MUTUNCIN ƳA MACE!

Chapter 10

by @zmchubado


"Mama me kike ci ne na baka na zuba ?, ki kwantar da hankalinki yanzu duk zan fiddaku cikin rud'ani kuma zan gaya muku ta yadda akayi kayan Sumaiyya suka shigo hannuna " ya furta yana sakin murmushin mugunta, Furzar da wani iska mai zafi yayi sannan ya dire kallonsa akan fuskar Sumaiyya da tashin hankali ma ya hanata motsa koda 'yar yatsarta ne, yace"Aranar ashirin da bakwai ga watan Yuli sanda na raka uban gidana kwaso kayayyaki acikin garin Bauchi sai dare yayi mana, hakan yasa muka tafi Villa hotel da misalin taran dare domin kwana, Wani abun mamaki sai nayi kicibus da kanwata Sumaiyya tana fitowa daga wani daki ayayin da wani gardin yabiyo bayanta daga shi sai gajeren wando da singlet ya jawota ta dawo da baya " dauke kallonsa yayi daga gareta ya koma duban sauran mutanen dake katafaren falon da kallo daya bayan daya yana fadin"yanzu wannan labarin dana bayar wani irin fassara ne mai sauraro zaiyi mata ? " yo! karuwanci taje yi mana in ba haka ba menene zai kai yarinya budurwa otel ita ba aure ba in banda karuwancin ? " Mamansu Muntasir ta furta Zuciyarta cike da farin ciki da wannan al'amarin.
"Tabbas ni kaina da kuma mijina shaida ne don awannan ranar shashantar damu tayi akan cewa ta manta da littafinta awurin kawarta kuma suna da test awashegari don haka zata je ta karbo, Ni kuma kuskurena daya dana bata izinin fita ba tare da sanin Abban Adil ba, koda ya dawo fada ya dungayi yace don me zan bari ta fita acikin wannan daren bada izininsa ba ?, wallahi yayi fada sosai don ko kanwarsa ce ta uwa daya uba daya karshen gatan da zaiyi akanta kenan na nuna damuwa karara, ashe dai ba nan taje ba.." nan ta kwashe labarin yadda akai da Fu'ad da shima karetan da yayi, Muntasir shine hadda nuna musu Video clip d'in daya samo awurin wani ma'aikacin hotel d'in, amma saida ya biyashi kudi tukunna kafin ya samu wannan leakage d'in wanda cctv camera na hotel din ya kwasa, nan suka ga Shigar Sumaiyya cikin hotel din tana ta waige waige kamar mara gaskiya, amma anki nuna yadda tattaunawarsu ta kasance da Dr.Gana, Muntasir ya saka an yanke wurin, sai fitowarta kawai suka gani da kuma lokacin da shi Dr.Gana din ya biyo bayanta ya jawo hijabinta, sai Fuskar Muntasir din da ubangidansa Alh.Namaru da aka hasko, Shikenan!   ,kowa sai sallalami yake yi yana tofa albarkacin bakinsa, yaya Asiya tace"wayyyyo Abun dariya wai kunkuru ya yi wa bushiya ƙafa, Baba me nake gani ne haka kaida Shalelenka yau sai gaku arana tsaka tana toyaku ?, d'iyar daka fifita akan sauran ya'yanka, d'iyar da kafi alfahari da samun irinta, d'iyar da aka tsaya kan tsayin daka na ganin ta samu gurbin karatu, kai magana ma in zaayi maka ita in ba zancen Sumaiyya bane tofa bazaka baiwa wannan zancen muhimmanci ba, yau gashi ta kwab'e muku, mun ganku arana yana toya tsakiyar kanku, ayau Sumaiyya ta kwaso maka degree d'in karuwanci, Allah ma yasa dai babu rabon juna biyu..." haka sauran ya'yan ma sukayita yi dashi, Maman shalele kuwa kasa magana tayi, Maman muntasir ta dubeta tace"hehehe Badi'atou yau ba bakin magana ne ?, duk da cewa nasan ke d'in ba mai fiya magana bace amma yana dakyau kidan tofa albarkacin bakinki aciki..." kai tsaye Mama tace"tambayata ga Muntasir shine acikin wannan bidiyon daya nuna mana meyasa ba'a nuna abunda ya gudana tsakanin Sumaiyyar dashi abokin ma'ashar nata ba ?, ai ya kamata mu gani " Anty Asiya tace"an gaya miki 'yan hotel sukan nuna sirrin mutum ne ?, iyakacinsu wannan dai da kika gani, in kuwa har kika ga an nuna miki cikin dakin tofa sai in ya kasance ana zargin wanda ya kama hayar wannan dakin da aikata wani mugun abun ne..."da sauri Muntasir yace"Yauwa gaya mata dai..."
