Page 71
💫MARYAMA💫
By.
Ummu Fadeela.
71...
Babu wanda ya yi zaton jin haka daga gareshi ciki kuwa harda Daada da ta yi rokon.
Wani irin jiri ne na ji yana kwasata daga zaune dan haka na kwanta a wajen a hankali,farin ciki ne ya bayyana a fuskar Innarmu yayinda wasu tarin hawaye suka cika kwarmin idanunta, baffa kuma ya yi kokarin boye duk wani abu da yake ji a ranshi fuskarshi normal kawai.
Allah ya maka albarka Jabiru, kamar yadda ka amince da bukatata, ina so a daura auren a yau ba sai gobe ba, kamar yadda kamin alkawari....
Kamar yadda Daada ta bukata a ranar da dare aka daura auren Jabeer da Maryama a karo na biyu, cikin masallacin dake layinsu baffa.
Ba wani mutane na kirki iya wadanda suka halarci sallar isha ne kawai, tunda aka gabatar da daurin auren Jabeer yake jin kanshi wani iri kamar mutum mutumi haka yake jin kanshi. Da kyar ya iya kai kanshi gida ba tare da ya zube a hanya ba.
Direct part nashi ya wuce ya kwanta saman doguwar kujerar dake palon, ya rasa wane irin feeling yake ji jikinsa, ya san dai baya farin ciki kuma kazalika baya bakin ciki.
Meerah ce ta shigo da gudu palon sanye da uniform na islamiyya ta haye kan cikinsa.
"Daddyna, daddyna ina ka tafi sai yanzu ka dawo?"
Dan bude idanunshi da suka kada jajur ya yi yana kallonta, "Babyna ba'a cire miki uniform ba, ina mommy?" Mommy tana kwance a daki tun dazu dana dawo, tace abu ya fada mata a ido sai kuka take yi kazo ka cire mata Daddy".
Wara ido ya yi akan yarinyar yace, "Da gaske? tana ina, me ya shigar mata idon?" ya fada yana mikewa gami da daukarta a kafada,.
Lokacin da suka shigo Umaimah na kwance saman gadonta kudundune cikin duvet ta yi kuka har ta godewa Allah, ita taje ta roki Daada ta aikata abun da ta aikata kuma ita ta shirya mata duk abun da zata fada, sai dai tun da Daada ta kira ta shaida mata abun da ya kasance tana sanya mata albarka ta nemi nutsuwar jiki dana zuciyarta ta rasa tun lokacin take kuka ta zubar da hawaye ya kai galan daya amma bata samu sassaucin abun da take ji ba, tana jin time da Meerah ta dawo daga Islamiyya amma ta kasa tashi ta cirewa yarinyar uniform balle ta mata wanka ko ta bata abinci, haka kuma ta kasa turata wajen Salima ko yan aiki. Da ta gaji da tambayar da take mata ne yasata fadin abu ne ya fada mata a ido.
"Maimahhh!" ya kira sunanta yana hawa saman gadon, Meerah gudu kije wajen anty salima ta cire maki kayan ta maki wanka kinji?"
to Daddyna" ta fada tana fita da gudu.
"Maimahhh plssssss!"
Ya fada kamar yasan abun da ke damunta. ko motsi ba tayi ba hakan yasa ya zagayo gefen da fuskarta yake, ya ce.
"meke damunki?
Ko in kira dr ne? meerah tace abu ya shigar miki ido taso mu gani"
Ko motsi bata yi ba hakan yasa ya sanya hannu ya yaye bargon da ta rufa dashi yana dagota, a fusace ta mike with shouting ta ce, "Get out of here,i don't want to see your face anymore just get out". Ta fada tana zare ido da nuna mishi kofa.
Sakare Jabeer ya yi yana kallonta, tunda yake bai taba ganin Umaimah cikin irin wannan yanayin ba a tsawon rayuwarsa bai taba kallonta cikin fushi ba tsawon lokacin da ya santa har kawo zaman su karkashin inuwa daya," Ka fita na ce bana son ganin fuskarka kuma!".
Ta kuma fada da karan da ya fi na farko har saida anwar dake bacci ya firgita gami da tsala ihu.
