Page 72
💫MARYAMA💫
By
Ummu Fadeela.
72...
"Daddyn Meerah mei yasa za ka yi haka? why all this da kake aikatawa Pretty? Ashe da akwai lokacin da zai zo ka dinga shuning na Maryama tamkar ba hamma Jay da na sani ba akan Prettynshi? You have to be patient akan abun da ya faru komai yana tafiya ne akan zanen kaddara"
Tun da ta fara magana ya jinginar da kanshi da kujera gami da lumshe idanunsa.
Kalmar zanen kaddarar da ta ambata ne ya shashi dagowa da sauri ya zuba mata jajayen idanunshi da suka rine kamar gauta ta sha rana ya ce.
"No Maimahhh ba haka bane, ko zaki iya bambanta min tsakanin kaddara da kuma jarabawa da kuma son zuciya? This is rubbish ba komai zaku dauka ku daurawa kaddara ba, wani abun babu ruwan kaddara a ciki, wani abun kuma ubangiji ya kan jarrabi bawa dashi dan ya gwada karfin imaninsa kamar yadda wani abun kuma son zuciyace tsantsa.
Tsantsar son zuciya Maimahhh and soyayyar maryama a....." sai kuma ya yi shiru yana dafe saitin kirjinsa mikewa ya yi yana cigaba da kallonta still hannunshi bisa saitin zuciyarshi ya cigaba da fadin.
"Ta bani wahala maimahh, ta raba ni da nutsuwata ta rabani da lafiyata ta rabani da abubuwa dayawa sai dai wani abun takaicin kuma shine har yanzu soyayyarta..." rumtse idanu ya yi bai karashe ba ya juya da shigewa daki da sassarfa.
Still Umaimah ta yi a wajen abubuwa dayawa suna bijiro mata, idan duk abubuwan da Pretty ta yiwa Hamma Jay still soyayyarta ya na hana mishi nutsuwa, so what about her, me yasa babu wadda ya taba tambayarta yadda takeji akan tilon masoyinta da son zuciya na wasu ya yi sanadiyar rabuwarsu, shi wani hali yake ciki yanzu.
Istigfari ta yi da sauri tuna cewa ita matar aurece kana ta fita daga bangaren gabadaya itama.
Tsakar dare Jay da kanshi ya zo ya dauketa har dakinta ganin bata zo ba, daga yanayin rawar kafar da ya nuna mata ta tabbata babu wani alaka da ya shiga tsakaninshi da Pretty, dan ta san shi ta san wayeshi,yana daga cikin jerin mutane masu yawan bukata.
**************
Haka muka cigaba da kasancewa tsakaninmu da Umaimah akwai mutunci wadda na tabbata hadin Allah ne kawai.
Yayinda Allah ya kimtsamin kaunar danta Anwar a raina kusan komai na yaron ni na ke yi kwana ne kawai bama yi tare, abinci kuma tare muke cin dinner dashi while breakfast da lunch muke yi mu biyu dan Yana fita da sassafe kwana biyun nan baya dawowa kuma sai dare kamar dai akwai abu mai muhimmanci da yake gudanarwa.
Har lokacin kuma tsakanina dashi baya wuce "Fine" idan na gaisheshi.
Yau ya kasance Umaimah ta gama kwana biyunta, a lissafi nine zan karbi miji.
Ina lura da irin abubuwan da take yi cikin kwana biyun, babu wani aikin kirki dan komai masu aiki ke yi da ya danganci kasa, upstairs ne basu da hurumin hawa dan naga ita ke sharewa ta goge, hakama bangaren hamma jay ita ke gyara komai a can.
Tun safe na ke tunanin inyi ko in bari dan tsira da mutuncina? Wani sashin zuciya mai kwaba ta da barin yafi rinjaye.
Dan haka na cigaba da zama na a palon dake sashen mu nida Umaimah ina kwance saman doguwar kujera anwar kwance bisa ruwan cikina, tsabar na cin da nake yiwa yaron har ya fara sakewa da ni.
Umaimah da Salima kuwa suna dakin Umaimar tana tayata sauya fasalin zaman kayanta a wardrobe.
