7-8 tirƙashi
Aisha ba ta lura da hakan ba, domin hankalinta gaba ɗaya yana kan Moneer,
Bayan ɗan lokaci, moneer ya ta mbayi Aisha cikin murya mai sanyi, “Tun yaushe jameelu yake fama da wannan ciwon?”
Aisha ta amsa masa tana kuka, “Ban sani ba, yau ne kawai na fara ganin yana yin hakan dan lafiya lau muka kwanta.”
Moneer ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce, “Da kuka lura bejin daɗi .Da kun haƙura da kwanciyar auran na wannan daren zuwa ya samu sauƙi ay,”
Da sauri Aisha ta kalle shi cike da mamaki, domin ba ta fahimci dalilin da ya sa ya furta kalamansaba, .Amma data kai dubanta jikinta taga ɗaurin ƙirji tayi shi jameelu da gajeren wandone ta dena mamaki domin ta hakane ze gane wani abun ya shiga tsakañinsu. A daren tunda da zasu fitone tasa hijab ɗin.
“Ban san abin da ze faru ba kenan” ta ce cikin rauni. “Da na san haka, da tun farko baa faraba”ta faɗi hawaye na biyo idanunta
Moneer bai amsa mata ba, sai dai ya ci gaba da tuƙinsaAmma a zuciyarsa akwai wani abu da yake ɓoyewa dan tsintar kanshi yayi da jin ɗacin amsar da aishan da bashi..
Ba tun yau ne ya fara tunanin Aisha ba da jin wata mahaukaciyar shaawarta.Tun ranar da ya gan ta ta dawo gidansa tare da jameelu wani tsohon abu da ya yi shekaru yana ƙoƙarin binne shi a zuciyarsa ya sake farkawa wato shine ZALLAR SHA'AWAR aisha da yakeji wacce tasa yayi yunƙurin auranta abaya.Amma iyayenta suka hanashi sukaba jameelu.Shaawar da ya taɓa yi mata ba ta mutu gaba ɗaya ba.Ya dai koya wa kansa yadda zai ɓoye tane.
Amma Kuma yanzu, ganin Aisha a cikin gidan nasa, musamman ganin yanzu data dogara da shi a lokacin da take cikin matsalane, ya sake buɗe wani ƙofa da ya kamata ace ya kasance a rufe.Wato ƙofar tunanin yadda zebi ya kauda Zallar shaawar aisha dake cikin zuciyarsa..
Bayan wasu mintuna, suka isa asibitin.
Da motar ta tsaya, ma'aikatan asibitin suka fito da gadon ɗaukar marasa lafiya, suka ɗauki jameelu suka shiga da shi cikin gaggawa.
Aisha ta bi su da sauri, amma kafin ta shiga ɗakin emergency, moneer ya riƙe hannunta.
Cike da mamaki ta waigo ta kalleshi jin ya riƙetan
“Ki zauna a nan.”ya faɗi a hankali
Aisha ta kalle shi.Tace
“Me ya sa? Ina so in shiga wajen mijina ne.”
Moneer ya ce cikin natsuwa, “Aisha, likitoci suna aiki. Idan kika shiga za ki hana su aiki cikin sauƙi.”
“Amma…”ya katseta
“Ki amince da ni.”
Ta yi shiru.Tana kallonshi
Moneer ya sake kallonta na ɗan lokaci, sannan ya ce,
“Na miki alƙawari zanyi iya yi na inga na ceci shi.”
Aisha ta gyada kai, ta koma ta zauna.
Moneer ya juya ya shiga cikin emergency.
Kodaa ya shiga, sai ya tsaya na ɗan lokaci yana kallon jameelun da likitocin da suke ƙoƙarin taimaka masa.
Fuskarsa ta canza.Zuwa mugunta da son cinma buri da ɗaukar fansa.
abin da Aisha ba ta sani ba shi ne, a cikin wannan dare ne moneer ya fara tunanin ɗaukar matakin da zai iya canza rayuwarsu gaba ɗaya.
Yana son Aisha.Kuma wannan karon, ba ya da niyyar sake barin ta ta sake kubce masa cikin sauƙi.
Shiyasa yaje yaja tawagar maaikatan domin ceton jameel ɗin kamar yadda ya nuna a zahiri wanda a baɗini ba haka bane.
Bayan wani lokaci mai tsawo da Aisha ta yi zaune a kujerar da ke wajen ɗakin emergency tana ta addu'a, sai ƙofar ɗakin ta buɗe, Doctor moneer ya fito da wata irin damuwa a fuskarsa, wanda ganin hakan ya sa Aisha ta miƙe da sauri ta nufe shi, domin tun lokacin da suka iso asibitin zuciyarta ta kasa samun nutsuwa, musamman ganin yadda aka shiga da jameel cikin gaggawa ba tare da an ba ta cikakken bayani kan abin da yake faruwa dashiba.
“Doctor moneer, ina yayan?” ta tambaya cikin rawar murya, tana kallon fuskarsa domin tana son gano ko akwai wani abu mai kyau ko mara kyau da zai faɗa mata.
Moneer ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce, “Aisha, ki yi haƙuri, amma akwai wani abu da ya kamata in gaya miki.”
Jikinta ya yi sanyi.Tace
“Me ya faru da mijina?”
Moneer Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, “Yanayin jikinsa bame sauƙi ba ne, kuma bayan binciken da muka yi, mun gano cewa dole ne a yi masa aiki cikin gaggawa domin a samu damar ceton rayuwarsa.”
