PAGE 16
by @swrites22
Zuwa safe fuskar Hameedah ta kumbura tayi suntum haka ma hannunta, tana fitowa suka hade da momma, a firgice tace, "Subahanallah Hameedah, hatsari kikayi ne? Yaushe kika shigo gidan? Me ya sameki haka?". Ta jero mata tambayoyin cikin tashin hankali, dan duk wanda ya kalli Hameedah sai ya firgita gabadaya kamanninta sun sauya.
" Bakomai momma". Ta fada tana wucewa dinning ɗin .
" Zo nan Hameedah". momma ta faɗa cikin seriousness .
Dawowa tayi wurinta ta zauna kusa da ita, "Me ya faru dake?". Fashewa tayi da kuka me haɗe da takaici kafin tace, "Momma ya Moha ya tsane ni baya so na, daga kawai na tare shi Ina bashi labarin shirye shiryen bikin da muke, wai na raina shi ya hau duka na da mari daƙyar Ya Faez ya kwace ni".
"Yi shurunki Hameedah zan dau mataki". Ta faɗa a hassale tana ɗaukan wayarta ta dannawa moha Kira amma wayar a kashe, Faez ta kira ring daya ya dauka Assalamu alaikum momma ina kwana?
" Lpy kalau faez Kana gida ne ko ka fita ?
"Ina gida momma ban kai ga fita ba dai
" Muhammad fa?". kallon moha yayi yana tsaye yana daura igiyar canvas ɗinsa, a darare yace yanzu dai yake shirin fita
" kuzo yanzu". Ta fada tana kashe wayar. Shuru Faez yayi kafin ya nufi moha yace, " An yanka fa ta tashi".
kallonsa yayi da neman Karin bayani dan shi ya ma manta da aika aikar da yayi jiya. "Ina jin fa Hameedah ta fadawa momma abinda kai mata jiya, dan tace muje tana neman mu". Qara gyara zaman rigarsa yayi haɗi da jan tsaki yayi gaba, bin sa a baya Faez yayi yana masa magana amma bai kulashi ba har suka shiga bangaren Momma, tana zaune Hameedah na kusa da ita da kumburarriyar fuskarta, rigar bacci ce a jikinta da tsayin ta bai wuce guiwarta ba, gaban rigar duk a bude, tunda suka shigo idonta na kansa har suka karaso.
Durƙusawa sukayi suka gaida momma dan dukda rainon Europe ne amma hakan bai taba tarbiyyarsu ba dan ko suna koyi da abu mai kyau a junansu indai moha yayi wani abu mai kyau to su ma zasu kwaikwaya haka su ma idan sukayi shi ma zai kwaikwaya.
Bata amsa gaisuwar ba ta jeho musu da tambayar, "Me Hameedah ta ma ka mata irin wannan dukan mutuwar?"
Shuru sukayi kansu a kasa, nan ta fara faɗa ta Inda take shiga bata nan take fita ba harda Faez saida ya samu rabon sa, sosai ta wanke su tas soso da sabulu, Hameedah kuwa sai murna take dan tasan tunda har an masa fada dole zai sauko ya bata haƙuri.
Shi kuwa gogan ransa ne ya qara baci ganin yadda Momma take fada duk a sanadiyyarta, kuma aka hada harda Faez da shi ma yake bashi haƙuri ya kyaleta, qala ba wanda yace har momma ta gama fadanta sannan faez ya shiga bata haƙuri, shi dai Moha Miqewa kawai yayi hadi da watsawa hameedan wani kallo yayi waje.
Ganin a yadda ya fita yasa sauri sauri Faez ya karasa bawa momma hakuri ya tashi zaiyi waje, tace "Kunyi break ne ?
" A a momma
" To Kai kaje ka yi mana tunda shi wancan dan zafin ran yayi zuciya saboda an masa fada?
" Zamuyi a office Momma, mun gode
"To shikenan adawo lpy". Da haka ya sa kai ya fice saidai ba moha ba motarsa, number sa ya fara nema amma a kashe, sai kawai ya koma ya ɗauki key motarsa ya fice shi ma.
