MUTUNCIN ƳA MACE!

Chapter 2

by @zmchubado

Haka Sumaiyya ta koma gida tunani da damuwa fal ranta, sai take ji kamar ta kashe kanta, da sauri ta k'wabi kanta da wannan banzan tunanin data tuna makomar duk wanda ya kashe kansa to fa kai tsaye wuta zashi, addu'a ta dunga yi da kuma karatun alqur'ani kan Allah ya kawo mata mafita kafin takwas d'in daren da suka ajje.idar da sallar magrib d'inta kenan, ta dan sake tab'a karatun Qur'ani sama sama sannan tayi add'ua ta shafa, kana ta mik'e tana ninke sallaya ayayin da take tunanin irin karyar da zata shararawa su Yaya Basira har asamu su batta ta Fita adaren nan.Bayan ta gama yanke shawara da zuciyar ta, Kai tsaye ta nufi dakinta, ta sameta tana sallah, danta Adil kuma ya bingire da bacci agefenta, Zama tayi har sai data jira ta sallame sannan ta juyo gareta tace"ya akayi ne k'anwata na ganki wata sum sum dake ? Ko akwai wani damuwar ne ?" 

Shiru babu amsa da alamun tayi nisa cikin tunani, hannu Yaya Basira tasa ta tab'o ta"ke! Sumaiyya." Firgigit! Ta dawo hayyacinta hadda sa hannu tana dafe k'irji, sai sauke numfarfashi take tace"Kai Yaya har kin ban tsoro wallahi."Tace"wai ni meke damunki ne ? acikin 'yan kwanakin nan nasa miki ido sosai na lura kwata kwata baki da walwala, kamar akwai abunda ke damunki amma zurfin cikin tsiya ya hana ki bud'e mun cikinki, ey Sumaiyya ? baki son ki gayamun damuwarki sabida ba ciki d'aya muka fito bako ?" Da sauri Sumaiyya ta matso kusa da ita tana girgiza kai alokaci daya kuma wasu hawaye masu radad'i na shirin kwaranyo mata, ta kamo yatsun Yaya Basira tace cikin raunin murya"haba yayata meyasa kike fadin irin wannan maganar da ko kadan batta da dad'in ji ? Ni ko kadan bana mana kallon 'yan uba, ji nake tamk'ar uwa daya ce ta haifemu, dan haka na hadaki da girman Allah karki sake irin wannan tunanin, kuma zancen damuwa babu abunda ke damuna kawai kewar su Baba nake tunda na dad'e ban je gida ba."

Ajiyar Zuciya Yaya ta sauke tace"Kai Sumaiyya 'yar Baba, gashi Baba ya nace sai kinyi karatu tunda mu mun ki maida hankali muyi, to don Allah Sumaiyya yadda tsohon nan yake fad'i tashi akanki dan ganin kin cimma burinki arayuwa, ki dubi girman Allah da soyayyar dake tsakaninsa da fiyayyen halitta karki bashi kunya, ki bari ki gama makarantar nan lafiya ba tare da an samu wata matsala ba, sannan duk inda zaki shiga kuma ki fita ki cigaba da tsare mana _*MUTUNCIN KANKI*_ ,Sosai mutuncinki yake da matuk'ar daraja agareki damu kanmu danginki, Sumaiyya ko baki san da cewa bayan mahaifinmu kece haske ga danginmu ba ? dalili kuwa shine kasancewar acikinmu duka kece kika dakko halayen Baba Sheikh saf! Komai baki baro ba hatta da kamanninsa da komai ma, shiyasa idan kika lura yafi kaunarki akanmu, hakan ne ya jawo sauran ke tsananin kishi dake, ki sani zub'ewar mutuncinki yana nufin zub'ewar mutuncin gidanmu ne, dan haka ki rikeshi dak'yau kar kiyi sakaci, ki bari mu aurar dakai cikin mutunci kamar yadda aka aurar da sauran matan Zuri'a.." kuka yaci mugun karfin yaya Basira, ita kanta Sumaiyyar kukan take sosai tamk'ar zata had'iyi zuciya ta mutu, musamman ma da taga Yayar tata na mata tuni ne tamk'ar wacce tasan abunda take shirin aikatawa adaren yau...."Sumaiyya kina da tarin masoya da mak'iya masu nufinki da sharri sosai, akwai masu son shiga tsakaninki da mahaifinki domin wargaza kyakkyawar alakar dake tsakaninku amma fa ki sani sai in kece kika bada damar faruwar hakan, Shiyasa nake sake zaburar dake da ki dunga k'ok'arin gayamun damuwar ki ,ni kuma na miki alk'awarin baki shawarwari na gari.." 

