BAKİN ALKALAMI…….

Chapter 15

by @maidambu41

Chapter 15


Daga haka ya wuce massalancin asibitin, alwala yayi ya wuce ciki ya gabatar da sallah,ya jima sosai yana addu'a. Sannan ya wuce gidansu da yake Nasarawa din ya samu mahaifinsa. Lokacin da ya same shi a parlourn kallon Mustapha yake yana son yayi magana amma ya kyale shi domin babu amfanin sake fama mishi ciwon da yake damunsa. "Kayi hakuri!" Iya abinda ya furta kenan," girgiza kai yayi ya wuce ba tare da ya ce uffan ba. 

             Duk wanda ya kalle shi yasan yadda yake ƙoƙarin danne abinda yake ransa. Abin bude baki Abban tskiya ya kai mishi amma bai ci ba nan ya cewa Mahaifinsa ."Abba don Allah ka huta! Kada ka saka damuwana a ranka, ina lafiya kuma babu abinda zai faru in sha Allah."

      Zama Abbanshi yayi ya ce mishi." Na san halinka na san kuma ka hakura kada ka kullaci Hajiya don Allah bata da laifi, Asma'u ba rabonka ba ce!" Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo ya ce mishi. 



"Abba kada ka damu, dukkansu ƴan uwana ne." Ya furta tare da  mikewa zuwa ban daki, akwai wani abinda matukar zaka yi kuka tow zaka ji sauki amma idan ka bar shi a ranka har abada ba zai daina cimaka tuwo a ƙwarya ba. Lumshe idanu yayi kafin ya bude yana murmushin karfin hali. "Ba kome Abba!" Ya kara furtawa,  shiru Abbansa yayi yana kallon yadda ya shiga ban dakin, yana jin ya kunna ruwa, ba zai ce kuka yake ba amma yasan ai ba aiki yake ba, can sai gashi ya fito yana share hannunsa da wani karamin towel amma jikinsa rawa yaƙe. "Ko kana bukatar wani abu ne?" Girgiza kai yayi kafin ya ce. "A'a!" Ganin har lokacin bai ce komai ba,da Abbanshi da yake bakin kofar ɗakin shigowa  yayi ya rike hannunsa da yake rawa. . Tare da janyo shi jikinsa yana buga bayansa. Ajiyar zuciya yake saukewa a hankali.. "Kayi amfani da haka, ka gayawa Allah zai sauya maka da abinda yafi alkhairi." Haka yayi ta rarrashinsa. 


       Har yayi shiru sannan Abbansa ya bar shi tare da barin ɗakin, yaji haushi amma kuma ganin shi kansa Mahaifin Naanah Asma'u ba yadda ya iya, ya kai kusan karfe daya na dare yana ƙoƙarin fahimtar me yasa Adam yayiwa Mustapha haka? Wannan tambayar har gari ya waye kai har yayi sahur bai daina jin shi a ransa ba. Daga masallaci bayan sun dawo sallah asuba, ya kwanta ya huta. 


     Fitowa yayi dauke da kayanshi yana kallon bangaren Abbanshi. Shiru yayi yana jin wani irin abu a ransa. Amma ba yadda ya iya haka ya nufi kofar dakin Abbanshi ya tura a hankali sannan ya ajiye mishi takardan ya juya yayi waje. Bai shiga motar da suka zo da shi ba ya juya ya fita daga cikin gidan. 


   Lokacin da ya fita Abbanshi ya bude ido, a hankali ya mike daga kwanciyar ya nufi inda takardan yake ya dauka. 

*Abba kayi hakuri ka bawa Abba Babba hakuri na ajiye mishi sako a dakina ka bashi ayiwa Naanah Asma'u hidima,  ni zan koma Austireliya in sha Allah na isa zaka ji ni! Abba ina lafiya ba matsalar kome kace Ammy ta taya ni da addu'a kawai nake bukata na gode sosai* 

      ...... Mustapha Ladan 

 Dakin Almu ya wuce ya duba kan teburin ya ga kudi ne mai yawan gaske, daukowa yayi ya nufi dakinsa, ya ajiye wanka yayi ya shirya Tsaf, sannan ya nufi can Amarewat, a kofar gidan ya samu dan uwansa. Mika mishi hannu yayi suka gaisa. 

