5-6
Aisha ba ta ce komai ba, sai dai ta kalli ɗakin da za su zauna, tana ƙoƙarin shawo kan kanta da ƙarfafa zuciyar a cewa ba komai zai faru ba.
Sannu a hankali Aisha da jameelu suka fara sabawa da rayuwar da suke yi a boys’ quarters ɗin, inda kowannensu yake ƙoƙarin yin abin da zai iya domin su tara kuɗin da za su yi amfani da shi wajen neman gidan kansu.
Moneer kuwa yana mutunta zaman nasu sosai, domin duk da cewa gidan nasa ne kuma boys’ quarters ɗin yana cikin harabar gidansa, bai taɓa zuwa wurinsu ba ko shiga cikin rayuwarsu ba tare da wani dalili ba, kuma wannan abin ya sa Aisha ta fara samun ɗan kwanciyar hankali.
Kuma duk abinda suke buƙata shi yake musu,abinci sutura,ba abinda be musuba,domin sabbin akwatunan dake cikin ɗakinsu mallaka musu yayi dan cike suke da sabbin kaya shaddoji da atamfofi da leshina kuma yabasu kuɗin ɗinki.Ya zame musu bango agidan da rayuwarsu.
Da ike iyayen su aisha da jameelu ƴan sudanne da karatun almajiranci ya kawosu nigeria gar zuwa lokacin da suka aurawa aishan ɗan uwanta jameelu,se suka tattara suka koma sudan ɗin sabida tsadar rayuwa a nigeria,shiyasa ba wani nasu da yasan sun koma gidan moneer.
************
Wani darene me cike da soyayya da nuna ƙauna tsakanin Aisha da jameelu,bayan sun samu biyan buƙata,ya shiga wanka,ya fito,sede yana fitowa ya yanke jiki ya faɗi aƙofar bayin dake cikin ɗakin nasu yana riƙe mararsa,numfashinshi na sarƙewa.
Da farko Aisha ta ɗauka wasa yake yi, domin tasan halinsane tsokanarta amma da ta juya ta kalle shi sai ta ga yana zufa sosai, fuskarsa ta canza, numfashinsa kuma yana fita da wani irin wahala.
Da sauri Ta diro agado tana ɗaura zaninta a saman ƙirjinta tana kiran sunansa.Ta nufeshi ta kamoshi“yaya lafiya? Me yake damunka?”
Jameelu ya buɗe idanunsa da kyar, sannan ya ce cikin raunin murya,
“Aisha... ban ji daɗi cikina marata...”ya kasa ƙarasa maganar sabida ciwon daya murɗeshi
Hankalinta ya tashi sosai, ta ɗora hannu a goshinsa, sai ta ji jikinsa da zafi sosai bana wasaba.
“Subhanallah! Yaya jikinka ya yi zafi sosai, me ke faruwa da kai?”
“Ban sani ba,” ya amsa, sannan ya rufe idanunsa saboda tsananin ciwon da yake ji.
Aisha ta fara neman wayarta cikin firgici, tana tunanin wanda za ta kira a wannan lokaci na dare, amma da ta duba lokaci sai ta ga ƙarfe biyu na dare, kuma babu wani mutum da ya zo mata a rai wanda zai iya taimaka musu cikin gaggawa.
A lokacin ne sunan moneer ya faɗo mata a zuciya.Ta tsaya cak, domin nan take ta tuna irin abin da ta taɓa faɗa wa jameelu game da rashin son ta kasance tana neman taimakon moneer, amma da ta sake kallon mijinta sai ta gane cewa wannan ba lokacin tunanin kunya ko abin da mutane za su ce ba ne.Rayuwar mijinta ce take gabanta.
Ba tare da ƙara tunanin komai ba lokacin da taga idanun jameelun sun kakkafe, ta ta fita da gudu daga ɗakin, ta nufi babban ɓanaren moneer ɗin tana kuka hankalinta atashe.
