PAGE 32
by @swrites22
Ummu bata fito ba saida taji tafiyar Daddyn su Jamila, tana fita Abbah ya ce, "Zo muyi magana Raheela".
Da to Ummu ta amsa sannan ta karaso ta zauna kusa dashi, nan ya kwashe duk shawarar da suka yanke da daddyn Meelah ya sanar mata, Ummu tayi Murmushin jin daɗi tace, "A gsky muma mun so tafka namu kuskuren, kuma sai muka nemi mu gyara kuskure da kuskure...." Nan ta kwashe yadda sukayi da Maesha ta faɗa masa, shuru yayi yana tunani can kuma ya dauko wayarsa ya dannawa Moha kira.
Suna shirin tashi daga aiki yaga kiran Abbah saida gabansa ya fadi amma ya ɗaure ya amsa da sallama suka gaisa Abbah yace, "Dama na kira in sanar ma ne tunda abu ya gabato ka fara zuwa ku fahimci juna da ita ko".
"To Abbah in sha Allah zanzo, Nagode sosai Allah ya kara girma". Haka sukayi sallama ya kashe Moha dadi ya isheshi dan haka bai saurari kowa Bama ya barwa Nashed sauran aiki ya wuce gida don yaje ya shirya.
Shi kuwa Abbah yana kashewa yace, "Ki ɗauki wayarta a daki na ki bata sannan ki sanar mata gobe idan Allah ya kaimu zata koma makaranta, ni zan ɗan fita". Ya Ƙarashe yana Miqewa, Ummu ma ta tashi cikin farin ciki ta rakashi tana masa addu'ar a dawo lpy.
Yana tafiya ta koma ɗakin Maesha ta sanar da ita abinda Abbah yace, taji dadi ta wani ɓangaren amma ta wani gefen kuwa sai yake tsarguwa da kanta, a haka dai suka kammala abincin dare ita da Ummu suka shirya shi sannan Ummu ta bata wayar ta.
MOHA
A bangaren Moha kuwa yana komawa gida ya hau shiri sai ga Faez da Nashed sun iso a tare, Faez ya kalle shi yace, "Wannan shirin fa?".
"Zance zan tafi mana".
"Ina kenan?". Faez ya sake tambaya.
"Gidan su Mamy ".
Faez yayi sororo sai kuma yace, "Zuwan da zakayi a takatsantsan shi ne kakewa wannan shirin?".
"Inji wa?". Nan ya kwashe yadda sukayi da Abbah ya sanar masa.
"To Alhamdulillah, nima jirani bari na shirya muje gaba-daya".
Nashed yace, "Nima kwa rakani muje inga Rashida mu gaisa ko".
Faez yace, "Ya kamata kuwa".
"To kar dai ku daɗe". Moha ya faɗa.
"Sabon shiga kenan". Faez ya fara yana dariya, Moha ya harare shi.
Saida sukayi sallar magriba sannan suka hau shiri Moha ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda Royal blue dinkin fitted da yayi matuqar yi masa kyau, ya daura agogon rolex silver colour ya kawo zanna bukar ya daura ya feshe jikinsa da turaruka masu sanyin kamshi.
Nashed na zaune bakin gado yana sanya socks shi ma yayi kyau cikin wani black lush yard da ya matuwar haska farar fatarsa shi ma ya sa zanna bukar data dace da kayan.
Can na hango oga Faez sanye da irin yard din Nashed saidai shi nasa caramel colour ne ya kawo dara ya daura sai wani gyara mata zama ake. Gabaɗaya ɗakin ya ɗauki kamshin turarukan da sukayi amfani dasu dan in kana daga ƙofar part ɗin sai kaji kamshi. Dakyar su Faez suka fito da Moha dan daga ya gama wannan sai ya tsiro da wannan, sai qalqale qalqale ake.
Fitowa sukayi suka nufi part din momma, Papi kawai suka tarar a parlourn da alama shima fitowarshi Kenan barka da hutawa suka masa ya dago yana kallonsu yace, "Aa yan samari za a fita ne?".
