Chapter 5
by @zmchubado
Babu b'ata lokaci sai gashi ya iso makarantar acikin motar uban gidan sa, Sumaiyya ta bud'e murfin motar ta antaya ciki, kanta akasa ta kasa had'a k'wayar ido dashi, shi kuma kallonta yake yana dan murmusawa, hannunsa akan guntun gemunsa yana ja kamar mutumin arzik'i..
"Sumaiyya ba tare da wani b'ata lokaci ba in har kina son in rufa maki asiri to ya zama lallai ki mallakamun kanki nima in kwashi rabona abunda nake..."...be kai ga k'arashe zancen nasa ba yaji saukan wani zazzafar mari, da 'yar yatsa take nunashi muryatta na mugun rawa"me...meyasa ?, meyasa hadda dan'uwana ?, meyasa hadda dan'uwana acikin masu son lalata rayuwata ?, meyasa hadda dan'uwana acikin jarabawar mutuncina ?.." kuka yaci mugun karfinta duk dahakan bata saduda ba ta cigaba da magana tana kukan"ya Allah tun jiya nake rokonka daka sassautamun ka canzamun kaddarata, kowanne ne zan runguma da hannu bibbiyu, koda kuwa kaddarata da Dr.Gana ne ya fiye mun wannan sau dubu malala gashin tunk'iya, ya Allah ka duba wannan dangantakar dake tsakanina da _*MUNTASIR..*_ ka tseratar da _*MUTUNCINA...*_
Tsawon lokaci suka dauka ba tare da yace da ita komai ba sai girgiza kai yake yana sakin munafikin murmushin dako za'a danneshi kasa asa mishi wuk'a awuya shi kansa bai san manufar wannan murmushin ba, can ya furzar da wani huci ya dubeta yace"to sai me inna hayeki kuma ina matsayin dan'uwanki ?, ciki daya muka fito ? Shin baki tab'a jin inda uba ya danne d'iyar cikinsa bane ?, to Sumaiyya kar wannan al'amarin ya baki mamak'i, ki saki jikinki bafa wani abu bane da kike neman kashe kanki akansa, rayuwa ce kawai ki bari kawai mu cita da tsinke, aljanna ta mai rabo ce, sai kigama shugaban tantirai ya zama mai gadin gidan aljanna, sannan kuma abun nan bada nufin cutar dake nake shirin yi ba, a'a sai don jindadinmu gaba daya da kema kanki ki samu natsuwar zuciya.."..."menene abun jindadin da kuma samun natsuwar acikin Zina ?, kana abu kamar ba daga tsatson malami ka fito ba, yaya Muntasir meyasa kake k'ok'arin biyewa son zuciya bayan ina da tabbacin zuciyar taka tana da sani akan Zunubi da kuma fitintinun dake tattare da abunda kake niyyar aikatawa ? "Sumaiyya! wai menene acikin wannan abun da zamuyi sau daya kawai fa ba wai mun dungayi kenan ba amma sai kumfar baki kike kina gayamun Allah, an gaya miki na mantashi ne ?, abun nan fa babu wanda zan bari ya ganmu munayi, haka kuma babu wanda zan gayawa wannan shine alk'awarin dana daukar miki in har tsoro kike ji." Sakin baki tayi tana kallonsa cike da mamak'in yadda zuciyarsa ta k'ekashe, wani irin mayataccen kallo yake jifarta dashi yana k'ok'arin tada motar yace"muje ko ? bazamu dad'e ba minti biyar kawai zanyi sannan in sauka kinji "yanzu yaya muntasir akan jindadin minti biyar kawai shine kake neman jefa mana kunci na zuciya na har abada ? akan jindadin minti biyar kacal kake neman jefamu cikin fitina, fushin ubangiji da kuma azabarsa ? Lallai sai ayanzu ne nake sake gasgata zancen da mutane ke yawan yi a inda suke cewa in kaga mutum kai dai ka barshi nan kawai don baka san zuciyarsa ba, ahakan dai kaga musa afuska