   "Yaya Babba." Kallonshi yayi fuskarsa babu yawo babu fallasa ya, "Naam Issufa!" Murmushin karfin hali suka yi. "Gashi inji Babanka!" Amsa yayi ya bude bakin ledar kudi ne mai yawan gaske. "Ya koma wurin aikinsa!" "Ubangiji ya tsare gabansa da bayansa!" Abba babba ya faɗa yana jin kwalla na cika mishi idanu. "Kasan me ya faru?" Girgiza kai yayi. A hankali ya shiga mishi bayanin yadda suka yi da Hajiya, wanda har ƙarshe suka fara shirin maganar Mahmoud..shafa kanshi Baban Almu yayi ya ce mishi."Allah ya kyauta!" Amma kana jin abin kasan akwai wata manufa da yasa haka ya faru.

"Rukayyah tayi har yaji, suka dawo da ita, Yaran ma basu sani ba, Uwar ce take ta borinta."

"Kada ka damu da borinta, kuma kada ka.juya mata baya a wannan lokacin, domin tana bukatar rarrashi ne sosai." 

"In Sha Allah!"


   Sun jima suna hira har Abba Babba ya gaya mishi zasu tafi asibiti ne, shima ya gaya mishi unguwa zai tafi sai an jima zai leka asibitin.

        Sallama suka yi Abba Babba ya shiga cikin gidan, shima ya wuce inda zai tafi 

***

Tunda  Abba babba ya shiga cikin gidan shi kanshi a dame yake domin ya rasa yadda zai yi da Maamah. Yana tsaye a kofar dakinta da yake rufe ya buga kofar tayi banza da shi. Lekowa Naanah Asma'u tayi tana kallonshi. "Mamana akwai wani abu ne?" Girgiza kai tayi, kamar wata yarinya yar karama. "To  me kike bukata!" "Babu!" Ta furta a hankali, "tow je ki kwanta!" Gyada kai tayi tana me rufe kofar dakinsu jikinta a mace. "Maman Maryama bude min mana!" Budewa tayi tana kallonshi tun lokacin da ya fara magana da Naanah Asma'u ta taso zuwa bakin kofar tana saurarensu, wani irin kallo tayi mishi tana faɗin. "Wallahi kada ka sake ka gaya mata wannan maganar ku karasa min yarinya don na rantse da Allah ba zan kyale ku ba na fada maka" 

     "Ki yi hakuri ki zo muje asibitin." Shiru tayi kamar bata ji shi, ita da Hajiya ai har abada ba zata taɓa yarda ta mata biyayya kamar da ba, asalin haushin Hajiya da Yaranta take ji domin tasan munafukai sune suka shirya kome,  juyawa tayi ta sako hijabi, ta fito tana kallon kofar dakin Hasiya wacce bata gidan tsawon kwanaki hudu kenan,duk da tana son tambayar ina taje amma sanin ba shi ne a gabanta ba yasa ta dauke kai, kallonshi tayi kamar zata yi magana sai ta fasa to me zata ce mishi? Bayan tana ji tana gani sun binneta da ranta, bin bayanshi tayi suka bar gidan.   Har wurin adadaita sawun da ya kira, suka shiga suna tafiya, yadda zaka fahimci yanayin fuskarta zaka kalla kasan ranta a ɓace yake abinda ta ɓoye na tsawon shekaru yau shine akan fuskarta. A bakin asibitin suka hadu da Adam wanda zai koma gida, abinda bai taɓa yi ba tsawon rayuwarsa yau shi yayi wato ya durkusa ya gaida wani cabɗijam amma yana ganin Maamah ya durkusa har kasa ya gaishe cikin girmamawa. Ita kanta abin ya zo mata sabon lamari, cikin wani irin yanayi mara daɗi ta amsa tare da dauke kai, har suka bar wurin yana durkushe bai mike ba, juyawa tayi ta ga har lokacin yana durkushe. Mai da hankalinta tayi ta cigaba da tafiya sai da ya ga tafiyarsu.. sannan ya mikewa yana me karkade jikinsa. Ba zai daina bawa Maamah wannan girman ba har ya koma ga Allah. Matuqar Maamah zata amshi aurensa da Yarta.. 