Kamota ya yi niyyar yi amma ta fita waje da gudu hadi da banko kofar,ido ya rufe kana ya bude a lokaci daya yana binta da kallo,sai a lokacin ya jiyo ihun da yaron ke tsalawa dan haka ya juya da hanzari ya daukeshi yana lallashi.
Umaimah ta dade a dakin da ta shiga rufe da kanta tana kuka har saida taji kamar hawayenta zasu tsaya, a lokacin dare ya raba sosai ta fara dawowa haiyaccinta,
"Astagfirullah"
Ta furta tana mikewa zaune, "Kukan me ki ke Umaimah?"
ta yiwa kanta tambayar, a sanyaye ta sauko daga gadon ta shiga toilet dake dakin, ruwa mai dumi ta hada ta yi wanka ta dauro alwala, kayan jikinta da hijab din ta mayar ta kabbarta sallah, raka'a biyu ta yi ta dade a sujjadarta ta karshe tana addu'oi sosai sannan ta sallame, kur'an ta dauka ta fara karatu cikin suratul-Noor.
Saida ta ji zuciyarta yayi sanyi sannan ta mike kamar wacce kwai ya fashewa ta bar dakin, dakinta ta shiga ga mamakinta Jabeer kwance bisa gadonta anwar saman kirjinsa, da alama bacci barawo ne ya kwashesa a wajen yana rarrashin yaron.
Without making any sound ta shiga closet ta shirya cikin kayan bacci, a hankali ta daga yaron daga jikinshi ta mayar gefe ta rufe shi kana ta maye gurbin anwar din da jikinta dake tashin kamshi.
Wani ajiyar zuciya ya sauke still yana bacci amma so stranded dan da ka ganshi kasan bayajin dadin baccin.
Jin wani abu dogo kamar igiya ne yasata dan dagowa tabi abun da kallo.
Headphone ne makale jikin kunnenshi hannu ta sanya ta zare guda daya ta makala a nata kunnen. Sautin wakace ke tashi a hankali cikin taushi da ratsa zuciyar duk wadda ya dandani zuma da madaci na soyayya,.
🎧🎶 Ajikin Kowa Da Akwaishi, Sannan baya tsufa, kuma baya jin rarrashi, baya Neman kofa,in zai shiga baka tare shi,don bashi da watta Suffa, Idanu basu ganinshi, balle kaimar Ihsani....Sooooo Kenan💘💔🎧🎶.
*************
Lumshe idanu ta yi ta na zare headphone din ta mayar kunnensa.
Kamo hannunta Jay ya yi yana bude birkitattun idanunsa da suka rine ya daurasu a kanta, cikin low voice kamar yadda ya saba fada ya ce, "Maimahhhh plssssss".
Bata ce komai ba hakan yasashi fara shafa gashin kanta yana tunanin ta ina zai fara fadi mata abun da ya faru, ga wani borin da ya sameta dashi wadda bai taba gani ko jin tayi makamancin haka ba, daga shafa kai jabeer ya zarce, umaimah bata hanashi abun da ya ke yi ba saidai kuma bata taimakamishi ba, shi yayi kidarsa yayi rawarshi. asuba ta gari.
_______________________________
Tunda ya furta kalmar ya amimce ya maida ni kamar yadda Daada ta rokeshi na zame na kwanta a wajen, gabadaya brain nawa ya toshe farin ciki zan yi Hamma Jay ya bani damar gyara kuskuren da na tafka a baya ko dai bakin cikin furucin sa zan yi na cewa rokarsa aka yi ya maida ni wadda ke nuna neman kai ake dani tunda sai an hada da roko kafin in samu mijin aure, uwa uba UMAIMAH, shin zan iya zama da Umaimah yar'uwata aminiyata karkashin inuwar Jayyy,?
Babu wanda ya kulani a cikinsu kowa watsewa ya yi, lokacin da Baffanmu ya kirani da dare ya mikamin wasu kudi da goro da minti ya ce, "Uwata wannan sadakinki ne, wannan kuma goron daurin aurene, dazu Jabeeru ya maida aurenshi dake, yanzu kina karkashin kulawar wani ne.
