Page 75
💫MARYAMA💫
By
Ummu Fadeela
75...
Juyamin baya ya yi yana tamke fuska ya ce, "Adadin maza nawa kika ba kanki bayan kin bar gida pretty?".
A zabure na tashi na ma manta da cewa babu kaya jikina, "Allah ka rufa min asiri duniya da lahira, na shiga uku Hamma jay mai kake nufi?" Na fada ina zaro idanu waje kirjina na dukan tara tara cikin kaina kamar ana buga drum da karfe haka nake jin wani waaaaaaaaann.
"Abun da na fada shi nake nufi pretty" ya kuma fada yana rumtse idanu shima a nashi bangaren.
Kuka na sanya iya karfina na fada kanshi." Kar ka min haka Hamma jay, don't do this to me, wallahil-Azeem babu wani mahaluki da ya taba kusantata a duniya, only youuu kai kadai ne wallahi kai kadai ne ka taba kusantata.
Kada ka zargeni mijina ka rufamin asiri kar ka zargeni aure da zargi ya haramta, and my heart ba zai iya jurar rabuwa da kai ba a wannan gabar plssss Hamma Jayyyyy kada kace haka wallahi babu wadda ya taba yi wallahi Allah kenan tun da na tafi ban taba samun nutsuwa na dogon lokaci ba plsssss don't say such thing again iam begging you."
Kuka na ke yi iya karfina dan da gaske maganar tashi ta bani tsoro, ashe kalubalen fita ka bar iyayenka yawane dashi? Ashe har yanzu ban gama fuskantar nawa kalubalen ba? Ya Rabb.
Tabbas da za'a bani loudspeaker sai na karade duniya ina fadawa mata darasin da na dauka ta bangarori mabambanta danmma Allah ya soni da rahamarsa ya takaita min wahalar.
Sosai na ke kuka ina rokarshi cike da tausayi, Jabeer bashi da zabi dan haka ya riketa shima,
"Ohk, kukan ya isa haka nan,na yarda dake dama ba zarginki nake ba, pretty ina da tsananin kishin abun da nake so,kece mutum ta farko da zata bada shaidar irin kishin da nake dashi especially akan ki shekaru ashirin da biyar na yi sonki da kaunarki suna ratsa jini bargo da zuciyat....."
Zaro ido ya yi ganin abun da na aikata, baiyi wata wata ba shima ya amshi sakon da na fara aika mishi yayinda reshe ya juya mai amsar sako ya koma bada sako. wani yanayi Jabeer ya shiga da a lokacin idan za'a tambayeshi sunanshi bazai iya fada ba, ya manta kowa da komai sai prettynshi ce a gabanshi.
A wannan dare muka kara zamantowa abu daya nida Hamma Jay a karo na biyu, Godiya ta tabbata ga Allah mai yalwata kirjin bayinsa da kimtsa musu soyayya ta gaskiya da bata tsufa ballantana ta gushe a zuciyoyin da aka kawata su har abadan.
Yana rike dani a gefenshi ya jingina da bedframe idanunshi a rufe, gashin kaina da ya rage tsawo tun zamana gidan kurkuku bai dawo normal ba har yanzu yake shafawa a hankali, murya ciki ciki ya ce, "My pretty!"..
"Hmmmm"
Na fada dan na kasa bude baki..
"Pretty, lets stay like this forever and ever".
"Hmmmm" na kuma fada dan na kula akwai wani yanayi atattare da shi. da asuba ma ko kafun ya fita masallaci sai da ya kuma ziyartar jahar kano sannan ya kimtsa ya wuce masjid, dan tun a daren jiyan ya yardar wa kanshi cewa ehhh shi ka dai dinne fa a wannan tashar.
Ko da gari ya waye yau Hamma Jay bai je office ba, a cikinmmu ya zauna cike da nishadi da walwala.
dtuk inda Maryama ta yi hankalinshi yana kanta, tun tashinsu Umaimah ta fahimci something happened dan haka ta ringa tausar zuciyarta lokacin da ta ga ta kusa kasawa tayi excusing kanta, ba yi ta shiga tasha kukanta sannan ta yi wanka ta fito...