Cikin sarkewar murya tace"inshaa Allahu Yaya bazaku tab'a kuka dani ba, kuma ina mai rokonki alfarma da ki cigaba da tayani da addua domin ina jin zuciyata na neman gazawa akaron farko arayuwata wajen biyewa sharrin shaidan, yaya ki taimakeni da du'a'i Allah yasa in cinye jarabawar da Allah ya safko mun domin kuwa hak'ik'a na fara fuskantar jarabobin da Allah ya rubuto mun na rayuwa..." Cike da tsoro Yaya Basira tace"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! ina fatar wannan jarabawar bai tab'o mutuncinki ba dai ko ?" Cikin tsoro da fargaba, da kuma dauriya tace"ko kadan!..." Yaya ta saukar da ajiyar zuciya tace"Alhamdulillah! domin mutuncinki shine babban damuwa, to Allah ya yaye miki duk wani abunda ke damunki, kuma Allah yasa ki cinye duka jarabobinki duniya da lahira." 

"Ameeyn dan darajar ma'aiki." taja bakinta tayi shiru ta hau watsa da zoben hannunta, Yaya Basira ta lura kamar akwai sauran magana abakinta tace"Kamar akwai sauran magana abakin naki ko ?" dan murmushi tayi tace"eh dama so nake in shiga makaranta in karbi BCH522 d'ina awajen Khadija na manta dashi ne dazu ahannunta kuma gashi muna da test d'insa gobe da sassafe." Tace"Ban tari numfashin ki ba amma adaren nan kikeson ki shiga makarantar Sumaiyya ? takwas saura fa ? Da kin hakura gaskiya...." kamar zatayi kuka tace"Yaya ki taimaka mun kar in fad'i kinga awannan zangon zan kare bana son in samu wata matsala, nasan mutuncina kike kokarin karewa, Allah ne mai kiyayewa da kuma tsarewa amma nayi miki alkawari fitar nan da zanyi babu abunda zai sameni insha Allah." Ba don taso ba tace"To shikenan Sumaiyya dan Allah kiyi sauri ki dawo kafin Abban Adil ya shigo bai sameki ba kuma kema kin san ransa zai b'aci matuk'a tunda an damka amanarsa ne ahannunki, kuma bazai so ace kin fita adaren nan ba tare da saninsa ba."

Tace"insha Allahu bazan zauna ba ina karba zan dawo." Yaya Basira tace"nayi zaton Fu'ad ne zai zo ya kaiki ai." Da sauri ta tari numfashinta"a'a ba zai samu zuwa ba yau aiki ta masa yawa." Yaya bata sake cewa komai ba ta shiga daki ta dakko kudi ta kara mata kudin mota, makarantar tasu dama bashi da nisa da gidan nasu.

Da sauri sauri ta fice daga gidan, acan waje ta rushe da kukan tausayin kanta tana fad'in"ya Allah ina mafita takwas saura, ina son in cikawa Baba burinsa amma bata wannan hanyar ba, Allah ka fiddani cikin wannan kangi, Allah na rokeka ka canzamun kaddara ta ko wacce iri ne zan runguma amma ba wannan ba.." kuka ya sake cin karfin ta, magana take ba'a cikin hankalinta ba.Wani tunani ya fad'o ranta, da hanzari ta latso Baba Sheikh awaya, awannan lokacin kuma Zaune yake a kangon limancinsa, mutane agabansa yana musu dan nasihu kafin lokacin isha'i yayi, sai ga kiran Sumaiyya, washe hakora yayi sai ya katse sannan shi ya kira ta, dama haka suka saba, baya tab'a daga wayar ta sai dai shi ya kira.