Kamar daga sama na jiyo muryar Fati tana kwada sallama, mai aiki biye da ita janye da wasu tika tikan akwatuna guda biyu, da hanzari na mike ina washe baki da fadin
"Wa nake gani haka? fati shine sai yau kika tuna damu ko?" rungume ni tayi har ina jin tsinin cikinta da ya fara turowa a jikina, da sauri ta cika ni tana tattaba jikina.
"Antinmu, kin yi rashin lafiya ne? duk kin wani zabge haka kamar ana yankan naman jikinki ana parpesu dashi?".
Take na ji wani iri a raina har idanuna suna kawo ruwa na ce.
"Fati duk kewar ku ne na ke yi, babu wadda yazo wajena"
Ganin yadda jikina yayi ne yasata yin dariya tace.
"Antinmmu ke da kike tare da Hamma Jabeer da Anti Umaimah wani irin kewa kuma zakiyi.
Bayan fa Innarmu da baffanmu babu kamar su wajen nuna miki soyayya".
Ta fada tana dariya.
"Hmmmm Fati Sanin da kika yiwa Hamma J."
Bakina ya subuce ba tare da na sani ba.
Kasake ta yi tana kallona sai kuma ta ce,
"Ga kayanki nan plsss ki shigar Innarmu ta bayar in kawo miki kuma ni bazan iya dauka ba"
Aiko nima bazan barki ki dauka ba maman twins" muka yi dariya ta ce,
"Antinmmu ina zuwa da akwai magana bisa dukkan alamu, bari in gaisa da Anti Umaimah ina zuwa yanzu, ina autar Inna" ta yi tambayar tana wucewa dakin Umaimah, ta juma a can suna hira da ita da kuma salima kafun ta fito zuwa dakina.
Ina zaune bisa gadona na kure waje daya da kallo anwar yana gefe na yana bacci, fati ta shigo, kallo daya ta yiwa yayartata ta fahimci ba karamar damuwa take ciki ba zama ta yi gefena gami da dafa ni, firgigit na dawo haiyacina dan babu shakka na yi nisan kiwo.
"Fati sai yau kika tuna dani ko, ina Innarmu da su Daada ya jikin nata"
"Au dama daada bata da lafiya ne? babu wadda ya sanar min kuma, amma dai garau na ganta yau ko kwallo zata iya bugawa, duk ba wannan ba, me ke damunki na ga duk kin kode haka?"
Dan uwa mai dadi, tabbas duk wanda ya rasa dan uwa ya rasa masoyi, take na ji hawayen da nake ta kokarin dannewa dan nuna mata babu komai suka ballemin, fashewa na yi da kukan da na fahimci zuwa yanzu tabbas rauni na yawane dashi
"Fati ina cikin damuwa, ban san yadda zan yi Hamma Jay ya yafe min abun da na aikata ya fara ganina a matsayin mutum ba".
subhanallahi! Allah ya rabamu da damuwa, meke faruwa antinmmu?".
Ban boyewa Fati komai ba iya wadda ya kamata ta sani na sanar da ita ina share hawayena na ce, "ki taimaka min yar uwata kada zuciyata ta fashe".
Nisawa Fati ta yi kafin ta yi ajiyar zuciya.
"Antinmmu ni na dauka abun da zaki fuskanta a wajen Hamma Jay sai ya fi haka, tabbas yana sassauta miki, kin san halin da ya shiga bayan baki nan?
Lallai baki sani ba mu da muka kasance dashi ne kawai muka san abun da muka gani, baki da lokacin kuka a yanzu I said it loudly wannan ba lokacin kuka bane a gareki.
Mikewa za ki yi ki gyara kuskuren da kika aikata a baya,.
Nan Fati ta dinga bata shawara mai amfani da bullewa kana hadi da gamsarwa.
Cikin sanyin yanayi na ce, "Fati kuma zan iya?".
"Why not, zaki iya mana. Dole fa sai kin daure kin kauda kai.
Ke da kika yi sa'a da anti umaimah kike tare, ai da wata ce wllhi sai inda karfinta ya kare wajen ganin ta hankada ki waje.
Yanzu yaushe ne zaki karbi girkin?".
Cike da rauni na ce.
"Wai yau ne inaga".
