Page 77
💫MARYAMA💫
By
Ummu Fadeela
78..
Kamar idanuna zasu zube a kasa tsabar yadda na zaro su na kure likitan da kallo, yayin da kirjina ke bugun tara tara, shima Jabeer kusan hakan take sai dai yafi ta jarumta...."Mun yi kokarin ganin munyi nasara akan aikin nan amma onfurtunately bamu dace ba sai dai kar hakan ya daga miki hankali madam, dan akwai plan b. Kuma insha Allahu muna da yakinin a shi zamu dace. but now,cikin bai shiga ba kamar yadda muka yi fata".
Gimmmmmm, haka naji wani irin kara a tsakar kaina idanuna da suka yi laushi na dago na kalli Hamma Jay da su sai dai upside down na ke kallonshi, kanshi a kasa kafafunshi a sama, a hankali na furta, "Babuuuu babyn kumaaa hamma Jayyyyy".
Daga haka ban kara sanin inda kaina yake ba,.
Lokacin da na farka akan gadon asibiti na ga kaina ana min karin ruwa. gaba daya ahalina suna cikin dakin, Jabeer shima ya yi zuru zuru kamar shi yake jinyar.
Duk tasowa sukayi gareni, "Sannu takwara,kin farka, kai Allah dai ya takaita miki wadannan jarabawowi haka," cewar Daada tana shafa kaina. Dukkansu sannu suka min harda Fati da tazo daga gidanta.
Kwana uku na yi ana bani kulawa a asibiti dan sosai nake kokarin shiga depression shi ya sa likita ya bada shawarar a dinga debe min kewa.
Dr.Ya kira Hamma Jay ofishinsa inda ya bukaci ganin iyaye dan ayi bayanin dasu, jiki a mace Inna da Baffa suka shigo suma
"Well,abun da yasa na ce kuzo dukkan ku don kuji bayanin mataki na gaba ne, aikin da muka yi bai yi nasara ba, amma da ikon Allah na biyun muna da yakini a kanshi".Dan shiru ya yi yana studying fuskokinsu da kyau.
"Mene ne plan b,din likita, yaya yake kuma me yasa kake da yakini akai" inji baffa.
"Shiri na biyu shine DASHE, Dole ne a debi kwanta da nashi a mata dashensu cikin mahaifarta, bayan an yi aiki akan tsagar da wajen ya samu, idan mun dace cikin ya fara girma akwai wasu hanyoyi da zamu bi dan ganin ba'a rasa cikin ba, and dole idan cikin yakai wata tara kafin delivery day dinta ai mata aiki a cire dan akwai risky idan aka ce zata haihu da kanta, dan za'a iya rasa uwar da babynn, bama fatan hakan amma dai yanzu matakin aiki da kuma dashen sune farko".
Cikin sheshsheka innarmu ta ce, "Taya ya likita zaka ce mataki na biyu shine mai sauki bayan duk kalubalen da ka lissafo?"
"Kar ki damu Mama da Allah muka dogara,idan kun amince sai a gudanar da aikin?.
"Baffa ina ganin ko dai kasashen waje ya kamata mu je ne?al'amarin ya fara damuna makura".
Cewar Jabeer yana kallon Baffa..
Ranka ya dade duk wata kasa da zakuje a duniya abun da zasu muku ke nan, idan ma kunyi sa'a kenan,dan wasu kam ina tabbatar maka mahaifar gaba daya zasu cire su yar and that's finale". Likitan ya karbi zancen,amma kaga mu ma a nan muna da isassun kayan aiki da kwararrun ma'aikata.
"Jabeeru kawai mu gwada nan din idan ka amince da tsarin da ya bayar"...Take Jabeer ya sanya hannu akan takarda inda aikin zai lakume kudi kimanin naira million goma.