Wani irin sanyine na ji yana ratsa daga tafin kafata har zuwa cikin kwakwalwata, take jikina ya fara daukar rawa ban karbi kudin ba kawai na rungume kafafun Baffa dake zaune bisa kujera na saki kuka.
Na dade ina kuka bai ce min komai ba har sai da ya ji kamar na fara fita a haiyacina sannan ya shafa kaina ya ce, "Ya isa haka nan, tashi kije Allah ya maku albarka".
***************
Duk yadda Inna ta so Daada ta barni ko nan da sati biyu ne firr ta ki, a cewarta tafi son inzo zaman makokinta daga gidana. babu yadda muka iya ina ji ina gani bayan kwana biyu da dare Baffa da kanshi ya shirya kaini har gidan Jabeer wanda ban karajin ko ganinshi a gidanmu ba tun ranar da abun ya faru.
Duke na ke gaban Inna ina ta kuka kamar raina zai fita amma ko ci kan ki ba tace min ba da sunan nasiha, kafarta na rike ina gursheken kuka nace, "Innarmu dan Allah ki ce wani abu, kimin nasiha Innarmu shirunki yana bani tsoro, kimin fada Inna badan halina ba, kice wani abuu". Na sake rushewa da kuka,.
Dagoni tayi itama tana mikewa da fadin yanzu dai ke ba yarinya bace ba. Kin san dama kin san hagu kin san daidai kin san akasin hakan, kije Allah ya muku albarka," Rungumeta na yi sosai ina kara bata hakuri daga karshe zareni tayi daga jikinta ta wuce daki, a dakin Daada kuwa zaune take ta hada shayi mai kauri tana sha kamar ba Daadar dake kuka da barin wasiyya cewa zata mutu ba, ko don likita yazo ya dubata har gidane?.Itama nasiha ta min sosai da sanar dani yanzu bani kadai bane, kuma har duniya ta nade Jabeer bai da matar mutuntawa irin Umaimah dan haka in riketa da kyau kamar yadda take kaunata fisabilillahi.
Ina kuka haka baffa ya tusani gaba muka shiga bayan mota drivern Baffa ya ja muka tafi, daga ni sai kayan jikina, sai wani akwati da na ga an sanya a bayan motar. Tabbas na tabbata matar cushe wannan karon....Palon gidan tsitttt ko ina tsaf tsaf, babu abun da ke tashi sai kamshi da sanyin nau'rar sanyaya waje.
Da sauri take saukowa daga stairs din sanye cikin kaya na alfarma tasha ado kamar ba itace ke wuni kuka ba idan Jay ya tafi office, har gaban Baffa ta durkusa da fadin, "Barka da dare Baffa, da kan ka kazo?" barka dai Umaimah ya gida ina amaryata da abokina,?" duk sunyi bacci baffa yasu Innarmu da jikin Daada?"
Ta tambaya tana mikewa da kama hannun Maryama ta rungumeta, "Barka da zuwa pretty, ina fatan alherin Allah da salamarsa ya wanzu cikin zamanmu tare da aminci. Baffa mu iso ciki mana".
Gyara tsayuwa ya yi da fadin Allah ya maki albarka umaimah, Allah ya raya miki zuriya, " ameen ta ce tana jan hannun Maryama, baffa mu iso ciki, bai musa ba ya bisu har sama, dakin da ta zabarwa Maryama dan Jabeer ya bar mata komai wuka da nama sai abun da tace yake yi, nan suka shiga, Masha Allah komai yaji a dakin tamkar na ita Umaimar Baffa bai zauna ba ya musu sallama da addu'ar alkhairi.
Bayan tafiyar Baffa da kamar minti talatin Jabeer ya dawo daga wani aiki da ya fita.
Umaimah na zaune a palon kasa har lokacin tinda ta rako baffa ta samu kanta da kasa komawa dakin,a gajiye ya shigo, da ita ya fara yin arba cikin ado da kwalliya,murmushi ta kakalo da cewa, barka da zuwa ango".
Hade rai Jabeer ya yi ya ce, "Maimahhh am jet tired, zoki min wanka".
Dariya ta yi tana mikewa ganin yana tahowa gareta, side hug ya mata ba tare da ya saketa ba suka cigaba da tafiya, "Wane ni da maka wanka wannan aikin amarya ne ai".
