MUTUNCIN ƳA MACE!

Chapter 4

by @zmchubado

"Hafsat anya kuwa zancigaba da amfani da shawarar da kika bani? Gabaɗaya na tsorata da yanayin Sulaiman kafin ya fita, yanada matiƙar sauƙin kai da sanyin Hali bantaɓa ganin yayi fishi irin na yau ba wlh Haf...."dilla dakata malama todan yayi fishin seme?"  Hafsat ta katse Asm'u ta hanyar faɗar hakan cikeda jin haushinta sannan tacigaba da cewa "wllh kedai Asm'u anyi wawiya na rantse da Allah ke in banda kin rako mata duniya har kya bari fushinsa ya ɗaga miki hankli?  Wllh dole ma Sulaiman ya Rainaki  ke idan kikai wasa ma sharar gidanki seta fiki daraja a inadanunsa koda yake  idan har baki ƙwatarwa kanki ƴancinki ba"   "Hmmm Hafsat kenan har zuwa wani lokaci zamu ɗauka a haka  nidashi? Ke kanki kin sani daurewa kawai nakeyi ina amfani da shawararki, amma wllh ni kaina a kusa nake indai akan Sulaiman ne Hafsat sam bana iya jurar kowani abu muddin daga Sulaiman ɗina yake balle uwa uba ace muna kwance gado ɗaya batareda wani abu ya faru a tsakaninmu ba, Hafsat ya kikeso nayi ne wai ?"  dariya Hafsat ta saki irinta rainin hankali sannan ta gallawa wayar harara tamkar Asma'un na gabanta tace "af na manta fa da shugabar jarababbun matan duniya nake magana  Waike Asmy meye matsalark ne? Kullum namiji kullum namiji sekace masifa wai nikam ke wace irin jarabbiya ce don Allah ?  Ina Bashir ɗin naki yake da bazakije ya sauke miki matsalar taki ba?"

