IDO DA ƘASA

Chapter 1

by @ummunasmah

*IDO DA ƘASA*


________________________________
***

________________________________


 *RASHEEDAT USMAN.*
      (Ummu Nasmah)


Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) shugaban manzanni.

  Kamar yadda na ɗaura alƙalamina lafiya cikin aminci akan littafin nan ina roƙon Allah ya bani ikon gama shi cikin aminci da lafiya.

  Tsokaci.
     Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne banyi shi dan cin zarafi ga kowa ba, duk wanda ta ga ko ya ga yayi dai-dai da rayuwar shi ta zahiri yayi haƙuri arashi ne.

  Gargaɗi.
    Ban yadda a juya min labari ta ko wacce siga ba tare da izini na ba a kiyaye.


Shafi na. 1

Tsaye ta ke jikin window tayi shuru tana kallon Najnal da ke zaune tana wasa da ƴar tsanar ta a tsakiyar falon, idanunta ta runtse tana jin tausayin yarinyar na ratsata hannu tasa ta goge guntun hawayen da ya biyo idanunta tamkar garwashi haka take jin zuciyarta a hankali ta furta.
"Na lura da kyau sau da yawa abubuwan da muke so, mukafi kwallafa rai dasu sunfi wahalar damu a rayuwa, kuma sunfi mana wahalar samu, sunfi nisa damu a da ne ake cewa mutum duk abinda zaiyi kar ya gaji har sai ya kai gaci! A yanzu kuwa ba'a ɓata lokaci wajen tsintar duk abinda ya suɓuce da gangan sau da yawa kana sake haɗuwa da mafiyin abinda ka baro a baya." tayi Maganar cikin ƙunar zuciya ta dawo kusa da yarinyar ta zauna tare da jawo ta jikinta tayi shuru cikin matsanaciyar damuwa, ita kuwa hankalinta yana kan wasa jin turo ƙofar falon nata ne yasata ɗaga idanunta tana duban waye ne, sanye yake da farar riga shirt ya ɗaura baƙin suite a samanta ya na sanye da baƙin wando hannunsa ɗauke da briefcase, fari ne dogo mai ɗan kaurin jiki baza'a kirasa da mai ƙiba ba, fuskarsa na zagaye da saje idanunsa sanye da Google glass kanta ta ɗauke daga kallonsa ta mayar gefe domin kuwa idan akwai abinda idanunta yafi tsanar kallo a yanzu shine, yarinyar da bata wuce shekara Uku ba ne ta tashi da gudu taje ta kamasa tana cewa.
    "Oyoyo Daddy."
Ture yarinyar yayi daga jikinsa cikin tsana da ƙyamar yarinyar ya watsawa yarinyar mungun kallo tare da jan doguwar tsuka ya shige, takurewa yarinyar tayi a gefe ta fashe da kuka, cike da ƙunar rai Lubna ta ɗago ta kalli ɗiyarta Najnal sosai ranta ya harzuka da abinda ya yiwa yarinyar, a fusace ta tashi ta bishi bedroom ɗin nasa tura bedroom ɗin tayi ba tare da sallama ba, yana tsaye jikin wardrobe yana rage kayan jikinsa ta tsaya a gefen sa cikin zafin rai ta fara magana.
    "Abbakar na gaji da ƙuntatawa ƴata da kakeyi, cin mutuncin naka ya tsaya iya ni mana Najnal meye laifinta yarinya ce fa ƙarama, ka sani ba'a sauyawa tuwo suna tuwon dai shine har gobe sunansa, dan haka Najnal bazata sauya daga ɗiyarka ba kaima ka sani, duk yadda zakayi ruwa bazai wanke ba, haka kuma ƙasa bazata goge ba, nayi danasanin auren ka a rayuwata wallahi Abbakar Allah ya isa tsakanina da kai ka cuci rayuwata da ta ƴata."
  Murmushi Abbakar ya saki tare da juyowa ya kalleta ya ajiye agogon hannun shi a gefen gado yace.
   "Danasani baki fara ba tukunna sai ranar da baƙin cikina ya kashe wannan Ƴar taki a ranar zaki fara danasani, amma yanzu baki fara ba, karki ƙara kiran Najnal da ɗiyata, na rasa meyasa ƙaddara ta haɗani inuwa ɗaya dake Lubna, Ki fice min daga ɗaki na daina kallon wannan mummunar fuskar taki, domin na lura ke shasha jahila daƙiƙiya ce marar zuciya."
   Idanunta ta runtse hawaye masu zafi suka silalo daga ƙwayar idanunta zuwa kuncinta.
   "Gaka nan babban jahili idan ba jahili ba waye zai dinga aikata abinda kakeyi, kafin ka kirani jahila kamata yayi ka fara kiran kanka jahili domin sunan da kai ya dace."
   Ta jefa mishi maganar cikin zubar hawaye a idanunta babu tsoro ko kaɗan domin ita kanta bata san lokacin da maganar tazo bakinta ba.
   Bakinsa Abbakar ya buɗe yana duban Lubna cikin ɓacin rai da mamakin kalamanta, ya nuna mata kansa da yatsa yace.
   "Ni kike kira da jahili Lubna?"
   Kanta ta ɗaga tana cije lips ɗinta tace.
  "Eh na faɗa jahili ƙarya nayi ne? ka kashe ni mana Abbakar ka huta nima na huta, ko da yake me yayi saura na girmamawa a tsakanina da kai Abbakar babu ko ɗaya domin kuwa ka gama kasheni kamin mutuwar tsaye numfashi na ne kawai ya rage baka ɗauka ba." 
  Ta ƙarisa maganar tana fashewa da kuka mai cin rai sauƙar mari taji a fuskarta wanda ya sata ganin gilmawar taurari masu tsananin haske, hannu tasa ta dafe fuskarta tare da ɗago kai tana kallon sa, duk da ba yau ta saba shan marinsa ba, hakan bai hana zuciyarta tafarfasa ba, da hannu yake nuna mata hanyar fita cikin tsawa yace.
   "Fice min daga bedroom! Kafin na illata ki idan banda ƙaddara meye zai haɗani da ƙasƙantacciya irin ki, ki sani nine wanda nayi danasanin auren ki."
  Ji take tamkar ana ƙara rura wutar dake ci a azurta domin kuwa wani irin raɗaɗi zuciyarta ke ƙara mata tamkar zata fashe, juyawa tayi tana sakin kuka ta fice, tsuka yaja tare da zama bakin gado zuciyarsa na masa hura idanunsa sunyi jajur iska ya fesar daga bakinsa ya naushi jikin gadon yana cije lips ɗinsa, a hankali ya furta.
  "Kin cuceni Lubna kin zalunci soyayyar da muka sha wahala kafin ginata, kin rusa kyakkyawar alaƙarmu da bazata taɓa gyaruwa ba har abada, kin cuce zuciyata."
  Take hawaye ya wanke masa fuska a hankali ya zame ya kwanta rigingine a kan gadon yana kallon sama, yana jin zuciyarshi na bugawa da ƙarfi runtse idanunshi yayi hawaye ya biyo fuskar shi, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ya fara furtawa a hankali.

