Page 76
MARYAMA💫
By
Ummu Fadeela.
76...
Gyara zaman gilashin idanunshi ya yi ya ce, "Kamar yadda kuke gani, wadannan sune sakamakon gwajin da muka gabatar. Kuma gwajin ya nuna......Tari likitan ya yi sau biyu ya dan kurbi ruwan gora dake gefenshi kana yasa tissue ya dan goge bakin,
"Afwan" ya fada ganin yadda muka zuba mishi idanu musamman ni H Jay yana rike da hannuna gam ganin yadda jikina ke kakkarwa.
Dan muskutawa dr ya kuma yi ya ce,
"Wasu daga cikin rukunonin kwayoyin cutar bakteriya da idanu basa iya gani ne sai da madubin duba rudu suka samu nasarar shiga cikin bututun mahaifarta suka haddasa blockage ta yadda ita bata iya producing kwayoyin hallitta idan naka sun shigo kuma waddanan hallitu suke yaki da su,amma kada ku samu damuwa Insha Allahu za'ai mata aiki kuma za'a dace da izinin Allah, takarda na biyun ya bude, ruwa ya kuma kurba yana share zufar dake tsatstsafo mishi kamar wadda yayi karya a gaban sarki.
Zuwa lokacin bani kadai ba,hatta Jay ya fara shan jinin jikinsa... yana muzurai ya ce, sai kuma dayan binciken ya nuna mana asalin uwar mahaifar ta ta samu tsaga ta dalilin cire ciki da aka taba yi ta karfin tuwo, cikin karafan da akai aikin kwakule cikin dasu ya yanka mata mahaif...."
Da sauri likitan ya kame bakinshi ya yi shiru ganin yadda Jabeer ya mike a haukace kamar zai cafkoshi, sai kuma ya dunkule hannu biyu ya naushi desk dake gabanshi take takardu da files files dake kai suka dinga watsewa a kasa da mugun karfi ya ce, Damn it noooooo!"
Sai kuma ya juya da sauri ya fita har yana hade hanya, tunda likitan ya furta dalilin cire ciki an yanka mahaifata na daina gane abun da yake fada, ban sani ba suma na yi a zaune ne ko mene ne? karan da yayi da zubewar takardu suka dawo dani hayyacina, a haukace na bi bayanshi ba tare da na dauki jakata da suka watse kan desk din ba.
Gudu na ke iya karfina ina bin bayanshi, yayinda gaba daya hankalin mutanen dake harabar asibitin ya yo kanmmu. jay bai damu da kallon da ake mishi ba, yasan da yawa ansan fuskarshi ko dai a zahiri ko a tv.
Bai fasa saurin da yake yi ba har ya cimma motarshi, thank God yau bai fito da securities ba da Allah kadai yasan abun da zai faru,yana yiwa motar key ina isowa, ban yi wata wata ba na afka ciki da sakin wani rikitaccen kuka, gudu Jabeer yake shararawa a kan titin iya karfinshi like his life depends on it,wani irin kara na sanya da masifar karfi na furta Jayyyyyyy ina faduwa a kanshi ganin wata tirela tayo kanmmu.
Kiiiiiiiiiii. Yayi wani irin wawan cin taya a gefen kwaltar, cikin amincin Allah gefen motar ce kadan tirelan ya goga cikin kiftawar ido mutane suka fara taruwa, sai dai kafun akai ga iso motar tasu ya kara bata wuta ya bar wajen ganin babu abun da ya faru, tashi na yi ina sauke ajiyar zuciya amma na cigaba da kuka.
Bai ce komai ba har muka iso gidan su Innarmu ga mamakina sabanin gida, a tare muka fito motar muka shiga ciki ina kwala ihu kamar an aiko min sakon mutuwa.
