PAGE 10
by @swrites22
Hannayen sa ya zube a aljuhu ya fara tafiya ya tsinto Muryar dake dan rawa na faɗin, "Dan Allah ina zanbi in shiga ciki?
Tsaya wa yayi jim sai kuma ya juyo, "Wajen wa ma kikace kinzo ?
"kanbuuu" Ta fada a zuciyarta dan ya fara kular da ita, daga ganinsa dan rainin wayo ne. Kaman kuwa yasan mai take fada yace in kin gama zagin nawa sai kizo muje". Ya karasa yana cigaba da tafiya.
Innalillahi wai wanna mutumin aljanine ne? sai jinsa tayi yace mutum ne kamarki".
" Au ashe a fili nayi maganar ma". Ta faɗa tana daura hannu kan bakinta, silent smile ya saki ba tare da ya tsaya ba yana gaba tana bayansa, yarinta da wautarta kawai yake hangowa karara, wani murmushin yakarayi, ba wanda ya kara magana har suka shige ciki nan ma tafiya suka fara zuwa wani sashe dan gidan babba ne. "Wai ina zamuje ne ai ba nan naga sunyi ba. Maesha ta faɗa ganin tafiyar taqi ƙarewa.
"Sayar dake zanyi tunda ke kika kawo kanki. Dariya tayi wadda tasa ya tsaya ya juyo yana kallon ta, "Haba Malam ai kaina ƙaramine ba tsada zaiyi ba.
Shuru ya mata yana kare mata kallo da wani irin expression data rasa a wani ma'auni zata daura shi. "Ki bude kofar can ki shiga.
" Akan me zan shiga wurin da bansani ba.
"Kin fiya surutu. Ya fada yana juyawa zai bar wurin, da sauri tayi tsalle ta sha gabansa, tsura mata Ido yayi tsaf ya hango tsoron dake tattare da ita, wata dariya ce ta taho masa amma ya danne daidai lokacin Hameedah ta fito ganin yadda suke facing ɗin juna suna kallon cikin idanun juna saika zata masoya ne kuma zancan arziki suke, hakan ya harzuqa Hameedah ta juya zata koma dan dama Yayarta tasa ta biyo bayan Maesha. Muryar Maesha taji tace, "Dan Allah tsaya, ni baquwace kuma".
Katseta Hameedah tayi, a dakile tace kece bakuwar dake tare da kawar aunty safna ?
Da sauri ta amsa da, "Eh ni ce.
"Biyo ni". ta fada tana komawa ta inda ta biyo, da sauri Maesha tabi bayanta tana ɗan waiwayen Moha.
Wani ƙayataccen parlour suka shiga, idonta ya sauka kan wata Mata da baza a kirata yarinya ba kuma baza a sata a sahun dattijai can ba tana hakimce akan kujera one seater taji adon gwala gwalai sai walkiya take. Su ya zeena suna zaune a two seater dake opposite da ita sai nabila da yar safnan dake wasa a tsakiyar falon, Nabil kuma Yana zaune a kasa kusa da kafar mamansa.
ƙarasa wa sukayi da sallama Maesha ta durkusa har kasa ta gaida matar. Cikin fara a ta amsa Mata har tana karawa da tambayar ya karatu ?
"Alhamdulillah. Ta fada tana zama a kasa kusa da Nabil ko ba a fada ba tasan mahaifiyar wancan dan wulakancin ne saboda tsananin kamar da suke.
"Ya zaki zauna a ƙasa, tashi ki hau kujera kinji.
" Bakomai Mama nan ma yayi. Ta faɗa kanta a ƙasa.
"A'a ban yarda ba, tashi maza". Haɗa ido sukayi da ya Zeenah dole ta tashi har kujera kusa da hameedah.
" Tun dazu ke muke jira ai, naga kin dade nace to ko kinyi batan kai ne.
" Eh whl hanyar na rasa ina cikin nema sai gaa ".
"Hameedah ko? Ai ni nace tabi bayanki". Safna ta ƙarasa mata.
" To ai sai mu wuce ko tunda kin gaida momman.
"Da wurin Haka Zeenah. Momma ta faɗa idonta akan Maesha. Ya Zeenah ta ɗan yi murmushi ba tare data ce komai ba.
" To ku dan jirani ina zuwa. Momma ta fada tana tashi ta haura sama, su safna kuma suka cigaba da hira a tsakaninsu har Momma ta dawo riqe da wata madaidaiciyar kyakyawar shopping bag ta miqawa maesha, "Ga wanna daughter ba yawa.
A kunyace tace, "A'a momma Nagode whl.
"Kinci gidan ku, ni ba mamanki bace". Ta faɗa cikin sigar wasa, ya Zeenah tace, "Karbi mana".
Hannu biyu tasa takarba tace, "Nagode Allah ya saka da alheri Allah ya Kara girma.
"Bana son godia, dake dasu safna ai duk ɗaya ne, Hameedah ki karbi number ta mana Kwa dinga gaisawa.
Murmushin yaqe hameedah tayi domin tunda taga Maesha taji sam hankalinta bai kwanta da ita ba, haka kawai taji ta tsaneta, wayarta ta miqa mata a yatsine tace, "Sa number taki .
Murmushi Maesha tayi ta karba wayar ta sa number ta sannan tayi flashing dan itama taga number Hameedah ba dan komai ba sai dan karairaiyin da Maryam course mate dinsu ke musu akan Hameedar, tana masu proud da ita.
Safna ta fara tashi kafin su ya Zeenah, su kawa Momma sallama, ita dai hameedah kwanciyarta tayi cikin kujerar. Safna ce tace hameeda baza a rakani ba yau
"Whl a gajiye nake yau sis, ma yi waya kawai. Da haka suka fice Safna da Ya zeenah na gaba suna hira Maesha da yaran na biye dasu, yana zaune a Inda yake dazu amma ita bata gansa ba. Nabil ta bawa shopping bag ɗin suka shige da ita baya sañnan ita kuma ta bude driver side ta shiga, ya Zeenah ta buɗe passenger front seat ta shiga, safna kuma ta shiga motarta itama.
Motar Safna ce ta fara fita sannan Maesha ta danna reverse suka bi bayanta, zubawa hannunta ido yayi yadda take murza steering cike da nutsuwa da kuma sanyi har suka fice daga gidan aka rufe gate din sannan ya sauke ajiyar zuciya.