PAGE 22
by @swrites22
WASHE GARI
Maesha da ciwon Kai mai tsanani ta tashi har batasan bude idonta ko da ummu taga shuru har 11am bata fito ba sai ta leqa dakin, shigowar Ummu yasa Maesha bude idonta daya dan tashi saboda kuka.
"Maesha lpy kike har 11am yau baki fito ba?". lumshe idonta tayi, a sanyaye tace, "ummu kaina ke ciwo sosai.
"Subahanallah gashi nan ai idanunki ma sunyi ja, kinsha magani?
"A a ". Ta faɗa a hankali.
"To daure ki tashi ki dan watsa ruwa kici wani abun sai in ɗauko miki magani ki sha".
"To". Kawai tace amma bata motsa ba.
Ummu ta sake cewa, "Sai fa kin daure in ba haka ba sai ya kwantar dake, kinsan yadda kike yin ciwo".
"To". Ta faɗa tana Yunqurawa dakyar ta tashi ta wuce bathroom ɗin.
Ta dade a ciki kafin ta fito tana dafe bango ta shirya cikin palazzo da vest ta koma ta kwanta, ummu ce ta sake shigowa dauke da tea da biscuits tace, "Tashi maza ki sha sai kisha magani".
Tashi tayi ta karbi tea din kawai ta kurba. "Biscuits dinfa?".
"Tea ma ya isa ummu". Ya fada ba tare data kalli ummun ba.
Cikin damuwa Ummu tace, "To Maesha ko dai ba ciwon kan kadai bane ke damunki".
"Ciwon kan ne kawai whl".
"Ohk to shanye shayin barin dauko maki maganin". ta fada tana tashi ta fice.
Ajje shayin tayi ta jingina da bango gadon, wayarta ce ta fara tsuwar neman agaji janyowa tayi sai taga sunan moha na yawo, silencing wayar tayi ta turata kasan pillow ta lumshe idanunta har ummu ta kawo mata maganin ta sha ta koma ta kwanta, ganin kamar bacci zata koma yasa Ummu lullubeta ta fice.
MOHA
Tun dare yake neman number Maesha bata shiga sai zuwa safe ya fara samun number Amma kuma bata picking, shuru yayi yana tunani wata zuciyar tace yaje gidan, noo zuwana a yanzu zai iya zama matsala, to amma mai zanyi? meelah wata zuciyar ta ayyana, da sauri ya shiga lalubo number Meelan Allah yasa yanada ita saboda irin haka.
Sai da ta kusan katsewa ta daga cike da tsiwar nan Tata tace, "Hello da wa nake magana?".
Saida yaja wasu seconds kafin yace, "Kina magana da Muhammad sameer Adam jikamshi, abokin doctor Faez ".
Shuru ta danyi kafin tace wanda muka hadu jiya a fabs? ".
"Yap!".
"Okay, ina kwana?".
" lpy". Kawai yace sai kuma yayi shuru ya shiga tunanin mai zai ce mata kuma, can dai ya nisa yace, "Maesha fa?".
"Tana gidansu ko baka san ba gidanmu daya ba".
Shuru yayi ita kuwa ta shiga ƙoƙarin ajje wayar taji yace, "kunyi waya da safe ne?".
"Nop amma zan shiga gidan zuwa anjima.
"Noo kije yanzu please-e". Ya karashe please din kamar bayason fada shuru tayi kafin tace ohk.
"And yauwa kice ta dau waya zan fada mata wani abu dan Allah, Nasan Inda matsalar take zanmata bayanin komai.
"Ohk". tace ta ajje wayar, tashi tayi ta dauki mayafinta ta fita, umma ta faɗawa zata shiga gidansu maesha ta mata adawo lpy sannan ta fita.
A falo ta samu ummu suka gaisa tace, "Tana ciki batajin dadi ciwon Kai, yau ko leqowa parlour ma batayi ba".