Daada ce ta fito daga daki saura kadan zaninta ya kai kasa, tayi azamar janyoshi ta na daura hannu a ka, "Mun shiga uku!me yake faruwa hari aka kawo mana ne muyi ta kanmu?" Innarmu ma ta fito daga nata dakin babu shiri turuss tayi a palon ganin mu jugum-jugum ni ina kuka Jabeer kuwa na tsaye kamar zai hadiye zuciya ga daada da zani a hannu.
"A'a gaskiya bakwa tsoron Allah, taya zaku zo ku firgita mu ku fitar da mu a hayyacinmu kuma ku tsaya cirko cirko kamar an dasa ku bakwa cewa komai! to aniyarku ta biku gaskiya bazan yafe firgita ni da akayi ina zaman lafiyata ba."Cewar Daada.
"Babana lafiya kuke? me ke faruwa haka,wani abun ya faru ne," Innarmu ta fada.
Takowa ya yi har cikin tsakiyar palon inda take tsaye, itace ke bashi dumi irin na uwa tun da ya taso a rayuwarshi, ita ce ke bashi shoulder da zai yi kuka a duk abun da ya sameshi don haka yana isowa kawai ya dan tsugguna kasancewar ya fita tsawo ya daura kansa bisa kafadunta yana sauke ajiyar zuciya da sauri sauri.
Inna tana ganin haka ta san wani abun yana damunshi, don haka ta fara shafa kanshi a hankali hankali yayin da take kallon Maryama da jikinta ke ta mazari kamar kace kyat ta arce da gudu dan tuni ta tsaida kukan.
Ya dade a haka sannan ya mike ya koma saman kujera ya zauna. Innarma zama ta yi, Daada dake ta kallon ikon Allah ta janyo Maryama dake halin firgita
"kya samu zama ai haka idan kun gama sai ku sanar damu abun da ke faruwa in kun gama dramar da kuke shiryamana a nan din".
Cewar Daada suna zama tare a kujera daya. Sallamar Baffa ne ya katse maganar da Daadar ta fara kafin ta ce, "Yauwa Alhassan, ai da kyar ne idan zan yafe abun da yarannan suka min yau, amma dai shigo muji abun da ya rikitasu haka tare dakai kafin muyi maganar shari'ar mu dasu.
************
Tiryan-tiryan Jabeer ya basu labarin abun da likita ya sanar dasu cewa mahaifar Pretty ta samu matsala sakamakon cire ciki da aka taba yi, lumshe ido ya yi ya bude idanun suna kadawa jajur sannan yace.
"Innarmu that means bazan ga d'a ko 'ya daga Maryama ba ke nan, bazata haifa min baby ba, me yasa ta min haka me yasa ta min haka? ya fada kamar zai yi kuka.
Gaba daya occupant na palon sanda zuciyarsu ya karye, gyaran murya baffa ya yi ya ce, "Jabeeru ashe baka yadda da kaddara ba, ashe baki yi imani da komai ya samu bawa a rubuce yake ba, ashe har yanzu imaninka yana da rauni? shin yanzu wa kake kalubalanta,? Ubangijinka? Wadda ya baka ni'imomi da kai kan ka yanzu baza ka iya kididdigesu ba? anya kuwa Jabeeru anya?."
Dan murmushi Inna tayi, ita ta fahimci abun da ke ran dan nata,a duniya duk wadda ya soka ya gama yi maka komai tabbas Jabeer na son Maryama don haka dole yaso tsatso daga gareta ko yaya ne.
"Babana ba likitan ya ce za'a iya yi mata aiki kuma a dace ba? me zai hana mu hakura da fushin haka dai mu koma dukkanmu muji yadda abun zai kasance ko tunda yanzu mafita ake nema".
"Wannan shine abun da ya kamata dijah, ba wai suzo su sakamu gaba suna kuka ba" cewar Daada,duk sadda Jabeer ya tuna dalilin cire mishi ciki,cikinshi na sunna mahaifar Maryama ta samu matsala sai yaji zuciyarshi ta girgiza, yana jin sai sa'a ma idan heartache na shi bai motsa ba yau din nan. Duk yadda yaso controlling kanshi kasawa yayi.