              Lokacin da suka shiga Yaran Hajiya, Zaitunah da Turai har da Atikah kallon Maamah suke irin kallon renin hankali da niman magana itama ai ba girmanta suka yi ba. Tunda tayi sallama, bata kuma musu magana ba. Sai da Abba Babba ya kalle ta,  dauke kai tayi ai kuwa Hajiya ta ce mata. "Nasan da Uwarki ce ba zaki zo ki zuba mata ido ba kina kallonta kerere ba. Naanah Asma'u jikata ce ina da haqqin na yi yadda naso da jikokita. Ke baki isa ba wallahi." Turo kofar yayi dama jikinsa ya bashi wannan fushi na Maamah zai iya haifar da matsala. "Ke har kin isa ki hana ikon Allah ne ba a hakuri na hakura da ke? Ke har kin isa ki nuna min iko da Naanah Asma'u? Aure ne na hada babu wanda ya isa hanawa sai Allah don na dauki yarinyar da shi kanshi ba sonta yake ba" "Hajiya ba haka ake ba, ba zai yiwu kayiwa mutum laifi kuma ka dawo ka fishi baki ba. Hajiya Yarta ce fa duk inda aka. shiga tafi kowa gaskiya, kin ga kuwa fada da tashin hankali ba namu ba ne, wannan rashin adalci ne Hajiya fisabiilillahi Atikah kuna ganin tana irin wannan abin baku hanata ba wannan wacce irin rayuwa ce?." 

               Juyawa yayi ya sunkuyar da kai ya ce mata. "Maamah!" Dakatar da shi tayi. "Kul ka kara kiran sunana, ba dai rayuwarta kake bukata ba ga ta can idan ka gama sai ka dawo min da ita ai kasan baka da nagarta da zaka zauna da wankakiyyar Yarinya irin Naanah Asma'u, ba gori nake ba, amma ai kasan duk abu me daraja da muhimmanci ana nima masa hadi ne mai kyau. Kai kanka baka da wannan Quality din da nake hangowa,  ai shikenan idan ta zama mushe ka dawo min da ita ina buƙatar ta!" Daga haka ta fita tana share hawayen da yake zuba mata.  Allah ya gani bai da wata manufa na auren Naanah Asma'u, sai akan ciwonta yana jin kuma yana tuna lokacin da ta fara ciwon, tunda likita ya kira ya gaya mishi, zuciyar bugawa tayi yasa shi tsayawa akan lamarinta, ba zai manta ranar da kurma ya fasa masa kai ba, a ranar Hajiya ta mata wannan dukar da ta rike kirjinta tana haki. Sanadinsa ta sami ciwon kuma in sha Allah shine maganin ciwonta.


      Har bakin gate din asibitin tafito tare da niman wuri ta zauna tana kuka,duk wanda ya zo ya ganta sai ya kalleta, fitowar Abba babba da Uban kowa yasata mikewa tana me share hawayen da yake zuba mata, "Maamah muje na kai ku gida!" Cikin wani irin fushi ya ce mishi. "Kana tsammanin Naanah Asma'u zata sayu da kyautatawa da kake yi ne? Ba da gwanjo ba ce, Y'ace me yanci, duk adalcin da nayi maka shine zaka saka min da wannan abin ko? 

Amma na rantse da Allah ka cutar min da Yarinyar da ba ruwanta ba zan taɓa yafe maka ba, wallahi ba zan taɓa yafe maka ba, matukar wani abu ya same ta!"  


Nan ya ce musu to su shiga ya ajiye su a gida shima can zai je, nan tayi tsalle ta rantse ba zata shiga motar Uban kowa ba. Kiri-kiri Maamah take ƙyamarshi. "Adam ka yi hakuri bari na tsare Adaidaita! " Shi ya tsare musu abin hawan, suka shiga cikin abin hawan,  zai biya ta ce mishi." Idan ka biya zan sauka!" Daga haka ya mai da kudin ya zuba musu ido yana kallon Napep din har ya bar bakin asibitin.." Me yasa kike haka?" " Tsawon shekaru talatin da wani abu ina fuskantar matsaloli da tashin hankali da ahalinka ka taɓa ganin nayi wani abu da bai dace ba?, duk wannan bai isa ba? Me yarinyar nan tayi mishi? Kasan yadda ya azabtar da ita kuwa? Kasan yadda ya konata da sigari kuwa? Kasan tun ranar da Hajiya ta bugawa Naanah Asma'u kafa a kirji tun daga ta hadu da wannan laluran kama san yadda take tsoronshi kuwa?" Cikin sheshekar kuka take magana ta kalli yadda ya kafe ta da idanu.  "Me yasa bata yiwa sauran Yaran yan uwanka haka? Saboda su ai iyayensu na da kudi ko? Saboda kai baka da kuɗi, eh kai talaka ne kai din dai baka da shi sai dai su baka kudin kara aure. Ka musu bauta su baka lada da haka? Yarinyar da kowa ya ganta yasan bata da lafiya, ita ka cefenar saboda son zuciya. "