***********
Haka rayuwa ta cigaba da gudana, Jay baya iya boye soyayyar Maryama ko a gaban waye, haka kuma baya boye ganin kima da mutuncin Umaimah ko a ina ne ba ya yadda wani abu ya same ta.
Wani irin soyayya yake gwadamin mai tsayawa a zuciya, haka kuma baya gajiya da making love dani, dare da rana matukar yana gida kuma matukar zan zo inda yake to shikenan sai anyi, ban sani ba ni kadai yake wa haka ko dai harda Umaimah, ko da dai ta taba sanar dani in dinga yawan shan fruit sosai dan ta kula shi din mabukaci ne sosai, lallai samun abokiyar zama irin Umaimah sai an tona a wannan zamanin.
Zuwa yanzu mun maida girkin Jay wajibi a kanmu tunda na fara shikenan, ko ranar girkina ko na Umaimah tare muke yin komai, kuma yana jin dadin hakan matuka.
Zaman lafiya muke sosai da ita,amma zahiri itace karfin zaman lafiyar, dan sau tari zan mata abu ta shanye ko kuma ta maida shi wasa irin namu na aminai a baya, haka yasa Jay yake yawan kiran Maimahh da yar aljannah...
***********
Yau ma kamar kullum Umaimah tana kwance a palon kasa kan center carpet, kwannan nan duka ina yawan lura da ita kamar akwai abun da ke damunta,haka kawai ta yi ta yamutse fuska kamar mai jin wari ko kuma tayi ta kwanciya a kasa, ko kadan bata da karfi a jikinta.
Yanzu ma kwance take war a kan carpet din idanunta a rufe, kukan da anwar ke yi ne ya tsannanta na fito daga kitchen ina kare musu kallo anwar na kwance jikinta yana kuka Meerah ma tana gefe tana tayashi.
Amma ko uffan Umaimah bata ce musu ba,da hanzari na karaso dan yau ko leka kitchen din batai ba duk da ranar girkinta ce haka na shiga kitchen din.
"Umaimah mai yake faruwa ne haka baki da aiki sai kwanciya kamar ruwa, kuma kinsan babu kyau kwanciya a irin wannan lokaci da maghriba ya kawo kai,bata ce komai ba sai muskutawa da tayi tana gyara kwanciyarta. jin muryata yasa Anwar tahowa gareni yana kuka, daukarshi na yi ina lallashinsa da lallashin Meerah at the same time. mai aiki daya na kira na ce taje da yaran ta kula dasu dan in gama girkin da na fara.
Sannan na matso kusa da ita, daure ki tashi maghriba tayi, ko dai mu wuce hospital ne uhyimm?"
Mikewa ta yi da kyar tana jingina da kujera ta ce,
"Iam not feeling well Pretty, kasusuwata ji nake kamar ana kwankwatsa min su, bana jin dadin duniyar like irin mutuwa zan y...."
Hannu na daura bisa bakinta..."Kulll, kar in karajin irin maganar nan a bakin ki, babu inda zaki je lokaci bai ba tukunna, daga dan zazzabi kawai sai ki fara zancen mutuwa.
Taso kawai mu wuce hospital su rabi sa karasa girkin, bari in kira Hamma Jay.
Cewar Maryama tana zakulo wayarta sak irin na Umaimah da Jay ya sai mata bai juma ba, yana shigowa gidan dan haka bai amsa ba sai saurin karasowa da yai, "Subhanallah!" ya fada yana tunkarosu, "What happen, maimahh me ke damunki,dama na kula baki jin dadi amma muje asibiti kin ki ban san ina kika koyo taurin kai ba, ya fada yana matsota. da sauri Umaimah ta toshe hancinta ta ce, "Don't come closer, i don't like this perfumes of your's,warin kashi yake yi".
