Chapter 6
by @zmchubado
Gangarawa gefen titi yayi ya paka, ya sakko cike da tashin hankali yana fad'in"Baiwar Allah! Baiwar Allah! dan girman Allah ki rufamun asirin karki mutu mun acikin mashin ki jefani cikin matsala.."...ruwan faro d'in dake gaban mashin d'in nasa ya dakko ya balle murfinta, sannan ya daga goran ya fara tuttula mata ruwan afuska, wani irin dogon numfashi taja kana ta soma d'an bud'e idanu kadan kadan, can ta saki atishawa nan idanuwan nata suka ida washewa ta saukesu fes akan mai adaidaitan dake hamdala aransa, afirgice ta zabura daga kwancen da take ta matsa can k'arshen sit ta kankame jiki tana fad'in"karka tab'ani wallahi na tsani jinsinku! baku da tausayi! baku da imani! baku dauki d'iya mace abakin komai ba face dabba wacce bata da daraja, na tabbata kaima fyad'en kake son yimin! kaima so kake ka zubar da mutuncin da nake tunanin ya sauranmun, so kuke in wulakanta kuma in tozarta a idon duniya amma ku sani Allah na kallo shi zai sakamun, kuma insha Allahu ni SUMAIYYA sai nayi k'ok'arin cinye _*JARABAWAR MUTUNCINA..*_ "
Sosai jikinsa yayi lakwas da jin furucinta, idanunsa ya sauka akan kafarta dake tsiyayar da jini, aransa yace"Innalillahi wa'inna ilaihi raj'iun kenan hakan na nufin fyad'e akai mata kenan ? " shiyasa nace waya sani ko kaima shi d'in zaka mun ?, bani hanya ni in wuce.." ta furta tana jifansa da harara, kunyace ta kamashi sosai ganin maganar tasa ashe ta fito fili, da sauri ya kauce ta fito tana d'an dingisawa, garin yayi bakikirin wanda kiris kawai ya rage ruwa ya ballo, mutane da ababen hawa kowa sai sauri yake ya isa mafakarsa kafin ruwan ya sakko, tuni hankalin Sumaiyya ya sake dagawa ta fashe da kuka tana fad'in"ya Allah wannan wani irin jarabawa ne haka ? "Malama ki shigo in kaiki inda zaki kafin ruwan ya sauko, Allah ya saka miki da abunda aka miki amma ki sani ni bana daya daga cikin irin suffofin mazajen da kika zayyano, ki sani ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai masu tsoron Allah amma basu da yawa acikin duniyar nan, kiyi hakuri kizo in kaiki Allah ne kawai zai bi miki hakkinki"...ko kadan kalamansa basu tab'a zuciyarta ba illa kara jin tsanar maza da taji ya ninku aranta, dogon tsaki taja tayi gaba abinta, ko kadan baya son ya matsa mata amma sai yaji aransa kawai yana son shiga rayuwarta don yaga ko akwai wani irin taimakon da zai iya yi mata, hakan yasa ya fad'a cikin mashin d'insa ya koma da baya..
Bayan bacewarsa ne hankalinta ya dawo jikinta, cike da sabon tashin hankali tace"Innalillahi jakata da wayata!" Hannu tasa ta toshe bakinta data tuna cewar ai adakin abokin Muntasir d'in ne ta manto da jakar, da wayar, kai da wasu muhimman abubuwanta acikin jakar..
