MUTUNCIN ƳA MACE!

Chapter 12

by @zmchubado

"Bayanin Uwar me zanyi musu bayan cin zarafin ƙanwata da ka daɗe kana yi?"  cikin yanayi na wanda ke dabda kiɗimewa yace "wai me kake ƙoƙarin faɗane Muntasir? Don Allah idanma wasa kakeyi pls ka dena man........   " Dalla malam rufemin baki Azalimi kawai  mayaudari  Wllh kaci amanar abotarmu dakai Lukman, bantaɓaji a raina na tsani wani mahaluki ba a rayuwata sekai kuma wllh bazakaci banza ba seka girbi abinda ka shuka!!!"  duk maganar da Muntasir keyi idon Lukman na kansa, kallonsa kawai yakeyi sabida tsabar kaɗuwa da mamakin abinda Muntasir yayi masa wata irin ƙwallar baƙin ciki ce kwance a saman ƙwayar idanunsa waƴansa sukai ja sabida ɓacin rai, bakinsa na Rawa ya nuna Muntasir a mugun ƙufule yace " Ni kaiwa haka ko muntasir? "nika gaiyato cikin gidanku kuma ka ratawa jakar tsaba ko?, to na rantse da ubangijin daya Halicci Annabi Adamu sekayi danasanin abinnan dakai min billahillaz..... Wani ɗan iskan mari Baba shaik ya sake ɗauke Lukman dashi sannan ya nunashi cikeda ƙunar zuciya yace "wani danasani xakasashi yayi banda wannan wanda ka sanyamu gabaɗayan mu?"  zeyi magana kenan  numgashinsa ya fara sama sabida fishi da ɓacin ran dayake ciki, da Sauri Abban Adil ya tareshi cikin yanayi  na Rarrashi yace " Haba Baba Sam be kamata ka bari ɓacin rai da fushi su dinga sarrafa zuciyarka ba a wannan lokacin, duk abinda zamuyi ko muyiwa Lukman baze taɓa goge tarihin abinda Sumaiyya ta aikata ba koma ince suka aikata ita Lukman  ba, don haka don Allah baba ka saisaita zuciyarka mu samarwa kanmu mafita ba tareda maganar nan ta fita waje ba"

"taya zan iya rarrashin kaina akan wannan abinda Sumaiyya ta aikata min ? Allah ya sani na baki tarbiya gwargwadon iyawata, haka kuma nasoki so mafi tsanani a cikin  ƴaƴan dana haifa a cikina,  na fifitaki samada kowa cikin ƴaƴana, Sumaiyya Meyasa zakiyiwa Ubanki Muktar Azare haka?"  ya ƙarasa mganar yana fashewa da wani irin kuka wanda yasa ba shiri ya zube akan gwiwoyinsa yana mecigaba da kukan daya kasa dannar kansa,  Sumaiyya wadda taci kuka harta godewa Allah kasa cewa komai tayi sabida wani irin zafi da zuciyarta ke mata, wani irin abu takeji a saman maƙoshinta yana taso mata,  idanunta da suka rine da kuka ta ɗago ta kalli Mahifinta wanda ke zubar da hawaye a sanadin sharrinda muntasir ya ƙulla mata tace  " haƙiƙa na karya tarihin wannan Ahalin tunda har na saka Mahaifina kuka da idanunsa!! amma inaso kowa dake wannan falon ya sani kuma ya shaida cewar Allah baya bacci kuma baya zalinci, haka kuma yana gaggauta karɓar Addu'ar wanda aka zalinta ba tareda haƙƙinsa ba,  ina Roƙon Allah da sunayensa Mafiya kyawu yaymin sakaiya akan duk wanda ya zalinceni har yay sanadiyar zubar hawayen Mahaifi......... Mari yaya Basira ta ɗauketa ɗashi wanda yasa ba shiri ta haɗiye maganar dake ƙoƙarin fitowa daga ƙasan  maƙogaronta, cikeda ɓacin rai tace "don uwarki har kinada bakinda zakiyi wata magana bayan duk hujjoji sun tabbatar da cewar ke ɗin Fasiƙace?, wllh ni kaina kin cutar dani Sumayya!  Nasoki so na gaskiya sabida har raina nakejinki amma kika cutar da irin yardar danai miki meyasa kikai haka Sumaiyya why?"   " hmmmm ai kibarta kawai yaya Basirah ni kaina sumaiyya ta mugun bani mamaki a lokacin dana ganta rashe-rashe a kwance kan gadon Lukman,  wllh yarinyar nan ta wuce duk yanda kuke zato, muguwar makira ce ga ɗan banzan taurinkai kamar jinjirar Jaka" Muntasir ya faɗi hakan yayinda yake jifanta da wani ɗan iskan kallo wanda yasa taji ƙirjinta ya buga da ƙarfi, kaf falon babu wanda ke firta alkhairi akan Sumaiyya sakamakon makircin Muntasir dayay tasiri a kunnuwansu da zukatansu, ɗagowa Baba shaik yay da jajayen idanunsa yana kallon Sumaiyya batareda ya iya furta koda kalma ɗaya ba, ajiyar zuciya ya sauke tarda ƙara share ƙwallar dake sakko masa yace  " duk wani wanda zeji ciwon abinda Sumaiyya ta aikata to wllh a bayana yake, don haka zan zartar mata da hukuncin danake ganin shine daidai akanta."  Muryar Emran dake tsaye jikin ƙofar falon tun lokacin da aka fara meeting ɗin ce ta katsewa kowa hanzari ciki kuwa harda  da baba shaik  dake ƙoƙarin yankewa Sumaiyya hukunci bisa laifinta yace " yanke hukunci cikin fishi sam ba aikin masu ilimi bane Baba duba da yanda ilimi kan zama hasken fitilar dake yaye jahilci,idan har zan iya tunawa dedai kaine ka karantar dani cewar Akwai ayar datai magana a  cikin alƙur'ani wadda take horar damu cewar  yanada kyau idan aka kama mutum mai lefi abashi dama ya kare kansa, haka kuma shari'a bazata yanke masa hukunci ba harse  idan me laifin ya gaza kare kansa da gamsasshiyar hujja  sannan ne ya halatta a zartar masa da duk hukuncin daya dace dashi don gujewa ɗaukar hakki da kuma  zalinci""