  A falo kuwa Lubna ta samu Najnal ta gama kukanta harta ɓingire bacci tausayin yarinyar ne ya ƙara kamata hannu tasa a hankali ta ɗagota ta ɗaura a cinyarta tare da kwanto fuskarta kan Najnal hawaye na cigaba da tsere saman fuskarta ta furta.
  "Ban taɓa zaton rayuwa zata juya min haka ba, ban taɓa zaton akwai ranar da Abbakar zai juya min baya ba, Abbakar mai tsantsar sona da tausayi na, wai yau ni ce a wulaƙance a wajen shi, nine Abbakar yake ƙuntatawa, tabbas duniya tafi gabaruwa iya jima."
  Numfashi ta sauƙe tare da ɗagowa ta shafi kan Najnal ta cigaba da cewa.
   "Meyasa kika min haka zuciyata!! Duk kece dalilin wannan wahalar rayuwar da nake ciki yanzu, gashi zunubin ki har ya shafi yarinyar da bataji ba bata gani ba, haba Abbakar meyasa babu zuciyar imani a ƙirjinka? Ina zanje naji sanyi waye zai jawo ni inuwar shi ya cire ni a wannan matsin rayuwar da nake ciki, ki yafe min Najnal duk laifina ne dana haifeki wataƙila da a cikin wata macen daban kika zo bani ba, da wataƙila kina cikin jin daɗi, da wataƙila baki fuskanci wannan baƙin cikin ba! Allah ka kawo mana ɗauki a wannan rayuwar da muke ciki."
  Tayi maganar tana ɗaukar wayarta ta duba lokaci 10:30pm hannu tasa ta share hawayen fuskarta tare da sanya Najnal a kafaɗa suka shige bedroom kayan bacci ta sanya mata ta shimfiɗeta a gado kamin itama ta shiga toilet tayi wanka tare da shirin bacci kafin tazo ta kwanta ta tofe ƴarta da addu'a, sai dai ina bacci ya gagari idanunta idan da sabo ta saba da bushewar idanu tun ranar da farin ciki yayi bankwana da rayuwarta.