(Ya salam! my dear sister in islam, this is novel, is an fictiuos story, tsara shi akayi ta yadda mai karatu zai amfana...Ki tuna cewa ba lallai ke idan kin fita yawon duniya ya zama kin dace irin na Maryama kin dawo gida ba, ta yiwu a can zaki mutu cike da fushin Allah da na iyaye a kanki,idan kin dace kin dawo kamar na Maryama ba lallai ki dace iyayenki da mijin naki su yafe maki ba,idan sun yafe miki ba bu tabbacin har lokacin mijinki ko saurayinki yana miki irin wannan soyayyar mai kama da na mutuwa ba, zai yi wahala yar uwa a dai zamanin nan da muke ciki, idan har still yana sonki, bai zama tilas a ce yana da makudan kudaden da zai iya dawainiya dake don neman lafiyarki ba mussaman tin da shi yana da yaran ke kuma ke kika sani,yan uwa mu yiwa kanmu nasiha tun kafun lokaci ya kure mana,babu alheri cikin hange hangen daular da muke hangowa a wani waje, mu duba ko yatsunmu ma dake jikinmu ba daidai suke ba,ki daina hango wani abu da Allah bai baki ba kice dole sai kin samu,yar uwa kar ki hango gida daga waje ki dinga buri da muradin shiga don kema ki dandani daular dake ciki, baki san wanne irin daula bace,ta yiwu bakar daulace irin gidan Sameera,kina shiga ta firgitaki ta jijjige miki hadda gaba daya. Allah ya ganar damu gaskiya ya bamu ikon binta, Allah ya azurta mu da arziki na halali daga cikin taskar rahamarsa da bata yankewa, Ameen ya Rahaman).
Koda aka sanar min irin aikin da za'ai min da kuma makudan kudade da zai lakume,ban san lokacin da na balle drip dake hannuna ba na dirko daga gadon,kafan H Jay dake tsaye na kama bayan na kai duke kasa, "Dan Allah ka yi hakuri, laifi ne ne. ba dan aika aikar da na yi ba da bama a wannan hali yanzu k.....
"katseni ya yi ta hanyar kamoni ya hada da jikinsa, su Inna dai sai kawar da kai suka yi gefe,.
"Banason jin irin wannan maganar daga bakinki,is enough ohk? "ya fada yana shafa bayanta gently.
"Wane irin enoum kuma jabeeru, kai dai baka son gaskiya, ka iya kwakume yarinya gaban mutane kamar dai baka da ta ido, to nidai baza ku makantar da ni ba sai dai iyayenku suga duhu ja'irai kawai, babu zancen enoum kuma a nan ka bar yarinya ta koka ta fidda bakin ciki ahto, ki bar ganin muna cewa da sa hannun da aka miki, amma kar nake kallonki aradu,tsafff na yi haddar halinki tun da can fade ne kawai da ban ba. don haka ki koka kuma ki yi istigfari, dukkanmu nan da kika ga muna zaune lafiya har kawo tsufarmu musamman ni, ai ban taba sanya uwata zubar da hawaye ba ban sanyata shiga taskun rayuwa ba yo kinga ai dole in gama da duniya lafiya yan nan, kawai ki yi fatan Allah yasan hakan kankarar zunubanki ne ya kuma zama darasi ga saura wadanda sukaji labarinki.
to ni dai yi maza ka sake ta haba duk ka cukuikuiyeta kamar dai masu yin gasar dambe." cewar Daada tana ballar goro da taunawa...
Dukkansu murmushi suka yi baffa dai ya mike sumi sumi ya fita abunshi, ya san Daada fa dole sai ana mata uzuri dan ta tsufa, lafiya ce dai kawai Allah ya bata.(nikuma na ce Dada fa gaskiya ta fada,).Yana rike dani har bakin gadon ina ta sheshshekar kuka ya kwantar dani yana shafa kaina ya ce "Ya isa hakanan nace ya sanya hannu yana goge hawayen dake ambaliya a idanuna. kawar da kai gefe Inna tayi tana jin wani irin farin ciki yana ratsata ganin irin zallar soyayyar dake kara tabbatuwa cikin idanun Jabeer akan Maryama.
*****
Washe gari kamar yadda Jay ya sanya hannu, aka yi min aikin cike da fatan samun nasara, ban juma a asibitin ba aka sallamoni dan na fara samun sauki, gidan Jay aka maida ni kamar yadda Baffa ya bada umarni sai dai maimakon sama,a downstairs aka gyara min daki dan bedrest da likita ya bani babu yawan zirga zirga da daukar abu mai nauyi, duk maitar Jabeer haka ya hakura dan shima lallabani yake yi...sosai nake samun gata da kulawa daga gareshi da Umaimah,dan sometimes ko ruwa zansha sai Umaimah ta rike min cup din a cewarta kar ya min nauyi.