Wai yau ne inaga"Fati ta maimaita, wato baki ma tabbatar ba kenan, anya antinmmu kin shirya gyara komai kuwa, yau zaki amshi girkin amma bakima tabbatar ba, and kina kwance at this hours bakiyi komai ba ba dole ki ta bushewa ba.
Kece mai laifi, dole ki sauke kai ki bishi kamar yadda nace miki a bayanin dazu."
"To yanzu ni me zanyi Fati?" yanzu tashi zaki yi in ta yaki shirya kayan nan ki wuce bangarenshi ki gyara yadda ya kamata Salima tazo ta gyara bangaren ku tunda lokaci ya kure sai kiyi azamar shiga kitchen".
"To fati zanyi, amma kuma ai masu aiki ke girki".
"Kan bala'i" cewar Fati tana zaro ido, to ki zauna masu aiki su girka mishi, yanzu fa sabon salo ne ake yi dole kema ki fitar da naki salon don zama da kishiya sai kin iya Salo antinmu. Ki shiga da kanki ki girka mashi ko babu yawa dai yasan ke kika girka.
Masu girkin sai su dafa na sauran jama'ar gida, maza tashi babu lokaci.
Da taimakon fati na shirya kayan da ta kawo min daga gida cikin wardrobe nawa sauran kayan shafa kuma muka jere su bisa mirror, wani kwalbar turare ta fitar daga jakanta ta mikamin,
"Ga wannan daga chad aka kawo min na dibar miki, yana da dadi sosai duk sadda zaki dakinshi idan kinyi wanka ki shafa, wannan kuma, yanzu zan hada miki da madara na sha ne, ta dinga fitar da abubuwa tana nuna min yadda ake hadawa, cike da mamaki na ce,
"Fati duk ina zan kai wadannan" hararata tayi tace, "ki tsaya sanya kar kisha hajiya," ga wannan kuma anti umaimah na kawowa itama dan dai inyi adalci amma bai kai yawan naki ba.
Kamar yadda tace haka akayi ta dinga dura min abubuwan da ta kwaba wasu da zuma wasu da madara, sannan ta ce inje in gyara bangarenshi kafin ya dawo muna fitowa idona ya sauka kan Umaimah dake kallo a palo ita da Salima suna hira sama sama, take wani irin kunya ya lullubeni naji anya zan iya wucewa gyaran side din a idanunta.
Fati ce ta katse min hanzari ta hanyar fadin, Anti umaimah akwai tsaraba fa, yauwa salima tashi ki gyara bangaren nan tas antinmmu zata gyaran bangaren Hamma Jabeer.
ji na yi kamar kasa ya tsage in shige dan kunya, da sauri Umaimah ta mike da fadin to muje ki bani tsarabar maman twins" pretty idan kin gama muna daki, daga haka ta ja hannun fati suka shige dakinta, salima kuma ta wuce kitchen na sama ta dauko sweeper da mop bucket,
"Antinmmu me kike jira a tsaye kuma?" na tsinkayi muryarta, ban ce komai ba na ja sagaggun kafata na wuce..
Sosai na zuba kwanji na gyara bangaren da ba wani datti ne dashi ba dama dan kullum Umaimah ke kalkaleshi, ba karamin haduwa dakin hamma jay ya yi ba kamar a kasashen larabawa, round bed ne fari kal kirar italy duk abun da ke dakin farine tas mai daukar ido, toilet din kam da kyar na iya gyaranshi dan wasu abubuwan tsoron tabawa na yi. tunda na zo goge mirror na ga ya kawo wuta alamar a hade take da computer ban kuma gigin taba wani abu ba.
A tsanake na gyara ko ina tas, sabon bedsheet da na gani shima fari tas mai kamar katifa na shimfida saman gadon, yana da fililuka masu yawa akalla zasu kai guda goma with different shapes, haka kawai na samu kaina da jera su that look so romantic, turare na kunna a burner na kuma fesa freshner da na gani na kara karfin ac na rufe dakin.
Lokacin da na dawo babu kowa a bangaren namu amma ko ina ya yi kal kal yana sheki, hakan yasa na sauko kasa, a kitchen na samu masu aiki suna ta kiciniyar girkin dare.
