SHI SO DABAN YAKE

Babi na goma sha shida

by @dijensy


16



Yau ta kama alhamis da tsakar rana ta ga shigowarsa tana zaune parlour da makulli a wajensa ya buɗe ƙofar gidan shiyasa bata ji bugu ba yana shigowa a parlour ya tarar da ita tana shingiɗe ta tashi zaune tana amsa sallamarsa ya ƙaraso yana zaunawa gefenta "Washh"Ya furta  yana kallonta "Bacci kike na tasheki?"Ya tambaya ta girgiza kai tana kallon hannunsa riƙe da file gajiya ta nuna a fuskarshi  "Sannu da zuwa"Ta faɗa ya amsa yana murmusawa ya buɗe file da ke hannun nasa ya ciro doguwar takarda yana miƙa mata ta karɓa tana dubawa ta ga takardar admission nata ne da ya mata printing jamiar bayero  fuskarta ɗauke da murmushi ta ke kalla tana karantawa kafin ta ɗago ta kallesa "Sannu nagode daga wajen aikin ka je ka ciro?"Hassan ya gyaɗa mata kai "Yau banyi zaman wajen aiki ba kasuwa naje marketing nayi zagaye a  garinnan kasuwa uku na shiga gashi na gamu da wani ɗan albarka ya so gudar min da waya"Jidda ta zuba masa ido tana saurararshi "Ta ya hakan ya faru?"


"Ina tsaye ya zo ya sameni wai ba ɗan gari bane ya zo wayarsa ta mutu ba chargy yana son kiran mutanen gidan da ya zowa nikuma ban kawo komai ba na bashi kawai ya gudu har na fitar da rai ni ban bisa ba ashe wasu matasa sun bisa suka kamashi suna dukanshi nidai na basu hakuri wayata da suka karba gurinsa suka bani na tafi"Jidda ta kyalkyale da dariya bata shirya ba  tana kallonsa "Gaskiya kaima Hassan kamar baka da wayo? kawai a zamaninnan sai ka yarda da mutum sai kace kai kadai ne a kasuwar ya ari ta sauran mana lallai kuma ka ji tausayinsa ka yafe masa?"


Murmushi yayi yana kallonta "Akan waya sai su kashe shi ? nawa take abin duniya ce fa Jiddaty".Ya faɗa ita dai baki ta taɓe tana jinjina kai tana tashi ta zubo mashi abinci "Ko zaka fara wanka?"Ta tambaya  yana kallonta yaji daɗin tambayar yana murmushi yace  "Ɗa'am" Jidda tayi murmushi jin ya faɗa da larabci kuma kalmar tayi daɗi a bakinsa tana buɗe warmer ta fara zuba mashi Hassan kuwa sai kallonta yake ta ɗago "Mene?"Ta tambaya yayi murmushi yana girgiza mata kai ya sauko ya zauna carpet ɗin kafin ya fara ci.Jidda yana ci tana satar kallonsa daga zaune da take kan kujera  da ya ɗago sai ta janye idanunta tayi kamar waya take dannawa yana gamawa da kansa ya fita da kwanon yaki bari ta dauke ya komo ,ɗaki ya wuce yana rage kayan jikinsa ya shiga wanka bayan fitowarsa ta shigo ɗakin ta tarar yana ƙarasa shiryawa ta zauna kan katifar tana ciro wayar daga charge da buɗe passcode ta ga alert notification ta duba tana ganin transfer da Hassan yayi mata dubu ɗari kallonsa tayi ya zauna kan darduma yana buɗe Al-Qurani zai fara karantawa "Kuɗin mene ka turo?"Ta tambaya ya ɗago yana murmushi "Kiyi ɗinki a cikin kayanki ragowar ki siyayya jaka da takalmin makaranta".