" Subahanallah, barin karasa ciki Ummu".
"To shikenan afito lpy". Cikin ta shiga ta zauna bakin gadon, maesha ta share hawayenta sannan ta tashi zaune tana faɗin, "Meelah yanzu kike tafe?".
"Fisabilillahi kukan da nace karkiyi shi kika cigaba dayi, haba maesha maisa zaki wahalar da kanki akan abinda bakida tabbaci".
"Meel.....".
" Kinga ina wayarki?". Meela ta katseta. Nuna Mata kasan pillow tayi ta janyota ta duba missed calls ɗin Moha ne rututu, kafin tace wani abu sai ga wani Kiran ya sake shigowa, dagawa Meelah tayi sannan ta mika Mata.
" Waye?". Ta tambaya da sanyin murya.
"Sa a kunne sai kiji ko ma waye.
" Ni bazan iya magana da kowa ba Meelah let me be". ta fada tana rufe idanunta, yanajin duk abinda sukeyi hakan ya sake jefa shi a damuwa.
"Maeshaaaa". meelah ta sake kiranta a kausashe. Buɗe idanun tayi tana kallonta.
"Karbi wayar nan ko na tashi na tafiya ta". Ba dan taso ba takarba ta manna a kunne ba tare data kalli sunan waye ba tayi shiru, "Mamyyyy, me sa kika kasa min uzuri ne, mesa baki tsaya kinji abinda zan fada maki ba kika bari kishi ya rufe maki Ido? Nasan ba lalle ki yarda danu a yanzu ba amma maybe idan kikaji yadda abun yake zaki yarda ........"
Daga haka ya kwashe komai tun dagakan danbarwar da suke sha da Hameedah na son sa da take zuwa kan karyar da take wa kawayenta na shi ne wanda zata aura. Ajiyar zuciya ta sauke tana janyo pillow ta kankame dan har wani sanyi sanyi tafara ji.
"Kiyarda dani mamy". Ya sake faɗa da sigar tausayi kamar wani maraya, bawan Allah duk ya susuce daga jiya zuwa yau.
"I trust you". ta fada da sanyin murya.
"Kin azabtar dani jiyan nan, wani azababben ciwon kai da ya rufe ni sallar asuba ma sai da safe nayi ta".
"Ni ma bani da lpyr ai".
"Me ya sameki?".
"Ciiwon Kai whl sai yanzu ma na sha magani".
"Yanzu jiya zuwa kikayi kina kuka ko mamy?".
"A'a ba kuka nayi ba, kawai dai ciwon kan ne".
"To in ba kuka kikayi ba barin kira FaceTime".
"A'a dan Allah". Ta faɗa da sauri dan tasan in dai ya ga idanunta sai ya fahimta.
Ajiyar zuciya ya sauke yace, "take care of yourself for me Mamy, and plz ki samu kije kiyi break na san bakici komai ba.
"Naci".
"Bakici ba".
"How sure are you banci ba?".
"Saboda nima banci ba kuma zuciyata ta bani ke din ma bakici ba, dan haka kije ki samu wani abun ki taba".
Dan yamutsa fuska tayi kamar Yana gabanta. "Please mamy do it for me".
"Naji to".
"That's my mamy, to bawa kawartaki wayar". Kallan meela ta samu Itama ita din take kallo, mika Mata wayar tayi, "Gashi yana nemanki".
karɓa tayi tace, "Hello ".
"Please make sure taci wani abu ohk and.... Sai kuma yayi shuru kamar baya san abinda zai fada ɗin yace, "Thank youuuu".
"Don't mention, sai anjima". ta fada tana hanging call din ta dubi Maesha tace, "To ai saiki tashi kije kici abinci tunda doctorn naki yayi magana".
"Hmmm wai meela ashe hameedah..... Nan tazayyane mata duk abinda Moha ya fada mata, Meela ta riqe baki tace, "Haba no wonder taje ta tare masu a gida, to wallahi sai kinyi da gaske Maesha tunda kinga ita yar uwarsace komai ba iya faruwa dole sai kin iya takunki".