Hmmm shiyasa nace kimin ai amaryata," sarai ta san ya fahimceta kaucewa kawai yake yi,.
Da taimakonta ya yi wanka, bayan ya fito ta fita dan shirya mishi dinner.
A babban tray ta shigo dashi dashi dan ta san idan dare ya yi yafison cin abinci a kasa, turuss ta yi ganinshi shirye cikin pyjamas silk milk colour yana cumbing sumarshi gaban mirror.
Daddyn meerah ya haka?" ta yi tambayar tana ajiye tray din bisa table.
"Me kika gani mommyn Meerah? ya tambaya shima yana mimicking muryarta, ya zaka sanya kayan bacci a nan, ka bari sai kaje dakin mana yanzu kam babbar riga da hula zaka sanya plsss ka fito sakkk ango bana son a samu mishkila.
"Maimahhh yunwa plsss" ya fada yana marairaicewa da shafa tumbinsa da yake tale shima tsabar exercise.
Sarai ta san basarwa yake yi dan haka ta koma bakin gadon ta zauna batace komai ba, abincin ya yi serving kanshi ya ajiye kan rug sannan ya zo ya daga ta cidakk zuwa kan rug din yana chukling nata da fadin, "
Fushin na menene gimbiyata? Jabeeru bawan Allah yana jin yunwa a taimaka a yi feeding nashi.
Duk yadda taso dannewa kasawa ta yi, dole sai da ta bashi abincin a baki har ya koshi yasha ruwa sannan ya mike ya fara pressup wai zai rage abincin da tula mishi dayawa.
Dariya kawai take yi bai tsaya ba saida ya kirga sau hamsin sannan ya mike, tattare kayan tayi zuwa kitchen, time da ta dawo yana tsakiyar gadonshi da laptop a gabanshi yana aiki.
Laptop din ta janyo da karfi ta rufe da rike kugu.
"Wai hamma Jay baka san dare ya yi ba, ka tashi ka shirya mana ka tafi dakin amarya wllh bacci nake ji ko d.....?" batai aune ba taji ta a jikinshi baiyi wata wata ba ya hade bakinsu waje daya, saida ya tsotse janbakinta duka sannan ya saketa yana numfashi sama sama yana kallonta da jajayen idanunsa yace.
"Wannan bakin ya koyi tsiwa yanzu,dole in fara ladabtar dashi.
Ba karamar wahala Umaimah ta sha ba wajen ganin Jabeer ya tashi yaje dakin Maryama ba, har sai da ta yi fushi zata tafi sannan ya mike amma da sharadin ba zai canza kaya ba kamar yadda ta bukaci sai dai ya sanya kaya kamar ango.
Yana rike da hannunta har dakin Maryama, rumtse idanu Umaimah ta yi lokacin da suka shiga dakin.
Maryama na zaune bakin gadon yadda ta barta babu alamar ta yi motsi a wajen sai sheshshekar kukan da take yi.
Shigowar su ne yasata yin shiru saidai still batayi motsi ba, ta kasan ido ta ke hangosu yana rike da hannun Umaimah gam kamar za'a kwace masa ita, sanye da kayan bacci, Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, wannan ango kenan?
A ranar da aka kawoni zai shigo da kayan bacci instead of babbar riga a hakama yana rike da hannun matarshi?" zuciyata ta fara raya min, da sauri na kori shaidanin dake kawata min hakan da auzubiyya.
Duk maganganun da Umaimah ke yi bana jinta inda hankalina yake daban, yawanci fatan alkhairi take mana da kara janyo hankalina wajen ganin mun hada kanmu da farin cikin wadda muke karkashinsa.
Mikewa ta yi daga karshe zata fita ya kara damko hannunta yace, tsaya in rakaki gimbiyata kar wani abu ya firgita min ke a hanya,"
"No, ka kula da yar'uwata da kyau ni zan wuce"
Cewar umaimah tana nufar inda Maryama ke sandare kamar statue, durkusawa ta yi daidai kunnenta ta ce.
"Pretty ina fatan zaki kirani gashi da asuba?".
Rumtse idanu na yi ina jin yadda kirjina ke kara hauhawar bugawa, dan tureta na yi da kokarin janyo fillown dake gefena, ganin haka ta fita da gudu, a guje shima ya bi bayanta yana cewa ta tsaya ya rakata.