Sai da Baba ya tsawatar musu sannan ko'ina yayi tsit, cike da bakin ciki ya dubi Sumaiyya yace cikin rawar murya"Sumaiyya kinci amanar tarbiyar da muka baki, lallai ayau na yadda da ake yawan cewa dan daka fi so shine yafi kunyataka, da wani irin ido kikeson in kalli jama'a in har suka ji wannan batun ?, ni da nake karantar da ya'yan wasu gujewa fadawa irin wannan kazantar, akodayaushe kokari nake na ganin irin wannan wutar bata kama agidajensu ba amma sai gashi ayau ni takamamun anawa gidan, Sumaiyya da wani idon kikeson in sake kallon mutane dashi ?, kai Muntasir wa'ennan kayayyakin su fa a ina ka samesu ko kuma ince taya akai suka shigo hannunka ? "Baba wallahi ban aikata ba sharri kawai yakemun bari kuji yadda abun yake...." wani irin wawan mari Baba ya kwasheta dashi wanda ya taba Zuciyar Haj.Badi'a, da sauri ta tashi tabar Falon don bazata iya jure cigaba da jin wannan sharrin da ake kullawa d'iyar tata ba!   ,"inna sake jin muryarki anan saina tattakaki, karya za'a miki ?, Fasika kawai! " Baba ya furta cike da tsanarta, runtse idanu tayi tana jin dafin aranta na sunan daya ambatota dashi!  ,"ina sauraronka ina aka samo kayanta ? "Washegari kuma dana je gidan wani abokina Lukman sai na sake mamaki da ganin Sumaiyya awajensa, ashe nemanta yake kuma ba wai da nufin aurenta ba sai don kawai ya lalata mata rayuwa ita kuma ta biye masa, ashe sun ma dad'e suna fasikancinsu Allah ne kawai ya shirya tona masu asiri, cike da rashin jin dadi na nuna mata alallai sai kun san halin da take ciki acan, shine ita da saurayin nata suka ji mun wannan raunin" ya furta yana zare bakin tabarau d'in Fuskarsa , nan sukayi arba da shanyayyen idon nasa, kowa ya fasa ihu hatta da yan'uwansa da Mamansu, sai sukayi kamar ba jiya ne ya fesa musu labarin komai ba!   ,ya cigaba"wai yama tsaya ahakan kenan, ada so sukayi su kasheni sai Allah ya taimakeni na samu na tsere na kai kaina asibiti, sai dai acan asibitin na nuna musu tsautsayi ne kawai ya afkamun don ada sunso shigar da hukuma ne ayi bincike kafin su tabani, nayi jinyar kusan sati uku kafin aka sallameni shine fa idona yakoma haka, babu wanda yasan halin dana ke ciki awannan lokacin inka cire yaya Basira itace kawai na kira na sanar da ita halin da nake ciki hatta zo asibitin tare da mijinta suka sameni " cike da mamaki Sumaiyya ta dubi yaya Basira da Abban Adil ashe su d'in munafukai ne bata taba sani ba?, tsawon lokacin nan tana tare dasu ashe irin kallon da suke mata kenan kuma basu taba zaunar da ita sun gaya mata ba ?, haba shiyasa ita Basirar ta canza mata, shi mijin nata ne dai yaki nuna mata komai!, tunaninta ne ya katse sanda ya cigaba da bayani"kafin asallameni Lukman ya nemeni ya rokeni gafara sannan yace in rufa masa asiri, nuna masa nayi kamar komai ya wucemun, shine ya mikamun ledar dake kunshe da kayayyakin Sumaiyyar wai tayi mantuwa ne kuma shi ya rasa yadda za'ai ya sameta layinta baya zuwa kuma shi yana tsoron yakai mata da kanshi, karban ledar nayi na nuna masa zan bata asirrance kuma komai ya wuce awajena, yanzu ma haka maganar da nake muku ya iso yana waje yana jirana tarko na d'ana masa shiyasa yazo, in kun bani izini bari inje in shigo dashi...." kai tsaye Baba yace"an baka...." ya fice, Sumaiyya dai jinta take kamar mutuwa tayi ake mata hisabi, shin me tayi wa Muntasir ne arayuwa da har yake k'ok'arin ganin bayanta haka ?

