MARYAMA

Page 74

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

                             By.

                 Ummu Fadeela

  

74...



Da sauri na ce, "Hamma Jay!"sai dai kafun in karasa ya shige dakin, hannun kujera na samu na zauna ina dan dafe kaina kadan.

Bayan kamar minti uku ya fito Umaimah na biye dashi a baya, da alamar shiya tada ita daga bacci dan yanayin yadda fuskarta yake dauke da alamar baccin da bai gama sakinta ba da kuma idanunta da suka yi luhu luhu kamar marar lafiya, tana sanye da kayan bacci doguwar riga kanta da hula.

Muna hada idanu ta sakar min wani kyakkyawan murmushi da ya sa na ji zuciyata ta narke, hannu ta mika min lokacin da ta iso gareni a sanyaye na karba mukayi musabaha ina kakalo murmushi, sai kuma na samu kaina da tambayar, "Umaimah me ya samu idanunki?".

Bude idanu tayi sosai tace, "me kika gani" ban bata amsa ba hamma jay ya mana sallama, kafadata ta buga cikin kasa da murya ta ce, "Pretty wuce ki rakashi mana".

Take na ji ta gama tsinka min zuciya, lallai Umaimah mutum ce, na sani ba tun yanzu ba, me yasa ni tawa zuciyar ta darsa min wani abu don kawai ya shiga gaisheta ya Allah give me the strenght.


Na fada lokacin da nake bin bayanshi, kafun in gama saukowa har ya kai bakin kofa da tafiyarshi mai cike da izza,"Allah ya bada sa'an abun da aka fita nema, Allah ya azurtaka da halal ya kauda idanunka da zuciyarka gami da gangar jikinka daga haram, kamar yadda ka fita lafiya yanzu, ubangijin dake saukar mana da ruwan sama ya dawar da kai lafiya cikin aminci."

Cak ya tsaya daga fitar da yai niyya, lumshe idanu ya yi sannan ya bude yana jin wani irin excitment yana ratsa shi, daga bakin pretty wannan ke fita or.....Bai gama tunanin ba yaji ta ce, "Hamma Jay kuma ka tsaya faaa".Cike da shagwaba ta yi maganar.

Juyowa ya yi, taku biyu ya iso gareta dan basu yi wani nisa ba. Hannayenta ya rike duka biyu yana dan murzawa, still yana kallonta har tsakiyar idanu, kallon da yake min yasa ni rufe idanuna da sauri a hankali ya furta "Thank you pretty, ki dinga yimin haka kullum i like it! dan rankwafowa ya yi ya sumbaci idanuna da na rufe yace, "Bye, sai na dawo"

Daga haka ya sakeni ya fita,zama na yi kan daya daga kujerun palon ina sauke numfashi sama sama, anya zan iya cigaba da abubuwan da Fati ta sanar da ni in dinga aikatawa kuwa? Hamma Jay yana bani kunya, abubuwan da yake min suna sani jin kunya sosai.

Lokacin da na koma sama ban samu Umaimah a palon ba, har kamar zan wuce dakina sai kuma na juyo na shiga dakinta tana kwance saman makeken gadonta ta rufa da bargo.

"Hmmmm,hajiya baccin bai isa haka bane?" yaye bargon ta yi tana mikewa "Wllh pretty jiya ban samu bacci ba ko kadan, sai da nayi asuba bacci ya kwashe ni, na fara ban jima ba kuma Daddyn Meerah ya tadani".

"Eyya,sorry, me ya hanaki baccin to?"

Na tambayeta ina ganin kumburarrun idanunta..

"Just tunani ne kawai" tunanin me Umaimah"....Dariya ta yi ta ce, "tunanin duniya da al'amuran dake cikinta mana, leave it pretty, baza ki gane ba.

So ya daren jiya ki dan bani labari mana" ta fada tana turo min kunnenta, murde kunnen na yi da karfin da sai da tayi kara sosai, Anwar dake gefenta yana bacci ya firgita ya tsala ihu, da sauri na suri yaron na fita a guje ina banko kofar, murmushi Umaimah ta yi a tsanake wasu siraran hawaye suka gangaro mata, da bayan hannunta ta goge ta koma ta kwanta.