Ta fada tana kuka, tunda ta fara fadar bai hana ta ba kuma bai amsa mata ba. Ya ji daɗin yadda ta fadi abinda yake ranta. Lokacin da suka iso kofar gidan, suka sauka haka ta wuce cikin gidan ta samu Yaran suna aikin gida yadda take kuka yasa duk suka mike suna kallonta. Dakinta ta wuce tana kuka sosai irin kuka me cin rai din nan, aikin da suka kasa cigaba da yi kenan suna tsaya a tsakar gidan Naanah Asma'u da ta fito daga cikin dakinsu ta tsaya tana kallon Abbansu. Kukan da Maamah take ba na kome ba ne, sai dai yadda take ji take gani zata rasa Yarta. Nufo Naanah Asma'u Abba yayi suka shiga cikin dakinsu. "Ina takardun asibitinki!" Zare fararen idanunta tayi tana kallon Abbansu bakinta yana rawa. "Ba tambayarki nake ba." Yadda ya daka mata tsawa sai da ita kanta Maamah ta fito tana fadin."me kake ƙoƙarin yi?" Bai saurareta ba ya mai da hankali akan yarinyar, domin  yadda Naanah Asma'u ta rikice tare da juyi kamar wacce ake juyata amma ta rasa me zata dauko mishi, "magana nake da ke sai na zane ki!" Juyawa tayi na karshe a gaban kayanta ta shiga buɗe jakar jikinta yana rawa, asalin rawar da jikinta yake hatta kashin jikinta amsawa yake.  Cikinta kuwa ya wani irin hautsinewa. A hankali ta fara ciro takardun tana ajiyewa har ta ciro maganinta da take sha. Daukar takardun yayi ya ce mata." Idan ita Maamah baki gaya mata ni me yasa ba zaki gaya min ba?" Hawaye ne ya Zubo mata. "Abba!" Yadda ta kira sunansa yasa shi isa kusa da ita, ya zaunar da ita yayi a bakin gadon, yana kallon yadda take kuka. Rike hannunta yayi ya ce mata." Na san kina tsoron yadda zamu ji ne ko? Kin manta Allah da ya jarabce ki da shi yana sane da mu ne? Me yasa kika yi shiru bayan kin san me yake damunki."

    "Kin san halin da muka shiga sanadin haka?" Girgiza kai tayi, a hankali ya mike tare da cewa. " Babu kyau kin ji ko!" " In sha Allah."  Daga haka ya bar dakin, Maamah zuwa tayi tare da zama a gefenta, " me ya faru?" Daura kanta a kafadar Maamah tana shashekar kuka.  "Kiyi hakuri Maamah!" Ta furta a sanyayye, shafa kanta tayi. Ganin yadda har lokacin Maamah kuka take sauran Yaran kannen ama sai suka hadu suka cigaba da kuka, pieceful home ya koma sad home,  kowa a cikin gidan baya cikin walwala. 


     Bayan laasar Uban kowa ya kawo cefane mai kyau, yana tsaye a tsakar gidan. Mairoh ta fito ta amsa tana kallon kasa. " An jima Hajiya zata dawo shine Abba babba ya ce na kawo mata."

 " Tow! " Ta shiga da shi cikin parlourn. Ya jima a tsakar gidan yana fatan ko da Maamah zata fito ya bata hakuri amma bata fito ba. Haka ya bar gidan. Dukkansu uku suka fito daga ciki suka fara aiki kafin karfe shida har sun gama adaidai lokacin Hajiya ta iso suna jin hayaniyar mutane a bangaren Hajiya, ɗaukar kayan abincin suka yi tare da nufar bangaren Hajiya, sai da suka yi sallama har sau uku sannan aka amsa musu, da yake Mairoh da tafi su rashin hankali dangwara kome tayi ba tare da ta ce musu cikanku ba. Khamilah ce zata yi magana ta ce mata. "Uban me zaki ce musu?" Jin haka yasa suka juya tare da barin su da mamaki domin Mairoh ta goge musu zero. 