  "Bayan zaka biya kuɗin registration kuma? yayi yawa ai wannan"Ta furta 'kwalla na tarar mata a ido lokaci guda tana kallon murmushin fuskarsa ta rasa gane wani irin mutum ne shi Hassan koyaushe baya gajiya da hidima ? "Babu yawa Jiddaty Allah sa ki fara saa"Ya furta ta amsa da ameen kawai jikinta a sanyaye "Nagode Allah ya ƙara buɗi".Ta faɗa wani irin abu ta ke ji akansa lokaci guda ya soki zuciyarta gameda dashi godiyar tata ma tana jin tayi kaɗan zuciyarta na faɗa mata da me zata saka mashi yayi farinciki ?wani irin tausayinsa taji tana ji damuwarsa da take ji a kwana biyun ta ji ta ninka kowacce wani irin shauqi ya lulluɓeta ta kwanta tana juya baya tunani take kwakwalwarta na tariyo mata abubuwa da dama da ta aikata masa na rashin dede tun daga ssnda ta shigo gidan zuwa ranar yau ,duk kiyayyar da take masa da rashin amanna da aurensu ta ji ta nemesa ta rasa katangar ta rushe sabon baqon yanayu ta ke ji lullube a zuciyarta.Karatunsa ta cigaba da saurara na tsahon lokaci ba abinda ke yawo a zuciyarta sai datasanin abubuwa da ta dinga yi masa marasa kyau duk ya shanye ya jure tana jin hassan bai cancanci haka ba ,har ya gama ya xo ya kwanta bata fasa tunani da saƙe saƙe ba kafin daga baya bacci ya ɗauketa.Washegari ƙarfe tara da rabi na safe Hassan ya gama shiryawa bayan sun karya Jidda ta kallesa yana goge takalminsa wayarta rike hannunta daya hannun tana wasa da yatsun idanunta a kansa "Yau ma zaka iya kai wa dare ko?"Ta tambaya "Eh toh ya danganta mai zan taho maki dashi?"Ya amsa yana ƙarewa da tambayarta fuskarsa da fara'a.


 Kai ta girgiza "Ba komai".Ta amsa ya kalleta yana murmushi "Sai na dawo"Ya faɗa Jidda tashi tayi ta bi bayansa daga ƙofar parlourn ta tsaya tana jingina jikinta "A dawo lafiya"Ya juyo yana kallonta ya amsa da ameen ya buɗe ƙofar yana fita ya ja kofar ta gaban gidan ta rufe Jidda ta juyo tana dawowa ɗaki saurin daukan wayarta tayi tana lalubar number cake vendor da ta sani ta kirata bayan ta ɗauka sun gaisa Jidda ta fara magana.


"Bento cake nake so pls zan samu yau ko wajen asr?"Ta tambaya ta ce mata eh kafin ta tambaya mai za ta rubuta a kai Jidda tayi murmushi "Ki rubuta I LOVE YOU".Cake vendor tayi dariya jin alamar Jidda a kunyace ta faɗa "Idan akwai samosa rap ina so"Jiddan  ta faɗa cake vendor ta tambaya guda nawa ta gaya mata nan take ta tura mata da kudin ,zaunawa tayi ta fara tsara abubuwan da zata buƙata na abinda take so shirya yau ɗin ,lekowa tayi waje ta kira almajiri tana bashi cefanen abinda take so ta rubuta masa don tasan wasu bazai iya furtawa ba  "Bakin titi zaka"Ta jaddada masa ya amsa da toh ya tafi ,da fitarsa ba jimawa ya dawo mata da abubuwa da ta bukata.Da kanta ta je shago ta siyo lemon exotic da berries 5alive ta dawo duk abinda take yi tana kula da lokaci lafiyayyan pride rice  ta dora a yayinda ta kwaba cincin tana addua Allah sa ta yayi daɗi aikinta ta duƙufa yau ko ta kan wayarta bata bi ba da yamma bayan ta kammala girke girkenta ta siyo ƙanƙara ta zuba cooler ta sa drinks ɗin nan ta sake gyara gidan ta saka turaren wuta ko ina ya dau kamshi me delivery ya karaso da bento cake nata da samosa nan da nan ta soya ba sosai yake da yawa ba ta gama shirya komai a parlour wanka ta shiga ta fesa cikin lace mekyau ta shirya tana yin dauri ta tsuma jikinta da turare  ita kaɗai take ta murmushi tana kallon madubi bata taɓa zato akwai rana irin yau da zata ji irin so haka ga Hassan ba a jikin mudubin take gwada yadda zata fara magana tana son ta bashi hakuri tana so ta bayyana masa yadda take jinshi a ranta zata mashi godiyar kyautatawar da yake mata hannunta ta kalla ba ko ƙunshi ta ji inama akwai damar yi sai dai ta tara gaba daman tayo alwala da tayi wanka sabida haka ana maghriba ta yi sallah ta ninke hijab din tana jinta kamar wata sabuwa amarya da aka kawo yau ,ita kadai tana ta murmushi ta ɗauki wayarta notification ta kalla na miss call nashi kusan tun ƙarfe uku da rabi ya kirata ba ta gani ba ma ganin yanzu lokacin dawowarsa ya kusa yasa bata bi kiran ba  tana tunanin ma bai wuce ya tambaya mai zai taho mata dashi ba ita kuwa burinta kawai ya dawo ya ga wannan bazatar da zata mashi a daren yau tana ta hango fuskarsa ya zai  yi? buɗe camera wayarta tayi tana ɗaukan hotuna daga baya ta ajje tana yi tana kallon lokaci daman ta ayyana zai kai dare din zaman jiransa ta zauna yi har isha tayi ta tashi tayi salla bata son sai ya dawo tayi yau bata son komai ya katse masu lokacin su.Bayan ta fito daga ɗaki tana zama taji kwankwasa kofa.Tashi tayi tana fita don ta gama ayyanawa Hassan ne ta buɗe tsaye ta ga ya Sadiq dukda ba hasken fitila waje amma ta ganeshi da wuri ko da yanayin jikinsa don yana da jiki kaɗan.