amma fir'auna azuci , malam zuciyarka babu Allah aciki, amace take, ka bud'e kunnuwanka dak'yau ka saurareni Ni Sumaiyya bazan bari ka samu abunda kakeso daga gareni ba, wai kai daya kamata ace amatsayinka na dan'uwana zaka tayani tattalin mutuncina amma abun mamak'i wai kai da kanka ne kake k'ok'arin ganin ka zubar mun dashi, yaya muntasir Allah ya dawo dakai kan hanya amma wallahi na gwammace kaje ka tonamun asirin da in baka kaina, Allah zai tsayamun don shi kadai ne yasan gaskiya kuma shine shaidata "
Ta fara kiciniyar bud'e kofa "Sumaiyya kalli nan ki ga, wallahi in har bakiyi na'am da bukatata ba nayi alk'awarin baiyyana wannan vidiyo d'in kowa da kowa ya gani." Afirgice ta waigo tana kallon wayar dake hannunsa, kuri tayi wa allon wayar k'irjinta na bugawa fiye da misali, da rawar murya takai hannu zata warce wayar tana fad'in"ina...ina ka samu wannan vidiyon ? na shiga uku yaya muntasir mena maka da zafi ne da kake neman ganin bayana ?" Da sauri ya janye hannunsa yana b'oye wayar, sai dariyar mugunta yakeyi yace"kinyi mamak'i ko ?, to kadan kenan daga cikin makircin Muntasir in har ya kudirta abu aransa sai ya tabbata ya cimma burinsa, yanzu muje d'in ko kuwa har yanzu kina akan bakanki ne ? " yaya muntasir wallahi kaji tsoron Allah, ka tuna zaka mutu watarana kuma zaka je ka sameshi.." kuka yaci mugun karfinta, bai saurareta ba ya figi motar aguje kiris ya rage ya buge wasu mutane..
****
Har suka isa Bauchi babu wanda ya sakeɗaga maganar sabida rashin lokaci ko kaɗan basu samu sun zauna ba har seda suka kammala abinda yakaisu sannan suka nufi masaukinsu a matiƙar gajiye, Sallah isha kawai Sulaiman ya iyayi sannan yay shafa'i da wutiri ya jima akan sallayar yana roƙon Allah mafita akan dukkan lamuransa sannan ya miƙe ya kwanta a saman doguwan kujerar dake ɗakin, murmushi kawai Muktar yayi tareda miƙewa shima daga saman sallayar ya kalleshi yace "Gamawa yadai naga duk kayi laushi ne I thought zamuyi magana ne akan batun da muka fara kafin mubar kaduna amma kuma da alama kamar bazan samu hankalinka yanda ya kamata ba" Shiru Sulaiman yayi tareda ɗan yamutsa fuskarsa sannan buɗe gajiyayyun idanunsa masu launin kalar brown yana kallon Muktar wanda shima ɗin kallonsa yake yace " Muktar let talk tomorrow pls wllh har banson tuna maganar nan nifa daka ganni na tsani yawan magana akan abu gudaɗaya, abu gudaɗaya kawai na sani zanci gaba da zuba mata ido tayi duk abinda taka dama zancigaba da haƙuri har zuwa lokacin da komai zeyi dedai Muktar!! "anya Gamawa kana ganin hakan shine mafita taya zakaci gaba da zama a haka sekace ba lafiyayyen namiji ba? Kaga malam wajibi ne ka ƙara Aure koda kaucewa fitinar datake tinkaroka, bawai ina nufin ka tilastawa kanka bane Gamawa amma at least kaima zaka samawa kanka mafita da kwanciyar hankali, taya za'ai namiji kamarka ya iya jurar rashin kusantar mace har tsahon watanni goma? Na tabbata hakan akwai cutarwa sosai ba kaɗan ba, dama ace tun farko baka da matar ne se'ace bakasan alfarmar dake cikin kusantar bane shiyasa to kariga ta taɓa ɗanɗanawa kanka alfarmar dake ciki shin ta yaya zaka iya jurar hakan?"