Tsakani da Allah take kulawa dani kamar kanta, ranar da muka koma asibiti aka tabbatar da shigar cikin kuwa ban san sadda na mike na durkusa kasa nayi sujudul shukr ba ina hawaye nake godewa Allah, Jabeer kasa rufe bakinshi ya yi, ya rasa me zai bawa likitan kawai ya ce mishi bana da kai da mahaifiyarka da matarka duk zaku tafi aikin hajji,"
Sai a lokacin ya kula da cewa ina durkushe, da hanzari ya dagani yana dariya nima ina dariya, gefe da gefen kumatu na ya rike muka cigaba da dariya hawaye yana bin fuskata. hannu yasa ya lakuce dimples dina ya ce, "dubeta mai son kuka kawai, oya ya isa haka. rungumeshi na yi da dan karfi, dan kara yayi yace, "Be careful pretty, kar ki janyo min asara,".Wannan likita dai yau yaga farar rana kuma yaga fararen masoya. tsabar yadda suka burgeshi baisan sadda ya fitar da wayarshi ba ya fara yi musu video cike da shauki.
******
Wani sabon babin nuna Soyayya da kulawa Hamma Jay ya bude a gareni,idan da soyayya tana yawa zan iya cewa nawa ta yi yawa,H J yana kaunata,Umaimah ko ta zama wani sashi na jikina,iyayena da yan uwana suna kaunata,.
Yau ma kamar kullum muna zaune dukkanmu a palon kasa. Tunda na dawo kasa sai yawanci hidimar gidan ya dawo kasa din, hamma jay da Umaimah da Meerah suna zaune a three seater kasancewar yau weekend babu inda yaje,twins kuma suna ta rarrafawa a kan carpet. ni kuma ina zaune bisa two seater Anwar yana kwance gefena, cikina dan kimanin wattani hudu cif ya fito das dashi gwanin sha'awa, ina rike da bowl mai dauke da pop corn a ciki ina ci. da shike cikin bai zo min da wani tsirfa ba kuma babu laulayi komai ci nake yi.
Hamma jay baya gajiya da kawomin duk abun da na bukata kana Umaimah bata gajiya da dafamin duk abun da nakeso,tuni na yi wani irin fresh, ko ina ya cika tsam hankalina a kwance, kallon labaran duniya muke a tashar aljazeera muna dan hira jefi jefi yawanci akan rayuwa ne, kamar almara kamar gaske naga an nuno hotonshi akan allon talabijin din, na ji kirjina ya bada sauti lokacin da aka tsaida hotonshi bisa allon talabijin din mai rahoto ya fara karanto irin criminal record nashi, hatsabibin mutumne mai asali daga Nigeria, babban dealer ne na hodar iblis wanda a yanzu mutum daya ne ke gabanshi a duk fadin duniya ta bangaren safarar hodar iblis din. Ya gagari kasashen duniya duk yadda aka so kamashi abun ya ci tura sai a jiya hadin guiwar jami'an (INTERPOL) yan sandan kasa da kasa suka yi nasarar kamashi a wani yanki dake kasar Dubai.
Hotunanshi ake nunawa daure da handcuff, hoton aka dauke mai rahoton ya bayyana,ya cigaba da zayyano irin bakaken harkallar da yake aikatawa da kuma yadda ya ringa artabu da jami'an tsaro a mabambanta lokuta kuma yana yin nasara, fuskar mai rahoton aka matsar aka sanya wasu kananan vidiyoyi na shi na yadda suka dinga artabu da jami'an tsaro,...Tunda aka fara rahoton hankalinsu gaba daya ya dauku a kai, ni kuma tunda kirjina ya bada sauti na fita a haiyaccina.
bana gane abun da ake fada sai wani irin jiri da nake ji, kamar a mafarki na ga hoton videon wani dare, daren da bazan taba mantashi ba a kundin kaddarata. lokacin da ake musayar wuta tsakanin su Abdallah da yaranshi da kuma yan sanda a Dubai, duk da bai yi haske ba kasancewar hoton cctv caught ne hakan bai hanani ganin kaina a ciki ba, haka bai hanani ganin chioma ba lokacin da muke bin jikin bango domin neman tsira da rayuwar mu.