"Ya sadiq"Ta furta a zuciyarta ta shiga tambayar me yake yanzu anan a wannan lokacin daman taji Anty baby tace ya shigo gari amma ba wannan lokacin tayi tsammanin zuwansa ba "sannu da zuwa"Ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe ƙofar da kyau don ya shigo dukda ba wani maraba tayi da zuwan ba yau ɗinnan ita da Hassan kawai ta tanadar musu bai ko motsa daga inda yake tsaye ba "Ba shigowa zan ba Jidda ,baba ne baya jin daɗi yana kiranki hijab kawai zaki ɗakko ki fito".Wani rasss ta ji a zuciyarta wani tsoro ya shigeta a lokaci guda sanyi har cikin ƙanta taji tayi weak "Ya Sadiq me ya sami baba?"


  "Bashida da lafiya ne kawai yake son ya miki magana ki je ki ɗakko hijab".


"Ya Hassan zai dawo in fara kiransa na faɗa masa".Ta furta tana barin ƙofar a buɗe ta juya cikin gidan jikinta har wani rawa yake ta ɗau wayarta tana shiga ɗaki ta buɗe sif ta curo hijab laluben number Hassan ta ke ta na son faɗa mishi ta fito parlour bayan ta sa takalmi har zuciyarta take jin wani abu ya faru da babanta,sau biyu ta kira a tsaye taji layin fitowa kawai tayi tana kallon kayakin ciye ciye a parlour ta rufe kofar parlour ta manta da makullin gidan sai da ta koma ta fito tana cigaba da kokarin kiransa ya Sadiq ɗin ya miƙa hannu yana tayata rufe ƙofar gidan ta saka mukulli kafarta sanyaye ta ke binsa ta ga yayi gaba bai ce mata komai ba ya tsaya jikin wata mota tana tunanin da abokinsa yake ya buɗe mata gidan baya ta shiga tukun ya rufe ya kewaya Jidda fargabar da take ji yasa ko gaishe da na motar bata yi ba Sadiq ya shigo shiru kawai ya ratsa motar cikin kunnenta take jin bugun zuciyarta na amsawa hannunta kan wayar tana shiga whatapp ta yi typing a chat nasu da hassan ta rubuta mashi cewa ya sadiq yazo gidan baba bashida lafiya sunyi kiranta'.Har suka hau titi ya sadiq bai magana ba shima abokin haka kuma ta kasa sake iya buɗe baki har suka iso gidansu sadiq ya fito ya kewaya ya buɗe mata ƙofar ta fito tana takawa gwiwarta ba laka ba wanda ta gani daga ƙofar gidan suka shiga ciki parlourn Umma suka shiga tana gaba a sanyaye tayi sallama ta hangi Umma zaune kan darduma ta jingina da kujera  ta ɗago irin kallon da Umma ke mata ya kai mata wani irin saƙo na abin tsoro ya tsarga mata "Umma meya sami baba?ina yake ?"Ta tambaya muryarta na karyewa ta durƙusa kan gwiwoyinta Umma ta riko ta tana kamo hannunta tasa ta taso ta kasa yin magana kai ta girgiza mata kawai. "Babanki yana asibiti an mashi waya Hassan suna asibiti ,ya gamuda hatsari shine suka je asibiti...."Jidda kawai kallon Umma take tana haɗa kalmomin maganganun da ƙyar fuskarta da damuwa ƙarara hannayenta kan kafaɗin Jidda ta juyo tana kallon Ya Sadiq yana juyawa ya fita bayan ya kara waya kunnensa ya fita tsakar gida.