"Na sani Muktar amma ta ya zan iya ajiye mata biyu bayan banida Ra'ayi akan hakan? Mace ɗayan ma kana ganin irin zafin kan datake haɗamin inaga na haɗawa kaina mata biyu? Bama wannan ba mu'ajiye maganar fitintinun mata a gefe wani tabbaci nake dashi akan matan wannan zamani Muktar?"
"Haba Gamawa don Allah ka dena tsanantawa ai a maganar Aure ba tabbaci kake buƙataba addu'a ya kamata kayi ubangiji ya baka mata taƙwarai na tabbata Allah zeji kokenka Sulaiman, ba lallai na iya gamsar dakai da tarin hujjoji ta fannin addini ba tunda nasan kanada sani dedai gwargwado kaidai kawai ka kyautata niyarka Allah ze baka mafita ta hanyar ƙara Auren." Muktar ya faɗi hakan yayinda yake dafa kafaɗar Abokin nasa dake kwance idanunsa a lumshe. Shiru ne ya ratsa gurin na kimanin daƙiƙu biyar ba tareda Sulaiman ya sake magana ba har muktar ɗin ya miƙe ze koma nasa masaukin ya tsinkayi tattausar muryar Sulaiman wadda ke ɗauke da wani irin amo a cikinta yace " dukda cewar bansan ta ina zan fara neman Auren ba amma tabbas Gamawa yayi appreciating shawarar da Muktar Ibrahim Bakori ya bashi" dukansu murmushi sukayi sannan Muktar ya ɗaga masa hannu ya fice daga ɗakin.
Washe gari ma hakance ta kasance garesu se yamma liƙis sannan suka koma masaukinsu bayan doguwar tattaunawa da sukai da shugaban Companyn dake jagorantar branch ɗinsu dake cikin garin Bauchi wannan dalilin yasa sukaci lokaci sosai, babban abin birgewar kuma shine bayan wannan har taron na musamman aka haɗawa Sulaiman don karramawa bisa jajircewar dayayi sakamakon aiki tuƙuru bisa Gaskiya da kuma amanarsa, don haka yau gabaɗaya seya samu kansa da tarin farin ciki mara misali har hakan ya gaza ɓoyuwa a taredashi sabida yanda yake walwala sosai hakan yayiwa amininsa Muktar daɗi a ransa, zan iya cewa yauma a gajiye suka dawo sedai saɓanin yau gajiyar batakai ta jiyan ba ajiyr Zuciya Sulaiman ya ski sannan ya dubi Muktar yace "don Allah idan babu damuwa inaso da safe ɗan mutan Bakori yaymin rakiya Zuwa Azare ingaida Wani malami na" sulaiman Ya faɗi hakan tareda faɗaɗa murmushinsa wanda ya ƙara baiyana cikakkiyar Haibarsa. Ba tareda damuwaba muktar yace "Na amince maka indai wannan ne dukda ban sani ba nasan ziyarar me mahimmanci ce gareka, ina fatan Allah ya nuna mana goben lfy" muktar ya faɗi hakan yayinda yake ƙoƙarin maida hankalinsa ga wayar dake hannunsa sabida ganin kiran Matarsa Zainab, miƙewa yayi aɗan hanzarce ya kalli Sulaiman yana murmushi yace "madam is calling inaga lokacin tafiyata nawa ɗakin yayi" be sake cewa komai ba yay waje abinsa shi kuma Sulaiman ya raka bayansa da murmushi a ransa yana girmama ƙarfin Soyayya da shaƙuwar dake tsakanin Zainab da Muktar, lallai samun cikakkiyar kulawa daga macen Aure zuwaga mijinta babban dace ne .