************
Ko da ya tashi tafiya a gida ya barni, ni dai na kasa hada ido da kowa ga damuwa da ya cika min zuciya.
Kamar yadda suka tsaida shawara washegari aka koma asibitin,bdukkanmu muka tafi hadda Daada Baffa da Innarmu, a reception suka zauna mukuma muka shiga ciki. sai da Jabeer ya fara da bawa likitan hakurin abun da ya faru jiya dr yace babu komai sannan ya daura da bayanin yanzu ina mafita.
Dan gyara zama dr ya yi ya ce, "Mafita daya ce zuwa biyu, na farko dai dole a mata flushing na fallopian tubes nata da ya samu blockage shine mataki na farko, aikin bashi da wahala a wajen yinshi amma wacce aka yiwa aikin zata dandani azaba duk ba wannan ba dole ne ana gama aikin ka kusanceta immediatly dole wannan haka ka'idar aikin yake. Idan an yi dace sai ciki ya shiga a lokacin ne kuma zamu ga shin za'aje mataki na biyu ne ko dai hakan ya wadatar,"
Waro ido Jabeer ya yi ya ce," How comes likita? taya zan kasance da ita a haka bayan kuma kace akwai wahala, and the worst part of it ma shine sai kowa yasan zan kebe da iyalina kuma a cikin asibiti?."
"Relax mana ranka ya dade, ai ba sai kowa ya sani ba dan VIP za'a kai ku. and wannan shine kadai solution duk inda zakuje a fadin duniyar nan abun da za'ai muku kenan," Jabeer dai jikinshi bai so haka ba amma ganin yadda Maryama duk ta fige lokaci kadan yace, "Yanzu ya za'ai,"
Likitan ya ce, "Ko yanzu kuke bukata za'a iya mata aikin as emergency ya fada yana tura mishi wani takarda, "ka sanya hannu anan".
Signing ya yi yana mikewa duk jikinshi babu dadi, salo salo Maryama ta bishi har suka shigo inda su Inna suke nan ya sanar musu za ai aikin yanzu har ya sanya hannu, duk addua suka yi da fatan Allah ya sanya alheri.
THREE HOUR'S AFTER.
Aka shiga da Maryama dakin da za'ai mata flushing din, tabbas aikine mai matukar wahala da azaba kuma babu damar a gusar mata da hankali, mintuna arba'in aka gama yayinda Pretty take jinta kamar lahira zata wuce tasha bakar azaba iya azaba ta galabaita kuma ta fita a haiyyacinta matuka, ana shigar da ita daki na mussaman likita ya garzayo inda suke zaune jigum jigum suna jiran ikon Allah ya ce, "Alhamdulillahi anyi aikin cikin nasara anma ana bukatar mijinta a kusa dan mu gwada jininsu,"
Jini kuma, me hadinsu da jini?" cewar Daada dan bata gane inda zancen ya dosa ba, "Daada likitane fa, kuma aikinshi yake yi" cewar Baffa,..
"Au kuma hakane, to maza jeka Jabeeru, " haka nan ya bi bayan likitan amma yana jin kamar sun san abun da zaije ya aikata.
Yanayin galabaitar da ya samu Maryama a ciki ya bashi tausayi matuka, lallai ana bukatar hakan da gaggawa ranka ya dade" cewar likitan yana fita da janyo kofar.
wajen kamar dakin gida yake sam bazaka ce asibiti ne ba, babban gadone har da kujeru a wajen.
Dago jajayen idanunta da suka koma kamar attarugu tayi, murya kasa kasa tace, "Me kake jira Hamma Jay, just do it, do it plssss i want to see my blood nima, get in plssss.
Sai hawaye shaaaa kamar an bude pampo, kana ganinta kasan ba 'a hankalinta take ba, she's feeling pain deep her.