Tsabar yadda kirjina ke bugawa ban san na mike ba da wani irin azabar karfi, kaina na hajijiya nake nuna tvn hannuna yana rawa
"ABDALLAH"
Na furta a lokacin da na ji wani abu mai dumi yana bin kafafuna kana idona ya fara rufuwa na tafi baga luuuuuu saura kadan in kai kasa Jabeer da ya taso a tamanin jin abun da ta fada ya tallabeta ta fada jikinshi idanunta suna rufuwa, a haukace ya fara shafa fuskarta yana kiran Maryamaaaaa Maryamaaaa.
zaro ido yayi ganin jini yana bin kafafunta "Nooo plsss, noo kar ki min haka pretty Noooooo". Gabadaya illahirin gidan sai da yayi amsa kuwwa ga muryar Jabeer, rikicewa Umaimah tayi gabadaya basirarta gudu ya yi a lokacin da kyar ta iya kiran, rabi, rabii rabiiiii, dukkan masu aikin dake bangaren a lokacin ba rabi kadai ba sun fito rabi driver, maza kira driver. kama Maryama tayi da Jabeer dake neman sandarewa a wajen suka fita tana kiran Nanny ta kula da yara.
A Emergency aka karbi Maryama da gudu Jay da Umaimah suka bi gadon da aka dorata a kai,sai dai kafun su iso tuni an rufe kofar dakin da aka sanyata.
Tsawon lokaci suna ta kai kawo a bakin kofar gabadaya sun kasa zama, gashi likitocin sai shiga da fita suke yi duk wanda Jabeer ya tare sai yace mishi "excuse me, minti daya" daga haka baya kara ganinshi, kusan awa daya da rabi suna kan Maryama don ganin sun ceto dan cikinta dake kokarin sauka, ba karamin wahala likitocin suka sha ba musamman babban docton da ya san irin yadda aka kwallafawa wannan ciki rai.
******
A hankali na bude idanuna da suka yi min nauyi tamkar an daura musu bulo inci tara a kan su. Cikin second daya gabadaya abubuwan da suka faru suka dinga dawowa cikin kwanyata daki daki, gabana ne ya fadi tunawa da cikina da nayi da kuma damshin da naji kafun in tafi duniyar suma."My babyyy" na fada da karfi ina danne marata da hannu,"My babyy, i lost my baby,innalillahi wa'inna ilaihirajiun,"
Da sauri dukkansu suka taso gareni, Innarmu ce ta rike hannuna da sauri ta ce, "Dawo hankalinki Maryama, kar ki lalata abun da aka taro da kyar." Wayyo Innata shikenan bazanga jinina ba, Inna na tuba na bi Allah na biki ba zan sake sanya ki zubar da hawaye ba wayyo na rasa babyna hamma jay come help me i lost my child."
Danne bakina daada tayi da karfi ta ce, "Can zaki ga shiga uku ba a nan ba munafuka, ko dan kinga ana tausaya maki ne kike son firgitamu ki fitar damu a haiyacinmmu eye? yarinya kamar yar maguzawa ya zaki dinga kiramana wayyo kin shiga uku daga farkawa,".
"Lallabata za'ayi kaka, ba lallai ku ku fahimci halin da take ciki ba sai wanda ya taba going through situation nata." cewar dr da ya shigo a lokacin tare da Hamma Jabeer.
Da hanzari ya karaso gareni, farin cikin da naga yana kwance saman fuskarshi ya yi nasarar kwashe kaso arba'in na damuwata, a gefena ya zauna hadi da kamo hannuna yana murzawa a hankali,ya ce, "Pretty, babynmu yana lafiya babu abun da ya sameshi cikin ikon ubangiji sun dakatar dashi daga faduwar da yai niyya."
Idona shabe shabe da hawaye na fara dariya ina dukan kirjinshi, Jabeer could'nt help it kawai ya rungume kanta ya fara sumbatar fuskarta suna dariya kamar su kadai ne a dakin.
