauki ciki hankalin mijinsu ya koma kan amarya ya riƙa yiwa Hajiya Bilƙisu wulaƙanci da cin mutunci karshe dai ya cikasa mata saki ɗaya da ya rage,tun daga wanann ranar Hajiya Bilƙisu ta dauki kuɗirin kwatowa mata ƴanci duk wacce miji ke musguna mata ko wulakanta ta da ta shiga kungiyar matan gida za a koya mata yadda zata saita miji, sai dai wasu mazajen basu iya jure canza hali da matan su ke yi lokaci guda,wannan dalilin yasa za ki ga da yawa ƴan kungiyan zaurawa ne wannan kenan ita kuma Hajiya Zulfa'u Allah ya jarabcita da  miji mashayin giya da bin matan banza a yadda muka samu labari Hajiya Zulfa'u ta zauna da mijinta tsawon shekaru amma bata taɓa faɗawa kowa halin da take ciki ba har mahaifiyarta,Allah ya albarkacita da haihuwan ƴaƴa biyu mata wata rana bayan mijinta ya dawo daga yawon dare ya far wa ƴarta ƴar kimanin shekaru sha uku a duniya ya jima yarinyar raunuka sosai kasancewar ya je mata ba a hayyacinsa ba kwananta uku a asibiti Allah ya karɓi rayuwarta a ranar da aka yi mata addu'ar bakwai Hajiya Zulfa'u ta nime saki wanda mahaifinta ya tsaya mata sai da mijinta ya sake ta bayan ta fita iddah ta haɗa kai da yayarta Hijiya Bilƙisu sun kafa wannan kungiya namu mai albarka,Hajiya Bilƙisu ce shugaba Hajiya Zulfa'u mataimakiyar ta to kin ji matsayin Hajiya Zulfa'u '' shiru Unaisa ta yi tana ƙara nazari kan maganganun da Jaleela ta faɗa mata can ta numfasa tare da faɗin ''abin da ya fi damuna shine kuɗaɗen da na kashe a yau,a ce uni guda na kashe sama da miliyan kai a gaskiya hankalina ya tashi'' baki sake suke kallonta kafin suka fashe da wata iriyar shu'umar dariya sai da suka yi mai isarsu kafin Jamila ta ɗago har sannan fuskarta dauke da murmushi ta ce ''ke da ki ke cikin ƙungiya ina ke ina damuwa da rashin kuɗi,kuɗaɗe sai kin ƙi in har kina cikin wannan kungiya'' cike da rashin fahimtar inda zancen Jamila ya nufa Unaisa ta ce ''albashi ake biya?" duk suka yi dariya Jaleela ta ce ''babu albashi amma dai za a daura ki kan hanyar da za ki riƙa samun kuɗaɗe a saukaƙe'' cike da ƙaguwa Unaisa ta ce ''dan Allah ku yi min bayani yadda zan fahimta'' plate ɗin da suka ci abinci Jamila ta dauka tare da nufar hanyar kitchen ta ce ''kar ki ji komai amarya zuwa ranar talata za a maki bayani dallah dallah ba za ki ji komai daga bakin mu ba'' ta kare magana tare da shiga kitchen yunƙurawa Jaleela ta yi tare da miƙewa tsaye tana faɗin ''kwantar da hankalin ki zuwa jibi in Allah ya kaimu za ki ji bayani daga bakin Hajiya Bilƙisu'' daga haka ta wuce kitchen tare da daukan ruwan gora,har dare Unaisa ta kasa samun sukuni duk yadda ta yi da Jaleela da Jamila su faɗa mata wani abu sun ƙi,lokacin bacci Unaisa ta cewa su Jamila su kwanta ɗakinta ita zata kwanta ɗakin Ɗalha fir sun ƙi cewa suka yi sun fi son kwanta ɗakin Ɗalha ita ta kwanta ɗakinta in kuma hakan bai yi mata ba to sai dai dukkan su ukun su kwanta ɗakinta,babu yadda Unaisa ta iya haka ta hakura ta kwanta tare da su cikin ɗakinta, misalin ƙarfe goma na dare Unaisa na kwance bacci ya kauracewa idanunta ta kore bed side drower da ido, wayarta ta shiga ƙara hannu ta kai ta dauki wayar ta ga Ɗalha ne ke kira kafe wayar ta yi da ido har kiran ya katse bata ɗaga ba,washe gari Jaleela da Jamila ne sun shirya abin kare Unaisa dai daurewa kawai take da kyar ta samu ta ci abin karen ba dan tana jin dadin sa ba,haka uni ranar Unaisa ta kasance kamar wacce aka aikawa saƙon mutuwa 














SHUUKRAN