****
Tafiyar Sumaiyya ba jimawa sai ga Lukman ya shigo gidan hankalinsa ba karamin tashiwa yayi ba ganin halin da Muntasir yake ciki, Muntasir wanda ya gaji da jiransa yana ganinsa yace"kai fa banza ne sai dana kusa mutuwa ne zaka bayyana ? " yi hakuri malam goslow ne ya tsai dani, baaba meya faru dakai ne haka ?, kutmelesi kaga yadda kake zubar da jini kuwa ?, ina fatar dai ba Sumaiyyar bace ta maka wannan aika aikar ?, " malam karka cikani da surutu muje ka kaini ko clinic ne awanke mun, sauran bayanan kuma zaka ji komai daga baya..." Lukman yace" Sai dai fa mai d'in babur d'ina ya kare, muje dai mu nemi abun hawa tunda kace tayar motar da kuka zo a ita tayi faci, Allah dai yasa mu samu abun hawan don ga iska nan ya taso..." suna fitowa adede lokacin mai adaidaitan nan wanda ya dauki Sumaiyya afarko shima yana isowa, akallon farko da yayi wa Muntasir sai da gabansa yayi mummunar faduwa, kuma ganinsu da yayi sun fito daga cikin gidan da Sumaiyyar itama ta fito ahargitse ya sakashi datsa ayar tambaya akansu "yauwa ga wata adaidaita nan.." inji Lukman, shine yasa hannu ya tsai dashi, da sauri suka fad'a ciki duk jini ya gama b'ata farar rigar dake jikin shi Muntasir d'in.
"Malam teaching hospital zaka kaimu, ina fatar da kudi awajenka ko ?" Lukman yayi tambaya yanakallon Muntasir "kai malam ja muje." acewar Muntasir sannan ya waigo zuwa ga Lukman d'in yana fad'in"ko nawa ne zan iya kashewa wajen ganin na samu lafiya amma inaso ka rubuta ka ajje sai na fanshi abunda yafi kudin dazan batar ajikin Sumaiyya, nayi alk'awarin lalata rayuwarta adalilin wannan raunin data ji mun.." Subhanallahi! Amma baaba ka kwafsa fa, taya kana namiji tsayayye kakkarfa sannan ka bari wata tatsitsiyar 'yar kilaki taji maka rauni ?, wannan ma ai abun kunya ne, amma ina fatar dai kaci nasarar dagargazar k'asar 'yar iskar dai ko ?" Wani banzan kallo ya watsa masa yana fad'in"kaima kasan wannan dole ne, infact a aikace yake kawai, sabida duk wani abunda Muntasir ya sanya gaba sai yayi k'ok'arin cimma nasara akai, nine d'a namiji na farko kuma jarumin da yayi nasarar kau da budurcin _SUMAIYYA!_ jarumin da yayi facakali da mutuncin KANWARSA, kuma ina fata Allah yasa rabo ya ratsa domin kuwa so nake in rabata da duk wani jindadi da kwanciyar hankali anan duniyar! saina tabbata ta zamo abun gudu da kuma k'yama acikin al'ummah " murmushin mugunta ya saki kan ya cigaba"Lukman in kunga Sumaiyya ta huta to MUTUWA ne tayi!"
Jikin Lukman ne ya koma yayi sanyi sosai dan bai tab'a tunanin muguntar abokin nasa yayi nisan hakan ba, saukar da ajiyar zuciya yayi yace"amma ni aganina ban ga laifin da tayi maka da har ta cancanci irin wannan hukunci daga gareka ba! har fata kake ta samu rabo dakai, kai ko kunyar wannan magana ma baka ji ?, to in aka gano cewa kaine ka mata cikin fa ? " lukman kenan har iyau baka san wanene _MUNTASIR MUKHTAR AZARE_ ba, kai dai inda ranka zaka sha kallo, yanzu Allah Allah nake ma mu karasa ayi mun dressing ciwon nan sannan inje in fara had'a mata gadar zare na farko kafin saura su biyo baya, ina fatar kana tare dani acikin wannan tafiyar domin kana da kasonka aciki ? " babu yadda ya iya illa bashi hannu suka kulla amana, kwata kwata ma sun manta cewar acikin adaidaita suke wannan hirar...