  "Shiyasa baya ɗaga kirana kenan"Jidda ta furta da wata murya ta dora wayarta a cinya tana kan chat ɗin da ta masa bai reply ba wani abu take ji na gaba da tsoro da ya sa ta dena jin wani abu a jikinta numfashi kawai take idan ta buɗe bakinta zata yi magana sai ta ji ta kasa Umma ta ga ta tashi ya sadiq da ke kofar ɗakin ya kirata ta fita a sanyaye Jidda ta bita da ido.Umma ya sadiq ya kamo hannunta suka bar kofar ɗakin ya girgiza mata kai "Suna hanyar dawowa sun tabbatar musu ya rasu".Ya sadiq ya faɗa da wani murya mai nuna firgici Umma ta yi kasa da kai ta dafa sadiq tana girgiza kai "Innalillahi wainna ilaihirajiun".Ta faɗa da ƙaramin sauti hijab ɗinta ta sa tana rufe fuskarta sadik ya kama hannunta yana ƙoƙarin ya ga ya sata tayi shiru ya yi sitting room da ita.Jidda kamar an dasata a wajen ta kasa tashi ta kasa yin komai tsahon mintina ya sadiq ya fita yana tarar da baba sun dawo a mota abokin baba ya fito sai baba yana tahowa a sanyaye sadiq ya tareshi "Sadiq,fa Hassan kwana ya ƙare Hassan sai haƙuri ya koma ga mahaliccinsa ".Sadiq ya girgisa kai yana furta innalillahi wainna ilaihirjiun baba ya shiga gidan daurewa kawai yake amma a rikice yake da tashin hankali.A sitting room ya sami Umma tana kuka ya shiga tambayarta Jidda ta taso tana nufar parlour baba ya dakatar da ita "Bar ni na sameta".Ya faɗa Sadiq ya kamo hannun Umma Anty baby tana tsaye bakin corridor kofar ɗakinta firgici da tsoro ya kasa sawa ta fito Umma da ta hangota ta karasa inda take a tsaye "Hassan kwana ya ƙare bansan me zan faɗawa Jidda ba Baby".Ta faɗa tana ƙara sautin kukanta.Shigowar baba parlourn Jidda ta ɗago tana kallonsa ya tsaya kanta "Jidda".Ta na kallonsa kawai hannu yasa ya dafa kafaɗarta ya sunkuya ƙasa ƙasa yake mata wasu maganganu da bata gane wajen zamansu ko alakarta dasu ba abu ɗaya ta sani shine Hassan yana raye kuma dawowa kawai zai daga unguwa ta mashi albishir da yakamata ace ya dade ya ji daga gareta."Allah ya fi mu son shi ,komai kika ga ya faru akwai dalili adduarmu shi yafi buƙata a yanzu kuma in sha Allah ya samu rana mai kyau jumaa Allah ya masa rahama ya mana".Jidda ta kalli Baba wani murmushi ya subuce mata "Wani Hassan baba? Ba dai hassan dina ba".Ta faɗa sai kuma wani abu ya bigeta murnushinta ya juya zuwa kuka hawaye  yana gangarowa daga idanunta Umma ta shigo daga ita har Anty baby kuka suke suka zo suna zama kusa da ita hadi da fara lallashinta ta tashi da sauri tana rikowa baba kaya tana girgiza kai "Ba abinda ya samu Hassan baba ba abinda ya samesa ku fada min gaskiya,meyasa kuka kawo ni nan Hassan yana gida yana jirana ya dawo ba abinda ya samesa baku fahimta bane Hassan fa".