Kashi kuma Maimahh?" kafun ya karasa ta fara kela amai a wajen kamar babu gobe, babu shiri ya dauketa maryama tabi su a baya sai asibiti.
*************
Ji Jabeer ya yi kamar ya sanya likitan a baya ya goyashi ya yi ta tsalle tsabar farin ciki lokacin da ya tabbatar masa Umaimah tana dauke da juna biyu na sati hudu.
Kasa rufe baki Maryama ta yi itama tsabar farin ciki, kusan son yara a jininsu yake dukkansu, ko dan basu da yawan zuriya ne? mussaman Jabeer yana ganin ta bangarenshi ne zuriya zasu taru a yanzu shiyasa yake jin farin ciki sosai.
Kwanan Umaimah biyu a asibiti ana kara mata drip sannan aka sallamota gida, tun daga wannan lokaci ta fara wani wawan laulayi da bata taba yin irinshi ba, babu abun da yake zama cikinta ko ruwan tasha sai ta amayar dashi,dama tun kwana biyun da tai a asibiti Anwar bai sha mama ba Innarmu ta ce a yayeshi kar yasha ciki dan haka na tattara komai na kayanshi ya dawo wajena mamarshi ko tana fama da kanta. Jabeer kuwa kusan tare suke wannan jinyar da Maimahh gaba daya shima ya zabge a take yadda yake lallabata kuma kamar zai mata numfashi ko ya cire cikin ya mayar jikinsa, duk abun da ta ce tanaso cikin kiftawar ido yake mata, ko don nasa a zuciyata ne wani abun sai inga kamar hadda ganganci take hadawa dan taga ya maida hankali a kanta.
Irin kulawar da Jay yake ba Umaimah bai taba ko da digon son da yake min ba a cikin ranshi, amma hakan ya darsa min sha'awar ganin nima nayi ciki da wuri dan haka na zage ko da Jay bai bukace ni ba which is very hardly ace ina lafiya kuma ba bin wata nake ba bai bukace ni dinba yana wahala, amma ko da haka watarana da kaina nake kai kaina a zuciyata ina addu'ar Allah yasa ciki ya shiga, amma man propose God dispose, a haka har cikin Umaimah yakai wata hudu ni kuma ina da wattani bakwai a gidan Hamma Jay cike da soyayya da kulawa,laulayin ya fara raguwa mata zuwa lokacin tana iya yin wasu abubuwa da kanta saidai wani irin girma da cikin yake yi fiye da wattanninsa wata hudu kawai amma kamar wata bakwai.
Tarairaya da kulawa babu irin wadda Umaimah da cikinta basa gani a wajen Jabeer sau tari na kanyi kuka cikin sujjada da rokon Allah ya bani nima har wata kusan takwas amma ban taba koda batan wata ba,da na kasa jurewa na yi wa hamma Jay maganar watarana, sai cewa ya yi komai lokacine nima nawa lokacin zai zo, abun har ya kai ga Innarmu watarana da tazo duba Umaimah da kawo mata miyar kuka da tace tanaso Innar ta mata take tambayata bayan mun shiga daki, "Maryama ince dai bakwa wadannan hadiye hadiyen na zamani da sunan tsarin iyali ko?"
Tuni zuciyata ta karye har hawaye ya kawo idona na yi saurin tsungunnar da kai na ce, "Ehh Innarmu".
Yanayin yadda na bata amsar yasa ta kuma fadin, "Amma dai ya tare dake ko?" nanma ehh na kuma fada mata, tace, "To a cigaba da addu'a Allah ya baku zuriya masu albarka,"wannan ya tabbatar min da cewa Innata ma tana son ganin gudan jinina a duniya.
Wasa wasa har cikin Umaimah ya shiga watan haihuwa babu labari a wajena, kulawa ko wacce iri Jabeer yana bani har ma fiye da tunanina, ga Anwar da yanzu zance ya zama dana dan wani lokaci kin mamarshi yake saboda ni.