Washe gari tunda sanyin Safiya Sulaiman ya shirya cikin wata dakakkiyar Gizna me launin kalar Sky blue an zuba mata ɗinkin haɗaɗɗiyar jampa kansa sanye yake da haɗaɗɗiyar hula zanna bukar irinta Asalin yankin medugurawa wadda keta baza uban ƙyali, kallo ɗaya zakai masa ka nazarci irin baiwar kyan da Allah mekowa me komai ya wadatashi dashi, sosai hasken fatarsa ya baiyana ƙarara hakama duhun gashin kansa daya kwanta luf'luf har zuwa dokin wuyansa bakajin tashin komai sena daddaɗan ƙamshin turaransa me ladabtar da zuciyar wanda ya shaƙa, yana ƙoƙarin gyara zaman haɗaɗɗen Agogon fatar da aka sarrafa da tsadaddiyar fatar damusa a hannunsa muktar ya shigo cikin shirinsa shima. Tsayawa yay yana kallonsa yace "masha Allah kayi kyau kamar wani sabon saurayi nanko cikakken tuzuru ne dakansa" dariya sukayi gabaɗayansu sannan suka ɗauki Haramar tafiya kasancewarsu maza yasa cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala haɗa komai nasu sannan suka kama hanyar Azare, kafin su shiga garin Muktar ya tsaya a wani katafaren shagon siyarda kayan Abinci sakamakon umarnin tsayawar da Sulaiman ɗin ya bayar, don yayiwa malam malamin nasa siyayya, siyayya taban mamaki yayi har seda abin ya bawa Muktar tsoro, a haka aka kwashe kayan aka zubasu a booth ɗin motar har seda motar ta ɗanyi ƙasa sabida nauyin kayan sannan sukaci gaba da tafiya jefi jefi sukan ɗan taɓa hira.
Wannan karan Sulaiman ne kejan motar sabida shiyasan inda zasu don haka cikin nutsuwa yake jan motar bada garaje ba har suka iso cikin garin Azaren, yayi mamaki ƙwarai sakamakon canjin dayaga ansamu a garin dukda cewar ya daɗe be kawowa malamin nasa ziyara ba, a bakin babban ƙofar gidan yay parking sannan suka fito gidane babba me fasalin gini irina masu kuɗin da unguwace me ɗan kyau da tsari sam babu ƙazanta a aria kokaɗan , a nitse Sulaiman ya fara takawa muktar na biye dashi har suka shiga babban get ɗin gidan sannan suka ɗauki hanyar babban falon da ƙofarsa ke kallon get ɗin, wata matashiyar Budurwa ce ta fito cikin hanzari batareda kula ba ta bangaji jikin Sulaiman dake tahowa Muktar na take masa baya, ja tayi ta sauri baya tana kallonsa lokaci guda kuma ta washe masa baki tace "don Allah yihaƙuri wllh sauri nake shiyasa ban lurada kai ba" kobi takanta beyi ba yay gaba abinsa a ransa yana girmama rawar kanta, a bakin ƙofar falon ya tsaya tareda zare baƙin takalmin fatar dake ƙafarsa ya Shiga falon yana faɗin "Assalamu'alaikum!
