13-14
Sai kwatsam hoton Jameelu ya bayyana a zuciyarta sosai.Ta tuna fuskarsa.Ta tuna muryarsa.Ta tuna irin kallon da yake mata.Ta tuna cewa shi ne mutumin da ta ke kira mijinta, mutumin da ta yi rayuwa tare da shi, har tana ganin kamar za su tsufa tare, sannan kalmar da ta fi tsoron ji ta fito daga zurfin zuciyarta kafin ma ta samu damar tambayar kowa.
“Jameelu…ya..”ta furta Muryarta cike da rauni,wanda tana furta sunan, sai abubuwan da suka faru suka dawo mata gaba ɗaya, kamar an buɗe wani ƙofa da aka rufe tsawon kwanaki bakwai, kuma a wannan lokacin hawaye suka fara zubowa daga idanunta ba tare da ta iya hana su ba.
“Jameelu ya mutu…”Ta furta kalmar cikin karyewar murya, sannan kuka ya kubce daga kirjinta, kuka mai tsanani wanda ya haɗa da mamaki, rashin yarda, baƙin ciki da kuma ciwon rasa mutumin da zuciyarta har yanzu take tsammanin zai dawo ya kira sunanta kamar yadda ya saba yi a kullum.
“Ya mutu… Jameelu na ya mutu…”
Moneer, wanda yake zaune kusa da gadon tun kafin ta farka, yana riƙe da jinjirar a hannunsa yana bata madara cikin natsuwa, ya ɗaga idanunsa zuwa gare ta, duk da cewa ya riga ya san cewa dole wannan lokacin zai zo, har yanzu kallon yadda Aisha take rushewa da kuka saboda mutuwar Jameelu ya sanya wani yanayi mai nauyi ya mamaye zuciyarshi wanda ya kasa banbancewa tsakanin tausayi da kishi .
“Aisha, ki yi haƙuri,” ya faɗa cikin murya mai laushi, yana ƙoƙarin rage mata kuka. “Na san abin da kika rasa ba ƙaramin abu ba ne, kuma na san babu kalmar da zan faɗa yanzu da za ta iya goge wannan ciwo daga zuciyarki, amma ki tuna cewa ke Musulma ce, kuma duk abin da ya faru yana ƙarƙashin ƙaddarar Allah wadda babu ɗan Adam da zai iya juyar da ita idan lokacinta ya zo.”
Aisha ta girgiza kai tana kuka, hawaye suna gangarowa kan kumatunta ba tare da tsayawa ba.
Moneer ya ci gaba da cewa, “Kin yi duk abin da mace za ta iya yi domin mijinta, kin nemi taimako, kin kasance tare da shi, kin yi addu’a, kuma Allah ne kaɗai Ya san irin ƙoƙarin da kika yi a wannan lokacin; don haka kada ki ɗora wa kanki abin da bai rataya a wuyanki ba, domin mutuwa ba ta neman izinin wanda ake so, kuma idan Allah Ya rubuta wa mutum wata ƙaddara, babu wanda zai iya hana ta faruwa.”
Aisha ta ci gaba da kuka na ɗan lokaci,sabida kalamansa da suka fara shiga cikin zuciyarta a hankali, musamman lokacin da ya tunasar da ita cewa mutuwa ba ƙarshen komai ba ce ga mumini,da kuma cewa abin da ya kamata ta yi yanzu shi ne ta roƙi Allah Ya gafarta wa Jameelu, Ya jikansa, Ya haskaka kabarinsa, Ya kuma ba ta ita kanta ƙarfin da za ta iya ɗaukar nauyin abin da ya rage mata.
“Ki daina yi wa kanki azaba da tunanin abin da ba za ki iya canzawa ba,” Moneer ya ce cikin nutsuwa. “Ki bar abin da ya wuce ga Allah, ki fuskanci abin da yake gabanki, domin har yanzu kina da rayuwa, kuma akwai wata amanar da Allah Ya bar miki wadda ya kamata ki kula da ita.”cewar moneer asanyaye
Aisha ta ɗaga idanunta zuwa gare shi cikin kuka,Moneer ya kalli jinjirar da take hannunsa,dake ƙoƙarin yin kuka sannan ya dawo da idanunsa kanta.
“Ki yi haƙuri, Aisha, ki yarda da ƙaddarar Allah, domin yarda da ƙaddara ba yana nufin mutum ba zai yi kuka ba ne, amma yana nufin zuciya ta yarda cewa bayan duk abin da ya faru, Allah Shi ne Mafi Sanin abin da Ya tsara wa bayinsa.”
Kalaman suka ci gaba da ratsawa cikin zuciyarta, har numfashinta ya fara daidaituwa, kukan da ya fara da ƙarfi ya koma sheshsheƙa, sannan ta share fuskarta da bayan hannunta tana ƙoƙarin tattara nutsuwarta.
Bayan ta ɗan samu sauƙi, sai ta kalli Moneer da idanun da suka cika da hawaye.
“Moneer…”
“Na'am?”ya amsa
“Don Allah… ina so in ga Jameelu.”ta faɗi cikin rawar murya
Moneer ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce, “Za ki gan shi, Aisha, amma ki fara samun ƙarfi.”
