SOYAYYAR ZUCI

Chapter 39&40

by @deeyamerh10

💖💖 SOYAYYAR ZUCI💖💖
(Love and Romantic story)
                  Written 
                      By
               Deeyamerh
07070647236
Page 39&40
Hanya suka kama inda Suke ta sharara gudu domin so suke kafin 9 na dare yayi su iya dan bazasu sami Jirgiba da shi suka hau.
Ko wacce mota shiru ne yake biyo baya domin kowa Allah Allah yake sukai da ita zasu ga AMMEY.
Suhaima ta jingina kanta da gilashin mota, tana kallon duhun da ke waje,duk da gajiyar da ke jikinta, ba ta iya rufe ido ba,domin bata taɓa yin tafiya me nisa irin wannan ba,gani take kamar idan ta rufe ido zata sun koma bayane.
A zuciyarta abu ɗaya kawai take maimaitawa sunan,Ammey ji take kamar tayi tsuntsuwa taje inda take.
Bayan kusan awa biyu da tafiya, Fatima ta juyo a hankali ta kalli Suhaima,tace"Ke ba za ki yi bacci ba?”
Suhaima ta girgiza kai "taya zan iya wani bacci AMMEY da ake magana ai ko karfe nawa zamu kai ido na biyu inshallah.
"Dan Allah karkisa Damuwa a ranki inshallah yau zamu ga AMMEY taga yadda yan matanta suka kara girma har ma da surukinta a gefe" takarashe zance tana dariya.shekaru biyu kenan ban san inda take ba, Yanzu Allah ya nufa na sani Ai Alhmdullah
Tana buɗe baki zatai magana kawai taji muryarsa cikin kunnanta
"Wife Ki dogara da Allah. Komai zai yi kyau,Bakaramin al'ajabi nashiga da naga tabbas Mahaifiyarki domin duk zuwan da nake Kano Allah bai taba hada da ita ba,shiysa ban ganeta ba Amma wani ikon Allah haka kawai naji ina sonta ga kunyarta da nake ji kamar Ta surukai Ashe kuwa Ammeyn tawace da gaske"
murmushi tai a hankali tana kallonsa dan batasan da me zata saka mishi domin ta silarsa zataga Ammey,ita kuwa ko dan halarcin da yayi mata zata soshi,zata koyawa zuciyarta sonshi.
________
Da misalin 11:30 na dare, suka tsaya a wani wuri domin suyi Sallah a huta kuma a cigaba da tafiya.
Kowa ya kama dakin da zai sallah ya huta dan har order abinci yasa aka kawo musu sosai suke jin dadin kasancewar SH a cikin su,domin yana basu girmansu sosai.
A kuma wanna lokacin suma su Baffa suke sun shigo Amma zasu tsaya a wani ƙaramin Hotal suyi Sallah,dan su jirki suka biyo,nan Abba yake sanar da su,suka zasu tsaya suyi Sallah ne kafin su kuma hanya.
Guduwa fatima tayi dakin su mama dan taga alamun SH ba kunyace da shi sai wani ruko Matarsa yake garata ta bashi waje.
Ai yana ganin ta fita yakuwa cafkiekayarsa dan wallahi Indai zai ringa ganinta kusa da shi to ba sauran zama bare kuma zancen kame kai tab.
Kallonsa tayi da shagwaba tace"SH kabari muyi sallah kada su Abba su jiramu kaji"a yadda tai maganar dole ya susuce.cikin sauri yace mata'Wife ki adanamun wanna shagwabar sai dagani sai ke a dakin Amma kina mun anan ai kashe Ni zakiyi ko kisa nayi abun kunya dan Allah sai dai su Abba suyi gaba Amma dai ke rikicin da kika taso tofa sai in kwantar da shi".
ai kuwa taga alamu dan SH irin mazan nan da Abu kadai yake sasu suji suna cikin Bukatuwa itako taga ta kanta,dan a dan yinin nan da sukai tagane hakan ina da kuma anbarau daga ita sai shi ai takade har buzunta.
A nutsu suka gama komai sannan aka kara kama hanya.tafiyar da bazasu kara tsayawa sai sun shiga jikin JEMETA.
_____________
Lokacin da agogo ya nuna 2:00 dai dai na dare a wannan lokacin hancin motarsu SH ta yanka zuwa cikin unguwar DOUGIREI,unguwa ce ta dau kudi da ke cikin garin Yola.
Suna isa tankame man gidan ba wanda bai kalla ba domin ba sai an ce maka gidan namsu abin duniya bane.
Da gudu get man din yazo ya wangale masu Get din domin yari da yasan za su iso a wanna lokacin,cin na kan motocin sukai inda hasken fitilo ke haska gidan wanda yakara masa kyau tamkar ranace sbd watar haske.
