ZALLAR SHA'AWA...

3-4

by @zahrasurbajo

Aisha ta zauna a gefen gadon da ke cikin ɗakin da  moneer ya ba su su zauna, tana kallon wasu sabbin akwatunan da suka cika kusurwar ɗakin, yayin da zuciyarta take cike da wani irin rashin kwanciyar hankali da ba ta iya bayyana shi da baki, domin duk da cewa ba su da wani zaɓi mai sauƙi bayan mai gidan da suke haya ya kore su saboda sun kasa biyan kuɗin haya a kan lokaci, har yanzu ta kasa yarda cewa ita da mijinta za su zauna a cikin gidan tsohon saurayinta, mutumin da a wani lokaci a rayuwarta ya kasance yana son ya aure ta, amma ita da iyalinta suka ƙi amincewa da auren saboda dalilan da suka shafi matsayinsa da kuɗinsa dan gujewa wulaƙanci se gashi yau gasu kuɗin nasa sun musu rana..
Ta ɗaga idanunta ta kalli jameelu wanda yake ta ƙoƙarin gyara botir ɗin rigarshi tace cikin sanyin murya

“Wallahi yaya, har yanzu zuciyata ba ta yarda da wannan shawarar da muka ɗauka ba, domin duk yadda nake ƙoƙarin ganin alherin da ke cikinta, ina jin kamar muna saka kanmu cikin wani yanayi da zai iya zama sanadin matsala a tsakaninmu nan gabane,abun sam beyi tsariba ace moneer ne ze bamu gurin zama”

Jameelu ya tsaya daga abin da yake yi, ya juyo ya kalle ta da kyau, sannan ya matso kusa da ita ya zauna a gefen gadon, yana ƙoƙarin fahimtar ainihin abin da ke damunta kafin ya amsa mata.
“Me kike tsoro, Aisha? Kin san ba zan taɓa kawo ki wurin da nake ganin zai cutar da ke ko ya rage mutuncin aurenmu ba, amma ki tuna cewa mun rasa gidan da muke haya ne saboda matsalar kuɗi, kuma a wannan lokacin ba mu da isasshen kuɗin da za mu biya wani sabon gida, don haka idan muka ƙi wannan taimakon da moneer ya ba mu, ina kike tunanin za mu je?”
Aisha ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta sauke idanunta ƙasa tana wasa da gefen gyalenta kafin ta ce,
“Ba wai ban san halin da muke ciki ba ne, yaya, kuma ba wai ina son mu kwana a titi ba ne, amma abin da nake tunani shi ne, shin da gaske babu wani wuri da za mu iya zuwa wanda ba gidan moneer ba? Ka san tarihin da ke tsakanina da shi, ka san ya taɓa neman aurena, kuma duk da cewa abin ya wuce tun da na riga na aure ka, ba na son mu kasance muna zaune a ƙarƙashin rufin mutumin da ya taɓa ƙaunata kuma aka hanashi,gani nake kamar ba dan Allah yakeson taimakonmu ba.”

Jameelu ya yi murmushi cikin natsuwa, sannan ya kama hannunta yana kallonta kai tsaye.Yace
“Aisha, kin san me ya fi muhimmanci a gare ni? Ina so kisani  ba ni da wata matsala da wannan wurin, domin na san ke matar aure ce kuma kin san matsayinki, sannan moneer ma bai yi wani abu da zai sa mu zarge shi da wata manufa ba; abin da ya yi shi ne kawai ya ga muna cikin matsala, sai ya taimaka mana ya ɗaukomu ya ce mu zauna a wannan boys’ quarters ɗin har sai mun samu damar tsayawa da ƙafafunmu.Meye abun damuwa aciki?”

Aisha ta kalle shi da idanun da damuwa ta cika, ta ce,

“Amma kasan mutane fa zasu magana akan hakan”

“Mutane za su yi magana mu ina ruwanmu tun da mun yi abin da ya dace,da rayuwarmune, Aisha idan mutum ya yarda da maganar mutane ya rasa abin da zai yi a rayuwarsa, ba zai taɓa samun zaman lafiya ba; ni abin da na sani shi ne, mu mun san abin da ke tsakaninmu, moneer ya san abin da yake nasa, kuma Allah Ya san abin da ke cikin zukatanmu.Dan haka mu barwa Allah kawai”
Ta yi shiru, amma har yanzu ba ta gamsu sosai ba.
Jameelu ya ci gaba da rarrashinta cikin tausasawa, yana gaya mata cewa ba zai bar ta ita kaɗai ba, kuma duk lokacin da ta ji akwai wani abu da bai yi mata daɗi ba za ta iya faɗa masa ba tare da tsoro ko ɓoye wani abu ba.

“Aisha, ki duba inda muke yanzu; muna da rufi a saman kawunanmu, muna da wuri mai aminci da za mu kwana, kuma babu wanda ya ce za mu zauna nan har abada, kawai muna buƙatar lokaci ne domin mu sake tsayawa da ƙafafunmu, don haka ki yi min wannan alfarma ki kwantar da hankalinki, mu zauna a nan na ɗan lokaci, idan Allah Ya kawo mana dama sai mu tashi mu nemi gidanmu.”

Aisha ta yi dogon numfashi, ta ɗaga kai ta kalle shi, sannan a hankali ta ce,

“Idan ka tabbatar min cewa wannan ba zai taɓa zama sanadin matsala tsakaninmu ba, to zan amince.”
Jameelu  ya murmusa, ya ce,“Na tabbatar miki, kuma ina roƙon Allah Ya sa ki daina tunanin abin da ya faru a baya, domin yanzu ke matar aure ce, ni kuma mijinki ne, abin da ya wuce kuma ya wuce.”

Aisha ta share hawayen da suka taru a gefen idonta, sannan ta gyada kai.

“To, shikenan, na amince mu zauna.”Jameelu ya yi murmushi cikin farin ciki, sannan ya ce,“Allah Ya saka wa moneer da alheri, domin a lokacin da muka rasa inda za mu je shi ne ya buɗe mana ƙofa.”