Gabaɗayansu idanu suka zuba masa musamman Muntasir da cikinsa ke neman ɗurar ruwa, zumbur yay da zummar ya kaima Emran duka amma Baba shaik ya dakatar dashi ta hanyar cewa  " haƙiƙa kayi gaskiya  kuma babu shakka nina karantar dashi hakan kallonsa ya mayar ga Sumaiyya wadda Fuskarta tai wani irin ja sabida kuka, duk kyawawan laɓɓanta masu launin pink duk sun saje da jan da hancinta yay abinka da farar mace sannan ya kyauda kansa cikin takaici yace "idan kinada hujjar da zaki iya kafawa wajen kare kanki to bisimillah"  tsagaita kukan datake rerawa tayi a hankali sannan ta ɗago ta dubi mahifin nata tace "Banida hujja Baba Amma inada sheda guda ɗaya tal" 

cikin ƙunar rai Hajiya Maryam mamansu Muntasir tace "uban waye shedar taki a nan da har kikeda yaƙinin cewar ze iya fitar dake a cikin bala'in da kika jefa kanki na Zinah?"  "Rintse idanunta tayi d sauri sabida jin mugun kalmar da Mama ke jifanta dashi na Zinah , ranta na zafi cikin yanayin sanyin halinta tace "wanda na riga a matsayin sheda ba mutum bane sabida mutane a cike suke da rashin gaskiya gamida cin Amanar makusantarsu idan har suka samu dama, ni'a yanzu Allah shine kaɗai shedata kuma hujjata haka kuma abin dogarona!!  Shikaɗai ne ze iya fitar dani akan wannan jarrabawar dana samu kaina a ciki, yanzu hukuncin Sumaiyya yana gareka Baba wllh duk abinda kayanke a kaina na zan karɓa kuma wllh bazan taɓayin kaico da hukuncinka ba!" tsaki mutanan dake falon suka saki kusan duk a lokaci guda,  Jikin Baba shaik ne yay sanyi lokaci guda kuma tausayinta ya fara ɗarsuwa a saman zuciyarsa,  ɓangaren Abban Adil da kuma Lukman suma ba ƙaramin sanyi jikknsu yayi ba wani irin tausayinta ne ya samu gurbi a zukatansu