Da ta isa ƙofar ɓangaren sai ta shiga kiranshi tana buga ƙofar,moneer cikin barci ya ji muryarta tana rawa yayin kiranshi.Yajiyota tana faɗin
“moneer, don Allah ka taimake mu.Ka fito”
Nan take ya farka ya gyagije sosai.Ya fito da gudu ya buɗe ƙofar yaganta ɗaure da ɗaurin ƙirji kanta a yamutse tana kuka
“Aisha? Me ya faru?”cewar moneer aruɗe
“yaya ne, ba shi da lafiya sosai, jikinsa yana ƙuna da zafi kuma numfashinsa yana wahala, ban san wanda zan kira ba, shi ya sa na zo wurinka, don Allah ka zo ka duba shi.”
Moneer bai tsaya ɓata lokaci wajen yin tambayoyi da yawa ba.Yace
“Ki koma wurinsa yanzu, Aisha, ki tabbatar yana kwance, ni kuma ina zuwa.”
Yana gama faɗa mata haka ya juya cikin gidan ya ɗauki jakar kayan aikinsa ya fito da sauri, sannan ya kira mai gadinsa ya tashi ya buɗe masa ƙofa.
Cikin ɗan lokaci kaɗan ya iso wajen boys’ quarters ɗin.Ya tsaya yana sallama.
Aisha ta fito ta tarbe shi tana cikin tsananin firgici da tashin hankali tke faɗin..“Don Allah ka taimake shi.”
Moneer ya kalle ta cikin natsuwa, ya ce,
“Ki kwantar da hankalinki, zan yi abin da zan iya.Insha Allahu ze samu sauƙi”
Daga haka Ya shiga cikin ɗakin kai tsaye ya durƙusa kusa da jameelu, ya fara duba shi cikin ƙwarewa, yana sauraron numfashinsa, yana duba bugun zuciyarsa da zafin jikinsa, sannan ya sake tambayar Aisha wasu abubuwa game da yadda rashin lafiyar ta fara.
Bayan ya gama dubawa, sai ya ɗaga kai ya kalli Aisha.Yace
“Dole mu tafi asibiti yanzu.”
Aisha ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi tace
“ Asibiti Yanzu?”
“Eh, yanzu, saboda ba zan so mu zauna muna jiran abin da zai faru ba.Agaba may be sakamakon bazeyi daɗiba shiyasa zan kaishi asibiti zanfi kulawa dashi acan”
Gyaɗa mishi kai kawai tayi jikinta na rawa
Nan take monerr ya fita ya kira mai gadinsa, sannan shi da mai gadin suka taimaka wajen ɗaga jameelu daga kan tiles suka fito da shi zuwa mota.
Aisha tana biye da su sanye da hijabinta tana addu'a, tana roƙon Allah Ya taimaki mijinta.
Da suka isa motar, suka saka jameelu a ciki, Aisha ta shiga kusa da shi, yayin da moneer ya zauna a kujerar direba, aisha kuma ya zauna a bayan motar domin taimaka wa jameelun..
Moneer ya kunna motar ya fice daga harabar gidan cikin gaggawa, yana mai da hankalinsa kan hanya, yayin da Aisha take riƙe da hannun jameelu tana cewa,
“Allah Ya taimake ka, mijina, don Allah ka daure"
Aisha ta ɗaga kai ta kalli moneer ta cikin madubin motar, kuma a karon farko tun bayan da ta amince su zauna a gidan nasa, sai tajinkunyarsa domin ta fahimci cewa duk tsoron da ta yi na zaman dashi gashi bai hana shi taimaka musu ba lokacin da suka fi buƙatarsa.
duk da irin saurin da yake yi, hankalinsa bai kasance kan hanya kawai ba, domin lokaci zuwa lokaci yana kallon Aisha ta cikin madubin motar, yana lura da yadda take riƙe da hannun jameelu tana kuka da addu'a, kuma a wasu lokutan idanun moneer sukan tsaya a kanta na ɗan lokaci kafin ya mayar da su kan hanya.