Gabaɗaya falon dagowa sukai suna masu amsa sallamar ciki kuwa harda shaike wanda ke zaune manyan magidantan samarin sun zagayeshi da alama karatu zasu fara dubada babban littafin Riyadussalihin dake ajiye a gabansa, fara'arsa baba shaik ya faɗaɗa tareda faɗin "Maraba lalle da ɗalibi me ƙwazo da karamci barka da Zuwa Sulaimanu" sosai sulaiman yaji daɗin yanda Baba shaik ya karɓeshi don haka suka ƙarasa shigowa da ƙwarinsu ɗaliban dake gabansa ya kalla yace "yau dai kam iya na wannan lokacin bazamuyi karatu ba don haka kuje abinku se zuwa dare idan Allah ya nufa" godiya sukai masa sannan suka mike suka fice daga falon Cikin gimamawa. Bayan sun zauna Sheik ya dubesu cikeda farin cikin ganinsu yace "Maraba lale Sulaiman barkanku da zuwa bari in shiga gida a kwo muku abinda zaku taɓa" ya faɗa tareda miƙewa ya nufi wata ƙaramar ƙofa dake cikin falon cikin hanzari, a ƙofar ɗakin Hajiya Maryam ya tsaya tareda buɗe labulan ƙaramin falon da sallama sedai babu kowa a falon hakan yasa ya nufi ɗakin Maman Sumaiyya yana shiga ya sameta a zaune a falon tana linke kayan Emran Autan taya dubeta da fara'a sosai a saman fuskarsa yace "Maman Shalele don Allah fura nakeso yanzu a dama a kawo min Rumfar karatu don Allah kar'a ɓata lokaci" murmushi tayi tace "malam nasanka da karamci wa bakinka amma yau dai kam naga fara'ar dake saman fuskarka tayi daban data sauran, meze hana ka bani labari?" ɗan jim yayi kaɗan sannan yay murmushi yace "ɗalibina danafi ji dashi ne ya ziyarce ni nasan ba lallai ki iya tunashi ba tunda be taɓa shigowa cikin gida ba, kedai hanzarta ki dama ki bayar a kawo yanzu" "malam babu yara fa a gidan duk sun tafi makaranta Sedai ko in baiwa Beebah ta kawo." ta faɗi hakan yayinda take kallonsa
Shiru ya ɗanyi kaɗan kamar bazeyi magana ba se kuma yace "to kibata ta kawo amma ki tabbatar kin mata kashedi akan rawar kanta da ace na samu Mamanta Ɗakinta danace ita ta dama ta bayar a kawo min" ya faɗi hakan tareda juyawa yabar ɗakin zuciyar sa nayi masa wani irin daɗi
Bayan Fitar Sheikh Hajiya Badi'atou maman Sumaiyya ta miƙe taƙe ta nufi Frich ɗinta ta buɗe tareda ɗaukar ƙaramin bokitin Fresh nono wanda ya fara ƙanƙa takai khitchine sannan ta dawo ta ɗauki fura da ayaba ta wuce khitchine dashi, blander ta jona kasancewar sunada wuta ta ɓare ayabar ta saka kuda ɗaya bayan ta bare tayi blanding sannan ta zuba nonon akai shima tayi balandin, furar ta ɗauka wadda ke zuɓa Ƙamshin gero dana kayan ƙamshi ta jefa a ciki tayi blanding ɗinshi sama-sama ta yanda bazeyi laushi sosai ba, wani haɗaɗɗen jug ta ɗakko meɗan girma ta juye a ciki sannan ta koma ɗakinta ta ɗakko wani ƙaramin bokiti wanda ke ɗauke da alkaki a cikinsa ta ɗakko wani babban akushi ta juye alkakin a ciki wanda yasha suger sosai ta rufe, tsakar gida ta fito bataji motsin kowa ba don haka ta nufi ɗakin hajia maryam kai tsaye wadda ta kasance uwar gidan sheikh wato mamansu Yaya Basirah da Muntasir, da sallama ta shiga falon Beebah ta samu a zaune tana buga Game a wayarta washe baki tayi tace "lah maman shalele ai tun ɗazun naje falo nku na baki labari yau baƙi Baba shaik yayi kinga haɗuwarsu kuwa? Koda yake gaskia ɗayan yafi kyau ammafa dana fito daga Rumfar Baba sheikh har bangajesa nayi bansani ba, shine da sauri na bashi haƙuri dan yace yana sona" ta