Wani dare Umaimah ta tashi da nakuda mai wahalarwa dan har yafi na cikin Anwar da tasha,dama tun da ta shiga watanta a bangaren Jabeer take kwana dan ko baka da tausayi idan kaga yadda ta zama sai ka tausaya mata. Dama Jabeer a shirye yake da lokacin dan haka babu bata lokaci muka wuce da ita asibiti sai salati take yi tana barmana wasiyya wai mutuwa zatayi,da hanzari aka karbeta zuwa dakin haihuwa, sai dai gwajin farko likita ya tabbatar da dole fa a mata aiki dan ga kan baby amma har zuwa lokacin bata bude ba.
Hannu Jabeer ya sanya yaa tuna wahalar da tasha last time amma da ikon Allah ba ai aikin ba ta haihu, sai dai wannan karon kam a gaggauce likitocin suka fara fede Umaimah, cikin kankanin lokaci aka ciro mata twins dinta kyawawa mace da miji suma dai basu mata kara ba dan sakkk Jabeer babu abun da suka bari na shi, koda aka fito dasu gabbanin asuba Jabeer kifa kai yai a kasa yana sujjada ga Allah da ya bashi wannan double bless din, ya dade yana hasashen yan biyu ne a cikinta amma dan kar ya bata tsoro yai shiru, gashi taki a mata scan a lokacin dan wani irin taurin kai cikin ya zo mata dashi sosai Jabeer ya ke lallabata a time din, karamin aikinta ne bai mata komai ba ta fara kuka tun farkon dare har tsakiyarshi.
Hannu nasa suna rawa na karbi yaran saura kadan in yadasu a kasa, farin ciki nake ji sosai amma gefen zuciyata yana tsungulina har hawaye ya na taruwa a idona a take, manya dasu masha Allah kamarsu daya da Jay kamar an tsaga kara,dagowar da yai ne ya karbi yaran hadi da rungumesu a kirjinsa yana ta wage baki yasani juyawa na share hawayen da ya silalo min,
"My pretty, zo ki gansu" ya fada hakoranshi gaba daya a waje, matsowa na yi ina kakalo murmushin dole na ce, "Kama suke da kai hamma Jay"
Lakace hancina ya yi ya ce, "No pretty, macen nan dake take kama, and i like it,na ji dadin yadda tayo kammanninki kuma ina sonta sosai, ni da yaran ya hada ya rungume gam yana jin wani irin farin ciki.
Nurse dai mamakine ya cikata, ga can uwar yaya ko dinke ta ba'a gama ba na wuyar ciro yayan da tasha, amma gashi ana rungumar wata da murnar 'ya tayi kama da ita, ohhh Wato lamarin RIJALU sai wanda ya yi su, namiji sai Allah.
"Ranka ya dade sanyi zai musu illah" muryar nurse din ta dawo da Jabeer duniyar gaskiya,ba don ya so ba ya mika mata yaran jikinshi yana ta rawa yace.
"A wane hali matata take ciki? to komai normal insha Allah, yanzu dai tana bukatar hutu..,da sauri sauri kirjina ke harbawa amma ina ta ambaton Allah a raina dan kar inji kunya, ganin yadda gabadaya ya rikice rungumeni Jabeer ya yi bayan ya dawo da idanunshi daga kallon da yabi yayanshi ya ce,
"Pretty kina murna?" yesss ina murna mana hamma jay, koba yayanka ba ai yaran umaimah nawa ne balle kuma sun fito ne daga kai zuwa ita, so kaga nice mutum ta farko da zan yi farin ciki".
"Ah ah, yau naga ikon Allah, cikinka zaka maida itane Jabeeru? kai ko kunyan idon jama'a bakayi a al'amuranka ka kwakume yar jama'a haka? ke kuma da shike sakarai ce kin sakar mishi jiki kamar wata sauna" Muka jiyo muryar Daada a bayanmu.