        "Yanzu yaran nan har abin nasu ya kai haka?" Inji Hajiya Atikah, "hmm ina ganin rayuwa a hannun Rakiya da yaranta." Inji Hajiya Innah, Shiru suka yi suka sannan suka fara zuga Hajiya kada a d'aga musu kafa, aure kuwa za ayi shi babu fashi sannan ta zauna da ita anan Hajiya tana ganinsu domin kuwa idan ba haka ba zasu mallake mata Uban kowa. "Ai matsalar shi bai da alkbla yadda zan san me yake faruwa da shi domin tsaf ana bashi rubutu irin nasu na malamai an shanye shi." 


      Bayan sun gama zuga Hajiya sannan Hajiya Turai da Zaitunah suka bar gidan,  bayan Isha ya shigo ya zauna yana me ɗaukar kunu ya sha. "Hajiya ina son kunun nan ki bar min nayi sahur da shi mana." "Hmmm!" Hajiya ta furta kanta yana sunkuye, "Hajiya ko har yanzu baki da lafiyar ne?" Ya kuma tambayar a matuƙar tsorace. "Hajiya gaya min me nene?" Kuka ta fasa mishi kamar yarinya karama Atikah tana kallon yadda take kuka fa amma bata hana ta ko dakatar da ita ba. Kasa zama yayi ya tashi tsaye tare da kallonta. "Hajiya yi min magana!" Wani irin nishi take tare da haki. Dawowa gabanta yayi tare da tsugunawa yana riƙe hannunta, "Hajiya menene?" Ya kuma tambayarta, Cikin shashekar da ta fice kukan tare da wani irin gagarumin nishi me nauyin gaske ta kara sautin kuka ta ce mishi. "Na ga yanzu hankalinka ya koma kan Rakiya da Yaranta, yadda suka juya hankalin baffanka haka zasu juya min hankalinka." Ta furta tana kuka, har cikin ransa yake jin kukan nata, Hajiya ita ce mace ta biyu bayan Mahaifiyarsa, sai Maamah ta uku. Rike hannun Hajiya yayi gam ya ce mata." Me kike so to?" " Babu sassauci a tsakaninku. Aure kuma idan har ka yarda da ni, ka nisanta kanka da ita domin akwai abinda dole sai anyi abu a kai domin wallahi zan rasaka!" Ta furta tana shashekar kuka da wani gunji. "Me ya faru kuma?" "Anan zaku zauna da ita ba zaka ajiye ta a wani wuri ba." Gyada kai yayi yana nuna mata alamar ya amince. "Ka yi min alƙawarin ba zaka taɓa." Shiru tayi tana jin nauyin abinda zata fada kawai sai ta fashe da kuka.  Shi ba yaro bane da zaa ce bai fahimci sakon Hajiya ba. Tana nufin ya ajiye Naanah Asma'u. Dama shi ai ba yana son auren don wani abu ba, kawai yana son yayi wani aiki ne na musamman. Don haka ya lallabata Hajiya zai tsaya ne ayi mata aikin zuciya yadda zata rayu. Amma batun wani tarayya Allah ya tuba me zan dauka a jikin Naanah Asma'u, ga manyan mata can da suke biyo shi tun daga wasu nisan duniya. Shi mace bata cikin tsarinsa da aurenta zai iya mata jinya don idan ya ce zai yi ba yarda za ayi ba. Idanun kowa na kanshi. Sannan a gefe guda ya raba ta da Mustapha da Mahmoud don ya nuna musu yana da ƙarfin da zai iya raba su. Ya kuma tabbatar musu shi kadangaren bakin tulu ne a karshi a kar tulu a bar shi ya b'ata ruwa.