  "Ni da abokina mun je mun ɗakko gawar Hassan yanacikin mota Hassan baya tare damu kiyi haƙuri Jidda ƙarar kwana ce ba wanda yake shirya mata".Ta ja baya tana fashewa da wani matsanancin kuka ta sulale ƙasa.



    

       Anty baby na zaune gefenta tana kwance ta ga ta motsa ta ɗago tana kallon Jidda tana buɗe idanu ta  sauke a kanta ganin tashi take son yi Anty baby ta taimaka mata ta zauna jikinta take jin ya mugun mata nauyi ta kalli Anty baby ta gane dai a gida take kuma ba mafarki bane ta kalli Umma kan sallaya nan take ta fashe da kuka  "Idan mafarki nake natashi Anty baby me nake yi anan?ina Hassan?"Ta shiga tambaya cikin kuka Umma ta idar da sallahr subh ta taho wajenta Baba da ya Sadiq suka kwana da gawar Hassan sai da asubahun fari ɗinnan ya tafi ɗakko Anty Ruƙayya da bata san me ake ciki ba ya faɗa mata mugun labarin da ya warware mata tunani suka taho gidan su Jidda har lokacin ta kasa gasgatawa ba Hassan ganin malamin Hassan da ya haɗa aurensa da Jidda sai shugaban makarantar ya sa ta tabbatar da rasuwan Hassan ta rasa ina zata tsindima kanta ta samu sukuni yan uwansu Hassan na kusa tuni labarin rasuwan ya samesu baba ya tambaya ina suke so a mishi sallah a kaishi suka ce sun amince a mashi komai nan ɗin.Jidda sam bata cikin hayyacinta sai surutai take Anty Baby ta zauna da ita da Anty mairo ɗakin Umma Anty Rukayya suna parlourn zaune da sauran mutane.An haɗa gawar Hassan baba ya sa sadiq ya kira Jidda suyi sallama ya dubi baba yana so ya faɗa masa Jidda ba a hayyacinta take ba "Kaje ka kirata  zata zo".Ya sadiq ya tashi yana zuwa ɗakin Umman ya faɗawa Anty mairo ta kalli a yadda take Anty baby ta matso kusa da  kunnenta ta raɗa mata "Zaki so a kaishi ba ki masa sallama ba ? ko addua kin masa ?hakan kike son shi?"Shiru tayi bata sake cewa uffan ba ta kalli Anty baby da wani yanayi ta kalli ya sadiq kuka ya subuce mata fiya da na koyaushe yayi kokari ya karasa inda take yana kamo hannunta ta tashi da kyar take takawa da taimakonshi suka fita suna wucewa parlourn Umma babu wanda hankalinsa bai tashi ba irin yadda Jidda ke sheshekar kuka gidan ya  ɗau shiru Anty Rukayya ta cusa kanta cikin Hijab Amal da ke gefe ma kuka take.Jidda ta sunkuya gaban gawar Hassan  tanakallon fuskarshi da rabonta da ita tun jiya da safe bayan fitarsa ta shiga girgiza kai "Bamu yi haka da kai ba ? Baka yin abinda zan ji haushi hassan meyasa zaka min haka meyasa zaka tafi ka barni?"Ta faɗa tana fashewa da tsanancin kuka tana ɗora kanta a jikinsa baba ya mata magana yace addua zatayi ba kuka ba da ta buɗe baki kuka sai ya cin mata a ciki ciki take adduar tana kuka bata tashi rikirkicewa ba sai  ganin zasu daukeshi Umma ta tasota tana riko ta suka koma ɗaki  a lallai baza a tafi dashi ba ta faɗi kan tile ta kwanta tana gunjin kuka "Jidda ki bari kukan bashida amfani kamar adduar da zaki masa".Anty baby tafaɗa muryarta a karye Umma ta zauna ta ma rasa wani rarrashin zata yi mata kawai ta zuba mata ido.Anty baby na kallon Jidda cike da tausayi ita da bata damuwa da Hassan yaushe son shi ya shiga zuciyarta haka? Take faɗa a ranta dukda dai tasan mutuwa ta wuce gaban komai.Su baba bayan sun kaishi makwancinsa suka dawo gida suna karbar gaisuwa ya kira Umma ya faɗa mata sun tattanbaya Hassan bashida wani bashi kansa wajen mutanen sa da yake muamala dasu tace toh alhamdllh,waya ya mikawa Umma ya ce ta bawa Jidda ta karba ta shiga ɗaki ta na kwance kasan tile har yanzu taki sauraran kowa Umma ta durkusa ta sa mata a kusa da hannunta da ta rufe fuskarta dashi Umma  ta tafi Jidda tana motsa hannunta ta kalli wayar Hassan da ta ajje mata ta sa hannu tana ɗauka ta jujjuyata tana kunnata ta kawo ta tabbatar wayar Hassan ce da ganin walpaper ta cusa ta cikinta tana kewaye hannunta ta sake takurewa waje daya ta cigaba da kuka mai sauti.......