"hmm Hafsy kenan wllh yanzu sam Bashir baya iya satisfying ɗina nifa barin gaya miki abinda baki sani ba wllh Sulaiman shikaɗai ne ke iya gamsar dani  harnai tsahon kwana 2 ba tareda na buƙaci namiji ba, ke duk yanda zangaya miki baiwar da mijina yake da ita sam bazaki taɓa Fahimta ba Sulaiman namijin gaske ne irin namijn da ko wace mace ke burin samu a rayuwrta, ko kssing ɗina yakeyi ji nake cikin ƙanƙanin lokaci na jiƙe gaba saɓanin bashir dase An haɗa da karime-karime, nifa wllh na gaji dashi don kawai banaso na shuka masa rashin mutunci ne mu rabu in rasa me ɗebemin kewar dazan rage zafi" dariya Hafsat tayi cikeda shakiyanci tace "lallai Asmey bakida mutunci wllh kice Bashir ɗin lagwani ne da wando kawai" dariya suka fashe dashi gabaɗayansu sannan  hafsat tace" karki damu zan aiko miki da wata ƙwayar magani kibashi yasha wllh dazarar kun hau duty zakiji ya cikaki dam in taƙaita miki dai har har cikinki sekinji matsinsa hajiya, "kai Hafsat kice har ihu lagwanin ze sani kenan?" Asma'u ta faɗa cikeda jin daɗi sabida yanda zuciyarta ta bushe "sosai ma kuwa don wllh ke kanki sekinsan maza sun shigeki Hajiya don haka ki manta da wani sulaiman ki mori Rayuwarki da Bashir idan ma kina buƙatar canji sena haɗaki da wani kusha Harka"  dariya Sosai Asma"u tayi tace "rufa min asiri bashir ɗin ma ya isheni yanzu dai yaushe zaki aiko min da ƙwayar tunda wannan mutumin ya tafi Bauchi?" "yanzun nan zan turo miki me mashin ɗin danake bawa aike ya kawo miki" Hafsat ta faɗa tareda katse wayar tana murmushi.   Miƙewa Asma'u  tayi tareda barin abincin akan daining ta nufi bedroom ɗinta wanka ta sakeyi ta fito ta tsara wata shegiyar kwalliya me ɗaukar hankali, sannan ta buɗe drower ɗinta ta zaro wata ƴar iskar riga wadda iyakarta cinyarta gaban rigar kuma dashida babu duk abu daya ne, gabaɗaya alfarkatun dake jikin halittarta seda ta fito dasu waje  sannan ta ɗakko wani daddaɗan turarenta me suna Woman desire ta fesa, wayarta ce ta fara ƙara don haka ta maida hankalinta akai tana kallo ɗan yatsina fuskarta tayi sannan takai hannu ta ɗaga tareda karawa a kunneta, tun kafin tayi magana taji ance "Hajiya gani a ƙofar gida na iso" a taƙaice tace "ka ƙwanƙwasa ka bawa me gadi ze kawo min ngd" daga haka ta katse kiran tana kallon kanta a mudubi tana  ba jimawa taji ana ƙwanƙwasa ƙofar falo hakan yasa ta miƙe ta ɗauki Hijab tasa ta fito zuwa falon tarda buɗe ƙofar ta karɓa ta juya ba tareda ta damu da irin gaisuwar da yake mata ba,   direct frich ta nufa ta zaro fanta me shegen sanyi donta san Bashir mayen fanta ne  buɗewa tayi tareda sakin murmushi ta buɗe robar maganin dake cikin baƙar leda a ɗaure ta jefa guda ɗaya a ciki ta rufe,  ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "hmmm Bashir kenan sarkin kishi nasan dole yaji ba daɗi sabida tunda Sulaiman ya dawo ban sakebi takansa ba, ya zama wajibi a gareni inyi aikin rarrashi"  ɗaukar fantar tayi da ta ɗora akan flet tareda cup ɗin glass ta fice ta ƙofar baya yanda me gadin baze ganta ba ta nufi ɗakin Bashir, bisaga mamakinta ƙofar a bude take  tana shiga ƙamshin turarenta yaywa Bashir dake tsaye yana ƙoƙarin kunna fanka maraba gabaɗaya tsayawa yay yana kallonta tareda sakin igiyar fankar ta faɗi ƙasa,    ganin haka yasa ta fara takowa cikin yauƙi zuwa gabansa tareda tabbatarwa da kant cewar tarkonta ya kama kurciya. Ajiye fantar tayi tareda buɗewa ta zuba masa a cup ɗin ta miƙa masa tareda hure masa ƙananan idanunsa daya kafeta dasu, lumshewa yay da sauri tareda karɓar fantar yakai bakinsa ya fara kurɓa sosai yasha fantar ya rage kaɗan a gindin kofin sannan ta fara wani irin shafa masa jiki cikeda karuwanci, cikin ƙanƙanin lokacai ta gama birkita masa lissafi zuwa yanzu duk wani hijabi na kunya dake tattareda ɗiya mace Asma'u ta gama cire nata *_(dama Zuciyar data bushe a sanadin maida zina abar aikatawarta ai wajibi ne suyi hannun riga da kunyar dake tattareda Mutuncin ƴa mace)_*  a haka ta dinga sarrafashi yana biye mata harta kaisu ga afkawa cikin zinar da suka saba gadan-gadan, bakajin sautun komai sena Asma'u  wadda ke ƙoƙarin sumewa sabida taurarin da idanunta suke gane mata, tabbas ta yarda da maganar Hafsat ba kaɗan ba a wannan ranar haka Suka kasance da juna cikin yanayi na jin daɗi da gamsuwar da bata taɓaji a tareda bashir ɗin ba.