Aisha ta kalli moner kamar wadda ba ta fahimci abin da ya faɗa ba.Tace
“Aiki?Kuma”
“Eh.”
“Amma Doctor, me ya same shi? TunDa safe har zuwa darenfa yana lafiya.”
Moneer ya yi ƙoƙarin kwantar mata da hankalinta.Da cewa
“Wasu cututtuka suna iya bayyana ne cikin gaggawa, kuma yanzu ba lokacin da za mu zauna muna tambayar dalilin da ya sa suka faru ba ne; abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa dole ne a ɗauki mataki cikin gaggawa.”
Aisha ta fara hawaye.Tace cikin raunin murya
“Zai rayu kuwa?”
Moneer ya ɗan yi shiru kafin ya ce, “Idan aka yi aikin da wuri, akwai damar ya rayu.”
A wannan kalma ce Aisha ta fashe da kuka.Tana faɗin“Don Allah, Doctor, ka cece shi. Shi ne mijina, ba ni da kowa a nan.Sai shi in ya mutu ya zanyi”ta faɗi cikin kuka
Moneer ya matso kusa da ita yace.“Ki yi haƙuri, Aisha.”
Ta share fuskarta da hannunta, sannan ta ce cikin kuka, “Amma ba mu da kuɗin asibiti, Doctor. Ka san halin da muke ciki, mun rasa gidanmu ne saboda rashin kuɗi, shi ya sa muka zo muka zauna a gidan ka, yanzu kuma ka ce sai an yi masa aiki; ina zan samo kuɗin aikin nan?”
Sadeeq ya kalle ta cikin wani irin yanayi da ya sa Aisha ta ji kamar shi kaɗai ne sauran gatanta.
“Ki daina tunanin kuɗi yanzu.”
“Amma…”
“Na ce ki daina.”ya faɗi a tausashe
Aisha ta yi shiru tana kuka.
Moneer ya ci gaba da magana cikin murya mai sanyaya zuciya.
“Ni zan ɗauki nauyin komai.Kama daga Asibitin, likitoci, magunguna, da duk abin da ake buƙata, zan biya.”
Aisha ta ɗaga kai da sauri.Ta kalleshi tace murya na rawa
“Da gaske?”
“Eh.”
“Amma Doctor, ta yaya zan biya ka? Wallahi ba mu da abin da za mu ba ka.”
Sadeeq ya yi murmushi mara ƙarfi.Yace
“Ban ce sai kin biya ni ba.”
Aisha ta kalle shi cikin mamaki.Tace
“To me kake so?”
Moneer ya zaro wata takarda daga cikin fayil ɗin da ke hannunsa.Yace
“Sa hannunki kawai nake so.”ya faɗi yana miƙa mata takardar
Aisha ta kalli takardar, amma hankalinta bai tsaya kan rubutun da ke jikinta ba, domin a wannan lokacin duk tunaninta yana wajen jameelu da take tsoron rasa shi.
“Me zan sa hannu?”
Moneer ya ce, “Takardar amincewa ce da aikin da za a yi masa, domin ba za mu iya ci gaba da ɗaukar wasu matakan ba ba tare da izinin iyalinsa ba.”
Aisha ta ɗan matsa kusa da shi.
“Idan na sa hannu, za ku fara aikin?”
“Eh, kuma ba za mu ɓata lokaci ba.Zamu gama”
Hannun Aisha yana rawa.Ta kalli ƙofar emergency, sannan ta kalli takardar da Smoneer ya miƙa mata, kafin hawaye su sake zubo mata.Tace
“Don Allah ka ceci shi.”
“Zan yi iya ƙoƙarina.”ya bata amsa
Aisha ta ɗauki biron dake kan takardar.A cikin yanayin tashin hankalin da take ciki, ba ta zauna ta karanta takardar dalla-dalla ba, domin abin da take gani a gabanta shi ne kawai rayuwar jameelu, kuma abin da take tunani shi ne yadda za a ceci mijinta kafin lokaci ya kure.
Ta sanya hannu a wurin da moneer ya nuna mata.
“Na gama.”ta faɗi gamida miƙa masa takardar
Moneer yasa hannu ya karɓi takardar a hankali.Ya duba sannan yace
“Eh, kin gama.”
Aisha ta share hawayenta.Tace
“Yanzu za ku fara aikin?”
Moneer ya gyada kai.
“Za mu fara.Sai ki tayamu da addua”ya faɗi gamida juyawa ya koma ciki fuskarsa ɗauke da wani shaiɗanin murmushi.
Ita ko aisha Ta koma kusa da ƙofar emergency tana addu'a, ba tare da ta san ainihin abin da ta sa hannu a kai ba.
Domin takardar da moner ya miƙa mata ba takardar amincewa da aikin kawai ba ce kamar yadda ya gaya mata.
A cikin takardun akwai yarjejeniyar da ta ba da izinin cire ƙodar Moneer guda ɗaya.
Aisha kuwa, saboda tsananin firgici da son ganin mijinta ya rayu, ba ta karanta ko kalma ɗaya daga cikin abin da ta sanya wa hannu ba.
Yana shiga cikin ya kalli takardar a hannunsa, sannan ya ɗan ɗaga idanunsa zuwa inda Aisha take zaune tana kuka.Fuskarsa ta yi wani irin mummunan murmushi mai wuyar fahimta.ya mayar da takardar cikin fayil ɗinsa ya maida ƙofar ya kulle.