     

                         ********


      A dai dai gefen titi motar tayi parking a yayin da matashin ya fito daga ciki ba ƙaramin matashi bane zaka iya sa shi a matakin late 30s a hankula bayan ya rife murfin motar ya ke takawa yana tafiya yana kallon kan kwaltar yana ganin tsirarin ganyayyaki da suke nuna alamar haɗari ya auku da yawanci ake ajjewa kan kwalta kwakwalwarsa na tariyo masa da daren jiya da bazai iya tantacewa zahiri bane ko mafarki yake ya rintse idanunsa yana mai dafe goshinsa wani sarawa da kansa yayi ,rumfar me shayi ya hanga da ke gefen titi daga gaba yayi yar tafiya yana ƙarasawa wajen mai shayin ya ɗago yana kallonsa yayinda yake zuba kayan shayi tukunyar "Barka da asubah".Ya gaisheshi kai kawai ya giɗa kamar yana tausayin kasa ya karasa rumfar ya shiga bench da ba kowa ya zauna daya benche akwai wasu matasa biyu ɗaya na shan shayi da biredi daya kuwa indomie yake ci suna hira da ta shafi rayuwa "Mai gida me za a saka? "Ya tambaya yana kallonsa ya ga har lokacin bai yi magana ba ganin matashin idanunsa ya sauka kan ledar indomie yasa ya fara tunanin ko kurma ne "Indomie da kwan za a sama ?"Ya ga ya giɗa kai mai shayin ya fara kaɗa kwai suka cigaba da hirar rayuwa mai shayin ya kawo zancen haɗarin jiyan yana faɗin "Jiya fa anan nan kamar kiftawar ido da magriba ɗinnan idona bai kai wajen ba kawai muka ga wani akwance mota ta kaɗe sa nan take aka zare ran ta yadda zaka gano kawai karar kwana ce bawan Allah nan ko jini bai fita a jikinsa ba yana kwance ne kawai kamar ace tashi".Mai shayin yake faɗa.


"Allahu akbar ,kaji ajali mai motar fa ? Shi bai gani  bane ya shigo?"Ɗaya cikinsu ya tambaya.


  "Ina fa mai mota da ba ma a ganshi ba ya tafi ni bana jin wanann mutumin yasan ya kade mutum fa Allah yasa da wani dan sanda ya zo wucewa a machine nan aka yi asibtii dashi nidai mutuminnan nasan ya rasu shi dai ɗan sanda ya sa dole aje asibiti a tabbatar da aka kira  yan uwansa suka zo wajen"


"Kai ba wani bai sani ba wallahi haka suke azzalumai irinsu nadayawa su kade mutum su ƙara gaba kamar sun kashe dabba  wani hisabi sai a lahira kawai tsayawarce bazai ba ai wasu basu dau rai a bakin komai ba".


 Wani irin kokawa yake da numfashinsa yana jin wani  yanayi na taso masa suka ga ya mike matashin ba tare da yace komai ba ya zaro kudi a wallet nasa ya mika masa 3k yana ficewa daga rumfar mai shayin ya bisa da kallo kafin yace me yaga yayi nisa "Kaga wani kuma tafiya yayi fa? Kuma ya bar indomie Allah sa wanann kalau kamar dai ba lafiya".