Dakatar dasu na yi da fadin su bani awa daya akwai abun da zan yi a kitchen din, suna fita na dauki apron na daura da fara tunanin me zan girka.
Dan murmushi na yi tuna wani abu ba bata lokaci na dauraye tukunya na tare ruwan sink tap na kunna gas gami da daurawa na rufe. Kaza na fitar a freezer na zuba cikin kwano na karashi bakin ruwa dan ya narke Luckily na samu soyayyen kayan miya cikin freezer din dan haka na fitar hadi da sauran spices dana fitar cikin cabinet da na bubbude.
Rice na debo ganin ruwan dana daura ya na ta tafasa na wanke na juye a ciki, sannan na koma kan kazata, gyaranta na yi na zuba cikin tukunya kayan kamshi danginsu citta da nikakkiyar garlic da sauransu na zuba da isashshen albasa na daura shima a gefe.
Kan kace me kitchen din ya dume da kamshin tafashen da nake yi, Fati da Umaimah ne suka shigo tare tana rike da Anwar.
"To madam kece a madafar ashe na ji gaba daya gida ya dumame da kamshi, mai ake shirya mana haka?"
Cewar Umaimah tana jingina da cabinet, ban bata amsa ba sai karbar Anwar da na yi a hannunta ina mishi wasa da tambayar yaushe ya tashi?"
Yanzu na jiyo kukanshi nima salima ta daukoshi ga Fati kuma wai driver ya zo daukarta zasu wuce.
"What" na fada ina zaro ido amma Fati kice mashi sai anjuma mana, ki jira abinci plsss, duk yaushe ma kika zo dan Allah?" na fada kamar zan yi kuka.
Rufa min asiri antinmmu, kema fa a gidanki kike hmmm, barni in yi biyayyar aure.
Duk yadda na dage kin zama fati tayi, haka muka rakota ina rike da Anwar har bakin kofar palo a kunne ta rada min, "Karki manta duk abubuwan da na fada miki fa?"
Ban ce mata komai ba, amma ina tunanin kar in gama shan wahala may be ma ko kallon abincin bazai yi ba balle ya ci, amma kalmar sai na yi hakuri da Fati ta dinga nanata min dazu shi yake karfafa min guiwa.
Tare muka koma kitchen din da Umaimah tana tambayar me zata taimaka min dashi,
"Ke dai ki huta Umaimah, na ma kusa kammalawa ai,salad da na fitar zan yanka ta dauka ta fara wankewa, ni kuma na zari towel na anwar da ta sakala akan kofa na goyashi, murmushi ta yi ganin yadda na damare yaron a bayana, wani irin dadi hakan yake mata, kun san dai ance mai yaro wawa.
Soya kazar na fara ita kuma ta na yanka salad din muna hira sama sama, cikin lokaci kadan na gama hada miyar stew da yasha naman kaza yaji spices sai tashin kamshi yake yi.
White rice din da ya gama nuna da jumawa na kwashe cikin kwanukan da Umaimah ta saukar daga jerin kwanukan dake kitchen din, miyar ma na juye na shirya akan babban tray da plates da spoons serving spoon, to hajiya baki hada salad din ba." cewar Umaimah.
"No Umaimah, I prefer it haka, ya fi.
Dage kafada kawai tayi irin ohk din nan.
Da taimakonta muka kai abincin bangaren Hamma Jay bisa table,a lokacin har an idar da sallar maghriba don haka muka wuce dakunanmu batare da na ba Umaimah boy nata ba.
Itama bata yi yunkurin karbarshi ba. Wanka na silla sosai bayan na fito na shirya cikin atampa ta pink colour dinkin riga da siket da suka yi matukar amsa ta, ban shafa komai ba a fuskata sai pencil da na gogawa idona da chappet a lebe sai turaruka da na yiwa kaina wanka dashi.
Na rama sallar maghriba da ta kwace min Na gabatar da isha.
Anwar na kuma yiwa wanka ganin ya tashi na mike na kaishi dakin Umaimah, manshi na dauka a kan mirronta ita kuma ta bani kayanshi, a nan na shirya shi kafin na mika matashi na ce ta bashi mama, itama tayi wankanta tasha ado amma yau sabanin atamfa da na saba ganinta dashi, doguwar riga yar kanti ce jikinta mara nauyi sai yar hula da ke kanta.