Bayan sun gaisa dakyau tace cikin rauni"Babana so nake ka sake raunana zuciyata da _*Tsoron Allah..*_ " asanyaye yace"Samar da tabbatacciyar dabi'ar _*Tsoron Allah*_ da kuma inganta ta yana bud'e idanuwan zuciya a kan waswasin shedan, sannan kuma ya kare mutum daga afkawa cikin komar shedan, shi kuma al'Qur'ani mai girma yana la'akari da imani, shi ne abu na farko kuma ginshik'i domin dank'wafe mamayar shedan, wani jigo daga cikin abubawan da ake nasara a kan shedan da rundunoninsa shi ne _*Tawakkali ga Allah*_ tsarki ya tabbata a gare shi, _*Tsari*_ wato isti'aza shi ma'anarsa na nufin neman mafaka ga Allah madaukaki, sannan yawan ambaton sunan Allah yana baiwa mutum basira kuma yana nesanta shi daga waswasi, ya kuma toshe kofofin da shedan ke bullowa ta cikinsu.Dan haka ki zamo mai yawan ambaton Allah, neman tsarinsa, da kuma yin tawakkali, hakan ne zai jefa wa Zuciyarki tsananin tsoronsa akodayaushe, Allah ya tsare mun ke."

Cikin rauni da rawar murya ta amsa da"Ameeyn Babana nagode kwarai da gaske." Daga haka sukai sallama ya sauke wayar daga kunninsa yayi wa screen d'in kuri da ido, nan da nan zuciyarsa ta afka cikin kunci ya shiga nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, tabbas yana ji ajikinsa akwai wata 'yar musifa data fuskanto 'yar tasa gaba, ya sani duk cikin ya'yansa Sumaiyya ta fisu Zurfin ciki, da kamar wuya aga ta zauna tana zayyane maka damuwar ta, cikin ransa yace"ya Allah ka tsare mun Sumaiyya da tsarinka, ka kareta da kariyarka dan albarkacin hasken Al'Qur'ani mai girma.."

Sosai ta dan samu salama da sassauci azuciyarta bayan sun kare waya da mahaifin nata, amma har yanzu babu abunda ya sauya zani na son cimma burin mahaifin nata, ta sani muddin ta kuskura ta samu matsala to hakan na nufin samun matsalar ta dashi mahaifin nata domin kuwa arayuwarsa ya tsani faduwa.Tuna hakan ne yasa tayi saurin warware wata 'yar takarda domin kwafe lambar Dr.Gana daya rubuta mata yace in lokaci yayi ta nemeshi.

Dr.Gana kuma awannan lokacin yana kwance saman makeken gado a Villa hotel yana jiran k'ira daga Sumaiyya, tuni har ya kwab'e kayan jikinsa, sai ya rage daga shi sai boxer da singlet.Yana ganin bak'uwar lamba yayi saurin dagawa, muryatta mai zak'in gaske ya daki dodon kunnuwansa"na shirya yanzu zan kamo hanya saika aikomun da room number." Cike da farin ciki ya gaya mata yana dariya kamar wani soko, kittt ta katse ranta ajagule, sai istigfari take acan kasan ranta, acan bakin titi ta samu taxi drop har gaban hotel d'in...

