Chapter 14
by @maidambu41
Chapter 14
Yadda yazo ya wuce ta gabansu yana busa hayakin wiwin din a tsakiyarsu zai tabbatar maka cewa idan ana niman dan takife to maganar gaskiya aka samu Uban kowa magana ya ƙare, hayakin ne ya shiga hancin Naanah Asma'u, ta kalli Almu ta ce mishi. "Sai da safe!" Ta bar wurin ba shiri, bin bayanta Almu yayi yana faɗin. "Muje na rakaki!" Hango shi suka yi a lungu yasa suka sauya shawara su bi kofar gidan sai dai suna zuwa suka samu ya rufe kofar gidan. Sun san duk niman magana ce don haka suka koma kofar. Kamar munafuka haka tazo ta wuce bai kula ta ba. "Kai a tunaninka zaka samu yadda kake sone?" Dariya yayi yana kallon shi ya shafa kanshi. "Bana isa ka min dariya ba, idan kuwa ka ga kayi nasarar samun abinda kake wallahi bana raye ne, wannan kan sai ka samu sauran da na bar maka, amma ba isa ba kuma ina gaya maka sauyin yanayi daga gare ni!" Daga haka ya wuce yana dariya, irin dariyar muguntar nan me shiga jiki mutane.
Ya gama ɗaukar charge yadda ya dace, yana shiga parlournshi yaji wayarshi tana kukan niman agaji. Kallon wayar yayi ya dauke kai, har ya katse aka. sake kira yaƙi ɗauka. Kusan kira 69 Babansa ya mishi amma bai dauka ba. Buga mishi kofar parlour aka yi ya mike tare da fitowa Abban tskiya ne ya mika mishi wayar. "Gidanku!" Amsa yayi ya saka a kunne aka ce mishi. "Ka ɗauki kirana Yarona!"
Kashe wayar yayi ya fito ya kawo ya mikawa Abban tskiya wayar ya koma ciki, ya zauna tare da ɗaukar wayar Abbanshi na sai da ya kusan yankewa, sannan ya ɗauka tare da zubawa wayar ido. Yana jin Abbansa yana magana amma bai kula ba har ya gaji ya katse kiran. Ya kashe wayar bakiɗaya.
Lokacin Sahur Abba babba ne ya kira Mustapha yazo ya amshi wayar, ya je ya dauko musu. Buga mishi kofar Mustapha yayi yana fitowa da wiwi yana busawa ya ce mishi."uban me zan maka?" Ajiye mishi abincin yayi. "Mtseew! Banza" ya dauki abincin. Duk abinda yake baya fasa cin abincin Maamah, ga wannan ruwan zafinta mai daɗi, haka ya zauna ya cinye tuwon shinkafa ce da tayi ji dumame mai daɗi, miyar kuka ce gashi har lokacin da wani kamshin tuwon ya kama yake yi.
A hankali ya fara ci yana tuna kuruciyarsu, yadda idan ya zo gidan ya samu an gama dumamen ake zuba mishi. Haka zai ga Naanah Asma'u tana ɓoye kanta kada ya kalleta. Har ya cinye abincin bai sani ba. Murmushi yake idan shirinsa.
*
Kwanaki biyar bai leka hajiya ba, asalima Hajiyar ce take cikin tashin hankali rashin ganinsa duk ta birkice har jininta yana kara hawa gani take kamar an ɓoye mata aka yi. Sai da Abba Babba ya zo ya saka shi a gaba. Tana ganinsa ta fashe da kuka. Yana zuwa inda take ta rufe shi da duka tana kuka. "Me nayi maka? Idan auren ce baka so sai ka gaya min, akan me zan saka ka dole bayan ko waɗanda na haifa ban musu dole ba balle kai da kake maraya, idan Mufidah ce baka so an fasa ka gaya min wacce kake so a cikin ko Naanah Asma'u kake so?" A yadda tayi maganar yasa shi kasa ɗago kai amma yadda ya rike hannunta gam yana jin kamar wannan damar da yake da ita na ƙarshe a gare. "Idan kika bani ita me zai sa nace bana sonta? Waye xai ki jinin mutanen kirki? Waye xai ki tsotso na gari? Waye zai ki nagartacciyar ɗiya daga mutumin da yake faɗi tashi don ya kyautatawa mahaifiyarshi. Waye zai ki yar matar da bata taɓa d'aga muryanta akan kowa ba, amma ni ba shine mafita ta ba. Kawai gara na mutu babu aure akan ayi min dole! Kada ki shigar da ni rayuwar kowacce mace balle na lalata musu gobensu, ya mutumin banza ne da ban samu tarbiyyar uwa yadda ya dace ba. Ban san kawazuci ba." Wato da iya kalmai Uban kowa ya daure su bakiɗaya. Sannan ya ki amincewa da maganar auren Mufidah, sannan ya ce nuna matuƙar zata amince ya auri Naanah Asma'u zai amsa amma shi yana tsoron kada ayi mata dole.