*****
Tun bayan tafiyar Sulaiman sosai hankalin Baba shaik ya karkata akan maganar da Beebah ta kalli
idansa ta faɗa gameda Sulaiman sosai maganar tai mugun tsaya masa a rai, tabbas shima zeso hakan takasance sabida Sulaiman mutumin kirkine da tarbiyarsa takai kowani Uba yay fatan haɗa zuri'a dashi, sedai dama ace watace daga cikin ƴaƴansa ta faɗi hakan ba Habibah ba da babu shakka ze tsaya mata wajen samun cikat burin ta na Aura matashi yana matiƙar jin tsoron wawtar Habiba sabida ba wani cikakken Hankali gareta ba musamman a wajen furta magana da kuma yanayin rayuwa na yau da gobe, ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske har seda yaja Hankalin Maman Shalele Dake kwance a gefansa zuwa gareshi kasancewar itace da girki, tashi tayi ta zauna tareda tokare bayanta da filon datai matashi dashi ta dubeshi cikeda damuwa tace "Baban shalele lfy kuwa? Na lura dakai a ƴan kwanakin nan tamkar akwai wani abu dake damunka, na damu sosai a sanadin sauyin danake gani a tareda kai wllh ina roƙon Allah yasa ba wani babban al'amari bane". Shiru Yay mata batareda yayi yunƙurin magana ba har tsahon daƙiƙu biyar sannan ya maida kallonsa gareta cikin yanayi na na damuwa yace "ni kaina bansan meyake damuna ba a ƴan kwanakin nan amma inajina jikina cewar kamar akwai wani abu mara daɗi dayake shirin tunkaroni!"
"subahanallahi haba malam meyasa kake faɗar haka kadafa ka manta cewar Annabin Rahama ya horemu akan kyautatawa kanmu zato daga ƙofofin ubangiji" "na sani Badi'atou babu shakka gaskiya kika faɗa, wannan dalilin ne yasa nake roƙon Allah ya bani ikon ɗaukar dukkan abinda ze tunkaroni mekyau ko akasin haka, wllh inajiwa kaina tsoron ranar da imani na zeyi rauni akan duk wata ƙaddara dazata sameni Badi'atou" "malam donnAllah ka kwantar da hankalinka insha Allah babu abinda ze tunkaroka se alkhairi" a haka taita kwantar masa da hankali da tausasan kalamanta harya ɗan samu nutsuwa haka kawai yakejin gabansa na yawan faɗuwa wanda shi kansa besan dalilin faruwar hakan ba, Addu'a kawai yake tsanantawa akan lamarin dukda besan menene ba.
****
"tsaki sulaiman ya saki tareda kallon muktar dake driving yace "kashhh wllh naso ace na tunada wuri aida ka rakani gidan wani uncle ɗina a cikim garin Bauchi nan" wani kallo Muktar ya masa tareda maida hankalinsa kan tuƙin dayake yace "taɓ amma kaidai kam Allah ya shiryeka wllh anya Uncle ɗin gaske ne kuwa?" murmushi yayi yace "na gaske ne mana kawai dai ban cika shiri da matanshi bane shiyasa ban damu da zuwa inda yake ba, kuma wllh matarsa itace sila sam batason wani ya raɓeshi se ita da ƴaƴanta da danginta" girgiza kai kawai muktar yayi yace" hmmm wani aikin se mata" a haka sukaci gaba da tafiya suna ɗan taɓa hira har suka iso Kaduna, seda sukaje gidan Muktar dake Unguwan Rimi sannan sulaiman ya karɓi motar ya wuce gida.
