PAGE 2
by @swrites22
SAIFUDDEEN MUHAMMAD TAFEEDAH shine asalin sunan sa dan asalin garin Maiduguri ne qabilar shuwa Arab, shi kadai ne awajen mahaifinsa Malam Muhammad tareda mahaifiyarsa malama aisha, su bawasu masu kudi bane amma suna da rufin asiri sun sha wahala kafin Allah yaba su da' suka sa masa suna saifuddeen wanda suke Kira da saif daga shi kuma basu sake haihuwa ba. Saif ya taso cikin gata da kulawa yayi primary da secondry school dinsa a kauna private school Maiduguri bayan yayi graduation na kammala secondary school suka shirya tsaf domin zuwa Kano ziyarar yayar mahaifinsa a hanya ne suka hadu da accident Inda take a wajen mahaifansa suka rasu aka kawosu AKTH saif kadai ne yatsira a cikinsu dukda shima yajijji rauni amma ba sosai ba, yayar mahaifinsa ita ta daukeshi awajenta ta dama Allah bai taba bata haihuwa ba Yan uwan mahaifiyarsa sunso su karbeshi amma yayar mahaifinsa tayi firr tace basu isaba dole suka hakura suka barmata, bayan arba in din mahaifansa yasamu schoolarship a Qatar, bawani bata lokaci ya tattara ya tafi Inda yafara karantar business administration, a shekara ta biyu allah ya hadashi da raheela awani supermarket ita ba yar garin bace hutu tazo wajen kanwar mamanta, ita balarabiyyar kasan Oman ce tun daga nan suka fara soyayya har hutun ta yaqare ta koma can Oman din amma kullum suna maqale a waya, bayan ya kammala karatunsa ne ya dawo Nigeria yafara business har Allah yasawa abin Albarka cikin kankanin lokacin yaje can Oman din ya aurota har iyayenta ma suka sake taimaka masa da wani abun wanda dashi yaqara bunqasa business dinsa. Yarsu ta farko mai suna zeenerh an mata aure tana zaune a abuja da yayanta biyu Nabil da nabeela sai mai bi mata Aisha wadda suke cewa maeesha sai kuma auta Ameer, tsakanin maesha da ameer shekara daya da rabi ne shiyasa sukafi shakuwa saboda kusan tare suka taso.
maesha yarinyace Mai kimanin shekaru sha takwas a duniya, fara ce tas dan ita carbon copy na mahaifiyarta ne, tana da doguwar fuska da dogon hanci da idanuwa dara dara wanda suka Kara kawata cute face dinta bata da girman jiki domin idan Ka kalleta Ka kali ameer zaka zata shine babba.
CIGABAN LABARI
A gaggauce tafito sanye da Arabian gown navy blue colour ta yane kanta da madaidaicin mayafin kayan, fuskarta fayau bawani makeup sai kajol da tasa. " sabahul Khair Ummu".ta fada tana shigowa kitchen din, "Sabahul nur habibaty, badai har kin shirya ba ?
"wallah ummu na mayi late Allah yasa lecturer nan bai shiga class ba.
"Baza ki tsaya abbah naku ya fito ba Kenan
"ummu nafa makara ta fada tana zuba tea
"To shikenan amma kya tsaya ki karya ai
"A a ummu zanyi a can kawai.
" tho shikenan a dawo lpy take care of yourself". sumbatar goshin ummu tayi a gaggauce ta ce idan abbah ya fito ki fadamasa na wuce.
" to saikin dawo Allah ya tsare .
tana fita tasamu napep ta fada masa Inda zai kaita dan ta dauka meela ta wuce cox school ɗin su ɗaya haka course ma.
tana shiga school ta hadu da coursemate dinsu Maryam bayan sun gaisa maryam ta ce kinga munyi late wallahi ance har ya shiga fa .
"mun shiga uku harya shiga fa kika ce?"
"Ai dago kafa zakiyi mu hanzarta, karki tsaya wannan tafiyar take ta masu tausayin ƙasa".
" Ai saidai kikawo jirgi ya dirar da ni kawai ". Haka suka wuce suna hira, ta baya suka shiga suka nemi wuri suka zauna, sai bayan 2 hrs sannan suka fito.
"huh gsky lecturer nan akwai naci whl ga lecture sa is so boring. Wai ina Meela ne, banganta ba ?
"Kuma gashi da alama ma bata shigi school din ba, amma in na koma gida zan leqa gidansu naji ko lpy.
"ALLAH yasa lpyn. Ni bari na wuce maesha kya gaisheta.
Da haka sukayi sallama kowa ya nufi nasa wurin.