A wurin Abba karami mahaifinsa kenan ya kalli Abba tsakiya da ya sunkuyar da kai. Mustapha yake ji a wannan wurin kowa buƙatarsa kanshi kawai ya sani. Ko kafin su tawo sai da Mustapha ya kara rokonsa akan ya nima masa auren Naanah Asma'u, sannan ya gayawa Abba karamin cewa zasu nimawa Mustapha auren Naanah Asma'u. Amma yanzu saboda buƙatar ɗansa yana son shure maganarsu. "Hajiya Mustapha yana son Naanah Asma'u, kuma mun gama magana da Harisu kafin na zo, dama ke da Yaya muke so muyiwa magana."
Fir Hajiya ta rufe idanunta ta ce musu. "Makaho zaka bawa Uban kowa auren Naanah Asma'u ko. Ba zaka bashi bane?" Kanshi a kasa ya ce mata. "Hajiya ba zan iya hana shi ita ba, amma ya duba a cikin yan uwanta ita na rigada na bawa Mahmoud!" Shiru ɗakin yayi, ta sani ita ce ta gaya masa kada su tsaya jiran Mustapha. "Amma ai Mustapha yana sonta Yaya kuma kai ma kasan ban da soyayya me zai saka Mustapha ya tsallake Austria yazo nijar ganin jikin Uwata kai ma kasan da yadda suke kaunar junansu. Kuma."
"Idan har ni na haifi Makaho na bawa Adamu Asma'u ranar juma'a za a daura auren. Ko bayan raina wanda ya fasa auren nan Allah ya isa ban yafe ba. " Kallon Uban kowa tayi ta ce mishi." Jeka Allah ya maka albarka aure an gama ranar juma'a ɗaurin aurenku!" Ta fada tana rarrashinsa don kada ya sake fushi da ita.
Bakiɗaya Abba babba ya shiga wani irin tashin hankali da nai taɓa tsintar kanshi a ciki ba. Bakiɗaya yaji kome ya tsaya mishi. Kamar wanda bai da kuzari haka ya bar dakin yana jin kome ya tsaya mishi. Rayuwar yarshi kawai yake ji haka ya isa gidan ya zauna a dakin Maamah shiru yana kallon ƙasa. "Alhaji lafiya?" Kamar ya fashe da kuka ya bata labarin, yadda ya sunkuyar da kanshi kasa yana jiran yaji me zata ce. Fita tayi ashe tana fita hijab ɗinta. Barin gidan tayi zuwa Azin.
Yadda Hajjama ya ganta tasan ba lafiya, Yayunta suka biyo bayanta. Tana shiga parlourn Hajjama ta fashe da kuka. Babu wanda ya ce mata komai. Har ta gama suka tambaye ta. A hankali ta warware musu komai. Murmushi Hajjama ta yi ta ce mata. "Sai ki kwaso kafa ki zo don an hana dakin auren Asma'u?" Dariya take tana faɗin. "Ashe da sauranki Rukayyah, ai an gama ta rigada ta yanke hukuncin kuma daga mu har mahaifin Yarinyar bamu da abin da zamu yi. Kul ki lalata aikinki na tsawon shekaru. Allah ya bada zaman lafiya yasa itace hanyar shiryarshi."
"Hajjama Naanah bata da lafiya! Idan aka yi haka kashe ta zai yi tun tana yarinya yake mata mugunta." Ta fada tana kuka. "Ba abinda zai faru, idan baki nutsu ba itama haka zata kasance. Dukkansu kin san halinsu idan yana da muni haka naki idan yana da kyau haka naki, ku bata shawara ta koma ta rike Yarta ta nuna mata muhimmancin hakuri, kema ai bakya son Mahaifin Asma'u da kika yi hakuri ba ga rabonsu ba. Ki gane wani abu. Dole ki koya mata hakuri da shi musamman da ya kasance murdadden mutum. "
Nasiha tasha shi, Maamah kasa ɓoye laifinsa na baya tayi. Ai kuwa Hajjama ta rufe ta da fada har d zuba mata casbi. Wanda haka yasa ta mata tas ta ce mata. " Ba a shiga tsakanin bawa da Mahaliccinsa, ke kika ce ya ɗauki kasadar jinyarta yanzu kike gaya min ya taɓa aikata wani abu a baya, ya yanzu ma ɗan daba ne. Gara shi nashi a fili yake. Kada ki yarda Allah ya jarabce ki da shiga takalmin wanda yake niman shiryar Allah!"