faɗi hakan cikeda wauta tana wani langaɓar dakai, itadai Maman Shalele kasa magana tayi illa kawai tace "kije ki ɗauki fura a ɗakina ki kaiwa baƙin malam nidai don Allah banda shirmen nan naki idan kinje kuma banda shirita don Allah kikai musu kawai ki fit... "ban gane banda shirita ba waime kika ɗauketa ne Badi'atou? To wllh ki iya bakinki dan cikina be haifi shiriritacciyar ƴa ba don haka ki nemi Shiriritacciya a can jami'ar da kuka turata, amma karki sake ƙoƙarin zagin ƴata!" ta faɗi hakan cikeda bala'i. Murmushi kawai maman Shalele tayi batace komai b ta juya zuwa ɗakinta zuciyarta na mata zafi, seda aka jima sannan Beebah tazo ta ɗauki sassanyar furar ta Nufi Rumfar shaik da ita sannan ta dawo ta ɗauki akushin alkakin shima takai se kallon Sulaiman take babu Ko ƙiftawa tana murmushi kamar zata cinyeshi, har seda shake yace ta ajiye ta tafi sannan ta mƙe ta fita tana waiwayensa duk abinda take Muktar na lura da ita a ransa kuwa dariya yakeson yi amma kuma kunyar shaik da nauyinsa suka hanashi yin hakan, sosai sukasha furar suna zuba santi hakama alkakin nan dai suka shiga hirar yaushe gamo da shaik sun dan jima sosai sannan sukai masa sallama Sulaiman ya ajiye masa 100k tareda sa yara su sauke kayan abincin daga bayan mota, da fari ƙin karɓar kuɗin yayi seda Sulaiman yay da gaske sannan shaik ya karɓa yana me sanya masa Albarka, basu sukabar Bauchi ba se ƙarfe 1:00pm rana.
Bayan sun tafi yasa aka shiga da kayan abincin gida Beebah na ganin haka ta fito da hanzari ta samu Baba sheik zaune a falonsa, washe baki tayi tace "Baba wannan waye? Nidai koma dai wayeshi ban damu ba dama ze amince ai daka bashi Aurena." kallonta yay da idanunsa waƴanda ke ɗauke da sirrin kwarjini a cikinsu sannan yace "ada inai miki kallon shashasha Habiba Ashema shirmanki ya wuce haka, ke ana girma ana ƙara hankali amma kuma ke rashin kunyarki da wautarki gaba suke ƙarayi ubangiji ya shiryeki" fashewa tayi da kuka harda hawaye tana buga ƙafa tace "uhmm to nidai ina sonsa Baba shei....... Carbin hannunsa ya kai mata jikinta da sauri ta miƙe tabar falon tana matsar ƙwalla don wllh ita harga Allah taga mijin Aure. Wannan shi ake kira so daga ganin farko...........
****
Da yammaci misalin biyar saura sai ga wani almajirin Baba Sheik ya sameshi arumfar karatunsa yace"malam ga daliban Sharifiya sun iso fa suna jiranka azaure." Da sauri ya mik'e yana gyara tabarau d'insa nasu na masu ciwon ido yace yana mai washe hakora"to to to to!! madallah ace musu ina zuwa." Almajirin ya amsa da "toh' sannan ya fice, shi kuma Sheikh ya shiga cikin gida ya karbo kwalin biscuit biyu da kuma madaidaicin bokiti shake da nono mai shegen kauri da sanyi, sai kofuna jere awani faranti, wasu manya manyan almajiransa ne suka tayashi kwasowa shi kuma ya mara musu abaya, tun kan ya kariso yake fadin"ikon Allah! yanzu duk wannan tawagar na Sumaiyya ne ?" Sosai jikinsa yayi sanyi shine hadda zubar da kwalla, ahankali ya furta"Sumaiyya mai jama'a kenan, Alherin Allah, rahamarsa da kuma albarkansa ya cimmiki duk inda kike." Yara ne yan kucukucu sai kuma 'yan manyansu wa'enda bazasu dara shekaru tara tara zuwa goma goma ba, daliban Sumaiyya kenan a islamiyyar da take zuwa, suna matuk'ar kaunarta hakan yasa duk wani juma'a sai sun ziyarceta da yammaci don samun ladan