   Washegari da sassafe bayan ta gama azkar da karatun Alqur'ani da ta saba ta tashi ta shiga kitchen breakfast ta haɗa musu kasancewar bata jin daɗin jikinta, indomie kawai ta dafa ta soya ƙwai sai ruwan zafi da bread, ta kawo danin ta jera, ƙofar bedroom ɗin shi ta kalla tare da runtse idanunta ta doshi bedroom ɗin kamar yadda ta saba ko wacce safiya, da sallama a bakinta ta shiga yana zaune bakin gado ƙarisawa tayi ta tsaya cikin sanyin murya tace.
   "An tashi lafiya.?"
 Tamkar mai ciwon baki murya can ƙasa ya amsa da.
  "Alhamdulillah."
"Na kammala breakfast, bana jin daɗi indomie kawai na dafa da ƙwai sai ruwan zafi, dan Allah ina son magana da kai idan zan samu lokacin ka."
  Sai yanzu ya ɗago idanunsa ya kalleta yace.
  "Zaki iya magana ina da lokacin da zan iya sauraronki yanzy kiyi magana ina jinki."
  Fuskanto shi tayi ta zauna a saman table kafin ta sauƙe numfashi tace.
   "Abbakar kayi haƙuri dole ne yasa yau zan furta wannan kalmar duk da nayi maka alƙawarin komai rintsi komai wahala bazan taɓa rabuwa da kai ba, sai dai ban sani ba ashe alƙawari mai nauyi na ɗauka da bazan iya cikawa ba, dan Allah ina son ka sakeni, ka bani takardar saki dan Allah Abbakar ko zan samu naje nayi rayuwar ƴanci, ko zan samu sanyi ko kaɗan ne acikin zuciyata, duk da ka samin ciwon da bazai taɓa daina min raɗaɗi ba har ƙarshen rayuwata."
  A firgice ya ɗago ya kalleta tare da furta.
  "Saki! Lubna yau kece da bakinki kike furta na sake ki, Gaskiya ne Hameed yayi ƙoƙari kun shirya zakuyi aure ne shiyasa zaki nemi na sallame ki.?"
   Murmushi mai ciwo Lubna ta saki tace.
  "Ban damu da duk abinda zaka faɗa ba, bani da wani amsar kuma da zan baka, dan Allah ka sakeni Abbakar shine kawai abinda nake nema a wajenka yanzu, komai ya ƙare tsakanin mu babu amfanin cigaba da zama cikin alaƙar da ta gurɓace."
   "Lubna kina da inda zaki zauna ne idan na sakeki, nasan ke kanki baki isa ki tunkari iyayenki ba ko?."
  Cikin ƙunar zuciya tayi dariyar da yafi kuka ciwo.
  "Hakane kayi gaskiya bani da ƙwarin gwuiwar tunkarar su, yau kaine kake min gori? hakane na rasa martaba ta a wajen iyayena, tabbas yau nafi kullum nadamar ƙaunar da na maka, da kamin gorin abinda na aikatawa iyayena akanka, Abbakar soyayyar ka ta zamo min tsakuwar Ido kullum ina tambayar kaina, shin gaskiya ne kaine kake wulakanta ni, ko dai mafarki ne da ban farka ba har tsawon shekaru uku, na gama haƙuri na tsawon wannan shekarun cikin ƙuna da ƙuntatawar ka, Abbakar zuciyata tana min ciwo idan na sake wani shekarar tare da kai tabbas babu makawa ciwon zuciya ne zai kasheni, na zo gidanka da niyyar samun farin ciki, nabar gidan mu da hawaye, saboda na yarda da kai ina jin zaka zamo min bango majingina kuma ka maye min gurbin iyayena, ashe ban sani ba cewa babu cutar da tafi dogara ga wanda bashi da zuciya, ashe ban sani ba cewa babu wanda zai iya maye maka gurbin iyaye tabbas rayuwata darasi ne." 
 Murmushi yayi yace.
  "Burinki shine na sakeki kije kuyi Aure da Hameed na juma da hasashen wannan tuntuni kuma nasan dama wannan ranar zatazo da zaki tambayeni takardar saki, amma wallahi Lubna bazan taɓa sakeki ba, burinki bazai taɓa cika ba, haka zakiyi rayuwa a gidan nan ke ba aurarriya ba, kuma ke ba sakakkiya ba, yanda kika ci amanata kika ƙuntatawa zuciyata haka kema zaki zauna cikin ƙunci har abada ke da wannan ƙasƙantacciyar ƴar taki ina ƙara gargaɗanki daki daina dangantani da ƴarki."