Koda na fito maimakon in koma dakina sai na kuma sauka dan aiwatar da abun da ke raina.
Cake na dauko irin ta leda din nan guda biyu a kitchen na daura su saman plate bangaren Hamma Jay na kai shima na ajiye saman table kana na bude fridge na dauko ruwan gora da soft drink, sai wani holladia yoghurt da na dauko dazu na sanya a fridge din dan ya yi sanyi suma na jeresu bisa table din.
Saura kadan numfashina ya shige cikina lokacin da na juyo da nufin fita shikuma ya sanyo kai cikin palon hannunshi rike da briefcase, kirjina ne ya bada sautin dammm lokacin da idanuna suka shiga cikin nasa.
Lumshe ido Jabeer ya yi kana ya bude su a kaina, da sauri kuma ya kawar da kanshi gefe ya cigaba da tafiya zuwa dakinshi.
"Sannu da zuwa" na fada ina nufar shi zuciyata tana ankarar dani shawarar Fati ko uffan bai ce ba ina isoshi yana shiga dakin, nan ma lumshe idanu yayi yana shakar kamshin da dakin ke yi kafun idanunshi su sauka bisa tsarin da akayiwa gadon,take yaji kaso saba'in na gajiyarshi ta watse.
Ajiye briefcase din yayi ya wuce bathroom nan ma komai tsafff cike da farin ciki ya shiga gabatar da uzurinsa har tsawon wani lokaci sannan ya fito..
Ganin bai amsa min sannu da zuwan da na mai ba yasa jikina yin la'asar don haka na koma kan kujera na zube yaraf tamkar kayan wanki, a kallah na kwashe fiye da minti talatin a wajen sannan Hamma Jay ya fito shirye cikin three quarter wando da singlet hannunshi dauke da laptop yana zama bisa kujerar da na lura kullum akai yake zama.
Ban yi kasa a guiwa ba na mike. Gefen kujerar da yake kai na je na tsugunna kaina a kasa.
(kece mai laifi dole ki yi kasa da kai antinmmu)
Maganar Fati ta dawo min don haka nace, "Sannu da zuwa hamma Jay, in kawo maka abinci a nan ko dai a sama zaka ci?" Muryata tana rawa alamun a ko wanne lokaci kuka zai iya taho min.
Still bai ce komai ba sai kokarin operating laptop nashi ya keyi. cikin rawar murya na kuma fadin, "Da hannuna na girka maka abincin yanzu in kawo nan ne ko.....?" ban karasa ba sakamakon kukan da ya kufce min.
Taune lips nashi na kasa ya yi tamkar zai huda su yana tura babbar yatsar kafarshi cikin lallausar center carpet dake wajen, ban yi zaton zai yi magana ba ya ce,
"Haka kika ga yar uwarki na yi? ta taba cin abinci a nan ba tare da ta kira ki ba?" da sanyi yayi maganar baza ka dauka ma shi yake maganar ba, da hanzari na mike ina fadin.
"Bari in kirata yanzu" ko taku biyu ban yi ba Umaimah ta shigo palon kuyi min uzuri na zo a makare," cewarta tana isowa kusa da jay, side hug ta mishi ni kuma ta mika min hannu mukayi musabaha, a hankali na ce, "ka taso to".
Kasa jurewa ya yi sai da ya dago kai ya ganta yana mikewa, kamar yadda naga Umaimah ke yi haka na janyo mishi kujera itama na ja mata suka zauna, plate na dauko na fara serving nashi,white rice din na zuba sannan na bude miyar, a take ya lumshe idanu dan wani kamshi da ya buge shi, akan abincin na zuba miyar hadi da cinyar kaza sannan na yaryada salad kadan a gefe na daura mishi spoon natura gabansa plate dake dauke da cake din can na janyo shima na ajiye gabanshi na zuba hallandia yoghurt dake tashin raba a glass cup shima na ajiye mishi.