*KADUNA STATE*
(Malali Umaru Muhammed Road)
A nitse ya faka motar cikin yanayinsa wanda ke baiyana tsantsar kwanciyar hankali da rashin damuwar dayake ciki ya fito daga cikin motar tareda gyara Riƙon ƙaramar jakar dake hannunsa, a nitse yake takawa cikin salonsa harya isa Bolcony ɗin daze sadashi da falon gidan da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga falon wanda yaketa tashin ƙamshin turaren wuta, wara ɗan manyan idanunsa yayi yana shaƙar ƙamshin daya kasance baƙo a gareshi don besabaji ba Asma'u wadda ke ƙoƙarin fitowa daga khitchine ta ɗauke da wata haɗaɗɗiya kula ta zaro ƙananun idanunta masu haske tana kallonsa, Ajiye kular tayi sannan ta dawo tsakiyar falon ta hanzari ta rungumeshi ƙam tace "maraba da gwarzon maza kuma jarumin daya ƙware wajen dannar zuciyarsa" ɓoyayyiyar Ajiyar zuciya Ya sauke sannan ya saki murmushi yace "thank you" zare jikinta tayi daga nasa ta wani cuno baki gaba tace "oh iya kalmar ladan kaɗai dazan samu daga gareka kenan bayan tsahon kwanaki biyun daka kwashe baka nan?" "kafeta yay da manyan brown ɗin idanunsa with surprise bisa canjin daya gani a tareda ita cikin ƙanƙanin lokaci, hure masa idanu tayi hakan yasa ya lumshe idanun a hankali ba tareda ya buɗe cikin hanzari ba, kafe kyakkyawar fuskarsa tayi da idanu tun daga kan tip pink lips ɗinshi da wani kwantacce gashi yaywa ƙawanya har zuwa dogayen lashe's ɗinsa, tsawonta ta ƙara tareda temakon dogon takalmin dake ƙafarta donya fita tsaho sosai a hankali ta ɗora lips ɗinta akan nashi ta fara kissing nashi cikin wani irin salo me tafiya da zuciya, Shidai Sulaiman tsayawa yay cak tamkar an dasashi sabida tsabar mamakinta dayakeyi jin dayay tana dabda ta birkita masa lissafi yasa ya dakatar da ita ta hanyar zare bakinsa daga cikin nasa yace "pls barinyi wanka na huta jikina akwai gaji..."Ummm nidai sedai muyi tare" ta faɗi hakan yayinda taja hannunsa tayi gaba shi kuma yana biyeda ita, Sun shiga ɗakin ta wani faɗo mishi a jiki tareda kai hannunta ta fara ƙoƙarin zare masa hular kansa cikin ƙanƙanin lokaci ta gama rabashi da kayan dake jikinsa dagashi se boxers, gabaɗaya kansa ɗaurewa yayi da abubuwan da Asma'un keyi mamaki ne ya cika zuciyarsa na sauyin daya gani a tareda ita, be ƙara sarewa da lamarinta ba seda suka shiga toilet da sunan yin wanka nan da nan ƙwaƙwalwarsa ta dakata da aiki na wucin gadi sabida yanda Asma'u ke bawa batirinsa caji. Wankan da basuyi ba kenan suka fito aka kama wani aikin daban intaƙaice muku dai Ranar Sulaiman a cikakken ango ya kwana.