Sulaiman ya fita daga gida be dire ko ina ba se office ɗin Muktar dake Unguwan Rimi wanda ya kasance babban Amini a gareshi, kasancewar a ƙarƙashin Company ɗaya suke aiki hakan ya ƙara taimakawa wajen cigaban Amintarsu, da sallama ya shiga office ɗin tareda zama bisa ɗaya daga cikin kujerun dake gurin ya dafe kansa ba tareda ya kalli Muktar ɗin ba,  zuba masa idanu kawai muktar yayi yana kallon ikon Allah tabbas yasan akwai abinda ke damun aminin nasa sabida kasancewarsa bame yawan magana ba,  miƙewa muktar yayi ya ɗakko masa bottle water me shegen sanyi da cup ya ajiye masa aiko yana ajiyewa Sulaiman ya ɗaga goran ruwan ya kafa a bakinsa ya fara sha be sauke ba seda ya kusan shanyewa sannan ya ajiye goran yana sauke numfashi, dafa kafaɗunsa Muktar yayi yace "meke faruwa dakai ne Sulaiman dahar zaka fari ranka yay irin wannan ɓacin? Nasanka sosai irin sanin da ya wuce ayi musali dashi  don haka ka sanar dani meke damunka?"   muktar ya faɗi hakan yayinda yake ƙoƙarin zama a kujerar dake facing wadda sulaiman kekai, ɗan jim yayi kamar bazeyi magana ba sannan ya ɗago manyan fararen idanunsa da suka fara sauya launi ya shiga zaiyanewa Muktar dukkan abinda ke damunsa a gameda Asma'u. Tabbas "muktar nasan na mata laifi amma kuma meyasa zatai amfani da wannan damar ta gaiyatoma kanta ɓaƙin ɗabi'un da ba nata ba?, kasani inada kawaici sosai haka kuma abu ne mawuyaci mutum yaga fushi na amma yau seda Asma'u ta ƙure haƙuri na, wllh Muktar sena koya mata hankali tayanda nan gaba bazata sake gigin tamin irin shirman datamin ba."  wani dogon fasali Muktar yaja sannan ya ruƙo hannunsa yace "look Gamawa" dayake sunan dayake kiranshi dashi kenan yace" sam kada kace zaka ƙuntata mata ta hanyar zamantakewa ammafa ni anawa ganin meze haka ka hukunta ta ta hanyar dazata ladabtar da ita ba wadda kai kakeso kayi amfani da ita ba."  kallonsa Sulaiman yayi cikeda ƙosawa da zancen yace "ban fahimce ka ba malam kamin dalla-dalla" dariya muktar  yayi har seda fararen haƙoransa suka baiyana yace "ina nufin meze hana ka ƙara Aure!"  da sauri Sulaiman yace "Aure kuma ?"  "Ae tabbas Aure shi kaɗai ne mafita a cikin irin yanayin da kake ciki malam" zeyi magana kennan Muktar yace "kaga malam tashi mu kama hanya idan kai ka manta da doguwar tafiyar dake gabanmu ni ban manta ba kuma da motarka zamu tafi"  muktar ya faɗi hakan tareda jan hannunsa suka fice daga office ɗin tunda dama shi yake jira,, har suka shiga mota suka fara tafiya maganar muktar ce ke masa yawo a tunaninsa har suka isa Bauchi be gama tsaida matsaya akan maganar ba...........
        ******

*BAUCHI STATE*

Hannu Abban Adil ya daga zai kifa mata mari bayan ta kariso yana fad'in"Daga gidan uban wa kike..?" Da hanzari Fu'ad yayi saurin cafke hannun muryarsa na d'an rawa yace"Abban Adil ka natsu man ko baka ga shirin maka bayani nake ba sai gata ?"...asanyaye ya kwace hannunsa yace"to ina sauraronka." Fu'ad ya saci kallon Sumaiyya wacce ita ma d'in kallon nasa take zuciyarta na cike da tsoro da kuma fargaban abunda yake shirin gaya masa...
idanunsa sarke acikin nata yace"Tabbas wajen khadijan taje amma sai akayi rashin sa'a littafin baya hannunta, ashe yana hannun wata abokiyar karatun nasu kuma gidansu yarinyar akusa yake da makarantar, bashi da nisa shine taje." Yayi k'ok'arin kareta, Sumaiyya itace hadda sauke wani nannauyar ajiyar zuciya tana hamdala aranta..

"Ina littafin yake mu gansa.." Abban Adil ya fad'a yana mik'a mata hannu, Allah ya taimaketa dama dashi ta fita, sai kawai yaga tafidda hannu daga hijabi ta mik'a masa, bai karba ba ya sake sako mata wata tambayar"amma akan wani dalili ne yasa kika kashe wayarki ?, tsawon dakik'u goma ta kasa magana, can ta daure tace"dama akwai wanda ya takurani ne dazu ban san wanda ya bashi lambana ba shine na kashe wayar ganin ya dameni da k'ira." Ta karashe maganar tare da saddar da kai kasa ganin irin kallon da Fu'ad ke watsa mata, ajiyar Zuciya Abban Adil ya sake saukewa akaro na ba adadi kan ya dubi Fu'ad wanda yayi saurin kai kansa kasa gudun kar ya gano cewa k'arya ya sharara masa domin ya kare budurwan tasa...." to Mallam Fu'ad ni dai ba wai ban yadda da abunda ka gayamun bane, amma aganina tunda makarantar kaje dubo mana ita kuma aka taki sa'a ka samu labarin inda take, to kuma ai bai kamata ku dawo daban daban ba, tare yakamata aganku..."....Saurin katseshi yayi"Abban Adil karfa ka manta wayarta akashe yake balle mu samu damar communicating, sannan gidansu yarinyar da taje d'in ba sanin gidan nayi ba, Khadijar kuma muna gama magana hakuri ta bani tace inyi hakuri bazata iya mun rakiya gidan ba dan ta dora abinci awuta, hakan yasa kai tsaye na komo abuna don atinanina ma zan tarar ta rigani isowa."