Lumshe idanu Umaimah ta yi ta bude, wasu hawaye ne suka cika mata idanun ta daga kanta sama ta mayar dasu, sannan ta tako cikin nutsuwa zuwa gabansu ta hada Jabeer din da Maryamar ta rungumesu duka, tasowa ya yi ya sumbaci fuskarta itama nan suka cigaba da celebrating,sai da likitan yace a bar Maryama haka ta huta...Da daddare bayan komai ya lafa Jay ya tambayi Maryama abun da ya firgitata haka, bata boye musu ba ta sanar dasu wanda aka nuna a tv shine Abdallah wanda ta buge a dubai ta gudo nigeria, thank God bai rasu ba, nan suka jajanta tare da godiyar Allah da akayi nasarar kamashi, kuma irinsu ba'a jinkirin yanke musu hukunci.
********
Kamar yadda likita ya bada umarni bayan kwana biyu shine a bar Pretty a asibiti har sai lokacin da za'ai aiki a cire babyn yayi dan gujewa afkuwar wani accident din nan gaba, haka kuwa akayi.
bangare na musamman aka ware mata tamkar gidanta, sosai take samun kulawa daga bangarori da dama na yan'uwanta uwa uba soyayyar da mijinta yake nuna mata a gaban ko wanne mahaluki.
Kwanci tashi asarar mai rai, kwanaki suna ta tafiya, abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa harda dauko baban Umaimah da Jabeer ya yi ya dawar dashi Abuja, babban provision store ya bude masa dan yace bazai iya zaman banza ba,ya samu wata bazawara mai yaya bakwai amma basa tare duk sun yi aure ya aure abunsa suna zamansu lafiya, Jabeer bai manta da oganshi zubairu kafinta ba da sauran abokai wadanda akasha wahala tare,dama ya dade da fara ginin wani katafaren kamfani na furnitures wanda ya sanyawa suna (JMU FUNITURES NIG.Lmt.)dan haka ya dauko oga zubairu ya daura akai da sauran abokanshi na da, wadanda suka yi karatu kuwa ya samar musu aiki mai tsoka. babu abunda kake ji a bakunan su sai lallai abota tayi rana tsakanin su da Jabeer.
Ta dalilinshi sun fita a kangin talauci da fatara Ummarsu Umaimah kuwa garin bin bokaye dan a dawar mata da Umaimah gida a ruguza aurenta ta hadu da wani boka dan damfara inda ya kwakule idanunta ya yarda ita a jeji, da kyar aka samota yanzu haka bata gani duniya ta juya mata baya, kanwarta basira da ke taimakonta yanzu kullum cikin fada suke babu zamanlafiya dan sata take mata ita kuma babu idanun balle ta gani, mamar Siyama kuwa ta rasu shekaru biyu da suka gabata dalilin gobara wanda spark na wutar nefa ta haddasa.
**********
BAYAN WATA BIYAR.
A lokacin cikin Maryama ya shiga wata tara ciff da ikon Allah ranar litinin da safe aka shiga da ita tiyata bayan shafe wani lokaci likitoci suka yi nasarar ciro mata sankaceciyar yarta fara kal kyakkyawa dan wannan ya idan ta tashi tabbas sai tafi uwar kyawu cike da nasara da kuma bakin ciki domin mahaifar Maryama ta kuma tsagewa dole domin gudun rasata Jabeer ya kuma sanya hannu aka cire mata mahaifar baki daya. koda Maryama ta farfado aka sanar mata, bata damu ba sai ma godiya da ta mikawa ubangiji da ya bata guda dayan ta bakin Daada
*Ohhh takwara wannan ya taki itace kalen hanji kam". Gabadaya dakin dariya aka sanya.
Ana gobe suna aka sallami Maryama daga asibiti.
Ranar suna yarinya taci sunan Innarmu KHADIJA, Maryama bata yi kasa a guiwa ba itama ta ba Umaimah zabin sunan da za'ai wa yar alkunya, Umaimah ta sanya mata MIFRAH.
Ba karamin arziki aka tarawa Maryama ba a sunan Mifrah dan har mamaki abun ya dinga ba mutane, su Innarmu dai da addu'a suka bita Allah yasa arzikin ya bita har girmanta.
