RIKICIN DUNIYA

Chapter 9

by @meenatyandoma

RIKICIN DUNIYA...*

©️ Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

CHAPTER 09
…Turbune fuska ya yi. "Kuna da gaggauwa. An fada maku kowane aiki ne za ayi bugu Daya yayi?"
"Tuba muke Bakurmi. Ba gaugawa ba ce kwabe mana take kokarin yi, Yan unguwa ne har sun Fara tattauna zuwan da Kasim ke yi wurin wasila Shi ya sa na ce Bari mu zo wurinka a kulle mana bakinsu."
Shuru ya yi na wani lokaci ya rufe idonsa gam ya na wasu surutai. Wani irin sautin Iska tamkar a makabarta ya rika yawo a wurin.
Tsorata Wasila tayi ta kama hannuwan Umma ta rirrike tana waige-waige. Ya dauki lokaci a haka kafin iskan ya lafa zuwa can ya kalli Umma.
"Bakunan wasu sun rufe. Wasu kuma har abada ba zasu tana rufewa ba saboda sunfi karfinmu"
"Na shiga uku! Dama akwai aikin da ya fi karfinmu?"
Dariyar mugunta Boka Bakurmi ya babbake da ita daga bisani ya turbune fuska. "Kwarai kuwa akwaisu, wadanda suka tsaya suka dogara ga Allah sunfi karfinmu. Amma ki sani aikinku ya yi sure kamar an Daura ne mutuwar Shi KO ita sune kadai zasu Hana faruwar haka" 
Cike da farin ciki suka baro wurin bayan ya Basu sabbin magunguna Wanda Wasila zata yi amfani da su.
Kasancewar akwai wadatatttun kudi a wurinsu abin hawa suka hau ya sauke su har gida.
Lokacin da suka dawo maraice ya Fara yi Domin magriba ta kunno Kai. Ruwa Wasila ta watsa babu maganar azahar bare la'asar haka ta baje ya kwashi baccinta. Karar Kiran Kasim ce ta farkar da ita...
Gidansu Nadiya
Inna ce tsaye a Kan Nadiya. "Nadiya! Nadiya!!"
Murtsuke Ido tayi tana Mai turo Baki. "Haba Inna don Allah, mutum yana bacci Amma ba za a Bari ya karasa baccinsa cikin salama ba?"
"Jira nake ki tashi dama tambayarki nake sonyi. Shin ya Ku Ka yi da Kasim, saboda naga alamar ba kuyi waya ba Kai uwa uba ma banga kafarsa a gidan nan ba"
"Wane Kasim kuma?" 
Lugeden tashin hankali ne ya ziyarci Inna sakamakon Jin abinda Nadiya ta fada. "Ke banson shashancin banza. Kasim din har guda nawa ne da za ki ce wane Kasim. Kina gani komai ya kare mana hatta awarar nan jarinta nema ya ke ya karasa karewa Amma kin tsaya kina wauta da sunan Jan aji."
Tabe Baki Nadiya ta yi. "Wai Kasim! AI tuni na seta masa hanya ni yanzu KO sunansa ba ni so a Kira a gabana. Bari in datse Miki zance ya koma karami, number dinsa ma jiya na gogeta. Babu sauran wata alaka a tsakanina da Kasim don haka ki daina yi mini maganarsa."
Zaman Yan bori Inna tayi.
"Shi ke nan. Makiya sun rabaku yau ni na shiga uku, gaske KO dai mafarki nake?" Ta karasa maganar tana daga murya.
Jamila da ke gefe da sauri ta kama Inna.
"Subhanallahi! Inna me ke faruwa haka za ki zauna kasa kina neman yin kururuwa?"
"Komai ma yafaru Jamila. Nadiya CE ke kokarin tona mana asiri"
"Inna ban gane ba. Me nadiyar tayi?"
"Ta rabu da Kasim anyi mata asirin an Rana su."
"Inna Lokacin rabuwarsu ne yayi babu Wanda ya isa ya tonawa wani asiri a wannan duniyar. Saboda haka ki daina fadar haka"
"Tashi ki bani wuri kema sakarar banza. Ai mantawa nayi da har na kawo kuka a gidan mutuwa. Wadda bata San inda ke Mata ciwo ba ita zan sanarwa da wannan matsalar"
"Allah ya huci zuciyarki Inna" ta karasa maganar tare da mikewa.
Juyin duniya Inna ta yi Amma Abu Daya Nadiya take a kai Shi ne ba zata komawa Kasim ba. Idan kuma aka matsa Mata tabbas zata hada kayanta ta gudu ta koma inda ba a yi Mata maganarsa.
Inna ta Kara tsorata matuka sannan ta fahimci tabbata akwai asiri ciki lamarinta Amma ta ina zata fara? Zuciyarta tafi zargin Wasila saboda kwata kwata ta kasa mantawa da zuwan da tayi na karshe a gidan kaf alamomin rashin gaskiya sun bayyana a wurinta.
Amma babu yadda zata yi in ma ta CE suje wurin Malam bawa babu kudi a hannunsa ga rashin abinda zasu ci ya Fara masu sallama.
Yau ta kama ranar Daren gama exam dinsu suna fitowa a cikin makarantar aka Fara yima wasu kunshi, wasu kuma suka nufi gida. 
Nadiya da Wasila ma daga school gidan kunshi suka nufa ba su suka dawo gida ba sai ana magriba.
Kallonta kawai Inna ta yi zuciyarta cike da kuna. Jira take Allah ya Kai mu gobe KO sauran Jarin awararsu ne sai ta kaiwa Malam Bawa anyi masu aiki. Ba tare da tasan zuwa wurinsa Shi zai karasa rusa farin ciki da walwalar data rage masu.