Kuka tayi ta mata tana faɗin."shi kenan haka rayuwar Naanah Asma'u zai kare?" " Kada ki ja da ikon Allah irin wannan auren rabo na iya kashe duk wanda ya ce ba zai yiwu ba." Dakyar suka cusa mata ambaton Allah a bakinta, har ta nutsu Baban Mahmoud shi ya dawo da ita sai a lokacin Yaran suka fahimci bata gidan. Ya samu Abba babba suka fita ya mishi nasiha da lallai kada ya biyewa Maamah da Naanah ya bi Allah ya bi mahaifiyarshi, wallahi rahama ce Allah yake son mishi da ya bashi Yara mata sannan Allah ya bashi yar da kowanni namiji yake burin mallakarta a yadda ya mishi magana zaka fahimci, Mahaifin ya sha addini ya koshi. "In sha Allah zan yi yadda kace!" Haka suka rabu.
Tunda Maamah ta shiga daki ta rufe kofar dakinta. Har suka gama abin shan ruwa babu wanda ta fahimci me yake faruwa a cikin gidan.
Lokacin da Mustapha ya samu labarin bawa Adam Auren Naanah Asma'u ji yayi kamar baya cikin duniyar bakiɗaya. Jikinsa na tsuma ya mike tare da nufar asibitin. Lokacin da ya isa ana shan ruwa Hajiya Turai tana zaune da yarta Hamidah, tana ganinsa ta fara wani iyayi ya kafe Hajiya da Idanunsa masu cike da wani irin bakin ciki me haɗe da takaici da yake tunzura zuciyarsa ga aikata kome yake kallon Hajiya Innah, wacce itama ranta ba daɗi. Tasanshi tasan halinsa ciki da waje. Sunkuyar da kai yayi yana murza hannunsa idanunsa sun yi jajjur Murmushin bakin ciki ya sake a hankali ya sosa giransa na hagu. A yanayin da yake cikin ita kanta kallonshi take cike da razana, muryanshi mara amo ce ya daki dodon kunnenta inda ya ce mata. "Hajiya baki da imani, kuma kin ci amanata" da mamaki ta d'ago kai tana kallonshi idanunta cike da bakin ciki mara iyaka, ya sake murmushi yana me mikewa daga kujerar ya ce mata. "Baki da adalci, kina son kanki da abinda kike so, waɗanda kike so kike warewa domin faranta musu." Ajiyar zuciya ya sauke saboda yadda maganar take cikinsa, tabbas a cikin ransa zafi yake ji ainun, ya juya zai fita ya ce mata. "Ba don kaina ba, Maamah Rukayyah da Yaranta sun cancanci farin ciki da adalci amma don son zuciya irin naki , kin san halin Adam sarai kika dauki mutuniyar kirki kika bashi, wallahi tarin zunubi da azabar Allah suna jiranki!" Yana gama fadar haka ya saka kai ya bar ɗakin.
Ji yake kamar tura shi ake domin shi yayi duniyar ta mishi kaɗan kamar a tsuke yake jinsa. Yadda yake tafiya zaka ɗauka mahaukaci ne ko ƙwayoyi ya sha. A hanyar da zai kai shi wurin motarshi ya haɗu da Abba Babba ya kawowa su Hajiya abin bude baki. Haurawa titi yayi bai sani ba. Sai fisgo shi Abba babba yayi da karfi ya tsaya jikin wata mota da take gefenshi. "Abba babba me nayi maka haka?" Dariya Abba babba ya ce mishi." Ka sha ruwa kuwa?" "Duk yadda zaa yi da rayuwa kada ka sake a san ciwon da yake ranka. Naanah ka rasa amma ba ka rasa rayuwarka ba. Kayi hakuri Ubangiji yana tare da kai, duk wanda ka yayi nasara a rayuwarsa ka duba yadda ya faɗi. Allah ya maka albarka ni nasan yadda kake kaunar Naanah Asma'u. Don Allah koda ba zaka ji daɗi ba, ka marawa kanwarka baya ta yi biyayya ga Mijinta kai ma dan uwanka ne. Dukkansu ƴan uwanka ne, dukkansu suna buƙatarka a tare su don Allah kada haka ya janyo wata rigima ko fitina, Allah ya baka wacce ta fita."
Kifa kanshi yayi a tafin hannunsa, yana jin wani irin yanayi kamar zai yi kuka. Haka ya d'ago kai ya ce mishi. "Naanah Asma'u ta sani?" Girgiza kai Abba Babba yayi ya ce mishi. "Kada ka damu hakkina ne na fahimtar da ita, idan ma ba a gaya mata ba, ba wani abinda zai faru kawai kyaleta."
"Abba kasan tana da ciwon zuciya?" Murmushi Abba yayi ya gyad'a mishi kai, " na sani!" Tashi yayi ya ji wani kwarin gwiwa ya zo mishi. " Allah ya basu zaman lafiya da zuri'ar dayyiba.....