ZALLAR SHA'AWA...

11-12

by @zahrasurbajo

Bayan ya duddubata ne ya fahimci ba wai kawai Aisha da take fama da mummunan tashin hankali ba ne take cikin haɗarin iya rasa rayuwarta, har da jaririn da ke cikinta shima yana cikin haɗari.Shiyasa ya yanke shawarar y mata cs
“Ku shirya ɗakin CS yanzu!” ya bada umarni.
Wasu daga cikin likitocinne suka sake shigowa domin su taimaka, amma Moneer ya dakatar da su.
“Ku tsaya a waje. Zan gudanar da aikin.Family nane”ya basu amsa
Nan da nan kuwa Aikin ya fara.Bayan ɗan lokaci, aka ji kukan jariri na tashi cikin ɗakin.Ya ciro mata yarinya kyakkyawa sosai, wadda kamanninta sosai da mahaifinta Jameelu.
Moneer ya kalli jaririyar na ɗan lokaci, sannan ya ba da umarnin a kula da ita.

Aisha kuwa har yanzu tana cikin dogon suma.ta san cewa mijinta ya mutu amma.Ba ta san cewa ta haifi ɗiyarta me kama dashi ba.Ba ta san cewa an yi mata CS ba tanade kwance ne rai a hannun Allah monneer na kulawa da ita da dukkan ƙoƙarinsa..
A gefe guda kuma, aka kai gawar Jameelu wani ɗaki na musamman domin adana gawarwaki,dan a jira Aisha ta farfaɗo, domin  a ba ta damar yin sallama da mijinta, sannan a tambaye ta wanda ya kamata a kira daga cikin danginsa domin yi masa janaiza..
Moneer ya tsaya shi kaɗai a bakin ƙofar ɗakin yana kallon gawar Jameelu dake kwance zaa turashi cikin hidan sanyi,
A wannan lokacin ne nauyin abin da ya faru ya fara sauka a zuciyarsa.Amma daya tuno mutuwar jamiluce zata bashi damar mallakar aishane yasa komai yabar zuciyarsa yasa hannu ya tura gawar cikinn gurin sanyin yana murmushi.

Kwanaki bakwai suka shuɗe tun daga ranar da aka yimata cs,take kwance bata farkaba a cikin waɗannan kwanaki bakwai data kasance a kwance a kan gadon asibiti, jikinta yana karɓar kulawar ma’aikatan da Moneer ya ɗora wa alhakin kula da ita, yayin da shi kuma yake yawan zama kusa da ita fiye da yadda mutum zai yi tsammani zeyi dan tabbatar da cewa ta samu kulawr da tace tunda ita yanason ta rayu saɓanin jameelu.
 saboda yana ɗauke da jimamin abin da ya faru a zuciyarsa, da kuma wani irin shiri da yake yiwa rayuwarshi da aisha da har yanzu bai bayyana wa kowa ba.

A rana ta bakwai ne Aisha ta fara motsa yatsun ƙafarta a hankali, sannan numfashinta ya fara canzawa, kafin idanunta su buɗe sannu a hankali bayan dogon barci da tayi da ya kasance kamar wata doguwar tafiya tsakanin rayuwa da mutuwa, inda abin da ya fara bayyana gare ta shi ne hasken ɗakin da ya sauka kan rufin idonta, sai kuma ta ji nauyin jikinta da wani irin kasala da ya mamaye ƙasusuwanta, kamar wadda ta yi tafiya mai nisa ba tare da ta sani ba.

A hankali Ta lumshe idanunta na wasu daƙiƙu tana ƙoƙarin fahimtar inda take, sannan tunaninta ya fara dawowa mata a kanta,ta shiga ganin komai kamar hotuna waɗanda suke wucewa ɗaya bayan ɗaya, har sai da tunaninta ya kai ga daren da Jameelu ya fara rashin lafiya, yadda hakan ya firgitata, yadda ta fita da gudu neman taimako, yadda aka ɗauke shi zuwa asibiti, da kuma yadda ita kanta ta shiga cikin wani yanayi da ba ta sake iya tuna komai ba.