 Jin tsayiwar motar yasa ta ajiyar zuciya da ta ji kamar shekaru biyu na kewar Ammey sai yanzu ta fada daga taukare mata kirji da tayi.
 juyo yayi ya kalli Suhaima"Mun iso.”
Ta kasa motsi domin jita ke kamar an danneta,yau idanuwanta zasuyi tuzali da mahaifiyarta wanda basu san dadin barinta gidan ba,wasu Hawaye masu dumi ne suka zubo mata,ta buɗe ƙofar motar a hankali,Kafafunta suka taka ƙasa,duk da bata san ya kan gidan yake Amma tana da tabbas idan tayi magana da karfi zasu ji,kuma sunsan da zuwan gidan.
A can cikin gidan kuwa 
Ammey tana zaune tare da Hajjiya,Sai jin muryar Suhaima suka daga harabar gidan tana kwalawa Ammey kira.
"AMMEYY
Ammey ta ɗago kai,Wani irin yanayi ya ratsa zuciyarta,ta kasa sanin dalilin da ya sa sunan nan ya yi mata wani tasiri na daban
 Cikin sauri ta dafe kanta kafin wani gume ya wanke mata fuska kamar an watsa mata ruwa,kusan 5mins tana haka kafin taji komai ya dawo mata kanta,da sauri ta mike tsaye tana kallon hajjiya da fadin"Ina nake nan?Ina ya' ta Suhaima ina Mijina? Duk a lokaci daya take jirawa hajjiya wanna tambayar cikin murna da hamdan yaran suka fara murnar dawowa AMMEY cikin hankalinta,Ai kafin Hajjiya ta sake magana suka ji Muryar suhaima tana kara kwalla mata kira hawaye duk ya wanke mata fuska.
"AMMEYY ta kina ina? AMMEYY kizo na ganki nayi kewarki sosai take kuka Amma haka take maganar domin uwa itace mafi soyiwa a rayuwar nan,idan kana so kaga dai dai to Kabi mahaifa ka.
“Su…haima AMMEYY ta amta da sauri yana mai yin waje Allah ya tai maka bata zama na hijab duk da rashin lfyar da tayi.
A wannan lokacin ne Mahaifiya da ɗiya suna gab da haɗuwa bayan shekaru biyu bada tare.❤️‍🔥
“Ammeyyyyy!”
Kafin kowa ya iya cewa komai, Suhaima ta tafi da gudu ta rungume Meta,cikin jikinta tasa itama
“Suhaima"Muryarta ta fito a hankali.
“Ammeyyyy!”Sai kuka ya balle.
Ba kuka na farin ciki bane kaɗai a'a Kuka ne na shekaru biyu,Kukan kewar uwa,Kukan tambayar ina kika shiga?
Kukan daren da Suhaima ta kwanta tana tunanin ko za ta sake ganin mahaifiyarta.
Ammey ta rungume ta, hannuwanta suna rawa.
"Suhaima kice a gabana". Alhmdullah 
 Ammey nice ka ƙara matse ta a jikinta.
“Na yi kewarki… wallahi na yi kewarki sosai.”Ammey ta fashe da kuka.
Kaff gurun ba wanda ya iya rike kukansa duk da dare yayi amma su a gurinsu tamkar rana ce..
Fatima ta rufe bakinta da tafin hannunta tana kuka,Abba ya juya gefe, yana share hawayen da suka cika masa ido,Dady kuwa ya sunkuyar da kansa,Mama kuwa ita kukanta duk yafi nasu domin sun saba da juna sosai.
A haka a Hajjiya ta matso kusa da su da dafa kan Suhaima “Alhamdulillah"Ta maimaita“Alhamdulillah… Alhamdulillah
SH yana tsaye Bai ce komai ba,Idanunsa kawai suke kallon Ammey,Amma a wannan karon, shuɗin idanunsa sun sake yin wani irin duhu mai ban tsoro saboda tsananin fushi,Hannunsa ya dunkule,Ya kasa manta abin da ya gani a baya Matar da aka samu cikin wannan hali,Matar da ta rasa nutsuwarta,Matar da ba ta iya gane kanta ba,Matar da tsawon lokaci ana fama da ciwan da ba a fahimci dalilinsa ba.
A hankali wata nutsuwa ta shiga cikin zuciya da ruhi,a hankali AMMEYY ta dago da kanta Idawunat suka sauka akan Abba da duk damuwa tasa ya kara rame wayayi Duhu amma duk da haka gayun yanan.sakin Suhaima tayi taje gareshi ba kunya suka rungume juna duk kokarin da Abba yayi domin rike kukansa abin ya ci tura,ba wanda yace kada suyi domin yau ranar kukance dole kuwa ayi ta.