   ****

Bayansa Mama tabi da kallo harya fice daga ɗakin zuciyarta a cike tabda son sanin matsalar ɗan nata, a sanin dataiwa Sulaiman yaro ne me masifar zurfin ciki idan abu yana damunsa baze taɓa gaya maka ba sedai kai ka fahimta a radin kanka ajiyar zuciya ta sauke me nauyi tareda cewa "koma meke Damunka a ranka ubangiji ya sani ina roƙonsa da yaye makashi cikin Sauƙi Manu" miƙewa tayi ta faɗa toilet sabida gabatowar lokacin sallar Azahar, ƙarfe uku dedai Abbansu ya shigo gidan kansa sanye cikin wata baƙar dara irinta yankin maidugurawa, falon Gwaggo ya fara shiga da sallama ɗauke a bakinsa a zaune ya zameta tsakiyar falon se matsar ƙwalla take tana kallon Aman wanda ya tsula mata fitsari a saman kafet, da sauri ta kalleshi tace "yauwa wllh daman jiran dawowarka nake tunda matarka da ƴarta sun gama raina ni, yanzu sabida Allah da ma'aiki wannan rayuwa ce Nuhammadu?  Nidai kawai nasan zuwan zainabu  gidannan badan kowa tayi ba sedan tazo ta kasheni ita da wannan koɗaɗɗen ɗan nata me kama da zabiya,  basuda aiki se ƙuntata min nidai kawai Ka kirata ta gyaramin ɗakina tun kafin nayi mata Allah ya isa"  murmushi kawai Abba yayi yace "kiyi Haƙuri Gwaggo barin kirata tazo ta gyara miki" ya faɗi hakan yayinda ya shiga ƙwalawa Zainab dake ɗakin mama Suna hira da Asma'u kira, da sauri ta miƙe tareda amsawa ta fito kanta yafe da ɗankwalin Atamfar dake jikinta a falo gwaggo ta sameshi nan Abba ya shiga mata faɗa akan ta dena barin Aman na zuwa falon Gwaggo indai har tasan bazata dinga gyara mata ba, zaro ido Gwaggo tayi tareda dafe ƙirji tace "wayyo Allah ni salamatu na shiga uku yau ni 
  Muhammadu ze tonawa Asiri, yanzu kai bakaji kunyar kallon idon  jikata a gaban idona kace mata karta sake shigowa   ɗakina ba? Ikon Allah to wllh nidai babu ruwana bance ka gaya mata haka ba" se kuma ta fashe da kuka ta fara matsar ƙwalla da bakin zaninta,  dariya zainab ta farayi ƙasa-ƙasa shiko Abba sakin baki yayi yana kallonta sabida tsabar mamakin yanda ta juya masa magarsa  juyawa yayi zebar falon da sauri gwaggo tasha gabansa tace "kaga Muhammadu Allah ya baka haƙuri naga kamar ka ƙullaceni a ranka tonidai babu Ruwana gaskiya na faɗa"  ta ƙare maganar tana kallonsa  ɗaga kansa kawai yayi yace "shikenan gwaggo aike zan bawa haƙuri tunda kece akayiwa ba dedai ba" dafe ƙirji tayi ta zaro ido tace "Muhammadu meyay zafi haka naga kana naman ka ƙullaceni ? To nidai aniyarka sedai ta bika wllh zoka tafi tun kafin ka juyamin zance " fita yay daga ɗakin fuskarsa ɗauke da murmushi a ransa yace "ubangiji ya rabamu lfy da iyayenmu " falonsa ya wuce kai tsaye bisa ga mamakinsa seya riski Sulaiman a falon ya kafe Makekiyar   Tv dake falon da kallo seka rantse yana fahimtar abinda akeyi a tv ɗin.

