Chapter 8
*RIKICIN DUNIYA...*
©️ Meenat A. 'Yandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
CHAPTER 08
..."Yarinya kin kawo abu mafi tsada, don haka dole aiki ya tafi a yadda kike so"
Malam Bawa ya karasa maganar cikin murya irin ta tsofaffi.
"Malam kana nufin shi kenan aiki ya ci?"
Umma ta fada.
"Tukunna dai. Da farko zata fara mantawa da wanene Kasim, daga nan kuma sai dayar muguntar da kuka shirya zata afka ciki"
Murmushin mugunta Wasila ta yi.
"Na fahimta! Amma ya labarin idan tasan muna tare da Kasim?"
Shuru Malam Bawa ya yi, tare da dogon nazari.
"Karki bari ta sani a yanzu, domin muddun ta sani zata iya rikicewar. Rikicewarta kuma daidai take da dawowar abin da muke kokarin boyewa. Ko zata sani ki bari ta ji a can wajen wasu ba a wurinki ba"
"To Malam mun gode amma turaren da ka haɗa, ta yaya zamu yi mu kaiwa Nadiya shi ba tare da ta gane muna kokarin cutar da ita ba?"
Cewar Umma
“Ku bar turaren a hannuna. Jikina na bani zasu zo, tabbas ma zasu zo”
“To shi kenan malam mun gode”
Wasila ta karasa maganar tana ajiye masa kudin aiki.
Gida suka dawo zuciyoyinsu makil da farin ciki.
“Umma!”
“Naam Wasila”
“Kasim ya ce mini yana kofar gida in fito yanzu”
Zaro ido Umma tayi cikin firgici
“Ki rufa mana asiri a unguwa irin ta talakawa, a ga Kasim na zuwa wurinki bayan ansan saurayin aminiyarki ne”
“Umma har don wannan abin shi ne har zaki tayar da hankalinki. Su ma munafukan ai zasu yi tunanin yazo wajena amsar ma Nadiya sako ne ko kuma wani abin. Ni dai na fita kada ki rikeni nan har ya gaji da tsayuwa ya tafi, kinsan yanzu muke gina soyayyar ba wani kwarin kirki tayi ba”
Tana kaiwa nan ta zaro gyale ta fice.
Tun daga cikin zauren suke aikawa juna murmushi.
"Barka da zuwa Kasim"
"Barkanmu dai Baby! Kin ji ni shuru ko?"
"Hmm! Ai na zata ka tafi ne shi ya sa na ce bari idan dare yayi in kira ka"
"haba wane in tafi ba tare da nazo na ga sarauniyata ba. Abin da ya saka banzo da wuri ba wannan sakon na saka daga Katsina aka kawo mini"
Ya na kaiwa nan ya zura hannunsa cikin mota tare da dauko wani kwali.
"Baby ga alkawarinki"
Ya karasa maganar yana mika mata dalleliyar waya.
"iPhone 12" ta Furta bakinta na kyarma.
"Ka...kasim yanzu wannan tawa ce?"
"Kwarai kuwa ko ta yi miki kadan ne in Karo miki wata irin ta"
Ya karasa maganar yana murmushi.
Kukan kissa Wasila ta fara yi.
"Na gode! Na gode! Ubangiji ya saka da alkhairi ya mallaka mana juna"
Rufe fuska tayi tana murmushi.
"Amin Baby! Ina so in wuce gida amma kafin nan mu je in gaisa da Mama"
A tare suka shiga gidan, Inna na zaune tana gyaran gero.
Bayan sun gaisa kudi ya ajiye mata suka fita tare da Wasila.
Wani kukan kissar da ya kara tafiya da imanin Kasim Wasila ta hau yi kada ya tafi ya barta.
Da kyar ya samu tayi shiru ya tayar da mota yayi gaba...
Gidansu Nadiya
Ganin yammaci yayi tare da Inna suƙa nufi Gidan Malam Bawa, suka bar Jamila a kofar gida tana soyar awara.
Murmushin mugunta ya saki bayan jin abinda ke tafe da su.
Turaren daya tanada kafin zuwan su ya ce kullum ta rika shafawa sau biyu a rana.
Da farin cikinsu tun a hanya Nadiya ta hau murza turare. Sai dai isar kamshinsa cikin kwanyarta ji tayi tamkar ana yamutsa mata tunani, lokaci daya kanta yayi wani irin jim! Da kyar ta samu ta karasa gida ta zube ta hau baccin wahala.
Tun dawowarsu take bacci har garin Allah ya waye. Maganar magriba da isha'i babu ita.
Wanka ta yi kasancewar yau karfe bakwai suke da exam.
Sak irin wayarta ta gani a hannun Wasila. Dama tana da niyyar tambayarta.
"Wannan wayar fa? "
"Labarin da tsayi, ki bari idan muka gama exam zan labarta miki"
Ba ita ta samu sukuni ba sai da taga sun fito dakin jarabawar sun nufi gida.
"Kinga iPhone 12 ko?"