Mommyn Sadeeq ma da matarshi Khadija sun zo suna inda suka kawowa Maryama sha tara ta arziki dan Sadeeq kyautar mota sabuwa dal ya aiko wai na Mifrah ne, amma kememe Jabeer ya turbunawa fuskarshi toka yace baza'a amsa ba, da kyar su baffa suka sanya baki amma can gidan baffan aka kai ya durata a gareji daga karshe ma oga zubairu ya baiwa motar,..
Rayuwa tayi musu dadi, Umaimah da Jabeer sun mallakawa Maryama kyautar Anwar na har abada ganin yadda duk da ta samu nata amma ba ta daina son yaron ba, Maryama ta hada yayanta biyu ta rungume abunta, Jabeer yana ta samun cigaba da daukaka a wajen aikinshi babu abun da suka nema suka rasa, yawanci danginsu na nijar hatta da wadanda suka hada kaka na biyu zuwa uku babu wanda baya dandanar arzikin Jabeer. su Inna da Baffa da Daada kam babu abun da zasu ce sai alhamdulillahi anyi auren Salima itama babban dan kasuwa ta aura.
Komai yana tafiya musu yadda suke so tamkar su suka tsara, dama ance komai ya baka kuka watarana zai baka dariya.
Tsakanina da Umaimah bakajin komai, kishinmu a daki muke nunashi amma a zahiri watarana ma hadewa Jabeer kai muke yi ya kasa gane inda muka dosa.
***********
Yau ma kamar kullum muna zaune a palonmmu tsakiyar yayanmu dukkanmu farin cikine fal fuskokinmu dan Mijinmmu ya gama tenure dinshi kuma luckily an yi renewing masa wani tenure din dan haka kowa ka gani farin ciki fal ransa.
Da sallama ya shigo shima fuskarshi dauke da murmushi, zama yayi bisa three seater, mikewa na yi na kawo masa ruwa,hular dake kanshi ya cire yana karewa adon da muka rangada dukkanmu kallo wani irin dadi yana ratsa ranshi.
"Wai ni matan nan me sirrinne naga sai wani kyau kuke karawa? tukunna ma yau girkin wacece dan wllh rudani kuke yi in kasa gane abun da nake ciki".
Duk dariya muka yi harda yaran da basu san abun da akewa dariyar ba, hannu ya mika ya dauki janaan da jawad da suka zo gareshi a tare ya dagasu sama yaa musu wasa, yan lukutayena kuma me sirrinne kuke ta kara jiki haka, ganin haka meerah da anwar ma suka zo a guje ya dagasu dukkansu ya sumbacesu sannan yace ina Mifrah rikici.
"Hmmmm kaifa kasan rikici daddyn meerah, wannan dakyar idan ba boading school zamu kaita ba idan ta girma, yanzu na gama zagaye palon nan da ita na samu tayi bacci tana can dakina bisa gadonta, cewar Umaimah, duk dariya suka sanya Jabeer ya lakace hancin Maryama yace, "Maimahhh ai gado tayi, haka nasha wahalar renon uwar lokacin da take kamarta. Turo baki na yi gaba ina dire kafafu sukuma suna min dariya.
To duk ba wannan ba, ku matso kuji wani albishir,"
Da sauri na zauna a gefenshi ta hagu umaimah ta zauna a gefen dama, wani dan jaka da ya shigo dashi ya janyo gami da budewa, wani box ya fitar ya bude, "wowww"dukkanmu muka furta a tare, wata kyakkyawar DAHAM ce sarka da dankunne da bracelet kwance a ciki sai sheki take yi kamar zata kashe idanun mai kallonta, gefen da Umaimah take ya juyo yana murmushi ya kamota zuwa jikinshi, sarkar dake wuyanta ya zare a hankali, cikin wani salo mai rikitata ya sanya mata daham din a wuyanta, dankunnenta yacire ya sanya mata na sarkar, ya kamo hannunta ya sanya mata bracelet din, sannan ya sumbaci hannun doguwar sumba ya ce, "This is for you wife,I love you".
Wani irin yarrr Umaimah taji a jikinta take wani hawaye ya balle mata,rarumoshi ta yi tana kuka Maryama ma ta riketa, bai ce ko