Ba karamin tausayi ta bashi ba jin abun da ta fada har sai da ya matsar da kanshi gefe ya yi kokarin maida hawayen da suka ciko idanunshi babu shiri..
Cike da tausayawa yake binta ganin ko ina na jikinta ya nuna irin azabar da take karba, amma a hakan cewa take ya yi sosai tana son ganin blood nata itama....
***********
Umaimah dake gida ta kasa hakuri sai da ta zo asibitin ga danyen yara ga dinkin tiyata.
Kwannan Maryama biyu a asibiti likita ya sallamesu da tarin magunguna ya basu sati biyu su dawo a duba ko aikin ya yi kyau, amma da sharadin kar ta yi aikin komai an bata bedrest.
Don haka direct gidan Innarmu aka maida ita cewar Daada a gidansun can hawa da sauka ma kawai ya isheta, yanda ake kulawa da ita kuwa tamkar kwai akan cokali.
tsabar rashin kunya irin na Jabeer kusan tarewa ya yi a gidan, yana fita yake dawowa, idan wani aiki ya rikeshi kuwa bini bini zai kirata a waya. kulawa irin sosai dinnan yake bata, kwana ne kawai baya yi a gidan Innarmu amma ko yaushe yana nanike da ita,addu'a kuwa dukkansu suna yi na fatan an yi nasara a aikin itama Maryama ta dage da addu'a da istigfari, Innarmu kuwa masa (waina) ta dinga yi ana sadaka dashi.
************
Yau kwanakin da likita ya bayar suka cika, kusan dukkansu sukuku sukuku suka tashi yaudin, karfe tara na safiya ya shigo gidan shirye cikin wani yadi ash colour dinkin half jumper idan ka ga Jabeer a yanzu dole ka tsarkake girman ubangiji dan wanda ya yi mishi sanin da ba lallai ya ganeshi da wuri ba yanzu gaba daya hutu da jin dadi sun sauya shi.
Babu kowa palon time da ya shigo, dan lellekawa ya yi sannan ya yi wufff ya fada dakin Maryama,...Ina zaune bakin gado na yi tagumi, addu'a kawai nake a raina na ji shigowarshi, a hankali na dago kaina muka hada idanu, cikin takunshi na kasaita ya matso gareni yana murmushinshi mai sanyani mancewa da kaina da kuma inda nake.
"Ban hanaki zama shiru kina tunanin nan ba?" ya fada yana janyoni gefenshi.
"Hamma Jay tsoro nake ji, ina jin tsoron kar muje ba'a dace ba, my heart can't take it any longer."
Rungumeni ya yi ya ce, "Nima ina tsoro pretty, ina tsoron kar ace bamu dace ba,ina tsoron kar ace bazaki haihu min baby ko guda daya ba, but i have faith, i have faith in Allah, ina da yakinin ubangijin da ya azurta Annabi zakariya da samun haihuwar Annabi Yahaya zai dube mu,"
"Hamma jay laifi na ne. Da ban cire wancan cikin ba dai da yanzu babynmu ta girma, watakila ma na kara haifo was......"
"Shhhhhtttt" ya fada yana daura yatsarshi saman lebena gami da kara janyoni jikinshi ya rufe ido, duk sanda ya tuna abun yana jin daci a ranshi, yana kuma jin haushinta na dan lokaci, matsalan shine soyayyarta tana rinjayar fushin a take.
bayan wani lokaci kadan muka dunguma hospital din, wannan karon ni da shi sai Daada rigima kawai muka tafi banda innarmu.
Wasu gwajin aka kuma yimin, shiru muka yi gaba dayanmu kamar ruwa ya cinyemu lokacin da nurse ta shigowa da dr da result din gwajin da akai min. duk tsura mishi idanu mukayi cikin wani irin yanayi, kamar yadda ya tsurawa takarda idanu shima yana kallo...........