Koda na fita nima ajiyar zuciya na sauke ina addu'ar Allah ya bani ikon danne wannan abu da nake ji game da Umaimah akan Hamma Jay.

Wanka na yiwa Anwar kasancewar yanzu ba'a rasa kayanshi a dakina na shirya shi tsaff sannan na kaishi wajen Nanny nace ta hada kunu ta bashi, wanka nayi bayan na dawo ko mai ban shafa ba na kwanta nima duk da uwar yunwar dake tsungulata, haka na yi bacci, sai twelve na rana mukayi breakfast da Umaimah dan ita ta tasheni ma wai yunwa take ji, already masu aiki sun gama komai su Salima da Meerah suna School, dan haka gidan sai mu kadai.

Jefi jefi muke hirar da yawanci tuna baya ne,idan ka ganmmu baza ka dauka kishiyoyi bane a zahiri kam..

muna ta zaune har yan makaranta suka dawo sannan muka tashi, bangaren Jay na koma na dan gyaggyara duk da ba abun da ya sameshi, amma haka naga Umaimah tana yi, sai gaf da la'asar na shiga kitchen da niyyar dafa abincin dinner, ina farawa Umaimah ta shigo ta kama aikin itama muna yi tare, kamar tasan abun da ke raina ta ce, "These days daddyn Meerah baya dawowa da wuri, inaga akwai aiyukka sosai a office dake rikeshi".  

Allah ya taimaka kawai nace muka cigaba da aiki.

Har muka gama bai dawo ba, wasa wasa har wajen karfe takwas Hamma Jay bai dawo ba, wani wanka na dandansa bayan sallar isha, yau abun da ban taba yi ba na yi wato kwalliya harda jambaki da hoda tsayawa kawai na yi ina kallon fuskata a madubi ganin yadda na yi wani irin kyau mai bada mamaki, ashe gaskiyan hausawa da suka ce ko kanada kyau ka kara da wanka idan kana wanka kuma,ka kara da kwalliya.

A palo na samu su Umaimah da yaranta tana koya musu homework, "Wowww pretty, kin ga yadda kika yi kyau kuwa? ehh antinmmu sai kin ganki kamar kajol na India, cewar salima tana kwace zancen.

Rolling idanu na nayi wani dadi yana kamani na ce, "Na gode, amma duk kun fini kyau ai,"

Anwar ne ya lallabo ya sauka daga kafar mamarshi ya taho gareni da dan gudunshi dan ya iya tafiya sosai yanzu yana fadin, "Ummie,Ummie yana daga min hannu,duk sadda yaron ya ambaceni da Ummie, sai naji wani abu a raina, tunda ya fara magana kuma Ummie yake cemin kamar yadda Mommynsu ta koya musu, dagashi na yi sama muka fara juyi a palon muna dariya ni dashi.

Rufe idanu Jabeer ya yi ya bude ya kuma daurasu a kanta yadda ko ina na jikinta ke juyawa kamar wata dawisu, pink lips nata da ya santa dashi sun sauya zuwa red dariyar da take yi ya taimaka wajen bayyanar siririn wushiryarta kana da lobawar dimples nata. 

Tun fitowarta ya shigo bangaren sakamakon hayaniyarsu da yaji a can, hakan yasa bai karasa site nashi ba, yana tsaye jikin kofa ya harde hannu gabadaya maganganunsu yaji, ganin yana shirin loosing control ne yasashi yin gyaran murya,a take suka nutsu suna juyowa gabadayansu,da gudu Meerah ta nufeshi da shagwabe murya, "Daddyna nima kamin irin yadda Ummie tayiwa Anwar".

Dagata ya yi sama yace, "My sweetheart baki san kinyi lukuta bane yanzu?" tana rike hannunshi ya shigo ya zauna a daya daga kujerun dake zagaye a wajen gami da daura kafa daya kan daya.

"Sannu da zuwa Hammanmu" yauwa Salima karatu ake ne?"dukkanmu sannu muka mishi ya amsa Umaimah ta daura da fadin, "Saura kadan mu bazama gidajen radio da talabijin mukai cigiyarka".

Shafa kai ya yi da fadin, "Really"  

"Ofcourse, munga dare ya yi sosai kar muna zaune bamusan ka bata ba" Sosai maganar ta bashi dariya har saida ya dara yana shafa kan Meerah. 