Haka AMMEYY ta rungume mama da Fatima suma,kafin su gaida ga Dady A hankali ta mai da kanta ga SH kasa hada ido sukai sai kawai tai masa murmushi wanda ya jishi har cikin jikinsa.
Haka suka dunguma sukai cikin parlon inda hajjiya tace kawa yaje ya huta idan Allah ya kai mu safiya aji duk yadda Abu suke.
Haka kuwa akai inda aka bawa Kowa dakinsa,dan su Baffa sun sai zuwa safiya zasu iso,Amma sai da yaji muryar Ammey a waya haka 'ƴa'ƴanta tun kan su ganta suke kuka.
Ba wanda ya iya barcin kirki dan Abba salloli kawai yake yana godewa Allah da ya dawo masa da Ammey lfy.ita kuwa Aikin kallonsa kawai take.konda ya idar sosai ya sake rungume kayarsa yana fada mata irin tashin hankalin da ya shiga da irin tabar da suhaima take wani gurin suyu dariya wani wajan ayi kuka.
Bangaran SH kuwa ya kasa bacci ganin suna gida daya Da Suhaima Amma tabarshi shi kadai ai sai tazo ya yararrashi kayarsa ko,ganin tunani bazai kai masa ba yasa ya meke ya ciga bangaran Hajjiyar,gashi bai san dakin da take ba,haka daga waya ya kira Nihal yace ina aka kai masa Mata ko da fada masa cewa yayi ta kai mata wayar,a gabansa ta fito ta shiga dakin suna zaune ita da Fatima suna ta hirar AMMEYY.
Sallama tamusu sannan tace"Anty gashi wai ji Boss zai miki magana,baki sake take kallonta domin ita bata san wani Boss ,dariya tayi tace to Yaya SH nake nufi sai a lokacin tai murmushi ta karba duk abinda ake yanajin su.
Cikin nutuwar da tasamu tace masa"ummm, "Please ina parlon Hajjiya fito ki karbi sako".bata kawo komai ta ce masa to.
Yana Ganin fituwar ta ya bita da kallon dan da alama ko wanka batai bare rama sallar da take kanta.
Tana karasuwa tace masa"gani.
"Eh na ganki muje part Dina kikarba"
SH me makon ka tahu dashi dan Allah Ni komeye ma na gode fa,iya farincikin da kasani a yau wllh ngd.
"Oh da gaske "ya fada yana mata kallon kasan idon da take ganewa idan yana ji da fitina.
Cikin sauri tai ƙoƙarin juya Amma yasa hannu ya dauketa kamar baby yayi waje da ita,duk abinda suke Fatima da sister dinsa suna kallon suna shan dariya.
Bai dire da ita ko ina ba sai cikin Toilet ya sakar mata ruwan dumi a kai,kallons tayi kamar zatai kuka"yanzu wani kaya zan sa dan Allah da kaji kamin wanna"?wanna duk ba abin damuwa bane gidan mijinki jike dan haka bazaki rasa kaya ba".to naji fita nayi wanka kaji Beb.
Murmushi yayi wato shi zata yaudara har da ce masa Beb ko to bari tagani,kayan jikinsa ya fara cirewa a hankali ai ganin abinda yake shirin yi yasa ya juya masa baya da sauri.
Yana gama cirewa yashigo cikin Shower din,duk yadda ta noke kada ya cire mata kaya duk a banza dan sai da ya mai da ita kamar yadda yake kafin yara masu wanka.
Sosai wankan yaja lokaci dan tabe tabensa kawai yake yi da sunan wai wanka ake Meta,gaba daya ya dagula musu lissafi karahe sungumarta yayi sai kan Bed dan wallahi yayi kokari tun a toilet bai nuna zilamarsa ba.
Duk yadda taso daurewa sai da tayi masa kuka dan Abin nashi na sauki,kamar kayan wanki haka yake cakuda,da magiya ta hadi ya barta tai wani wankan,ko da tafito ya ajiye mata kayan da zata,batai ma maki ba tunda yana da kanne mata sai ta kowa fita yayi yakarbo mata,duk sallolin sai da tayi kafin ta haɗa da nafila domin godiya ga Allah bisa wannan ni'imar da yayi musu.
Haka tanaji tana gani yasa a gaba sai da sukai raka'a biyu wajan neman Allah yasa musu zaman lafiya a cikin Auran su.haka ya dafa kanta wajen kwararo addu'ar اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ
Allahumma innī as’aluka khayrahā, wa khayra mā jabaltahā ‘alayhi, wa a‘ūdhu bika min sharrihā, wa sharri mā jabaltahā ‘alayhi.
Sosai tasha addu'o'i har abin mamaki ya bata ashe haka yake da ilimi abin sai ya sake burgeta.
Har 4 idonsu biyu ta hanata koma,da gifina kala kala karshe zuba masa ido kawai tai dan gaba daya ya kure mata manejin kai.