Sosai so suke suyi wasa da hankalin Habib (Abban Adil) har dai sukayi nasarar gamsar dashi, ya shiga ciki domin basu wuri su d'an gana, bayan shigewarsa Fu'ad ya dubeta rai ahad'e yace"kin ga dai na miki halacci na kareki ko ?, to nima yanzu sai Kiyi k'ok'ari ki gayamun gaskiyar inda kika je." Babu yadda Fu'ad bai yi da ita ba amma fir taki gaya masa gaskiya sai kuka, haka suka rabu rai duk ba dad'i...

    *Washeqari..*

Kafin takwas d'in safiya tabar gidan, sai kusan sha daya suka fito daga lacca, tunda suka fito sai fad'a Khadija take ta mata akan tsai da gaskiya, tace"ban san meyasa kika musu karya cewa wurina zaki zo ba, sai dai bazan matsa miki don neman jin dalili ba tunda tun farko baki so mu sani ba shiyasa kikai rufa rufa, amma ina so in baki shawara karki kuskura ki bari rashin gaskiya yafi rinjayar gaskiyarki domin kuwa zai iya jawo miki cin Karo da munanan matsalolin rayuwa da kuma b'ata mu'amalarki da mutane, zai zamana ma ko nan gaba in kin gaya musu gaskiya akan wani abu bai zama lallai su yadda ba sabida tun farko kin b'ata rawarki da tsallenki, sannan kuma Sumaiyya ki rage zurfin ciki dan abunda yafi cutar dake kenan.."

Suna tafe ne take mata wannan jawabin, hostel suka nufa don hutawa kafin su shiga daukar darasi na gaba, asaman karamin gadon Khadija ta bararrake tana hutawa ayayin da ita kuma khadijar ta hau kiciniyar dafa musu dan abunda da zasu saka aciki.Sosai tayi nisa cikin tunani har bata san hawaye ya soma digar mata ba, sai ji tayi ana girgizata ana"Sumaiyya!ke Sumaiyya! wai me yake damunki ne ?", firgigit! ta dawo hayyacinta ta sauke kallonta akan Khadija tana maida ajiyar Zuciya, waskewa tayi ta kau dakai gefe tana fad'in"kamar me fa?, ni nace miki wani abun na damuna ne ?".."baki ce ba amma duk wanda ya dubeki sau daya kawai yasan kina cikin damuwa balle gaki har hawaye kike." Jin abunda ta fad'a yasa tayi saurin sa hannu tashafa fuskarsa ai kuwa taji ta tab'o ruwa, tabbas hawayen nan na damuwar dake gallazar zucinta ne.....Khadija ta katse mata tunani"haba Sumaiyya yanzu duk yadda muke ni dake bai ci ace kina gayamun damuwarki ba ?, ko kuwa baki yadda dani bane?" Bata san sa'adda ta fashe da kuka tana fad'in"Yaya muntasir shine damuwata ayanzu..." 

"Wanene kuma Yaya muntasir kuma meya afku tsakaninku da har yasa kika tsinci kanki cikin damuwa ?"...cike da mamaki tace"ya...ya...yaya muntasir kuma ?, meya kawo zancenshi anan kuma ?" Ta furta arud'e, tab'e baki Khadija tayi tace"Allah ya k'yauta, kici damuwarki ke daya tunda bakya son atayaki dashi" tana gama fadin hakan tabar wajen, wanka ta shiga domin watsa ruwa ayayin data bar Sumaiyyan da tsananin mamakin ta yadda akai har sunan Yaya muntasir ya subuto daga bakinta zuwa waje..