Wani kululu na ji ya tokare ni a kirji har sai da na tsaida numfashina na wucin gadi, amma bance komai ba na nufi briefcase da ya ajiye bakin kofa da wata bakar leda mai dan girma.

"Jakar kawai zaki shigar, wannan ki dubashi a kitchen and ki kawo mana dinner yau a nan zamuci,"

Na tsinkayi muryarshi, "To" kawai na fada na zari ledar da jakar, har daki na kai mishi jakar sannan na dauko abincin da muka girka semo da miyar vegetables da ya sha nama zuku zuku.

Inda suke na kawo na dire a tsakar palon, kitchen dake bangrenmu a sama na shiga gami da bude ledar, gasassun kajin gidan gona ne tika tika kamar an dura musu sha ka fashe kwance cikin ledar, koda na bude nadin da aka musu sai walkiya suke tsabar maiko da tashin kamshi, babban tray na dauko na daurasu bisa na dauko knife da fork, har zan fita na dawo, fridge na bude na dauko watermelon da apples da kuma lemu,rufe kajin nayi dan kar su huce na hau gyaran fruits din na juye cikin wani glass bowl mai dan fadi na hada duka na fitar. zuwa inda suke zaune suna hira sama sama...

"Woww Daddy ka ce yau an tuna da madallah suya kenan,?"cewar Umaimah ganin kajin... Yesss domin jin dadinku ba" Ya fada yana kallon Maryama kasa kasa.

Babu wanda ya ci abincin na kirki ya ce kowa ya zo ya ci kaza dukkanmu muka hadu akan tray din harda Meerah da salima da Anwar shima,..(Yar'uwa ki koyawa mijinki cin abinci cikin iyalinki irin once in a while dinnan basai kullum ba, hakan yana da wani sirri sosai a ciki).

Cike da nishadi kowa ke ci, kun san dai abu idan ya kasance special irin a kawo daga wajen nan akwai armashi don haka nima ban cuci kaina ba na zage na ci sosai, shi ya fara mikewa ya je wash hand basin dake dining area ya wanko hannunshi, duk tsiyar mu kasa cinye naman mukai, dole ragowar Salima ta kaiwa yan aiki a downstair.

Bayan kimtsa wajen Salima ta dauki Meerah suka shige dakinsu bisa Umarnin Umaimah, itama ta mike tana saba Anwar a kafada ta ce, "Yau dai baccin wuri zan ta matso Jay ta dan sumbaci hannunshi shima ya sumbaci goshinta tace, gudnight tana mika min hannu, mukayi musabaha, halayyar Umaimah akwai abun burgewa a ciki, tambayar kaina nake ko dai ita bata jin abun da nake ji ne, ko dai dauriya kawai ta fini.

"Madam zan yi wanka" muryarshi ta dawar dani daga duniyar tunanin da na lula.

Mikewa ya yi ina binshi a baya har bangarenshi, direct ba yi na fada domin hada mishi ruwa kafun ya furta min wannan kalmar da na tsana na (haka kikaga yar'uwarki na yi.).

Da sauri na rufe idanuna time da na fito ganinshi tsaye rike da waist nashi ya daura sabon towel a iya kugu, na gane sabone ta kwalinshi da na gani a gefe, ta tsakanin yatsuna na ke dan lekoshi, nasha sanar daku cewa hallitar jikin Hamma Jay tana bani tsoro, yanzun ma hakan ce ta kasance yasa na rufe fuskata.

"Na hada maka ruwan" Na fada still fuskata a rufe, takowa ya yi zuwa gabanta, ban san ya iso ni ba sai ji na yi ya ce.

"Hmmmmm" 
Da sauri na bude fuskar jinshi a kusa dani sosai, yatsarshi ya sanya a kasan habata ya dago kaina da shi yana kare min kallo, idanun na kuma rufewa ruff dan wani irin faduwa gabana ya yi ganin wasu abubuwa da suke yawo cikin idanunshi.

Yatsa yasa ya dangwali jambakin da na goga a lebena ya koma jajur gwanin sha'awa, jambakin da ya dangwalo din ya daga saitin fuskata yace, "Whats this?" 