*BAUCHI STATE*
(Azare)
"Af malam tun jiya naso nayi maka magana akan kayan Abincin danaga an shigo dasu amma kuma Allah bebani iko ba se yanzu" Murmushi Baba shaik yayi tareda Ajiye kofin Furar dake hannunsa yace "wllh Ɗalibina ne wanda nake yawan baku labarin himmarsa da ƙwazonsa shine ya kawomin dayazo jiya" maman shalele tai murmushi tace "Allah sarki ubangiji ya saka masa da alkhairi ya kuma bashi zuri'a ɗaiyiba" da "amin" malam ya amsa sannan yace "bana taɓa manta Ranar da nasan Sulaiman wata rana a babban masallaci bayan mun idar da sallar ishsha'i muna dabda mu fara karatun littafin Riyadussaliyin ya shigo sanye da kayan Bautar ƙasa a jikinsa, ina lura dashi yaje ya samu guri daga ɗan nesa damu ya zauna tareda ɗaukar littafin Riyadussalihin ɗin shima ya kasa kunne yana sauraron mu, a lokacin sena dubi ɗalibaina a wannan lokacin nace "A wani shafi muka tsaya?" ba zato ko tsammani naji yana karanto gurin da muka tsaya tareda yin bayani dedai da wanda nayi a jiya. Sosai mukai mamakinsa don bantaɓa kula dashi ba se'a ranar haka ya ƙaraso gurin ya zauna sosai sannan muka fara karatu gabaɗaya, tundaga ranar ya zama cikakken ɗalibina don har mahaifinsa dake zaune a garin GAMAWA seda muka ƙulla zumunci dashi a sanadin Sulaiman harya kamala bautar ƙasarsa yabar Azare be dena zuw ɗaukar karatu gurina ba, wata rana da jimawa ya kawomin katin gaiyatar ɗaurin Aurensa a lokacin nayi murna sosai har naji dama ace ƴatace ta dace da mijin ƙwarai kamarsa" murmushi maman shalele tayi tace "malam kenan ai komai muƙaddari ne daga Allah ubangiji be ƙaddara hakan ba Suma yaran Allah yay musu zaɓin mazan ƙwarai." "Amin ya Allah" a haka hirar ta tsaya malam ya fita donya duba lafiyar sauran iyalansa yana fitowa ya tsinkayi muryar Hajiya Maryam tana Faɗin "Basirah me kikace?" ɓangaren Yaya Basira ta saukar da numfashi
***
Daqyar Sumaiyya ta samu wani abun hawan ya kaita har gaban makarantarsu alokacin har an soma dan yayyafi, dama tun kan su karaso ta ari wayarsa ta kira Khadija tace ta fito waje ta jirasu gasu nan karasowa kuma ta taho da kudi, dayake ta haddace lambarta akai shiyasa.
Bayan sun sallami mai adaidaita Khadija take tambayarta "Sumaiyya yana ganki haka ? Dan Allah ayau kadai ki dubi amincin dake tsakaninmu ki taimaka ki gayamun abunda ke Faruwa arayuwarki " kuka Sumaiyya ta fashe mata dashi dan bata jin ayau zata iya b'oye damuwarta dan tana da bukatar alallashi zuciyarta, ya zama dole Khadija ta san duk abunda keta faruwa ayau d'in nan..jerawa sukayi suna tafiya cikin makarantar ayayin da Sumaiyyar ke bata labari, ta bata labarin Dr.Gana da kuma yadda akai yaya Muntasir ya kamata da kuma bukatarsa daya bijiro mata dashi, har zuwa sanda ya jata har zuwa gidan abokinsa ita kuma asannan bata cikin hankalinta sanda ta bishi don burinta kawai ya goge vidiyon dake wayarsa, hakan yasa ta bishi har dakin tana rok'onsa ba tare da tasan cikin tarkonsa zata fada ba.
Khadija ce ta fashe da kuka tana fad'in"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wannan wacce irin musifa ce ? Sumaiyya dan'uwanki kafiri ne babu Allah aransa tunda har zai iya miki wannan ta'assar, Allah ya saka miki amma ya zama dole mu dau mataki akai..." da sauri Sumaiyya tace"a'ah Khadija mu barwa Allah komai, yana kallo kuma zai sakamun, na gaya miki damuwata ne ba don ki dauki mataki akai ba amma don kin matsa ne shiyasa, Ni Sumaiyya nabar Muntasir da Allah, ki sani ana gaggawan karban addu'ar duk wanda aka zalunta "yanzu Sumaiyya haka zamui shiru da wannan babban al'amarin ? " batsar da zancen Sumaiyya tayi bayan sun Shiga hostel ta dauki bokitin Khadija tace"bari dauraye jikina " bayan ta fito wanka ne ta nemi yaya Basira da wayar Khadija take sanar da ita cewa basu fito lacca da wuri ba sai gab da za'a fara ruwa, yanzu ahostel zata kwana, yaya Basirar bata kawo komai aranta ba tace"To Allah ya tsare Sumaiyya"
H/C ✍️