****

*KADUNA STATE*
*_(Umaru Muhammed Road)_*

A haka rayuwa ta dinga tafiyarwa Asma'u cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, sosai tai wani irin kyau gamida murza ƙibarta kamar ba Asma'un da kewar mijinta ta maida ita wata kala ta daban ba kamar kullum yauma a zaune take bisa saman ɗaya daga cikin kujerun dake falon, sanye take cikin wata shaiɗaniyar rigar bacci wadda ta baiyanar da duk ilahirin jikinta a waje. Kasncewar Asma'au macece me kyawun sura sosai ne yasa rigan yay mugun fitting ɗin jikinta

Hannunta ɗauƙe yake da wani ƙaramin kofin glass wanda ta cikashi da sassanyar madara me shegen kauri tanasha tana kaɗa ƙafa sabida yanda duniya ke mugun gara mata yanda takeso, wayarta dake gefanta ce ya ɗauki ruri a wulaƙance ta kalli wayar sabida jin sautin wayar tabbas tasan Sulaiman ne, tsaki taja me ƙarar gaske sabida yanda wani irin haushinsa ya cika mata ciki kamar bazata ɗauka ba se kuma can ta ɗauka tana yatsina fuska tace " mijin mace ɗaya ya akai?. Ɗan dariya Sulaiman yayi wadda ta baiyanar da mamakinsa ga kalmarta yace "Asmy!! I'm Sorry don Allah kada kiti fushi kinji babyna?. Bisaga mamakinsa seyaji bata fashe masa kuka Kamar yanda ta saba can ƙasan zuciyarsa seya samu kansa dajin wani iri a karon farko a rayuwarsa tunda sukai Aure, tabbas yasani sam baya kyautawa Asma'u kasan cewarta mace me karfin shi'awa. Amma a zahiri seya sake murmushi a karona biyu yace " dama nace barin kiraki ne inji lfyn ki babyna. Siririn tsaki taja wanda ba lallai yajita ba tace "ok to na gode. Ta faɗi hakn tareda katse wayar don wllh ya isheta da shegen surutunsa

A haka rayuwa ta dinga tafi lokaci na shuɗewa fatin Asma'u da Bashir kullum ƙara kusanci suke da juna abin haryaci uban na da, Bashir ne kwance saman jikin Asma'u duk ya gama ƙosawa da jarabarta kamar ze sakin mata kuka ya kalli tsakiyar idanunta wanda suka ƙanƙance yace "Antie wllh nagaji don Allah kiyi haƙuri haka man......... Sam bata bari ya ƙarasa abinda yakeson faɗa ba ta haɗe bakinta da nasa ciki sauri, sosai take kasheshi da wani shaiɗanin kissing wanda tunda uwarshi ta kawoshi duniya besan da irin wannan sample ɗin kissing ɗin ba, al'amarin da Asma'u take gudanarwa ga Bashir ɗin zazzafa ne wanda hakan ya ƙara ɗaga mazantakarsa zuwa cikakken namiji kuma me lafiya *((reders kuji tsoron Allah kada ku juya mana ma'anar labari zuwa canza bigiran rayuwarku, kada ki ɗauki kwatankwacin irin rayuwar da Asama'u take aikatawa da bashir wllh hakan kuskurene kuma tabbas zakiyi nadama, Kusantar zina ko aikata ta baya janyowa ɗan adam komai face zallar dana sani gamida ƙuncin zuciya, kada ku fassara mu ba daidai ba kawai mun rasa yanda zamuyi mu baiyana muku irim ƙazantar dake cikin Rayuwar Asma'un ne dole seta hakan ))* da zafi-zafi take aika masa saƙon nata wanda hakan ya zame masa alaƙaƙai dole shima ya fara mayar mata da martani cikin salo da ƙwarewa, bakaji sautin komai sena fitar numfashinsu zuwa yanzu shi kansa Bashir ɗin ta gama sauya masa akalar Rayuwarsa haka kuma abune mawuyaci ya iya samun macen da zata ɗaukeshi a yanda yake indai ba Asma'u ba, a duk lokacin dayake tareda ita ji yake duniyar na juya masa sabida irin tagomashin alkhairin dayake kwasa a sassan halittarta, wllh ze iya cewa sulaiman ya tabka babbar Asara dayay wancakali da wannan gagarumar alfarmar dayake da ita me tarin alfanu a jikin Asma'u don haka yake kallonsa a Sakarai kuma wanda ya rako maza duniya.