Da hanzari ya sakeni ya ce, "Yau naga ikon Allah, Daaada nida matata kuma kike sakin zance haka, wa ma ya fitar dake da asubahin nan?"
Sosa kai ya yi yana dan matsar da ido bayan sun hada ido da Innarmu dake tsaye tana jin abun da suke fada."Gyatumarka ta fito dani ja'iri kawai,,bai ce komai ba sai gaisawar da suka yi da Inna ashe Maryama ta kira ta sanar musu shine suka kasa hakuri suka fito.
Umaimah bata farka ba sai washegari har wajajen sha daya na safiya, babu kunya a gaban su Inna da Baffa ya rungume ta da bata kiss yana mata sannu, sai sune suka kauda idanu.
Kwananta uku aka sallamomu, Ba karamar liyafa Jay ya shirya ba na sunan twins,kaya kuwa tamkar kasuwar kwari ta kano ya kwaso gaba daya, dan daki musamman aka ware hadi da jibge kayan twins din a ciki,a bangaren kayan mai jego kuma duk abun da ya saiwa Umaimah bisa adalci nima ya saya min kuma na karba hannu biyu na yaba. ranar suna yara suka ci sunansu Hassana da Hussain, wannan karonma ni Umaimah ta tambaya sunan da za'a kirasu, na ce
"Mu kirasu Janaan da Jawad, sunan suna min dadi ko zamu sanya musu, " tana murmushi ta ce, "Done Ummie".
Sosai muka sha shagali naira ta yi kuka, gagarumar walima Jay ya shirya a nan cikin gidan kuma sosai ya kawatu masha Allah, a wajen walimar ina rike da Anwar da zuwa yanzu ni kadai ya sani a matsayin mamarshi sai zirga zirga muke yi da su Fati da itama dai ta gado su baffanmu dan yan biyu ta haifa duka maza har sun girma ma, muke jigilar baki dan Umaimah likita ya hanata zirga zirga saboda yanayin tiyatar da akai mata.
Kamar saukar aradu haka naji maganar da wasu tarin hadaddun mata gogaggu suke fada a kaina,ina tsaye rike da Anwar ina bawa masu aiki Umarnin fara raba souveniers da na yiwa Umaimah na suna da kuma takeaway din kaji da snacks da Jabeer ya bada odarsu mussaman daga wani hotel sukuma matan da na fahimci matan abokanshi ne wasu kuma abokan aikinshi ne amma bamu wani saba dasu ba sun fi sabawa da Umaimah.
Suna bayana duk da kasa kasa suke maganar amma radau na jishi har cikin kwakwalwata.
"Nikam ba wannan ce amaryar da yallabai ya yi ba,"cewar daya daga cikinsu
"Ehhh itace amma sai girman kan tsiya kamar wata yar qaruna bata yiwa mutane magana Ko dan taga tana da kyau ne oho..
Ba laifi kam tana da kyau dama ta haihu ne, naga yaron ma har ya girma gashi sak da uban masha Allah....Inafa bata haihu ba ai dan uwar gidanne ta nanike gam in fada miki tsabar kisisina itakam har yau bata ajiye mishi kwai ko guda ba sai girman kai da dagawa,..Gashinan an kare a kan yayan kishiya, ni idan nine ita wallahi sai na ajiye da ko ya guda daya akalla kafun in tsiri girman kai."
Wani irin sarawa kaina kaina ya yi, a take na fara jin hajijiya na dawainiya dani,marata na dafe ina tuno cikina da yadda likita yasa karafa ya markade cikin siyama ta jefa a gutter,Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, ba tare da na juya na gansu ba na fara jan kafafuna da kyar na mikawa Salima Anwar na nufi main house din ina ganin mutane bibbiyu.