---------------
MUHAMMAD SAMEER ADAM JIKAMSHI shine asalin sunansa mahaifinsa dan asalin kauyen jikamshi ne, makiyayane, Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa tun yana dan shekara goma shine babba sai kannensa mata biyu fatima da samna hakan yasa tun bayan mutuwar mahaifinsa mahaifiyarsa bata nuna masa Kashi ba dukda kankantarsa ta nuna masa neman na kai, ahaka yayi primary school a makarantar gomnati yagama ya shiga secondry, baibar kannan sa da mahaifiyarsa a wulakance ba duk jumma'a ya kan zuwa Kano neman dako har Allah yakaishi kamfanin wasu turawa suka jashi ajiki ganin yaron yana da kwazo gashi ƙarami amma yana neman na kansa hakan yasa suka bishi har kauyensu suka gana da mahaifiyar sa suka ga kannen sa .
Bayan ya kammala secondary school dinsa ne suka dau nauyin cigaban karatun sa a nan Kano inda ya samu gurbin karatu a BUK bangaren agricultural science, dole ya tattaro ya dawo hostel saidai duk friday Yana zuwa gida ya dawo Sunday bayan yagama ya yi service ne waannan turawan suka dauke shi aiki nan fa budi ya sameshi harya dauko mahaifiyar sa da yan uwansa ya dawo dasu kano. Daga baya yasayi gida ya bawa mahaifiyarsa a lokacin kannensa sun kammala secondary manema sun fara kawo masu hari baiyi kasa a guiwa ba yace su fito da wanda ya musu aciki in yaso su jona karatun a agidan mazajen su mahaifiyarsa ma ta bashi goyon baya sosai.
Ba bata lokaci akayi auran kannen nasa duk suna zaune a nan garin Kano kuma mazajen su ma alhamdulillah suna da akwai.
buɗi yayi budi Inda har Sameer Adam ya fara ketarawa kasashen waje turawan nan ne sukeson maidashi kanfanin su na can, nan mahaifiyarsa tafara matsa masa akan yayi aure Ko ta nema masa, cewa yayi ya bata zabi dan shi bashi da lokacin da zai iya tsayawa da wata bare aje ga maganar aure nan kuwa ta tambaya masa yar makociyar su asalinsu yan Ethiopia ne amma anan suke zaune da familyn su kusan rainon Nigeria ne asalin su ne kawai can din, yarinya mai hankali da nutsuwa, nan ya samu gida ya saya ya tare da amaryar sa.
Bayan shekaru biyar duk Inda ake zancen arziqi to ya zauna masa amma har lokacin ALLAH bai basu haihuwa ba daga baya yakoma America da zama gabaɗaya, shekararsu biyu da komawa America ata ukun Allah ya azurtasu da samun da namiji suka samishi suna Muhammad yaro yataso cikin gata da jindadi amma miskili ne nakin karawa idan kika ganshi Yana wasa da dariya to da momma ne ko papi ko kuma kakarsa ko a cousins dinsa dai dai kune zasu iya cewa sun taba ganin dariyar sa tun yana karami, ga zafin rai amma duk da haka baya wasa da karatu na boko da islamiyya, tun safe idan ya tafi sai 5pm yake dawowa, makarantar wasu misrawa ne suka bude ta kuma suna koyar da boko da arabi.
Tun daga kansa kuma Allah bai sake basu wata haihuwar ba haka Muhammad yayi primary yayi secondary In da graduation din sa ya hadu biyu dana kammala secondary dana saukar alqur'ani mai girma, abokansa biyu tun primary su kadai ne suka iya zama dashi suyi fada su shirya faez da nashed, faez dan Nigeria ne fulanin Adamawa ne babansa shine ambassador na Nigeria a America shi kuma nashed iyayansa larabawan dubai ne aiki ya kai mahaifinsa can .
su ukun nan Kansu ahade yake ko sunyi fada ba Wanda yake jin Kansu har su shirya hakan ya janyo abota mai karfi a tsakanin iyayensu .
Duk da zafin Kan Muhammad Wanda suke Kira da moha sun iya zama dashi haka kuma in yayi fushi su kadai ke iya tausar sa, bayan graduation din nasa ne alhaji sameer Adam yaso tattara kan iyalinsa su dawo Nigeria amma halin da tilon dansu ya shiga na rabuwa da abokan sa yasa suka nema mashi admission a Cambridge university London tare da tahowa suka barshi a can ba tare da sun so ba sai dan farin cikin tilon dan su Wanda zai fara karantar Architecture. Wanna Kenan.