Da sauri na bude idon jin tambayar da yai ina turo baki na ce, "Hamma Jay jambakine f...." ban karasa ba na ji saukar nashi lip din saman nawa, wani irin passionate kiss yake bani dukkanmu biyu kafafunmu ke kokarin gaza daukarmu, sai da ya wanke jambakin tasss sannan ya dago da jajayen idanunshi da shakakkiyar murya ya ce, "Daga yau kar in kara ganin kin sanya wannan abin".

Da kyar na iya tattaro yawun bakina da suka kafe na ce, "Amma kuma ai Umaimah tana sanyawa, me yasa ita ba ka hanata?"..


Kallona ya yi still idanunshi a rine ya ce, "Kina kishi da matata ne?" 

Tura baki na kumayi gaba idona yana kawo kwallah a take, "Ni me yasa zan yi kishi da matarka? kawai na tambaya ne ganin ita tana sanyawa".

Shafa pink lips din nawa ya yi, 

"Na fi son ganinsu a haka pretty, just ki yi abun da na fada miki, ban amince ki kara sanya musu kala ba, and ke daban umaimah daban ohk?"
Gyada kai na yi hawayena yana zubowa.

Ban yi aune ba na ji ya dagani sama kamar wanda ya dauki yar tsana haka yaji tsabar rashin nauyinta, Na shiga uku Hamma Jay me kake yi haka?" 

Na fada a firgice jin anyi sama dani, babu abun da ya fado min a lokacin sai rayuwar da na yi a gidan Sameera Da Qaseem.

Bai direni ko ina ba sai cikin katoton Bathtub da na tara mishi ruwan wanka, tsumbul haka na jini daga ni har kayana cikin ruwa, "Na fada miki haka Maimahhh ke kula dani ita ke min wanka amma ke naga alamar son jiki ya miki yawa" ya fada lokacin da yake shiga ciki shima, Hamma Jay na yi wanka fa, kuma ka bata min kaya yanzu".   

Yatsarshi ya daura bisa lebena da fadin "shhhhtttt, ba'a magana a bayi" 

Shirun kuwa na yi kamar ya danna min pause....Romantically ya janyo ni jikinsa na kwanta lamo cikin second daya na ji saukar rigata,a hankali sauran ma suka biyo baya, duk inda hannunshi ya kai tabawa yake da sunan wanka gabadaya ya gama cikani da kunya amma shi ko a jikinshi, a lalace a ka kare wannan wankar amma fita ya gagareni, dan babu yadda za'ayi in iya tashi a gabanshi haka after all what he did to me.
Ko ido na kasa hadawa dashi kamar dai ban sanshi ba tun asali, ko da dai ya canza, totally change.

Gama daure towel din ya yi a kugunshi ya juyo, ganinta da idanu rufe ya sashi sakin murmushi mai sauti ya dauke ta cakkk ya nufi fita bayin.

Wayyo ni wayyo Innarmu" na fada ina kare kirjina da hannuna, akan katafaren gadonshi ya ajiyeni yana dariyanshi mai kyau, a rikice na rarumi zanin gado na rufe gaba daya jikina, baice komai ba sai jikin madubi da ya nufa, shafe shafe ya yi yawanci turaruka ne sannan ya sanya wani jibgegen boxer da na kula yafi jin dadin kwanciya da irinsu.

"Hamma Jay plsss mana zanje dakina,"gira daya ya dage min bai ce komai ba, hamma Jay plsss mana, zan dauko kayan baccina ne". Difff ya kashe wutar dakin ya janyo Maryama kusa dashi a kunne ya ce, "You Don't need sleeping wears, I will cover you with my body". Ya fada a kunnena yana sauko da kanshi kan wuyana.

Jikina ne ya dauki rawa jin yadda gaba daya Jabeer ya sauya fasali a take daga wata jihar zuwa wata jihar haka yake ta chanza tasha cikin yanayi na fitar hayyaci, yayinda ni kuma na gama rikicewa dan tsoro, yana gab da isa madakatar da ya tunkara kawai na ji gaba daya jikinsa ya saki ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya da tamke fuska tamau kirjinsa yana gudu sosai, "Cikin wani irin murya mai cike da dan kaushi ya ce, "Pretty adadin maza nawa kika ba kanki bayan kin bar gida?..........