9-10
A Cikin ɗakin tiyatar, Doctor Moneer ya tsaya yana kallon Jameelu da ke kwance a kan gadon tiyata, yayin da amintattun ma'aikatansa suka kewaye shi suna shirye-shiryen aikin da zai fara. A matsayinsa na babban likita da ake girmamawa sosai a asibitin, Moneer yana da cikakken iko a kan sashen, kuma tun kafin a fara aikin ya bayar da umarnin cewa babu wani likita ko ma'aikacin asibiti da zai shiga ɗakin ba tare da izininsa ba.
Wasu daga cikin likitocin da suka ji cewa za a yi wa Jameelu aiki sun so su shiga domin su taimaka, amma Moneer ya dakatar da su kai tsaye, yana mai cewa aikin yana ƙarƙashin kulawarsa ne kuma shi da tawagarsa ne kawai za su gudanar da shi.
“Ba wanda zai shiga cikin ɗakin har sai na ba da umarni,” ya faɗa cikin tsayayyen murya dake nuna ba wasa.
Daya daga cikin likitocin ya kalle shi cikin mamaki yace.“Doctor Moneer, amma wannan aiki ne mai muhimmanci, ba zai fi kyau a samu ƙarin likitociba da zasu taimaka—”
Moneer ya katse shi.Da cewa“Na san abin da nake yi.Dan haka Ku bar komai a hannuna.Tunda de kunsan ba wai ban iya bane”
Saboda matsayinsa da irin mutuncin da yake da shi a asibitinne yasa, babu wanda ya sake ƙalubalantar umarnin nasa.
Bayan fitar ragowar likitocinne Ƙofar ɗakin tiyatar ta rufe.A ciki kuwa, Moneer da amintattun ma'aikatansane suka fara aikin.
Aisha tana can wajen emergency tana jirai, ba tare da ta san cewa a wannan lokacin mijinta yana cikin wani aiki mai haɗari ba.
A cikin ɗakin tiyatar, aikin ya ci gaba.Wanda Daga ƙarshe, an cire wa Jameelu ƙoda guda ɗaya.Amma bayan aikin, maimakon yanayinsa ya fara inganta, sai matsaloli suka fara bayyana, kuma jikinsa ya fara nuna alamun cewa ba ya samun sauƙin da ake tsammani.
Moneer ya ba da umarnin a ci gaba da ƙoƙarin cetonsa, amma yanayin Jameelu ya ƙara tsananta sakamakon yayin gudanar da aykin moneer ya cire ƙodarne ba tare da bin matakan da suka daceba.
A ƙarshe de, duk ƙoƙarin da aka yi bai yi nasara ba.Domin jikin jamilu ya kasa jurewa wanda a ƙarshe de Jameelu ya rasu.
Moneer ya tsaya na ɗan lokaci yana kallon sa, sannan ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi kafin ya cire safar hannu ya juya ya fita daga ɗakin.Bayan yasa an rufe jamilun da zani
Aisha kuwa tana can zaune a wajen emergency tana jiran labari me daɗi,duk da bugun zuciyarta daya sauya hakan besa ta karaya ba.
Shiyasa Da ta gan shi yana fitowa, nan take ta miƙe ta nufe shi.
“Doctor Moneer, ina Jameelun,ya samu sauƙin?”
Moneer ya tsaya a gabanta, ya kalle ta, amma ya kasa furta kalmar data wuce.
“Ki yi haƙuri, Aisha…”
Ay Da ta ji haka, sai jikinta ya yi sanyi.Tace a tsorace
“Me ya faru kake bani haƙuri?”
“Mun yi iya ƙoƙarinmu…”
“A'a!”cewar aisha tana toshe kunnunwanta da hannuntaTa fara girgiza kai, hawayen da suka cika idanunta suka fara zarya tana faɗin
“banason jin komai moneer,kawai Ka cece shi, Moneer! Don Allah ka cece shi!”ta faɗi cikin kuka me taɓa zuciya
Moneer ya kasa kallon idanunta yace
“Aisha, Jameelu ya…”
“Kar ka cemin jameelu ya mutu!”cewar aisha cikin wani ƙarajiTa fashe da kuka, tana ja da baya hannunta kan cikinta,sakamakon,wani irin ciwo mai ƙarfi da takeji cikin na mata
"jameelu ya rasu aisha sede mu duka mu taru muyi haƙuri"ya faɗi wasu hawayen munafunci na biyo idanunsa.
Durƙushewa tayi agurin jikina na rawa,
Moneer ya lura da canjin yanayinta nan take.Ya isa gabanta yana faɗin
“Aisha ki natsu,kinga ba ke kaɗai bace?”
Ta riƙe cikinta tana numfashi da wahala tana cije bakinta.
“Moneer… cikina…”kawai ta iya furtawa kan yayi wani yunƙuri kawai Sai ta fara zubar da jini.
Da sauri moneer ya riƙeta yana ƙwalawa nurses kira agigice,Nan take ma'aikatan jinya suka kawo gado suka ɗauke ta zuwa emergency.Moneer ya bi su da sauri.