Wata Ranar Alhamis tunda sanyin safiya Asama'u ta tashi cikin wani irin yanayi na rashin walwala gamida yawan faɗuwar gaba, haka kawai setakeji a jikinta tamkar wani abu mummuna yana shirin faruwa da ita a haka ta fito harabar gidan sanye cikin wata doguwar riga maroon ko bra babu a jikinta hakan ya bawa big boobs ɗinta damar fitowa sosai, koya ta motsa ƙafarta sesun kaɗa idan ka kalleta sekai tsammanin da gaiya takeyin hakan kuma sam ba haka bane yanayin tsarin halittarta ne a haka, har waje ɗakin Bashir taje se kuma ta samu kanta dajin tsoron shiga ɗakin, tana nan tsaye ya fito bakin ƙofar yana taje gashin kansa da cumb wanda ya ɗan cika sosai singlet ne kawai a jikinshi se gajeran wando wanda ya matse laps ɗinshi sosai, kafeta yay da idanu kamar yanda itama ta kafeshi da nata idon a wannan lokacin kowanne daga cikinsu akwai abubuwan dayake saƙawa a gameda ɗan uwansa wanda su kasu basu gama ƙaiyade matsalarsu da juna ba, juyawa tayi da sauri ta koma side ɗinta zuciyarta na wani irin bugawa tamkar zata faso ƙirjinta ta fito, binta yay da sauri yana kiranta har ya shige shima a hankali harya isa gareta ya tsaya yana kallon tsakiyar ƙwayar idonta wanda ƙwalla ya cika tab, hannunsa yasa ya ɗago haɓarta tareda haɗe bakinsu guri ɗaya ya fara kissing ɗinta gently, a nitse yakai hannunsa jikinta yana shafawa a hankali harya kai saman boobs ɗinta ajiyar zuciya ta sauke sabida jin yanaso ya birkita mata lissafi, duk yanda taso qin biye masa dole ta saki jiki dashi suka fara musayar wuta a tsakaninsu a haka dai suka sake afkawa tarkon zina wanda a yanzu ta riga ta zame musu jiki.

da safen wajen ƙarfen Goma jirginsu Sulaiman ya sauka a garin Kaduna, Sam bai kira wayar Asma'u ba sabida yanda yakeso ya bata mamaki da dawowar tasa, a haka ya ɗauki hayar motar ta ɗakkoshi tun daga filin jirgi har ƙofar gidansa, da fara'arsa ya tura ƙaramar ƙofar get ɗin gidan ya shiga kana kallonsa kasan yana cikin gagarumin farin cikin dawowar tasa, cikeda girmamawa mai-gadin gidan ya tsuguna yana gaisheshi da sakin fuska Saulaiman ya amsa masa sannan yace" pls Haruna akwai kaya a motar daya kawoni ka buɗe masa get ya shigo seku sauke kayan, Sulaiman ya faɗi hakan cikeda zumuɗin ya shiga ciki yaga Asama'u sannan ya wuceshi yana murmushi zuwa cikin gidan, da sallama ya shiga falon cikin takunsa na ƙasaita kyakkyawar fuskarshi ɗauke da yalwataccen murmushi wanda ya ƙara fito da sihirtaccen kyansa, Sulaiman ba fari bane sosai irin mazan nan ne choclet colour fuskarsa a zagaye take wadda ke ɗauke da dogon hanci gamida manya idanu, yanada yalwataccen gashi sak irinda yankin indiawan punjabi shiyasa salon kyansa ya kasance na musamman, a fannin tsarin halitta da cikar zati kuwa wllh sam ba'a magana domin sulaiman cikakken namiji ne irin mijin da ko wace mace ke mafarkin samu.

Wannan shi ake kira ga tsayi ga kyau. Ya salam!!!

Yana shiga be dire ko ina ba se bedroom ɗinsu nan take ƙirjinsa yay wata irin bugawa da mugun ƙarfi sabida abinda yay arba dashi........