Zamewa na yi kan pillow din da na kama na bude sabon pejin kuka, Jay yana isowa Umaimah tana rufe kofarta da jingina da kofar ta ciki tana sauke wani irin numfashi.
Jingina ya yi ta waje shima ya ce, "Maimahhh plsssss! ki bude kofar,i want to say gud nit to you,"
Shiru bata ce komai ba, kara sassauta murya ya yi yace, Plssss," nan ma batace komai ba sai hawa da saukar da makwgoronta ke yi, shafa kai yayi yana wani lallausan smile ya ce, "Ohk,na san kina jina zamu hadu gobe ne, gud nit.
Sai kuma ya yi shiru a hankali ya ce , "I LOVE YOU MAIMAHHH" daga haka ya juya ko bangaren dakin da Maryama take bai gani ba ya wuce bangarenshi.
Umaimah na jin wucewarshi ta fara bin guiwanta dake jagorantarta zuwa kasa ta durkushe da sakin wani irin kuka a wajen...
Yana shiga dakinshi direct bathroom ya wuce ya dauro alwala, ya dade yana nafilfili da addu'oi kafin ya kashe komai na wuta dake dakin ya shige cikin lallausan duvet na shi wani irin bacci mai cike da nishadi da dadi ya kwashe shi.
Umaimah ta yi kuka sosai harta godewa Allah, danma Anwar yana wajen nanny, meerah na wajen Salima daga karshe ta mike da kyar ta hau gadonta ta kudunduna a haka bacci ya kwasheta,...Maryama tun tana kuka a hankali har ta koma sheshsheka, shiru babu Jabeer babu alamarshi cikin kuka bacci barawo ya kwasheta yadda take a kife gefen hannunta.
*****************
A hankali na fara bude idanuna ina jin kamar gari ne ya waye kamar kuma yanzu na kwanta, inda nake kwance nake nabi da kallo ta sunray da ya shigo ta window kana nabi kayan jikina da kallo, a hankali na cigaba da baza idanuna cikin dakin saidai wayam babu kowa,hakan na nufin tun fitarshi bai dawo ba kenan? Jiki a mace na mike da kyar na shiga bayi ina jin kuka yana taho min amma ina kokarin ganin na taushi zuciyata.
Ruwa mai dan dumi na hada cikin bathtub na shige ina lumshe idanu sosai na yi wanka na gasa jikina da nake jin yana ciwo sannan na dauro alwala na fito.
Agogon dake dakin na gani ya nuna min karfe bakwai na safiya,, ya salam na furta ina dafe goshina, a gaggauce na tsane jikina da shafa mai da na samu a kan mirror din da turaruka, akwatin da aka shigo min dashi na bude, haka kawai na samu kaina da son sanya kaya wadda zai burge Hamma Jay.
Na dade da sanin yana son ganina cikin shigar atamfa musamman riga da siket, hakan yasa na dauko wasu yellowish atamfa dinkin riga da siket na fara kokarin sanyawa, wata zuciyar ta kwabeni da fadin
"Maryama wannan maganar da kike yifa yanzu ba wancan Hamma Jay din bane".
Take na ji zuciyata ta karye na samu kaina da cire kayan na watsar dasu saman gado na dauko bakar abaya na sanya gami da kabbarta Sallah, na dade zaune bisa sallayar ina karatun qur'an har wajajen karfe takwas da yan mintuna kasancewar saturday ce gidan tsitt babu motsin kowa a sama, mikewa na yi na dan gyaggyara dakin na shirya kayana cikin wardrobe dake nan da mayuka na gaban mirror kana na debi turaren wutar da na gani a mirror din na zuba cikin burner na kunna, babu jimawa dakin ya gauraye da kamshin turare da sanyin naura.
Ina zaune wajen har karfe goma da rabi banji gilmawar kowa ba..
Dakin aka bude Umaimah ta shigo shirye cikin atamfa hot red riga da siket ta kafa dauri ta murza jambaki kunne da wuyarta hadi da hannayenta sanye da kayan kawa sai walkiya suke yi ga wani irin kamshi dake tashi a jikinta kamar ta yi karo da tirelan turare tana rungume da Anwar hannunta daya kuma rike da Meerah suma duk sun cakare cikin ado kamar masu tafiya gasar sarakan kyau na duniya.