      Lallaba Hajiya yayi tare da mata alkawarin ba zai taɓa kula Naanah Asma'u ba, har sai idan Hajiya ce ta bukaci haka. Cikin kuka da rikicin son zuciya ta ce." Saidai idan zaka kara wani auren!!" Nan ya kalle ta ya ce mata." Hajiya aure dai kuma? Kin ga ni na fasa Auren nan kawai gara na kai kaina wurin hukuma su kama ni da aikata laifukan taaddanci"  Jin yadda zai ɓallo mata August yasa Hajiya ta sake wata irin kuka tana faɗin. " Shi kenan ka kula da kanka! Amma ka sani zan barka ka auri yarinyar ne kawai amma ba wai don ina so ba!" " Shi kenan na aji!" "Batun tafiya Niamey karatu ya ƙare!" "Hajiya!" Ya kira sunanta a dake. "So kike bakin ciki ya kashe Maamah? An yiwa yarta dole karatun da zata taimakawa kanta da al'ummar kasan zaki ce a hanata? Hajiya waye yake zuga ki? Ki gaya min domin wata sati zamu tafi Umara!" "Ɗan albarka babu me zugani!"

        "Tow daga yau babu ruwanki da Naanah Asma'u idan na ji wani abu wallahi duk abinda kika kafa min sharadinsa sai na rusa su." Ya fada tana kallon yadda take share hawayen da yake Zubo mata dama kuma ai fake ne.


       Dakyar ya samu ta kwanta bayan ta sha magani, bai ko kalli inda Goggonsa take ba ya fita. Yana barin ɗakin Hajiya ta mike tare da cewa. "Gaya min Auta ya zan yi da Uban kowa akan wannan al'amarin?" Da yake tana jin zafin damar da ta rasa ita da Yarta, yadda tayiwa Mufidah tanadin Uban kowa Allah kaɗai ya sani. "Hajiya sai dai mu nima mishi taimako ai kin san Rakiya ba haka ta bar Yaya Babba ba. Shima kada abin da ya faru da Yaya Babba ya faru da shi, tunda kin ga ga farin kafa, ga talauci da yake bin jininsu. Amma sai yadda kika ce?" 


      Hajiya Atikah ta manta ta haifi Yara mata, kawai rasa auren Uban kowa da Yarta tayi yana mata ciwo. Don haka ta zuga Hajiya sosai. A daren Hajiya ta nuna mata wurin ajiyarta akan za a tafi ayi rokon Allah yadda, ko anyi auren su tsani juna na, bayan sahur da asuban Hajiya Atikah ta wuce gidan Malaminta wanda tunda ta isa ta ga mata sun sha layi kamar ba watan azumi ba. Tana isa da yake akwai facemask a fuskarta. Tana zaune tun asuba har karfe sha biyu na rana. Ta shiga cikin malamin ya gyara murya tare da gyara zaman rawanin kansa yace mata.." Aure ai tun wancan lokacin na gaya miki yarki ba zata aure shi ba. Ita wannan yarinyar nan taurari uku ne a tare da ita sun sakata a tsakiyarsu. Kuma ban da Allah babu wanda ya isa dakatar da ƙaddaransu. Tun wancan lokacin nace miki Yarki ko sauran Yaran dangin basu da nasarar da zata hada da Yaran nan maza, Yaran dan uwanku shine ya haifa musu nasarar da zasu yi. Yanzu kin zo a haɗa tsana mai ƙarfi da kiyayya."  Murmushi yayi ya ce mata. "Yaron nan ba zai taɓa tsanarta ba, ita dai da take nakashe zaku iya nasarar cusa mata kinsa. Amma idan kuka ja hatta ni wutar da yake tartsasi a tsakaninsu tabbas zai kona kowa." 


       "Ya zan yi Malam?" Murmushi yayi ya ce mata. "Ita yarinyar ai gawa ce tafe, idan kuka yi hakuri ko ta mutu ko ta rayu amma babu kome a tsakaninsu sai ikon Allah da buwayarsa. " Zufa ne ya karyo mata tana kallon Malam ta ce mishi." Ba wani hanya ne?" "Akwai hanya yarinyar ki tabbatar kin bata wannan ta ci."