Maida glashinsa Baba shaik yayi tareda kallon Lukman dake zaune fuskarsa babu walwala yace " tunda kaine abokin shaiɗancin nata kaje ka turo min iyayenka ayi maganar Aure don wllh bazan ƙyaleka ba seka Aureta"  Wani irin zaro idanu Lukman yay yana kallon Baba shaik cikeda kaɗuwa, wata irin zuface ta fara keto masa a lokacin dayaga irin kallon tsanar dake fitowa daga idanun Sumaiyya. "Hamza lallai ka sanya idanu akansa da duk wata zirga-zirgansa sabida gudin karya tsere, Gobe insha Allah kaje ka sanar da iyayensa ni Muktar Azare ina son ganin ubansa don wllh baze lalata min ƴa yaci banza ba"    haka taron ya watse kowa na tofa albarkacin bakinsa akan sumaiyya    
       ******
Gwaggo ce Riƙe da ƙugu tana kallon Asma'u wadda ke ƙoƙarin gyara zaman mayafin dake jikinta tace "ke baiwar Allah ina fatan dai kin cikamin butata da ruwan da kika ƙarar min?" "Ae Gwaggo na zuba miki harda ɗaya ƙaramar ma duk na zuba" washe baki tayi tace "to madalla Allah dai ya mayar daku gida lfy, ammafa a ɗan kwana ɗaya da kukai da mijinki na lura kema ba baya bace wajen ƙazanta don haka sena leƙa naga abinda kika aikata min a makewayin nawa Zaki fita , tureta gefe tayi ta shiga bandakin aikuwa kafinta fito Asma'u tai waje don ita wllh wannan jarababbiyar tsohuwar ta isheta, har bakin mota Mama da Abba sukai musu Rakiya seda suka shiga suka zauna sannan  Sulaiman yace "Abba don Allah kar Gwaggo tasan yau zamu tafi kasan rikicinta yanzu zata fara"  Murmushi kawai Mama tayi tareda miƙawa Asma'u jakar dake Hannunta,  turaruka ne masu tsadar gaske se kuma wani sirirn chen a cikin akwakunsa. Kallon Sulaiman Zainab tayi tace" to Yaya Allah ya tsare hanya insha Allah idan ya dawo zamu kawo muku ziyara tunda duk gari ɗaya zamu koma da zama" murmushinta yay mata wanda ke ƙara masa kyau yace " Rabbi ya bada iko ki gaidamin Da Aman idan ya tashi"  a haka suka bar harabar Gidan Su mama na ɗaga musu hannu  gwaggo ce ta fito harabar gidan tana mitsitsika idanu tace " amma nidai wllh Allah ya isa tsakanina da wannan yarinyar matar Manu, yanzu sabida Allah Muhammadu abinda akaimin an kyauta min kenan?"   ajiyar zuciya Abba ya saki yace "meya faru Gwaggo?"  ƙwallar idonta tasa hannu ya share tace " Audigar mata fa ta cire min duk ta caɓe min makewayi da jini, wllh nidai ba ruwana sedai ince Allah ya isa tsakanina da ita"  baki Mama ta saki tana kallon Gwaggo ita kuwa zainab ba abinda take se dariya,  shiko Abba sabida kunya gabaɗaya kasa magana yay  shan gabansa Gwaggo tayi tana faɗin kallifa abinda tabar min A makewayi...... Kasa magana sabida yanda ya sandare a tsaye ana cikin haka Allah ya taimakeshi aka kirashi a waya ya fice yabarta nan tsaye baki buɗe da leɗar Auɗigar da Zainab tabar mata a toilet.
        *******
Babban abinda ke ƙona mata rai shine yanda Sam Baba shaike baya son sabgarta duk wani abu indai ta gurinta xe biyo toya gwammace ya haƙura dashi, wannan dalilin yasa damuwar datake ciki ta tsananta zuwa yanzu zata iya cewa tafi buƙatar Auren maƙiyinta Lukman da muntasir yay amfani dashi wajen tirketa akan zaman gidansu, ko waje bata iya fita sabida sauyin data samu a gurin ɗalibanta datake mugunji dasu  a gurin Mamanta kawai take samun sassauci da Emran idam har shima ya tafi makaranta to sedaifa ta wuni a ɗaki ba fitowa, wasu lokutan  har ɗaki Beebah take Zuwa ta shuka mata tijara kala-kala sedai kawai tayi murmushi ta ƙyaleta ita babbar masifar datafi damunta ma itace  tabon da Muntasir yay mata a Rayuwarta wanda baze taɓa gogewa ba.Tana  zaune falon mama Beebah ta shigo tace " Sumayya kizo inji Baba" gabanta ne ya buga da ƙarfi sabida tun bayan faruwar abinda ya faru bata sake ganin Baba ba sabida ya gargaɗeta kan cewar karta kuskura ta sake tinkarar duk inda yake balle tace zata kai masa matsalarta, komai take buƙata taje gurin uwarta tamata yau kuma kwatsam ace Baba yana kiranta?
Hawaye ne suka wanke mata fuska  ba tareda ta ankara  ba,  dafa kafaɗunta Mama tayi tace " Sumaiyya ki kwantar da hankalinki insha Allah babu abindaze faru  se alkhairi, kedai kawai duk abinda zakiyi kiyi gaskiya domin Ubangiji yana tareda bayinsa masu gaskiya maza tashi kije"    hijab ɗinta mama ta miƙa mata ta karɓa ta sanya sannan ta kama hanyar fita daga ɗakin, a hankali take ɗaga ƙafafunta harta isa babban falon Baba shaike kanta a ƙasa cikin sanyinta dayazama ɗabi'a garta tace "Assalmu'alaikum"  harta ƙaraso ta zauna a ƙasan ƙafafunsa be amsa mata sallamar ba cikin yanayin dattako Baba yace "Sumaiyyah" ɗagowa tai da sauri tanabin Mutanen dake falon lokaci guda kuma ƙirjinta ya buga da wani irin ƙarfi tace "Ba'ba'b..........


H/C✍️