Sallamar Abba ce ta taimaka wajen dawo dashi daga duniyar tunanin daya afka cikeda girmamawa ya miƙe yana murmushi yace "sannuda zuwa Abba" "Manu harkun iso kenan amma meyasa baka kirani a waya na dawo ba?" sunkuyar da kansa ƙasa yay still yana murmushi be dena ba  jinjina kai kawai Abba yay a ransa yana ƙara girmama kunyar da Sulaiman keda ita sekace wani mace  Mama ce tai sallama ƙofar Ɗakin hannunta ɗauke da wani ƙaton tray an jera manyan womers a ciki Daining ta wuce dasu sannan ta kalli Abba tace "yanzu ka shigo gidan Amma dan naji kamar maganarku da Gwaggo lokacin danake kan kwashe abinci "murmushi Kawai abba yayi yace "Ina shigowa kuma Senaga Manu ashe har sun iso?" "Ae wllh ni tafiyar tasu ma tamin sauri sosai" ta faɗi hakan tareda kallon Sulaiman da yay ƙasa da kansa tace "kaje ga abinci nan na kawo dan nasan wannan idon naka akwai yunwa a cikinsa .  Dariya Abba yay yace "kafin shi yaje bari ni na fara gaba" dariyar sukai gabaɗayansu sannan Mama ta fice ta bar musu falon, bayan sun kammala cin Abincin ne Sulaiman ya dubi mahaifin nasa cikin girmamawa yace "Abba dama akan maganar ƙarin girman dana samu a gurin aiki ne to shine suka aiko da waƴannan takardun tareda chek ɗin naira million 10, to ganin hakan yasa nace bari nazo gida na ƙara sanar dakai"  murmushi Abba yay yace "masha Allah ubangiji yasa albarka a lamarin ya kuma yiwa Rayuwarku albarka, sedai ina me ƙara jan kunnenka akan ruƙon gaskiya da kuma Amana don babu abinda yakai waƴannan abubuwan tura mutum zuwa ga matakin nasara a rayuwa, duk rintsi duk wuya karka yarda kaci amanar duk wanda Allah ya haɗaka zama dashi koda kuwa ace matarka ce Manu, inaso kasa a zuciyarka cewa Allah bayason masu zalinci dayiwa dokokinsa hawan ƙawara. Don haka don Allah sulaiman kazama me ruƙon gaskiya da kuma Amana koda wasa kada kai zalinci"  Abba ya faɗi hakan yayinda yake tsaida kallonsa akan Sulaiman wanda duk jikinsa ya ƙara mutuwa, wani dogon fasali yaja sannan ya kalli Abba yace "insha Allah Abba zanyi aiki da nasiharka aduk halinda zan tsinci kaina."  a haka hirar tasu ta ƙare ya miƙe ze fita ya tsinkayi muryar Abba na faɗin "Yaushe Rabonka da kaiwa Shaik Muktar Azare ziyara ne Manu"  ɗan shafa kansa yayi yace "Abba kwanaki naje fa nida Muktar"  "masha Allah ka kyauta sosai Amma dai kafin ku wuce Kadunan lallai ku biya ku gaisheshi daga nan ma ka samu wasu Addu'o'in daga gareshi Don Rayuwra nan seda addua" "to Abba insha Allah zamuje kafin mu koma goben insha Allah  barinje ɗakin Gwaggo"  Sulaiman ya faɗa yayinda ya fice cikin nutsuwa daga Falon. Ajiyar zuciya Abba ya saki yana bin bayansa da kallo harya ɓace masa da gani, tabbas Sulaiman ɗane nagari wanda ko wani uba zeyi alfahari dashi  a ransa yace "Allah yasa ka gama da duniya lfy Sulaiman ya kuma baka zuriyar da kaima zasu bika kamar yanda kake mana biyayya ........
     ****
Ji tayi Baba yace"Na baka...." Babu bata lokaci yaje ya shigo da Lukman daya gaji da jiransa awaje, dayake ya tab'a zuwa gidan shiyasa bai sha wahala ba, sai hira suke, Lukman yace"kai baabaah ina fatar babu matsala dai ko ?, ina tsoro kar ince musu tsautsayi ne yasa naji maka wannan raunin inji an shigeni da bugu, amma agaskiya abokina baka kyautamun ba daka jefani cikin wannan tashin hankalin..." murmushi Muntasir yayi yace"kai malam ka natsu ka fiye tsoro babu abunda zai faru, su d'in basu yarda dani bane, azatonsu danbe nayi har aka ji mun wannan raunin shiyasa nace bari in had'a kai dakai ka taimaka ka gaya musu cewa tautsayi ne.." dari bisa dari Lukman ya aminta cewa zai taimakawa abokin nashi...
Suna Shiga falon kallo yakoma kan Lukman, tun daga irin kallon da ake jifarsa dashi yasa shi shan jinin jikinsa, Muntasir yace"Wannan shine Lukman d'in da nake baku labarin nasa....." jikin Baba na rawa ya mik'e ya isa ga Lukman yana nunashi da 'yar yatsa yana fadin"Kai ne ?" Cike da tsoro yace"eh....eh nine amma don Allah kuyi hakuri tsautsayi ne...." bai gama magana ba yaji kawai Baba ya kwasheshi da wawan mari yana fad'in"tsautsayin ubanka ?, ka lalatamun rayuwar yarinya sannan kace tsautsayi ?, to billahil lazee na rantse da sarkin daya busamin numfashi sai ka AURETA!......" arude Lukman ya dubi Muntasir dake sakin killer smile yace"Muntasiru wai me yake nufi ?, amma ka musu bayanin dakyau kuwa ?....." hannu Muntasir ya daga ya wanke masa Fuska da mari yana Fad'in".......................


H/C