FreeArewaPen original
BELOVED HEARTS
- 1views
- 41chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Hey there! I'm SultyWrites AKA youngwriter. The Author of 10 fictional stories📚 A writer who believe that words have the power to inspire, to heal, and to transform. I aim to craft stories that reflect the beauty of our shared human experience, with all its complexities and n...
Sample · PAGE 1
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMZAMU FARA DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI.YAN UWA WANNAN SHI NE NOVEL NA FARKO DA ZAN RUBUTA, INA FATAN ZAKU BANI HADIN KAI TA HANYAR BANI ƘARFIN GUIWA, DA KUMA HAƘURI DA KURA KURAN DA ZAKU TARAR A CIKI. KAMAR DAI YADDA MASU IYA MAGANA KE CEWA "ZOMO BAYA KAMUWA DAGA ZAUNE".BELOVED HEARTS YOUNG WRITER Tafiya take sauri sauri saboda gabatowar magriba amma kallo ɗaya zaka mata kasan tana tare da nutsuwarta, sanye take da abaya baqa tayi rolling mayafin ga niqab daure a fuskarta, tana isowa kofar gidan da yake nasu ta tara da wasu samari biyu zaune suna hira, suna ganinta suka miqe suna fadin, "Ya maeesha sannu da dawowa".Yauwa barkan ku dai, Rahib ana zaune ana tattaunawar ne? ta fada tana knocking karamar kofar gate din gidan."Whl kuwa Ya maesha".Ɗayan ne yace to Rahib nifa zan shige sai kuma gobe idan ALLAH ya tashemu lpy." Ai kaji kai fa bansan meye matsalar Ka ba daga dan duhu ya fara sauka saika fara neman hanyar guduwa sai kace wata mace."To ai kai ka fini kama da matan saboda in ka fara mita kamar tsohuwar roba roba daga jiya nefa zuwa yau."Kai ne fa Ameer daga haka zaka miqe ai."Yanzu dai shikenan kayi min uzuri na shige sai gobe"."To ALLAH ya kai mu nima barin wuce". Daga haka sukayi sallama Ameer ya tura gate din gidan da maesha ta shiga ya shige. Salamu alaikum ta fada tana shiga cikin parlourn da bakowa, ɗakinta ta wuce ta ajje jakarta sannan ta rage kayan jikinta ta fice zuwa parlour, "ummu ummu ta shiga kwalawa mahaifiyar ta Kira.Sannu da zuwa harkin dawo kenan, ina toilet ina alwala naji sallamar ki ai, da yanzu nake cewa in na fito zan kiraki inji naga magriba tayi. "Ki bari kawai ummu yau na gaji ba karya yadda kika san zan sa ihu ga abun hawa in har shida tayi sai abinda ka gani kuma. Abbah bai dawo ba?"Bai dawoba inajin sai an idar da sallah dai."To barinje inyi sallah nima naji an fara Kira."Yakamata Kam. Komawa dakinta tayi ta shiga toilet ta ɗauro alwala ya fito ta shimfiɗa pray mat ta tayar da sallah magrib.Ameer kuwa yana shigowa ana Kiran sallah hakan yasa shi wucewa tap din dake compound din yayi alwala sannan yafita Inda mutane suke taruwa suyi sallah a can gaba da gidansu kadan.Sai da tayi sallar Isha ta tashi ta shiga wankan, bata wani dade ba ta fito ta shirya cikin simple doguwar riga Cotton ta fito, a nan parlour suka hadu da ummu ta dauko warmers guda biyu da sauri ta matsa ta karbi warmers din tana fadin ummu yanzu ina gidan shine baza ki kirani na tayaki ba."Gani nayi kina ta complaints kin gaji ne ai, yauwa maesha ni kuwa kinga ameer ne lokacin da kika dawo?"Eh Ummu awaje naganshi tare da rahib.salamu alaikum sallamar Ameer ta katse su. wa alaikum salam ameer ina kaje ne haka tun dazu nake nemanka?"La ban sani ba Ummu, ina tare da Rahib ai da ko a waya ne kin kira...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.