06
by @oumfatima33
*MEERAH*
*OUM FATIMA*
*06*
Kai tsaye wurin da muka shirya partyn muka nufa, muna zuwa ihu da tafi ya kaure wurin ana kiran Queen Meerah kasancewar sunan da mate ɗinmu ke faɗa min. Ita kuma Zeezee Princess Zeezee.
Hannu muka riƙa basu muna gaisawa kafin muka fara abinda ya tara mu, cikin natsuwa da wayewa muka gudanar da partyn namu. Don bamu da wani yawa, kasancewar private school ce ta yaran manya.
Gaba ɗaya sate ɗinmu bamu fi mu ashirin ba duka Mata da Mazan, don haka gaba ɗayanmu ne sai ɗai-ɗaiku da basu samu damar zuwa ba. Kiɗa muka ware muka sha rawa abin mu, ana ta ɗaukar video da hotuna. Anci ansha an gir-gije yanda ya kamata.
Ƙarfe 6 na yanma muka tashi saboda magrib da ta gabato, waɗan da ba a unguwar suke ba su suka fara tafiya. Da yake driver's ɗin su duk suna jiran su, wasu kuma dawo wa aka yi ɗaukar su.
Ƙarfe 6 Ya Aryan yace zai zo ya ɗauke ni, amma shiru har shida da arba'in, lokacin kuma aka fara kiran sallar magrib. Duk inda nake idan magrib tayi hankalina gida yake komawa, don haka yanzu ma nayi ta duba agogo ina jira amma shiru.
Haneef Class mate ɗinmu wanda ƴan Class ɗinmu ke cewa sona yake, saboda yanda yake shish-shige min da son in kula shi ako da yaushe. Don kullum in zai je School sai ya kai mana chocolate da biscuits masu tsada. Nice ma bana sake masa fuska kuma ko ya kai bana ci, sai dai Su Zeezee ke karɓa.
Yau ma ƙin tafiya yayi ya zauna yana min hira, da nuna min hotuna da videos ɗin daya mana a wayarsa. Wannan ne dalilin da ya saka na ɗan sake masa, don har bashi wayar Ya Aryan nayi ya tura min su.
Ganin yau na sake dashi yasa daɗi ya kama shi sosai, don haka bayan ya gama tura min yace.
"Queen a ɗan bani Contact mu ɗan riƙa gaisawa Please?." Ya ƙare da sigar roƙo. Harararsa nayi ina karɓe wayar nace masa.
"Waya faɗa maka wayata ce, ta Ya Aryan ce don ni bana da waya sai na kammala secondary school inji Ya Ajmal!." Na ƙare maganar ina ɓata rai. Don Dady yace zai saya min idan muka yi JSSCE, amma yayi maza yace ban isa ba tukuna, sai na kammala secondary.
"To ki bani ta Ya Aryan ɗin mana, ko kuma ta Mom ɗinki?." Ya ƙara tambaya ta.
"Amma baka da hankali Haneef, kawai sai na ɗauki Contact ɗin Ya Aryan ko ta Momy in baka? To ka kira ni a matsayin wa?." Na masa tambayar ina tsare sa da ido.
Sosa ƙeya yayi ya saci kallona, sai kuma yace.
"Friend ɗinki mana." Kallon baka da man kai nayi masa, daboda tuna wa da irin gargaɗin da Ya Ajmal yayi min a kan yin abota da Maza, tun ranar da ya watsa min partyna.
Ganin shiru Ya Aryan bai zo ba yasa na miƙe nayi Wa Zeezee sallama nace bari na tafi kawai, tunda babu nisa. Cewa tayi zata saka driver ya kai ni nace ta barshi kawai.
Laidar data haɗa min kayan partyn nawa ta ɗauko ta rako ni bakin gate, Haneef daya biyo bayanmu yace.
"Muje mu sauke ki mana."
"No thanks." Na faɗa ina yin gaba. Bina yaci gaba da yi yana roƙona, dakatawa nayi na juyo ina kallonsa. Haɗe hannayensa yayi wuri ɗaya yace.
"Please Queen?." Kafin nayi magana Zeezee ta riga ni da cewa.
"Please Bestie kije kawai ya sauke ki, kinga magrib tayi kuma Ya Aryan ɗin bai zo ba. Bani da zaɓi dole na amince, ai kuwa cike da murna Haneef ya buɗe min baya na shiga. Shiga yayi shima muka wuce Zeezee na ɗaga mana hannu.
A bakin gate nace a sauke ni, don haka driver yayi parking. Cikin sauri Haneef ya fita ya buɗe min ƙofar da nake ƙoƙarin buɗe wa da kai na.
"Thanks." Na faɗa masa lokacin daya miƙo min laidar kayayyakina. Murmushi ya sakar min sannan ya juya ya buɗe motar ya shiga.
Juyawa nayi da niyar shiga gida idanuna suka sauka cikin na Ya Ajmal dake tsaye jikin Motarsa, ya zuba min ido yana bina da mumman kallon dana fi tsana daga gare sa.
Ɓata rai nayi nima na haɗe fuska sosai, sai dai a baɗini a matuƙar tsorace nake don wani irin bugu ƙirjina ke yi. Na tsani abinda zai haɗa ni dashi ya saka ni gaba da waɗan nan idanun nasa.
Bai taɓa duka na ba duk abinda nake yi sai da ya tsare ni da waɗan nan kaifafan idanun nasa, waɗan da nake matuƙar jin yanda suke ratsa min gaɓɓan jiki na, suna raunata duk wani ƙwarin gwuiwar da nake jin ina dashi.
Idan ya tashi hukunta ni a kan wani laifin dana aikata, sai dai ya saka ni wani aikin da ya san zan sha wahala sosai. Kuma babu mai ƙwata ta, koda kuwa Ya Sultan ne, sai dai bayan nan ya bini da rarrashi. Hakan kuwa babƙaramin ɓata min rai take yi ba.
Nifa gani nake yi kamar duk gidan tsoronsa suke ji, don babu mai masa magana a kan duk abinda ya saka ni. Kaf gidanmu shi kaɗai ya isa ya ɓata min rai a zauna lafiya, shi yasa nayi matuƙar tsanarsa.
Ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauke na fara takawa ba tare dana kalli inda yake ba, ina gab da shigewa ciki naji saukar muryarsa da babu wasa ko kaɗan yana cewa.
"Zo nan!." Babu wasa ko kaɗan a muryar tasa, bare kuma kyakykyawar fuskarsa dake a matuƙar haɗe, wacce duk yanda na tsane sa na kasa ƙaryata baiwar kyawun da Allah ya masa.
Takawa na shiga yi a hankali zuwa inda yake ina ƙara ɓata rai wai ko zai ƙyake ni in tafi. Lokacin dana ƙarasa inda yake tsayuwa kawai nayi na duƙar da kaina ƙasa ba tare dana kalle sa ba.
Shima bai yi maganar ba sai idanun daya zuba min waɗan da nake jinsu ko ina a jikina, nafi minti biyar a tsaye har na fara gajiya amma bai tanka min ba. Ɗagowa nayi na saci kallonsa kaɗan na duƙar da kai ina tura baki ƙun-ƙuni fal raina, sai dai babu damar amayar wa a gabansa .
"Daga ina kike? Waye kuma ya sauke ki a mota?." Tambayoyinsa suka shiga cikin kunne na a ba zata.......
Ayi haƙuri da wannan Please.
Barkanmu da dare.