Page 73
💫MARYAMA💫
By
Ummu Fadeela
73...
Me yasa baki barina in yi rayuwa cikin salama? me yasa baki barin zuciyata ta huta? Why pretty, shin zuciyar da ta rayu da son ki ta cancanci wannan azabtarwar? I always told you that SON KI NE JARABTATA, and may be SON KI NE AJALINA Maryamaaaaa".
Ya fada yana kuma kankameni hawaye na zuba a idanunshi sosai kamar karamin yaro.
"Iam Sorry Hamma Jay, am sorry bazan kara ba, forgive me for the sake of Allah, bazan karaba, na dawo zan gyara kuskuren da na aikata a baya kuma Soyayyata idan ta kasance jarabawar ka lallai bazan bari tayi AJALINKA ba.
I am here with you, zan taimaka wajen healing wound da ke cikin zuciyarka, bazan karayin nesa da kai ba.
Sakeni ya yi ya hade goshinmu waje daya yana goga dogon hancinsa kan nawa still bai daina hawaye ba ya ce, "Kar ki kara gujemin pretty, without you iam nothing, i can't do without you, kar ki kara barina dan Allah, da sonki na rayu kuma dashi zan koma ga mahallici na ki daina bani wahala hakanan."
"I love youuuuu Hamma Jay, Ina sonka, ina sonka, ina sonka, And I love youuuu" kamar saukan ruwan sanyi haka ya ji maganar tata a zuciyarshi, bai san ya akayi ba sai ji ya yi ya kuma kankameta yana sakin kuka, ya dade yana rokarta da ta furta mishi kalmar i love you amma bai samu ba sai yanzu, kuka yake tsakaninshi da Allah kamar dan goye, hakan yasa itama ta fashe da kuka.........(It is possible to love someone, that his love makes you cry cry and cry again, this way?) Kun taba ganin soyayyar da ke saka Kuka?.....
Kuka take yi kamar an aiko mata da sakon mutuwa,hakan yasa shi sassauta na shi kukan ya ce, "Is ohk". Cikin sheshsheka ta ce, "Kaima ka dena kukan ka yana sani kuka",cikin murmushi mai tafe da hawaye yace, "Ohk, kece ai, kece kika sa gabadaya na zama wani rago kamar ba namiji ba. now kukan ya isa yanzu, hannu yasa yana goge mata hawayenta, yana gogewa wasu na fita. Itama tasa nata hannun ta fara goge masa nashi hawayen.
Hijab nata data kudunduna a ciki ya zare a hankali yana kwanciya da janyota kusa dashi suka kwanta, "Iam Sorry Hamma Jayyy" na kuma fada da rawar murya, hannu yasa ya lalubo bakina ya daura yatsarshi manuniya a akai ya ce, "Shhhhhhttttt".
Daga haka ya kara janyo ni jikinshi yana lumshe idanu. Sosai kirjinsa ke bugawa dan har a jikina nake ji,"kara motsi na yi na ce, "Hamma Jay, kirjinka yana sauri sauri"
A kunne ya rada min, "Kece sanadi pretty!" Bude baki na yi zan kuma yin magana ya yi azamar daura tafin hannunshi a kan bakin cikin murya kasa kasa ya ce
"Bacci plssss".
Ban kuma cewa komai ba haka shima sai yadda na kejin tsallen kirjinsa a bayana, da haka wani irin bacci mai dan karen dadi ya kwashe mu duka.
Karfe uku na dare Jabeer ya farka, a hankali ya zare hannunta dake zagaye bisa waist nashi da alama cikin bacci ta juyo har ta zagaye shi, lullubi ya gyara mata ya mike zuwa toilet ya dade yana sallah wanda shi kanshi bai san iya adadin raka'oin da yai ba, a ko wacce sujjada yana godiya ga ubangiji mai kowa mai komai da kuma rokarshi da ya bashi ikon kamanta adalci a tsakanin matan nashi.
Yana zaune a wajen har aka yi kiran sallah, rak'atal fajr ya gabatar sannan ya wuce masallaci.
Yana fita na tashi dan tun lokacin da ya tashi karfe uku nima na farka amma na kasa motsi a wajen, wani irin farin ciki nake ciki marar misaltuwa, duk sadda na tuna moment namu na daren jiya sai inji wani irin murmushi ya subuce min.
A gaggauce na gyara shimfidar gadon na fita, dakina na koma na shiga bayi da sauri na dan watsa ruwa na dauro alwala na fito jin an kabbarta sallah a masallacin da nake iya jiyo sautinsu har nan.
Riga marar nauyi na sanya na gabatar da sallah subhi bayan na idar na dade ina karanta adkhar sannan na gabatar da doguwar addu'a, agogo na kalla ya nuna min karfe shida da minti goma sha daya, dan haka na mike dan gabatar da aikin breakfast kamar yadda na kudurta a raina.
Ina sauka downstairs shi kuma yana shigowa palon dan haka na yi still a wajen ina tsungunnar da kaina kasa da fara wasa da zara zaran fingers dina, "Ina kwana" nafada dan wani irin kunyarshi ce ta lullubeni a take.
Tsayawa ya yi yana kallona kafin shima cikin kasa da murya ya ce, "Haka kika ga yar'uwarki na gaisheni, oya come here" ya fada yana nuna min gefenshi da nufin in mashi side hug kamar yadda Umaimah ke mishi.