Wani irin miyau na hadiye mukut take naji na tsani kaina, naji na raina kaina, tabbas a yanzu Umaimah ko da matar governor zata jera kafada.
Amarya alkawari ya cika, amarya alkawari ya cika.
Ta fada cikin sigar waka, tana zama kusa dani, take kamshinta ya bude min hanci.
Hannu nasa ina kakaro murmushi na karbi Anwar sosai na ke son yaron har cikin raina, ko don kaman da suke yi da hamma jay ne? Allahuaalam.
Gaisawa muka yi sama sama tace tana kallon meerah "oya go greet your Ummie". Gaisheni yarinyar tayi har tana zama kusa dani, inashafa kanta a raina ina jin da yanzu ina da wacce ta fi wannan girma fa.
Madam breakfast is ready, yana bangaren Hamma Jay everyweekend a can muke cin three times meal namu.
Ban musa mata ba dan dama na gaji da zaman dakin na mike tana gaba rike da hannun meerah ina binta a baya rungume da Anwar har side nashi.
Yana zaune palonshi sanye da jallabiya kirar Egypt hannunshi rike da remote control yana canza tasha suka shigo dukkansu gwanin sha'awa.
Ta kasan ido yake kallonsu yana amsa sallamar, daneshi Meerah ta yi da fara bashi labarin Mommynta ta ce wannan Ummie ne daga yau.
Side hug Umaimah ta mishi da fadin.
"Good morning Daddy"
Peck na kumatun ta ya yi yace.
"Morning Mommy"
Dariya ta yi tana zama, dan rusunawa na yi kadan idanuna suna cika da hawayen da nake ta kokarin controlling nasu na ce, "Ina kwana hamma Jayyy bakina yana rawa.
"Fine"
Kawai ya fada ba tare da ya maida hankalinshi a kaina ba.
A haka dai a kayi wannan breakfast da ko spoon uku na kasa ci tsabar damuwar dake raina.
Bayan an gama muka tattara wajen Umaimah ta goge komai kwanukan kuma ta fitar waje mai aiki tazo ta kwashesu, muna a palon har wajen karfe daya, yawanci hirar tsakaninsu ne sai kokarin da Umaimah take na ganin ta tsoma ni a ciki. amsata baya wuce ehh ko ah'ah.
Kiran sallar azahar ne yasamu kowa kama gabanshi don gabatar da sallah.
Haka muka wuni har dare nan ma tare muka ci abinci ana gamawa wannan karon na yi tafiyata daki don bazan iya jurar shareni da Hamma Jay ke yi tamkar kashine a gabanshi ba.
Haka muka cinye kwana uku ba tare da ya kwana a dakina ba, ba kuma tare da magana na minti biyu ya hadani dashi ba, idan na gaishe shima sometimes sai Umaimah ta ankarar dashi, a hakan ma amsar shi bata wuce "Fine" shikenan.
Ta bangaren Umaimah muna zaune lafiya,sau tari na kan manta cewa miji daya muke aure har sai naga sunyi wani abun.
************
Yau nake cika kwanaki uku a gidan, a ka'ida yau kwana na ya kare ba tare da ango ya kara leka dakin nawa ba tun ranar da aka kawoni,.
Muna gama cin abincin dare da duk kwanakin bana wani cin abun kirki amma bai taba nuna damuwarshi ba kamar da can baya, sai Umaimah ke yawan takuramin.
Mikewa ya yi yana goge bakinshi da tissue ya na kallon Umaimah yace, "Idan kun tashi ina son ganinku" daga haka ya wuce.
Tsawon lokaci ya dauka baice komai ba bayan mun shigo inda yake, kafun daga bisani yayi gyaran murya gami da bissimillah ya fara nasiha cikin hikima da azanci da nuna mana irin tarin ayoyin dake cikin rayuwarmu, wadda ko kasancewar mu a nan yanzu haka wani babbar aya ce da ya kamata duk mai hankali ya fahimta.
Sannan ya daura da fadin, "Sai ku yanke a tsakaninku kwa