      "In Sha Allah, idan ta ganshi zata na razana da firgita wanda shi zai  saka ya  rabuwa da ita." Ajiye mishi kudi tayi zata fita ya ce mata." Ina aiki akan mutane amma ban taɓa ganin aikin dayake hade da kauna mai tarin yawan gaske sai wannan, ƙaddara mai ƙarfi zata girgiza ahalinku, mamamkon ƙaddara hade da guguwar ƙaddara zata ruguza, amma ban taɓa jin ko tausayin al'amari irin wannan ba. Sai yanzu na tuna mafarkin da nayi, ki sani shi kamar mala'ikan kariya yake a gare ta. Ba zai sare ba ba zai juya ba kuma ba zai gaza ba sai ya bata duk wani abinda ta rasa kada ki ji a ranki zaki yi nasara amma kada ki saka faduwa a ranki." Mika mata hannu yayi ta kalle shi cikin rashin fahimta ta ce mishi. "Me kake nufi!" "Bani maganin!" "Na baka kuma Malam?" "Bani zan baki wani ne" ya fada mata, ba musu ta miƙa mishi, zuwa maganin yayi a cikin ruwa ya ce mata "zo ki ga ni!"  Zuwa tayi ta leka ƙwaryar. "Zaki iya dakatar da wannan haɗarin?" Girgiza kai tayi,  ya kara da cewa.." zaki iya hana wannan ruwan zuba? "  Girgiza kai tayi, murmushi yayi ya ce mata." Kyale musu ƙaddaransu domin akanta zai iya rabuwa da kowa a cikin waɗanda zai rabu da su har da wacce tayi renonshi. Magani ko wani tsafi, sihiri ko bokanci ba zai yi tasiri ba. Ki je ki bawa Allah zabi zai baki mamaki idan nayi wannan aikin ƙaddaransu ma kawai ta ishe ni, idan ki zaga nijar, kamaru, chad, kwatano, Nigeria,india, china, babu wanda zai dakatar da faruwar kome domin ƙaddara ce a tsakaninsu ƙaddara ce ta haɗa ita kuma zata yi ikonta da shari'arta. Shine kaddaranta ita ce Ƙaddaranshi. Sauran taurarin ita ce ƙaddaransu."

" Gobe ne daurin auren!" Ta fada kamar tayi kuka, 

"Babu abinda za'a fasa!" Ya fada mata, 

     Daga haka ya dawo mata da kudinta, haka ta fita jiki a mace, tana jin wani irin yanayi kamar hawaye ne ya shiga zuba mata..ya fito daga cikin dakin ya ce mata. "Ki godewa Allah da ya zare ki."


Koda ta dawo ta samu Yayunta mata sun zo , amma bata gaya musu kome ba haka suka zauna har aka sha ruwa. A daren Abba karami ya tawo da alawa, goro da chew gum. Ya tafi har gidan Abba tsakiya, ya same shi da yake bai da kunya gaya mishi buƙatar da yazo da shi, bai yi musu ba kawai ya bar kowa a inda yake ne. Suna dawo gida suka tattauna har da Abba Babba. 


     Washe gari juma'a gidan ya cika makil, babu wanda ya sani a cikin Yaran Maamah, iya Maamah da take ta kunshe kanta a daki tana kuka. Haka Abba yayi ta zirga-zirga tsakanin cikin gidanshi da gidan Hajiya,  wani babban tashin hankali da ya rasa yadda zai iya furtawa shine yadda yan uwansa suka tare a jikin Harisu mahaifin Adam. Karfe biyu da rabi agogon kamaru Nijar Nigeria, karfe uku agogon Ghana da chadi, aka shaida Auren Naanah Asma'u Muhammad Mustapha Ladan tare da Angonta Adamu Harisu Mustapha Ladan. Auren da ya samu halartar manyan mutane musamman waɗanda suke mu'amala da El Mayor ciki da wajen nijar, sauran jahohin Nijar mutane dayawa sun samu halartar ɗaurin auren. 


           Shelar ɗaurin auren da ya daki dodon kunnenta, ta fito tana kallon Maamah da ta juya zata koma dakinta. A yadda lamarin daurin auren ya zo ba zato babu shiri babu tsammani haka aka daura auren. Kara kallon kofar dakin Maamah tayi, ta juya tana kallon yan uwanta jikinta yana rawa. "Khamiee!" Ta furta jikinta yana wani irin rawa. Nufar Khamilah tayi zata bude bakinta ta ji wata zabiya ta rangwada guɗa da karfi wanda yasa gidan ya amsa bakiɗaya. "Allah ya bada zaman lafiya da kazantar daki, Allah yayi auren Uban kowa da Asma'u!" Dafe kirjinta tayi da karfi tare da jan wani irin numfashi da karfi ta zube a kasa sumammiya......