"Kwarai kuwa ta wace hanya tazo, domin na sani ko gidan da kuke ciki aka siyar ba zata siyu a wurinku ba"
Dariyar mugunta tayi Wasila
"Kin fadi gaskiya Nadiya. Sai dai kin manta da abu daya, shi ne dare ɗaya Allah kanyi Bature"
"Na amince mana saboda ban isa na ja da ikon Allah ba. Shi ya sa nake so inji ta yadda akayi wannan Bature"
"Kwanaki bana taba fada miki ba mun hadu da wani matashin mai kudi ta kafar facebook ba?"
"Eh kin fada mini kafin a sace wayar Umma kina facebook da wayarta. Lokacin har nake cewa kuyi hankali da samarin facebook makaryata ne mafi akasarinsu"
"Yawwa to dama kafin a sace wayar hatta location dina duk ya sani. Jina da yayi kwana biyu shuru shi ne jiya sai gashi ya zo har gidanmu"
A dan rikice Nadiya ta fiddo ido "gidanku kuma? To ya kuka ƙare, da gaske mai kudi ne?"
"Kwarai kuwa. Kudima kuwa abinda ke kudi, yanzu haka ya ce aurena zai yi nan da dan lokaci ƙanƙani. Shi ne ma ya kawo mini wannan wayar"
"Amma Wasila baki da kirki. Shi ne ko ki kirani mu gaisa"
"Hmm! Nadiya Kenan. Ce min yayi baya son kwashe-kwashe idan ya dawo ko kawata daya ce sai In bq Shi mu gaisa.
Har cikin zuciyar Nadiya bata ji dadin kalmar kwashe-kwashe da Wasila ta alakanta ta da ita ba. Sai dai tunawa da tayi da irin cin mutumcin da ta rika yi mata, sai taga ita ba komai Wasila ta fada mata ba.
Har suka karasa gida ba wanda ya ce da wani uffan.
Inna dake tsaye tana jiran dawowar Nadiya saboda ta ji shin Kasim din ya kira. Ganin shigowarta ya sakata yin kanta da sauri.
"Nadiya lafiya, ko Kasim ne ba lafiya? Duk na ganki wani iri"
Basarwa tayi.
"Inna ki fita batun wannan dan renin wayon, ni dai na yanke bazan sake kiransa ba muddun ba shi ya nemoni ba"
Ta karasa maganar cikin ko ina kula.
Tamkar rugugin saukar Aradu haka maganar tayi sukuwar sallah a cikin kwanyar Inna.
A rikice take kallon Nadiya da yanayin fuskarta ya fassara abin da ke cikin zuciyarta na ko in kula.
"Nadiya! Anya daga bakinki wannan maganar ke fitowa?"
Kallon mamaki Nadiyar ta yi wa Inna
"Na fadi wani abu wanda ba daidai bane?"
"Sosai ma. Cewa fa kika yi ba zaki sake kiran Kasim ba muddun ba shi ya nemeki ba. Ɗan renon wayo fa kika kira shi"
Ya Musa fuska ta sake yi a karo na ba adadi.
"Haka na fada Inna, saboda ji na nake saƙat kamar an rabani da ƙaya. Ai Kasim din ba shi daya bane sannan ba ɗan autan maza bane"
Karasa mutuwar tsaye Inna tayi tare da ɗora hannuwa a ka.
"Shi kenan! Mun shiga uku jama'a kodai an musanya mini Shaleleta ne?"
Gani tayi Inna na neman ɓata mata rai, don haka kai tsaye ɗaki ta nufa ta barta sake da baki.
Zaman yan bori tayi tana mai zabga uban tagumi.
"Yau ni na shiga uku! Me ke shirin faruwa dani. Anya yarinyar nan ba Wasila ke zugata ba, don ita bata da wani tsayayye. Ko dai zuciya tayi da Kasim ɗin? Kai aa bari In je In rutsata a dakin."
Tana kaiwa nan ta mike.
Zaune ta taddata tana kallo a cikin wayarta. A nan Inna ta sake tabbatarwa da kanta abinda Nadiya ta fada da gaske ne"
"Shalelena! Tashi muyi Magana kinji"
Ba don ta so ba haka ta miƙe.
"Haba shalele! Da hankalinki za ki bari kawa ta rika baki mugayen shawarwari a kan wanda kike so ki aura?"
"Inna nifa babu kawar dake bani shawara game da Kasim. Kawai na gaji da abin da yake mini shi ya sa"
"Gajiya kuma? Ina muka ga lokacin gajiya mu da muke nema. Nasan idan na sakaki abu kinayi, to don Allah kira Kasim yanzu da na fita"
Da to ta amsa badon ranta ya so ba. Ita kanta ta rasa me ya sa jiya zuwa yau ji take mugun haushi Kasim ke bata. Wayar ta dauka kai tsaye cikin contract nata ta shiga
"Bari ma ku gani, idan na shiga na goge kaf lambobinsa , sai inga mai sake takuramin a kan sai na kirasa"
Tana karasa maganar ta danna delete all...
Meenat A. 'Yandoma
***