   Hawaye ne ya gangaro daga idanunta kafin tayi shuru tana sauraron shi tace.
   "Har yanzu kana kan bakanka, har yanzu kana cewa na daina dangantaka da Najnal, Abbakar ayau dai na yarda na amince na daina danganta Najnal da sunan ka, amma ka sani dole zan bar maka wannan gidan da ka sakeni da baka sakeni ba, ka saurarani da kunnuwan ka domin wannan itace maganata ta ƙarshe tare da kai, domin kuwa ayau zan ɗauki zuciyata tare da ƴata mu bar maka gidan ka."
   Ta ɗanyi shuru tare da numfasawa ta cigaba da cewa.
   "Daga yau Najnal bazata sake kiranka Daddy ba, sannan ka saka a ranka kaima har abada bazaka taɓa ƙiranta ƴarka ba, saboda ban sama mata uban da zai raini jininta ba, in sha Allah Najnal bazata sake kallon wanda ya zargi mutuncin mahaifiyarta ba, wanda yace bata cancanci girmamawa ba, nice mahaifiyarta kuma zan kare mata mutuncin ta da rayuwarta in sha Allah bazata sake kuka a rayuwarta ba."
  Ta ƙarisa maganar tana tashi ta doshi ƙofa da sauri sai kuma ta tsaya tare da juyawa ta kalle shi tace.
 "Hameed! Hameed! Shine kullum tuhumar ka a kaina ba? Ka sani Hameed mutumin kirki ne da yasan addini da haƙƙin Ubangiji yana da mutunci da sanin darajar ɗan adam, kuma baya taɓa raina ƙauna, kasan meyafi daɗi da Hameed, mutum ne mai sanin ya kamata da darajar ɗan adam, ya fika ta ko ina yana da abinda zai iya ɗaukar mataki a kanka wanda zai iya maka ko wanne irin hukunci babu kuma mai tuhumar sa dalili, amma ya ɗauke idanunsa akanka, bai ɗaga idanunsa sama domin ya kalleka ba, saboda yasan shi ba tsaranka bane yafi ƙarfinka ta ko ina, ba irina ba da na ƙasƙantar da kaina saboda kai, kuma wallahi dole sai ka sake ni, sannan ka jira tsayuwarmu da kai agaban Ubangiji, nayi rayuwa dakai tsakani da Allah da zuciya ɗaya ban taɓa wulakanta maka aure ko keta maka haddin auren ka ba, amma kai Abbakar kaine wanda ka ketare haddin aure da alƙawari, Allah bazai barka ba domin kuwa ka cutar da zuciyar da ta yarda da kai fiye da iyayenta, ka cutar da rayuwata cutarwa mafi muni."
 Tayi maganar tana fashewa da kuka tare da ficewa da gudu ba tare da jira yayi magana ba, bedroom ɗinta tayi tare da faɗawa saman gado tana cigaba da rera kukanta yayin da zuciyarta ke ƙara iza wutar dake ƙara tafarfasa mata gangangar jiki.
 "Momy waye ya miki bulala kike kuka, Daddy ne ko Momy?"
 Taji Muryar Najnal hannu tasa ta goge hawayen tare da jawo ta jikinta ta saki murmushi ta girgiza mata kai tace.
 "A'a Daddy ai ba zai yiwa momy bulala ba, ciwo idon yake maza tashi kije ki ɗauko babyn ki sai ki kawo muyi mata wanka tayi datti."
  Da sauri ta tashi tana murna harda tsalle za'a yiwa babyn ta wanka, tana tashi hawaye ya sake biyo fuskar lubna cike da ƙauna take bin najnal da kallo mai haɗe da tausayi tana ji a ranta cewa duk itace ta cuci rayuwarta da bata haifeta a cikin ta ba bazata fuskanci zargi ba, a hankali ta fara tunanin rayuwarta ta baya mai cike da farin ciki idan har aka ce mata akwai ranar da zatazo ta risketa na baƙin ciki tabbas zata ƙaryata sai dai yanzu gata cikin tsananin zafin rana.



 Ummu Nasmah. ✍🏻