Ko ina a cike yake da mutane dan haka direct bangaren Hamma Jay na shiga hadi da rufewa da key ban tsaya ko ina ba sai bedroom na kwanta saman gadonshi na saki kukan da nake ta rikewa tun dazun, na yi kuka kamar an aiko min da sakon mutuwa har numfashina yana seizing.
tun ina yi da karfi har na koma sheshsheka a hankali kuma bacci ya dauke ni. ban san yaushe aka gama taron ba... jin wani abu mai sanyi yana yawo bisa fuskata ya sani bude idanuna a hankali na sauke su kan Hamma Jay, yana zaune bakin gadon sanye da bathrobe da alamar wanka ya yi.
Kuri idanunshi a kaina still hannunshi dake da damshin ruwan wankan da ya yi bai daina yawo akan fuskata ba.
"My Pretty, kin tashi? Duk kin daga mana hankali kinsa mun karade kaff titunan Abuja muna nemanki? me yasa kika rufe kan ki a nan?".
Sai a lokacin na dawo cikin tunani na tashi na yi na rike hannayensa duka biyu na kuma sakin sabon kuka..
"Ya salam!what happen pretty? me ya faru haka, fadamin mana, waya tabaki?."
Duk ya rikice sai sambatu yake yi, fadawa na yi kanshi ina kuka nake bashi labarin abun da ya faru dazun zuciyata kamar zatayi bindiga, na daura da fadin.
"Dan Allah Hamma Jay nima inaso zan haihu dan Allah.
Rungumeni ya yi tightly ya ce, "Pretty kin taba ganin wani ya ba wani haihuwa ne? shin su da suka haihu din wayonsu ne ya basu? shin ba zai iya amsa cikin second daya ba? ki daina damun kan ki akan irin wannan idan kin rasa ni'ima guda daya cikin tarin ni'imomin Allah, to ki duba sauran da ya baki sai ki gode mishi, beside pretty kwata kwata yaushe nema da har zaki tada hankalinki haka. da akwai wadanda suke shekara ashirin basu haihu ba, kuma Allah ya basu. Ke dan kin shekara daya baki haihu ba sai ki daga hankali".
"Ah 'ah ni dai muje asibiti, dan Allah muje asibiti su bani magani tun da ai kai gashi Umaimah tana haihuwa.
na rikice mishi dan haka yace yaji bayan kwana biyu zamu je asibiti din.
Washegari ko da su Innarmu da su Daada da basu koma ba har ma da maijego suka tambayeni abun da ya faru na rufe kaina a daki har sai da Aka kira hamma jay ya nemo spare key, cewa kawai na yi kaina ke ciwo kuma hayaniya ya yi yawa a nan din.
*********
Kamar yadda yamin alkawari bayan sati biyu da haihuwar Umaimah muka je asibiti. babban asibitin kudi ne mun samu layi sosai amma abunka ga manya bamu bi layi ba hasalima an san da zuwanmmu, dan haka a VIP aka ajiyemu dan dube dube likitan ya yi min sannan ya rubuta gwaje gwaje da za'ai min ya turani dakin gwaji tare da wata nurse, kusan yini muka yi abu daya daga wannan inji zuwa wancan daga wancan zuwa wannan, da kyar muka gama likitan yace sai nan da awa ashirin da hudu result zai fito dan haka gobe zamu dawo.
Wannan dare kusan ido biyu na yishi cike da damuwa da taraddadi dan ma mun biya gidan su Innarmu a can na karisa wuni, sun cikani da karfin guiwa ita da daada har ma da baffa, ko da na dawo ma Jay bai boyewa Umaimah ba kuma sosai tayi fatan nasara da addu'oi mai yawan gaske.
WASHEGARI.
Zaune muke gaban likitan ni da hamma jay, ban da bugawa babu abun da kirjina ke yi, yayinda Hamma Jay ya damke hannuna ganin sai rawa jikina ke yi. Gyara gilashinshi dr ya yi, yana kallon Hamma Jay ya ce, "Ranka ya dade kamar yadda muka gabatar da gwaje gwaje wadannan ya daga wasu takardu, sune sakamakon gwajin da muka gudanar kuma gwaji ya nun...