*****

Saukar ta keda wuya sai ga sak'on Dr.Gana ya shigo wayarta a inda ya aiko mata da RM No, RM 102.Gabanta sai bugawa yake wai ita ce ayau zata sa kafa cikin otel da sunan aikata sab'on Allah, wa'iyazubillah! Wani uban kuka ne ya kufce mata da sauri ta tattaro hijabin ta ta toshe bakinta.
Anatse take tafiya kan nan nata akasa dan gani take kamar idanun kowa akanta yake, bata wani sha wahala ba wata receptionist ta mata jagora har gaban dakin kana ta juyo ta barta nan tsaye tana tunane-tunane.

"Yanzu shikenan Sumaiyya kin yadda ki zubar da mutuncin kanki dana gidanku akan kwalin makaranta ? daga yau fa in kin saida mutuncin nam naki shikenan fa kin rasata har abada, Sumaiyya ki sake tunani.." Wannan shine abunda k'yakkyawan sashi na zuciyar ta ke gaya mata, shaid'anin kuwa cewa yayi"kar ki kuskura kiyi wasa da damarki domin kuwa wannan shine zango na k'arshe da zaki kare karatunki, kuma in kika samu matsala baya zaki koma, hakan na nufin kin rushe dukkan burin mahaifinki akanki kenan, yi maza Sumaiyya kar kiyi kukan dana sani akurarren Lokaci." da wannan mummunar huduba na shaid'anin wani sashin zuciyar tata ne yasa ta samu kwarin gwiwa tasa hannu ta murd'a kofar dakin, Fuska babu walwala ta danna kai ciki, gogan naku na ganinta yayi saurin dirowa daga saman gado yana washe jajayen hak'oransa kamar wawa, ya nufeta yana fad'in"haba Sumy darling zaki shigo wuri ko sallama babu sai kace kafira ?" Wani irin kallo mai cike da tsana ta kwasheshi dashi tunda daga kafarsa, Zuwa katoton tumbinsa kan ta dire kallon nata kan tsamin fuskarsa wanda ta yalwatu da bak'i da kuma sirkin fari farin gemu da kasumba a hagu da kuma damar fuskar tasa, tab'e baki tayi tace"sallama ana yinta ne awuri mai daraja kuma ana neman amincin ne awajen Allah zuwa ga mutumin dake tsananin tsoronsa da kuma k'ok'arin kiyaye dokokinsa amma ba mutum fasik'i kamar ka mai zuciya irinta fir'auna ba, mai cin mutunci da kuma keta haddin mata, wanda ko kadan bai san darajar 'ya mace ba alhalin *MACECE* ta haifeka..."

Hannaye yasa ya toshe kunnuwansa sannan ya doka mata tsawa"Ya isheki haka! ina fatar ba cin mutuncina kika zo yi ba anan ?" Ya furta yana kara kusanto inda take, Zuciyar ta tamk'ar zata fuzgo waje tsabar bugawa amma haka ta daure tace"har wani mutuncin ne kake dashi ? ka sani yadda ka shirya cin nawa mutuncin ayau haka zalika nima ashirye nake da inci mutuncin daya sauran maka, yau zan nuna maka ta yadda akai na banbanta da sauran 'yan matan da kaci zarafinsu, ayau zan kwatar mana 'yancinmu awajenka kafin zuwa lokacin da zan gangaro kan sauran mazan marasa tsoron Allah kamar ka, ka bani minti 10 kacal idan har na gaza to nayi alk'awarin mallaka maka abunda nake tinkaho dashi wanda kake k'wadayin samunsa akan arha, yanzu dai idan akwai alkalami da 'yar takadda inaso ka dakkosu sannan kayi shirin amsa mun tambayoyin da basu wuce biyu zuwa uku ba..."