“Don Allah ka kai ni,” ta roƙa, muryarta tana rawa. “Ko da ganin na shi na ƙarshe ne kawai, ina so in yi masa bankwana, ina so in ce masa ya yi haƙuri da duk abin da ban samu damar faɗa masa ba.Ina sonshi,ina kewarshi”ta faɗi hawaye na biyo idanunta
Moneer ya sauke idanunsa, daga kallonta ransa na masa zafi jin kalaman aisha,sannan ya ce, “Za a kawo shi gida, tunda yanzu kin dawo hayyacinki kuma jikinki ya fara samun sauƙi, amma kafin nan ki kira ’yan uwanku domin a sanar da su halin da ake ciki, su san cewa Jameelu ya rasu, su kuma shirya abin da ya kamata domin tsaida lokacin da za a yi masa sutura.”
“na bar wayar a gida” Aisha ta ce cikin rauni, “idan za ka taimaka min, ka kira su ka sanar da su, domin yanzu ban san inda zan fara ba.”
Moneer ya amsa mata kawai dan yasa samu tayi shuru,a lokacin ne Aisha ta fara ƙoƙarin tashi ta zauna, amma kafin ta iya yin hakanne wani sabon tunani ya buge ta da ƙarfi.
Cikinta.Shine tunanin da yazo mata.
Hannunta tasa kai tsaye zuwa cikinta.Ta taɓa cikinta a hankali, tana ƙoƙarin tuna dalilin da ya sa a baya take jin nauyi a jikinta, kafin idanunta su sauka kan jinjirar da ke hannun Moneer.
Fuskarta ta canza.Idanunta suka buɗe sosai.Ta kalli Moneer, sannan ta kalli jinjirar, kafin ta sake kallonsa, jikinta yana rawa saboda mamaki da tsoro da kuma wani irin tunani da ya fara taruwa a zuciyarta.
“Moneer…”ta kirashi murya na rawa
“Me ya faru?”cewar moneer aruɗe,dan ya ɗauka wani abunne dabam
Ta ɗaga hannunta tana nuna jinjirar da ke hannunsa, amma muryarta ta kasa fitowa da ƙarfi.Can ƙasaƙasa tace“Na… na haihu ne?”
Moneer bai amsa nan take ba, sai ya kalle ta cikin nutsuwa, sannan ya matsa kusa da gadon yana ɗauke da jinjirar a hankali.Yace “Eh, Aisha,Kin haihu.”
Aisha ta zuba masa ido kamar wadda ba ta fahimci abin da ya faɗa ba.Tace“Na haihu?”
“Eh an miki cs an ɗauko baby.”cewar moneer
“Haihuwa… ni?”cewar aisha tana shafa cikin nata
Moneer ya gyada kai.Yace“Kin haifi diya mace.”
Da sauri Aisha ta rufe bakinta da tafin hannunta, hawaye suka cika idanunta kafin su fara zubowa ɗaya bayan ɗaya, domin a cikin wannan lokaci ne farin cikin haihuwa ya gauraye da bakin cikin mutuwar mijinta har ta kasa bambance wanne ciwo ne ya fi nauyi a zuciyarta.
Moneer ya miƙa mata jinjirar a hankali.Yace“Ga ’yarki.”
Aisha ta miƙa hannayenta dake rawa, ta karɓi jinjirar kamar wadda take riƙe da wani abu mai tsarki da take tsoron kar ya faɗi, sannan ta matse ta a kirjinta tana kallon ƙaramar fuskarta da idanunta suka cika da hawaye.
“Ya Allah…”ta faɗi cikin Muryarta wacce ta karye.
Ta sake duba fuskar jaririyar sosai, sannan hawaye suka ƙara zubowa daga idanunta yayin da wani abu ya kama zuciyarta, domin duk da cewa ba ta san dalilin da ya sa take jin hakan ba, akwai wani abu a fuskar wannan jaririyar da ya tuna mata da Jameelu domin kama take dashi.
“Jameelu…”Ta faɗi sunan cikin kuka, sannan ta sumbaci goshin jaririyar.Tace“Da ace kana nan ka gan ta nasan da kayi farinciki…”Hawayen suka sake gangarowa.Taci gaba da cewa
“Da ka tafi ka barni sai Allah Ya bar min wani ɓangare naka,tabbacin Allah beso nayi kewarka,ina sonka mijina har abada bazan dena sonkaba…”Ta rungume jaririyar sosai, tana kuka , yayin da Moneer yake kallonta ba tare da ya ce komai ba.
Aisha ta ɗaga idanunta zuwa gare shi, sannan ta tambaya cikin muryar da ta cika da raɗaɗin rasa wanda take so da kuma farin cikin samun abin da ya rage mata daga gare shi.
“Me ya sa ba ka gaya min ba tun farko?”
Moneer ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce, “Saboda kina cikin yanayin da ba zai ba ki damar fahimtar komai ba, Aisha, kuma yanzu ne Allah Ya ba ki damar farkawa ki ga ’yarki da idanunki shine yasa.”
Aisha ta sake kallon jaririyar, ta shafa kumatunta a hankali, sannan ta lumshe idanunta yayin da hawaye suka ci gaba da gangarowa na raɗaɗin rasa mijinta abun ƙaunarta jameelu..