"Hmmmm". Kawai ta sake faɗa sannan ta miqe tace, "Muje parlour kawai Meelah".
HAMEEDAH
Tana tashi ta hau kiran Maryam ko tsayawa su gaisa batayi ba tace, "Ke Ashe wanna kawar taki Munafukace".
" Wace kawar tawa kike magana akai?".
"Yar makarantar ku Maesha makira nake nufi".
"Ikonnn Allah, toh fa me ya hadaku kuma.
" Ai ki bari kawai, whl tunda ta shiga gonata sai na Koya Mata hankali nafi karfin inyi kishi da ita, haaa". Ta faɗa tana jijjiga
" Ni kam mai yake faruwa ne ki min bayani .
"Wai Ya moha ta biyo har gida tai masa barbadai barbadai ta asirce shi, kuma ashe jiya maganar da kikai a gabanta jiya tana riqe da ita taje ta faɗa masa, ashe ma soyayya suke".
"Kanbuuuu". Maryam ta narka wata ashariya kafin tace, "To ai baki sani ba wanna in dai kinibibi da makirci baki ga komai ba munafuka ce ta bugawa a jarida ni kai na ina cike da ita, ashe kema ta tabo ki heee .
"Ta tabo karshenta kuwa ni zanyi maganinta saina Koya Mata hankali ".
Ta fada tana datse Kiran ta koma kiran Maesha saidai harta tsinke baa daga ba saida tayi Kira uku a na hudun ta daga, a fusace tace, "Ke Munafuka whl kifita a harkar mijina ke kinyi kadan ki so abinda zanso kinje kinyi tsafen tsafenki kun shigowa mutane gida kun barbada, to whl moha yafi karfinki nesa ba kusa ba.
Maesha da bayan sunyi breakfast suka dawo parlour suka zauna suna lbrn school da zaai resuming in the next two weeks wayarta tayi Ƙara ganin Hameeda yasa ta share saida meela taga baza a dai na kiran ba dai tace, "Dan Allah ki daga muji da wadda tazo".
Ɗagawa tayi tasa a handsfree saida takai aya sannan maesha tace, "To duk naji korafin ki amma da kikace na fita a harkar moha ai tun farko bani na shiga harkar sa ba shi ya shiga tawa kinsan mu bama chusa Kai a Inda baa yin mu, kuma mu bin mu ake bamu muke Kai kanmu ba, ko da yake ai mace mai mutunci ai ita akeso har abi, sannan kince nayi kadan naso abinda zakizo ai ke san maso wani kike yar wahala nikuwa kinga inaso ana so na ya kamata ki gane difference ɗin. Kince nayi tsaface tsaface to ki sani ni kwakwalwata ba tayi irin wanna toshewar ba, ba boka ba Malam mu da mai duka muka dogara kuma ki fita a harkata ni da Moha in ba haka ba ciwon zuciya ne zai kasheki, wawiya kawai wadda bata san mutuncin kanta ba". Maesha ta faɗa tana datse wayar rai ɓace dan whl yanzu itama wani irin haushin Hameedar takeji.
Meela ta saka sowa tace whl Maesha baki taba birgeni irin na yau ba, kin min daidai ko ba komai ana tauna aya dan tsakuwa taji tsoro. Ummm yau Maesha ce tayi baki haka lalle soyayya yaqin mata.
Dariya kawai Maeshan tayi tace, "In kikaji ana qi gudu to sa gudun ne bai zo ba, tunda yanzu nasan matsayin ta ai ba zan tsaya sanya ba.
"Sai dake ta Muhammad sameer bada kanki asare".
"Ke shiiii". Ta faɗa tana nuna mata hanyar dakin Ummu, tayi dariya tana faɗin, "Munafuka". Suka tafa.