3 DAYS LATER
Maesha ta shiga wani hali dan gabadaya ta daina samunsa a waya, ko text ta tura ba reply, duk ta ɗauki damuwa ta sawa kanta har wata yar rama tayi.
Daki ta shigo ta zauna bakin gadon tana me kallon agogon ɗakin 12:30pm gidan nasu yayi shuru don Ameer ma yana makaranta Ummu kuma ta koma baccin rana, duk ta rasa abinda yake mata daɗi wayarta ta dauko ta sake gwada Kiran sa dan wanna shine Karo na ba adadi data ke Kiran moha bata samu, luckily yau wayar ta shiga saidai har tayi ringing ta kare ba ai picking ba, tana ƙoƙarin sake kira sai ga Kiran sa na shigowa, hannunta har rawa yake wurin amsawa.
Kukan shagwaɓa ta sakar masa wanda ya sashi dafe goshinsa da hannu ɗaya yana juyi a kujerar tasa. Shi kansa yasan yayi missing dinta kawai dauriya ce yake yi, to me sa take kuka itama tayi missing din nawa Kenan? wata zuciyar tace masa no ba wani missing dinka da tayi, yarinyar da bata daukeka da wani mahimmanci ba ita ce har zatayi kewarka.
Ajiyar zuciya ya sauke saboda yadda yakejin kukan har cikin ransa, a sanyaye yace, "Mamieeee stop it please, bana son kukan nan".
Cikin shesheqa tace, "Meysa to zakayi punishing di na ta wannan hanyar, Kai ba'a ma mistake ne ko kuma kasan reason di na na yin hakan, whyyy?". ta ƙarashe tana cigaba da kukanta.
"To naji nayi laifi amma dan allah ki daina zubarmin da hawayen nan plz, kinji ". Shuru tayi tana ajiyar zuciya hadi da turo baki kamar yana gabanta.
"Mamynahhh". Ya kira sunan dawata irin murya data goge duk wani laifin sa a zuciyarta.
Kasa amsawa tayi sai lumshe Ido da tayi. " Me ya saki kuka?". Ya sake tambaya dan tabbatar da zargin sa.
"Umm ummm bakai bane Ka.. Ka rufe wayanka, ina ma text ma baka reply".
Ajiyar zuciya ya sauke muryarta kadai da yaji sai da yaji kaman yayi shekara baiji ta ba kaman ya janyota gabansa yai ta kallon ta haka yakeji, murmushi yayi kafin yace kinyi missing dina ne?
Shuru tayi ya sake cewa uhmmm?
"Kai ma ai bakayi missing dina ba
"Waya fada maki mamynah, nayi missing dinki over fiye da yadda kikai missing di na ma.
" To mesa ka rufe wayanka, ka daina kirana ka daina text.
"Kawai dai banji dadin abinda kika min bane shi yasa.
" To Kayi hakuri
" Shikenan it's ohk, tashi kisha ruwa
"Umm umm ni bana jin qishi
" To ni inaji ki dauko ki bani
" Ta ina zan baka ?
"Dauko ruwan sai na fada maki
" Wai da gaske kake ?
"Dagaske mana mamy amma karki kashe wayar
"To ". Ta faɗa tana tashi har taje kitchen ta bude fridge ta dauko ruwa tana yi tana kallan wayar kamar shine zai fito.
"Na dauko". Ta fada
"To koma daki". Ya bukata, wucewa tayi ta zauna bakin gado. " Na shigo". Dan jimmm yayi kafin yace sha ruwan.
"Eh?".
"Eh sha kuma ban da musu just do as I said". Saida ta harari wayar kafin ta kai robar baki ta sha kaɗan sannan ta ajje ta dauki wayar ta maida kunne, a tare suka sauke ajiyar zuciya yace, "To kinga yanzu ni na sha ruwan
"Ka sha ko dai na sha
" Ai in kin sha kaman na sha ne". sun dade suna waya har saida ta ware suna tsokanarta juna basu san lokaci yaja ba saida sukaji kiran sallar azahar sannan Moha ya kalli agogon office din, yana dubawa yaga sun kwashe kusan Hour suna wayar. Sallama ya mata da cewa zai kirata da daddare in ya koma gida kafin ya sauke wayar.