Sosai gaban Jabeer ya buga lokacin da yaga abincin, take wasu moments da bazai taba mantawa ba suka shiga rige rigen dawowa cikin kwanyarshi, rufe idanu ya yi ya bude yana tuna lokacin da yake kashe last coins da ya mallaka dan ganin Maryama taci naman kaza da hollandia da kuma wannan cake na leda da har gobe yake sayawa Meerah, yana tuna yadda yake aiki mai wahala dan abiyashi ya siya musu shinkafa a dafa da miya a yanka salad just the way ta zuba mishi din nan don shine favourite food nata a duniya.
A hankali ya sauke ajiyar zuciya, ba tare da na yi zato ba na ga ya dau spoon ya fara cin abincin.
Baka jin komai sai karar cokula a wajen har muka kammala muka tattare wajen da Umaimah, har wajen karfe goma muna wajen shi yana aiki a system nashi ni da Umaimah kuma muna kallon wani progrmme a zee world.
Mikewa Umaimah ta yi tana hamma tace, "To sai da safenku, ni dai bacci nake ji" daga haka ta kara bawa Jay side hug wadda na lura dabi'arta ce shi kuma ya yi pecking nata ta wuce, mun dade a wajen bayan shigar Umaimah kafin ya mike shima yana rufe system din ya fara tafiya, har ya iso kofa ya juyo ya ce.
"Nima zan shiga, zaki iya zuwa ki kwana a nan if you wish kamar yadda yar uwarki ke yi".
Rumtse idanu na yi da karfi,ina jin wani irin daci a wuyana, bance komai ba na tashi nima na fita daga side din. dakina na wuce na kuma dauraye jikina na shirya cikin kayan bacci wadanda suka kaimin har kasa, hijab na zumbula shima har kasa, tabbas ba don na amince nine mai laifi ba da babu abun da zai kaini dakin nashi, amma haka na taushi zuciyata na koma, kamar munafuka haka na shiga dakin, da sauri na rufe idanuna ganinshi tsaye bakin mirror hannunshi rike da cumb yana gyara gashinsa, jikinsa ko iya boxer ne irin mai girma har kusa da guiwa din nan.
Ko ina a mummurde kamar dan dambe, na dade da sanin haka hallitarsa take amma sai na yau yafi bani tsoro, ciki ciki na yi sallama ban kara yadda na kalli gefen da yake ba na iso na dofanu a bakin gadon kamar kace kyat in ari na kare,.
A zuciyarshi ya amsa sallamar, bai yi zaton zata zo ba, amma ga mamakinsa sai gashi ta dawo, sai da ya gama shafe shafensa ya tako ya hau gadon abunsa yaja duvet hannu yasa ya kashe light din da switch dake gefen bed din ya rage sai dimm light dake kan bedside gama jan duvet din ya yi ya rufe har kan kirjinshi sannan ya juya min baya ya yi kwanciyarshi.
A hankali na ji kamar ana warware min wani abu cikin kaina, take na ji na tsani kaina, lallai Fati bata kyauta min ba, da na sani ban zo ba. ban ankara ba kawai na fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, ina son tashi in bar dakin amma kafafuna sun hanani damar hakan domin wani irin rawa suka dauka kamar ana kada musu ganga.
Sosai nake kuka kamar numfashina zai bar gangar jikina.. bugun da zuciyarshi ya tsananta, gangar jikinsa ce ke neman bijirewa umarnin kwakwalwarshi, anzo lokacin da ya kasa jurewa kara taune lebe ya yi hadi da yin juyi daya ya kamota zuwa tsakiyar gadon.
Mikewa ya yi ya zauna bisa tsakiyar gadon yana rike da ita, sautin kukana na kara jina da nayi rike hannunshi. da sauri ya hadani da jikinshi ya matse gam gam, ina jin yadda gabadaya jikinsa ya dauki rawa, yayinda zuciyarshi ke barazanar ballowa tsabar yadda take bugu fiye da ka'ida.
kansa ya daura bisa nawa kan still yana makale dani, wani abu naji mai dumi da bana tantama hawayene ya diga a jikin hijab nawa ya ratsa ta ciki ya sauka akan kafadata, cikin wani irin murya da tun da can na sanshi da ita ya