Faez ya ɗan sosa Kai yace, "Eh papi dama zamu raka Moha zance ne".
"Karya yake Papi shi da Nashed ne zasuje, ni ban dani".
Dariya Papi yayi yace, "To miye abun musun kuma, ku tashi kuje Allah yayi muku Albarka a gaishemin da surukan nawa". Cikin kunya suka amsa da zasuji sannan suka fito.
A jikin mota suka tsaya Faez yace, "Ni za'a fara rakawa ko?". Yayi maganar cike da tsokana.
Ai kuwa Moha ya watsa masa wata harara yace, "Kai da kullum kake zuwa tsabar san kai kace wani kai za'a fara rakawa".
Haka suka hau kace nace shi da Faez karshe dai Moha ya haƙura kan su fara raka Nashed tunda su wuri ɗaya zasu, da wannan suka shiga mota ɗaya suka nufi gidan su Rashida.
Suna zuwa aka Sauke su a parlourn baki kasancewar Nash ya sanarwa da Rashida batun zuwan nasu aka kai musu refreshment.
Babban yayansu Rashida ne yayi sallama ya shiga falon suka gaisa dasu moha cikin fara'a ya gabatar musu da kansa sannan yace, "To waye namun a ciki?". Yayi tambayar cikin barkwanci.
Faez ne yace, "Dukkan mu naku ne ai".
"Haka ne kam, ai duk an zama ɗaya, amma ango nake tambaya".
Faez ya sake cewa, "Dukkan mu angwaye ne ai". Yaya Nasir yayi dariya yace, "Abokina haka zamuyi dakai".
Moha yayi gyaran murya ya nuna Nashed yace, "Gashi nan zaune".
"Kaga aikin manya ko". Yaya Nasir ya faɗa da sigar wasa yana nuna Moha.
Faez yace, "Dama shi ne babba ai". Nan suka sake ballewa dake shi ma irinsa ne, Rashida ce tayi sallama ta shigo kanta a kasa ganin yaya Nasir yasa ta kasa ƙarasowa. "Shigo mana kikayi tsaye anan".
Karasowa tayi ta zauna can gefe, yaya Nasir ya dan ci serious yace, "To Malam Nashed ga Rashida Ni dai tun yanzu zan fara jaddada amanar nan, a kula mana da ita, ita kadai ce mace a cikin mu dukda nasan sai kayi hakuri dan kanta cike yake da yarinta fal, dan haka sai ana kai zuciya nesa, Allah kuma ya tabbatar mana da alheri".
Suka amsa da Ameen Faez yace, "Babu komai whl, kuma mun karbi amana in mukaga zaiyi na daidai bama zamu bashi punishment a madadinka". Sukayi dariya sannan ya miqe sukayi exchanging numbers ya fita yana yiwa Rashida gargadin Banda shirme.
Dan shuru falon ya dauka na wani lokaci kafin Rashida ta gaishesu kanta a kasa tana wasa da bakin gyalenta.
Suka amsa Faez ya dinga dago Nashed dan ya dora shi a hanya saidai itama Rashida ta kasa sakewa, Moha yace Faez ya tashi su tafi mota su jirashi amma sai ya hanasu, shi dai Moha ficewarsa yayi ya barsu tare da Faez da ya gyara zama ya fara tsare su su dukan, sun yi kusan 30 minutes a ciki kafin su tashi tafiya Nashed ya ajje mata kudi a gefen kujera da take zaune ya mata sallama suka fito.
Direct gidan su Maesha suka nufa, suna isa suka samu Ameer a waje bayan ya ƙarasa sun gaisa ya musu iso zuwa ciki, suna kawo kai Maesha na fitowa daga kitchen kamar an korota, sai kuwa sukayi ido huɗu da Moha ai bata san lokacin data faɗa daki ba kamar an hankaɗata, su Faez dai basu ganta ba amma Ameer da Moha sun ganta, suka ƙarasa cikin falon suka zauna Ameer yace dasu bari ya sanarwa ummu.