Ya wangale baki zaiyi magana ta doka masa tsawa"kayi abunda nace in ba haka ba zan tara maka jama'a kuma kasan dai ina da damar aikata hakan tunda har yanzu kofa a bud'e take." Ta furta tana masa nuni da kofar dauke da murmushin karfin hali, asanyaye yaja jiki ya koma inda briefcase d'insa yake, ya bud'e ya ballo takadda daga wani booklet da kuma alkalamin rubutu, har yanzu tana tsaye kikam a inda take ko kadan bata motsa ba, sai umarni take bashi shi kuma kamar sok'o yana mata yadda takeso dan kawai ya samu ya keta mutuncinta, tace"in ka shirya zan soma watso maka tambayoyi, kuma sharadin yarjejeniyar tamu ita ce, Na farko wajibi ne ka rubuta tambayoyin da zan maka sannan kuma dole ne ka bada gamsasshiyar amsa akan wannan takaddar, ka sani in har baka iya amsa tambayoyin yadda ya kamata ba to kuwa babu kai babu cimma burinka akaina, ka amince ?" 

"Na amince..." ya bata amsa ba tare da wani dogon tinani ba, kana yaja katon tumbinsa gaban dressing mirror ya aza takaddar sama, ya daidaita alkalamin rubutunsa, Zuciyarsa cike da fargaban irin tambayoyin da take shirin watso masa...." Dr.Garba Gana Kana son ka aikata alfasha da Sumaiyya Ahmad Mukhtar ba don komai ba sai don ka bata grade, to ina fatar ka tanad'i dogon katangar da zaka gina atsakaninku da Allah domin kar yayi katobara da babban laifin da kuke shirin aikata wa ? Wannan shine tambaya ta ta farko agareka, sai ka bada amsa akan wannan takaddar kuma kar ka manta ka rubuta tambayar dana maka tukun kafin amsa."

Da sauri ya dago kai yana kallonta fuska dauke da tsantsar mamak'i yace"Sumaiyya wai me kike nufi dani ne ? wani irin wasan k'waik'wayo kenan ?" Mur tasha ta murd'e hannayenta ak'irji kan tace"Wannan ba wasar k'waik'wayo bace, wasar Zahiri ne wannan, True life yake Faruwa, kuma malam kar ka sake interrupting d'ina, ka amsa mun tambayoyina in duba in naga kaci nasara kamar yadda na dau alk'awari zan mallaka maka kaina k'yauta, in kuma ka fad'i shikenan sai ka hakura ka had'iye maitarka, sannan kuma wannan jarabawar dana baka tana iya fita waje duniya tasan irin halin da kake ciki, in kuma Allah ya dirsa mun birbishin tausayinka azuci, to ina iya rufa maka asiri....."

Katseta yayi with shock"Whattttt ???? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un amma ba haka mukayi dake ba, munyi dake zaki bani kanki sannan ni kuma in baki grade ki wuce.." yana maganar ne zufa na tsasstsafo mishi duk kuwa da cewar akwai sanyin AC, ganin irin tsoron dake kwance acikin k'wayar idanunsa hakan ya sake bawa Sumaiyya kaimi da kuma kwarin gwiwan abunda ta kudirta arai, lallai ita kanta tasan ta kad'a hantar 'yan maza, dole ne ayau tasa Dr.Gana ya gane cewa in shi amakare yazo, to ita sammak'o tayi, in akwance ya kwana, to ita azaune ta kwana, ma'ana sosai ta shirya masa.'yar yatsa tasa ta datse leb'unanta tace"shhhhh! an gaya maka kai kadai ne kake da sharad'i ? Nawa sharadd'in bai tashi zuwa ba har sai dana tabbatar dana shirya maka, so i'm very sorry daya zo maka akurarren lokaci.." ta kashe masa ido daya, sai kallonta yake kamar soko yana mamak'in yadda alokaci daya yarinya kankanuwa ke juyashi, tana neman maida kwakwalwarsa irinta yara, ji yake kamar kwata kwata bai ma tab'a yin wayau arayuwarsa ba...