ziyara na wannan rana mai albarka, basa fashi sai ko rashin lafiya ko wani kwakkwaran uzurin nadaban, ita kuma takan tanadar musu wani abun sadaka haka dai, kuma basa rufe taro sai da add'ua, haka zasu kwararo mata addu'o'i sosai tare da zuri'arta kafin su tafi, koda ta tafi makaranta yawancinsu basu yanke wannan k'yakk'yawar dabi'ar ba, sukan kawowa Sheik gaisuwar amadadinta, shi kuma sai ya tayata karba, awasu lokutan ma har kiranta yake awaya yace tofa ga tawagarta sun iso, haka zai saka wayar a handsfree suna sauraron gaisuwar da take mik'o musu, sannan suma su bita da add'ua, akarshe sheikh ya rarraba musu kayan ciye ciye kan su kara gaba cikin farin ciki, wannan k'yakk'yawar alakar ta zumuncin an dauki kusan shekaru biyar kenan ana yinta kuma har iyau bata mutu ba sai kara karfafa take, ayau dinma kusan sunfi na kullum yawa hakan yasa Sheik zubda hawaye...suna kiranta *SHARIFIYA*
Awannan ranar sun zuba wa Sumaiyya addu'oi kamar babu gobe wanda basu tab'a yin irinsa ba musamman da Sheikh ke sanar dasu cewa suna gab da fara jarabawarsu ta karshe kuma daga shi ta kare kenan, hakan yasa suka bita du'ai sai dai basu jidadi da rashin samunta ayau da ba'ayi ba awaya, adaidai wannan lokacin ita kuma Sumaiyya suna dakin wani abokin Muntasir suna gwabzawa...
Bayan kamar minti ashirin da shigarsu sai ga Sumaiyya ta banko kofar ta fito waje tana haki, gidan wani sururu ne sai ka rantse ma babu kowa aciki, da dan sauri sauri take cokale kafa tana nanata kalmar Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, har ta kusa da kofar fita gidan taji daga bayanta ance"Sumaiyya ki sani wallahi sai an buga sabon kafce! Koda ni Muntasir zanyi yawo tsirara acikin duniyan nan ne saina tabbata na lalata miki rayuwa ta yadda nan gaba bazaki moru ba ko agidan aurenki!." Wani makirin murmushi ya saki kan ya sake cewa"in ma na bari kin samu mijin auren kenan, wallahi kin aro match amma baki da players Sumaiyya Mukhtar Azare" ya ida magana yana nishi daqyar, hannunsa daya rik'e da kai inda jini ke tsiyaya duk ya bata masa fuska, kwayar ido kawai kake gani, tana kallo yayi latse latsenshi da karamin wayarsa ya kara akunne"hello Lukman zoka kaini asibiti" kit ya katse yana kallonta alokacin tana rike da hannun kofa tace"Muntasir na tsaneka!na tsani duk wanda ya sanka! na tsani duk wanda ya had'a wani alak'a dakai! haka kuma na tsani duk wanda ya nuna tausayi akanka! insha Allahu cin zarafin da kamun sai an ramamun akan *HABIBA* da kuma d'iyoyinka! daga rana irinta yau duk goshin dazan kai kasa, zan dunga roka maka masifa da bala'i ne arayuwarka, Muntasir insha Allahu awulaqance zaka kare ta yadda ko gawarka baza tayi dad'in gani ba..." SUMAIYYA wallahi kika bari na rikeki saina ci ubanki!" Ya zabura, aguje ta fice daga gidan, tana fita adaidai wani mai adaidaita na giftawa ta layin, da sauri ta fada ciki numfashinta na zuwa sama sama, ganin kamar babu lafiya atattare da ita yasa mai adaidaitan jan babur din aguje, sai da suka danyi nisa sun fita daga layin sun hau kan titi sai asannan ya waigo yana k'ok'arin tambayarta inda zai kaita kuma da abunda yake faruwa ya ganta ahargitse ? haba sai ganinta yayi zub'e akan Sit bata numfashi, jini sai diga yake daga kafarta zuwa kasa, wani irin gigitacciyar kara ya fasa.........
H/C✍️