Kamar kazar da kwai ya fashewa haka na nufeshi ina jan kafa da tura baki, rungumarshi na yi kadan ta gefe da fadin, "Good morning daddyn meerah".
Wara ido ya yi da yin dariya a cikin ranshi wadda na ji sautin a gefen kirjinsa, yace, "What!" turo baki na yi na ce, "Ba kace yadda Umaimah ta ke yi ba"
Murmushi kawai ya yi da shafa kaina ya ce, "Me zaki yi a kasa yanzun nan?" kitchen na nuna mishi da hannu, "zan dauki abune" na fada, ohk daga haka ya cikani ya haura sama binshi na yi da kallo ina dada godewa Allah da ya bani hamma Jay a karo na biyu.
Ko da na shiga madafar yau ma kukus din sai uzuri suka min da bani hanya, lafiyayyen kosai da yaji ganyen albasa irin wadda Innarmu keyi da hamma jay ya yi ta santi na soya, sai kunun gyada da na tuttulawa madara da banana flavour da kuma kwakwa da na yi.
Yayi matukar kyau kuwa na fito kitchen din har wajajen bakwai da wasu mintuna kasancewar bani da saurin aiki.
Bangarenshi na wuce da kwanukan na jere a sama, dakin na leka na ganshi a shirye tsafff cikin wasu tsadaddun suit wadda na lura yana yawan sanya suit idan zai fita ranakun aiki,duke yake yana sanya takalmanshi covers suma bakake.
karasa shigowa na yi ina zare idanu,da rawar baki na ce, "Hamma Jay fita zaka yi da sassafe haka?"
Bai ce min komai ba har ya gama sanya takalman ya dago,jikin dressing mirror ya nufa ya dauki turare ya fesa gami da daura agogonsa designer a tsintsiyar hannu.
Har na fara tunanin ko abun da ya faru jiya da kuma dazu a palon kasa mafarkine?.
Ban gama tunanin ba na ji ya riko wrist dina yana matsewa da karfi sai da na yi dan kara kadan, ya ce
"Wannan ne punishment naki, haka kika ga yar'uwarki ta na min da safe?" tabbas zuwa yanzu wannan kalmar ta haka kika ga yar'uwarki na yi ya fara isata, dan haka cikin shagwabar da yake hallitar Maryama kamar yadda kuka sani, na ce.
"Kuma me na yi hamma jayyy". Ta baya ya rungumeni ya turo kanshi dai dai fuskata ya na dan goga min sajensa ya ce.
"Ina dawowa masallaci zan samu ta gyara dakin nan ta kuma yin wanka tana jirana, ina shigowa zan kwanta ina bukatar jin dumin jikinta dan haka bata hanani damar hakan, bayan dan lokaci zata tashi ta hadamin ruwan wanka idan ranar aikice zata min wanka ta shiryani sannan ta dauko min breakfast a kitchen, sometimes ta yi feeding dina, wani lokaci kuma in ci da kaina, zata rakani har bakin kofar palon kasa rike da briefcase dina tana min a dawo lafiya cike da kulawa,ina fatan kin gane?" ya fada hadi da pecking kumatuna.
"To Hamma Jay kuma breakfast naje hada maka fa" ina kai karshe hawaye suka ziraro min.
Shafa kai ya yi da fadin, "Girki again? karki damu na jiya kadai ya isar da sakonki, yanzu kada in yi latti ina da aiki mai muhimmanci da zan gabatar a office. Daga haka ya sakeni ya fara tafiya.
"Na shiga uku! hamma Jay tun asuba ina kitchen dan Allah ka tsaya ka ci ko kadanne plsss" na fada ina binshi a baya da sauri,bai tsaya ba har sai da ya iso tsakiyar palon,jin irin magiyar da nake mishi ne ya sashi nufar dining area din ya fara bude kwanukan dake jere, matsoshi na yi kadan cike da rauni na ce.
"Dan Allah Hamma Jay ka ci ko kadan ne, da hannuna na girka maka shima" sosai raunin da nayi magana dashi ya yi tasiri a ranshi,duk saurin da yake yi sai yaji yana bukatar ci, hakan ya sashi janyo kujera da zama, hannu yana rawa na fara zuba mishi kosai din kana na zuba kunu a cup ina mika mishi,,"Tanks" ya furta a can kasan makoshi. ya ci kosan dayawa tare da kunu yana duba agogo ya mike da zarar tissue yana goge bakinshi,
"Na makara sosai," iya abun da ya fada kenan ya wuce, babu yadda na iya haka na bi bayanshi jiki a sanyaye da tunanin me yasa yake zamar min kamar wahainiya mai canza kala, kamar bashi yake kuka jiya ba, sai gashi yanzu yana sha min kamshi.
Binshi na yi da niyyar rakashi kamar yadda yace Umaimah na mishi, sai dai ga mamakina bangarenmu ya shiga ya durfafi shiga dakin Umaimah, Dammm haka zuciyata ta bada sauti.
"Yau ai kwananki ne me zai yi a can kuma?" zuciyata ta mani tambayar, ban jira na tantance ko bambance komai ba tsabar yadda na ji wani irin haushi a haukace na ce...