Katse masa tunani tayi data jefo tambaya ta biyu mai tsayawa arai"Dr.Gana ahaife ka haifeni, infact watakila ma har jika kayi dani because i'm just 20...." da sauri sauri yace"a'a banyi jika dake ba, babbar d'iyata ma ko sha biyar bata kai ba..." Sumaiyya ta murmusa tace"Dakyau, hakan na nufin dai ka haifi d'iya mace, to Dr.Gana ga tambayata anan ita ce, Shin in wani ya keta haddin wannan d'iya taka ya zaka ji aranka ? Na san da cewa ba karamin tattali kake domin kaga ka aurar da ita cikin mutunci ba, Dr.Gana ka tuna nima d'in d'iyar waninka ce wanda shima burinku iri daya ne na ganin ya aurar dani cikin mutunci, ka sani ko baka haifi d'iya mace ba, to macen dai ce ta haifeka, kaga kuwa abar darajawa ce agareka, sannan tambayata ta karshe ita ce" 'yan matan daka keta mutuncinsu ba'a son ransu ba ya zakayi da hakk'okinsu ? nasan da yawa sun tsine maka, to wani tunani kake akan makomarka ? shin ka tab'a zama kayi tunani akan gamuwar ka da ubangijinka ?"

Wani irin mugun sanyi ne jikin Dr.Gana yayi, tun akan tambayar ta ta biyu jikinsa ya mutu ya kasa cigaba da rubutun, sai digar hawaye, izuwa yanzu kuma shesshek'a kawai yake wanda zai nuna maka alamun nadama ta soma shigarsa, ita kanta Sumaiyyar kukan take rerawa ahankali, ta cigaba magana cike da dacin rai"Nadama ? ai ba yanzu zaka soma kukan nadama ba har sai izuwa lokacin da zaka fara girb'an abunda ka shuk'a, ka sani duk abunda kayi wa d'an wani to rubutacce ne sai an rama akan naka ko wani naka, ka jira ka gani ai ka haifi 'ya mace kuma tabbas itama _*BABBAN JARABAWARTA*_ na jiranta koba jima koba dad'e..." wannan maganganu nata ya kara k'aryar masa da zuciya ya barke da kuka mai kara, murmushin jindadi Sumaiyya tayi na nuna anci nasara akan abu kan tace"yanzu sai muyi abunda ya kawomu ko don lokaci na tafiya " cikin kuka yace"bana yi ki tafi kawai! banayi ki tafi kawai !" Dariya sosai abun ya bata sabida yadda yake nanata maganar yana daga kafad'a tamk'ar wani d'an yaro.

Tace"ga dukkan alamu Sumaiyya Ahmad Muktar tayi nasara akan Dr.Garba Gana, dan haka na barka lafiya amma da zaka karbi shawarata da nace kabar kukan nadamar nan don bazata amfaneka da komai ba, dole sai ya faru akan naka don Zina bashi ce....." 

"Sumaiyya ya isa ki bari.." ya furta yana mai toshe kunnuwa, dariya kasa kasa ta saki tana tafa hannaye tace"to na bari dama ita gaskiya daci ne gareta, kuma tunda naga alamun nadama atattare dakai zan barka da jarabawarka bazai fita waje ba, ya rage tsakaninka da mahaliccinka amma ina so ka addanata don watarana zaka bukace ta..."

Ta juya tabar dakin da sassarfa ayayin daya bita da kallo hawaye duk ya bata masa fuska, ko menene ya tuna kuma? oho sai kawai yabi bayanta da sauri daga shi sai wannan gajeran wandon da singleti, yana bud'e kofar yayi hanzarin jawo hijabinta ta dawo da baya babu shiri, cike da masifa ta waigo zata yanka masa mari sai kawai taji daga gefensu ance " *SUMAIYYA....* "

Afrigice ta waiga idanunta suka sauka akan wanda ya kirayi sunan nata, tuni hantar cikinta suka canza wajen zama, Zuciyar ta da huhhunanta duk suka shiga tsillo, Mutumin da ko kadan batayi tsammanin ganinsa a irin wuri haka ba wai shine take gani agabanta, dakyar ta kakalo murmushin dole sannan ta harhad'o haruffan sunansa tace...........




Comment
And 
Share fisabilillah

2sters H/C✍️