Wasa wasa fa damuwar yaya muntasir yabi ya addabi zuciyar Sumaiyya, ita sam bama ta tunanin Dr.Gana sai ta dan'uwan nata, ita kadai tasan abunda take ji ma tsoro hakan yasa tabi ta damu, yinin ranar duk bata da walwala, tun kafin atashi lacca ta sallami su Khadija ta futo, ta samu wani silent place ta zauna, tafi sama da minti ashirin zaune awajen kafin daga bisani ta saki wani wahalallen ajiyar zuciya ta ciro wayarta ajaka tayi 'yar latse latsenta ta kange wayar akunne...
Tun kan tayi magana taji saukan amon maganarsa"ina fatar ba kin kirani bane domin kice afasa kaiwa Sheikh sakonki ?" Cike da rud'u tace cikin rawar murya"wa..wani sak'o kenan kuma ?" Murmushin mugunta ya saki yace"Sakon da kika bayar aba Sheikh jiya a Villa hotel mana." Sai ayanzu ta gano abunda yake nufi hakan yasa ta fashe masa da kuka tana fad'in"dan girman Allah yaya ka tsaya ka saurareni, wallahi ban aikata abunda ranka ke raya maka ba, tsautsayi ne kawai yakai ni hotel d'in nan amma babu abun tirr d'in da ya gudana atsakanina dashi dan Allah ka yarda dani....."
"Sumaiyya kenan kibar raina wa kanki hankali dan babu abunda zaki gayamun in yarda dake, in ga abu da idona ai ko ban tab'a shiga aji ba nasan A yaneh? balle muma fa mun d'an tab'a bokon nan don haka babu abunda za'a nuna mana ko ab'oye mana, ke dai kawai ki yarda ya hayeki , ban ganku ido da ido ba amma na kamaku..."

"Yaya muntasir wallahi a'ah banyi ba...." ta furta tana kuka mai cin rai, yace"oh! Har yanzu musun kike ci ? toki cigaba, baki ma yi kukan koba har sai lokacin da zancen ya shiga kunnin Baba Sheikh asannan zaki san kiyamarki ta tashi....." ai tuni ta ida susuce wa jin ya ambato sunan mahaifin nasu, cikin fitar hayyaci take fad'in"Don girman Allah yaya ka rufan asiri wallahi duk abunda kakeso in maka matukar bai fi karfina ba zanyi maka shi muddin zaka bar k'yakk'yawar alakar dake tsakanina da Baba ya cigaba da wanzuwa atsakaninmu, fad'i me kakeso ?, nasan bukatarka bazata tab'a wuce ta kudi ba, gayamun nawa kake so ?" Dariya yayi yace"yanzu ke atunaninki kudade sune abin damuwar kowani mahaluk'i dake rayuwa acikin doron kasar nan ? to ni kudad'e ba sune abun damuwata ba domin bani da matsala dasu, ke kanki sheda ce na yadda ko kadan bana wasa da neman na kai, amma kefa ? magana kike akan abunda ba naki ba, abu ne wanda kikai dogaro akan wani, sai an baki sannan ki bani, idan baki gane ba to bari na warware miki filla filla, nauyin karatunki da kusan komai na rayuwarki Gwamna da dansa sun dauke miki, kai hatta damu kanmu danginki muna shan maik'onsu don albarkacinki, shine kike wani nuna mun takamar kudi abunda ba guminki ba ?, to bari kiji abunda yake _NAKI!_ _MALLAKINKI!_ wanda in kika mallakamin shi babu wanda zai zo daga baya ya goranta miki yace kinyi k'yauta da abunda ba naki ba, sannan ke kanki sai kifi samun kwanciyar hankali tunda abunda yake mallakinki ne kika bayar ak'yautar.."
Saurin taran numfashinsa yayi"yaya muntasir wallahi kwata kwata ni ban gane abunda kake nufi ba, nidai na fahimci cewar kudad'e ba sune matsalarka ba, amma sauran bayanan duk ban gane ba dan sun zo ne adunk'ule..." har ya bud'e baki zaiyi magana tayi azamar dakatar dashi"wallahi ana mun warning katina zai kare..." yace"kina ina yanzu ?" Asanyaye tace"cikin makaranta..." agogonsa ya duba yaga hudu saura, ajiyar zuciya ya sauke kan yace"ki jirani yanzu zan shigo makarantar in sameki, yau mukayi niyyar komawa Azare da ogana amma mun fasa tafiyar dan akwai wasu kayayyaki da muke saka ran shigowarsu ayau."....da "To saika iso." Ta amsa sannan ta katse, Sai juya maganganunsa take aranta, babu ma wanda yafi tsaya mata arai kamar dunkulallun kalamansa na k'arshe _*"abunda yake NAKI! MALLAKINKI! wanda in kika mallakamin shi babu wanda zai zo daga baya ya goranta miki yace kinyi k'yauta da abunda ba naki ba, sannan ke kanki sai kifi samun kwanciyar hankali tunda abunda yake mallakinki ne kika bayar ak'yautar.."*_

✍️H/C