  "Ai naga alama ko gaisawa bai damu ba kana gani rabonka ne y faɗo".ɗaya daga ciki ya fada suna cigaba da hirarsu.Motarsa ya shiga yana zama ya dafe kansa yana jingina da bayan kujerar da kyar  ya kunna motar yana barin wajen ,minti sha biyar ya kaisa gida da kyar ya tuƙo motar yana fitowa ya shiga katafaran gidan yawuce sama wani ɗaki kai tsaye wayarsa ya ciro hannunsa yana karkarwa ya kira wata number 'Hajja' shine sunan da ke kai tana ringing na farko ta ɗauka ya kara kunne.


"Kamal"Ta furta daga bangarenta hannunsa na rawa da kyar ya buɗe baki "Something terrible happened  last night Hajja".Cikeda damuwa ta tambaya "Me ya faru?"


 "I hit someone with my vehicle and i think he died".


 "Ya ilahi ,Kamal? where are you ?are you detained now or what tell me?"Ta shiga tambaya fuskarta damuwa ƙarara a ciki.


Rintse ido yayi yana murza fatar goshinsa"No ,look ....it happened so fast i ...it happened again i wasnt consious it felt like dream Hajja i didnt stop by yau da safe na koma wajen incident...i..."Katseshi tayi"Kamal listen to me kana ji ? Take a deep breath everyrhing will be alright you didnt kill him,lokacinsa ne yayi kana ji ko ?ina kake a cikin gida? Are you alone?"Ta shiga tambaya yayi shiru "Kamal".Ta sake kira bai ce komai ba "Hold on ,ka saurareni da kyau dont try taking any pills dont do anthing silly just be in your room ..."Bata ƙarasa ba ya kashe ta kalli wayar ta ga yanke kiran yayi da sauri ta fita tana shiga wani corridor ya kawota wani katafaran parlour ta ga yaran suna ta tsalle tsalle gefe guda daga kujera wata dattijuwa ce ta ƙarasa wajenta tana duƙawa kusa da kunnenta ta raɗa mata wasu maganganun ɗaya matar da ke kujera mai kallon ta dattijuwar  tana kallonsu tsohuwa ce amma da gani kuɗi ya zauna ta sha ado tana hakimce tana karkaɗa ƙafa daga shingiɗe tana taɓe baki fuskar dattijuwar ta ga ta canja dole tasan wani abu ya faru magana ta ga tayiwa Hajjan ƙasa ƙasa ta ga kawai  ta jinjina kai cikeda damuwa ta juya ta fita tana dialing wata number 'Kamal therapist' rubuce a jiki kiran ya kusa tsinkewa ta ji bai ɗauka ba tana katsewa ta kira wata number bayan an ɗauka tace  "Muhsin duk abinda kake yanzu ka barshi ka tashi ka  je gida Kamal is in danger".

"Okay"Ya faɗa yana katse kiran bai gama saurararta ba yayi tsaki yana kallon yadda suka zuba mashi ido siblings ɗin nashi dake parlourn maza da mata da ka gani kasan family ne "Its Hajja mental brother ɗinta ne ciwonsa ya tashi kila".Ya faɗa suka taɓe baki kowa da abinda yake cewa wata budurwa a ciki tace  "Sai ma kunga Hajja sanda muka je Morocco yadda ta rikice da ciwon ya tashi".


  "Kayi magana ace trauma suna decieving kansu addiction ne kawai shaye shaye ne ya sha masa kai".Wani guy da ke gefe ya faɗa Muhsin ya ɗauka car key yana ficewa bayan ya shiga mota  ya nufi gidan kai tsaye.




    *Ma sha Allah ,ina godiya da soyayyarku ga SHI SO DABAN YAKE kuma ina mai tabbatar muku wanann tafiyar mai kyau ce ina kuma mai baku haƙuri ga abinda yazo cikin shafinnan kowa dai yasani kulli nafsin zaaikatul maut Hassan zai cigaba da zama a zukatanmu mu da Jiddatyyy🥹🙏🏻🥰🥰  ku ɗakko biro da takarda characters sabbi na tafe sai kuna yi kuna jotting nasu 🤣🤣🤣 amma wannan romon ga masu cigaba da bibiyar littafinnan ne ,domin wannan shafin shine ƙarshen free page ga masu son cigaba ku biyo mu Arewapen zaku na samun update yan whatapp zaku iya biya kuma ta number da ke ƙasa.



Arewapen @dijensy

Opay

***

Khadija Ado Ahmad


Price:500


Contact-***