Yau ta kama ranar final wasu da shirinsu suka zo. Wasu kuma da kayansu suka zo suna Jira a gama exam su Fara shagulgulansu.
Duk da exam ake Amma ban hankalin Nadiya tunda ta tashi yau ta rasa gane me ke damunta. Faduwar gaba da tashin hankali take ji Wanda bata San dalili ba. Sai dai shigowarta cikin mutane ya saka ta rage jin abinda take ji. 
Ta bangaren Wasila kuma kallo Daya zaka yi Mata Ka fahimci tana cikin zallar farin ciki saboda Kasim ya Sanar Mata yau iyayensa zasu zo neman aurenta. Sannan akwai yiyuwar a Daura masu aure saboda Shi ya gama komai sannan Bai bukatar komai a wurinsu.
An gama exam anyi hotuna anyi shagulgula ansha rawa cike da kewar Juna an rabu.
Napep Daya suka shiga Kai tsaye Gidansu Wasila aka wuce dasu. Tunda suka karyo kwanar gidan gaban Nadiya ke faduwa.
Murza idanuwanta tayi KO sune suke yi Mata gizo. Da gaske motar Kasim ce tsage kusa da Gidansu Wasila. Kafin Wasila ta fita da sauri Nadiya ta fito tana Mai furta sunansa. Kallon banza ya watsa Mata. "Nadiya!ke ce ke da amarya TAFE?"
Wasila Kam mutuwar tsaye ta yi tana Jin wani jiri na tashin hankali ya kawo mata ziyara.
"Amarya kuma, wacece amaryar?"
Nuna Wasila ya yi "Wasila mana, KO bata fada Miki yau iyayena sunzo neman aurenta ba, to Allah dai yayi lamarinsa daga zuwa nema an Daura" 
Kafafuwanta kusan kayar da ita suke sonyi Amma da kyar da iya fizgo numfashinta dake kokarin daukewa. "Wasila da gaske ne abin da take fada?" Ta na rufe Baki hawaye suka wanke Mata fuska.
Karfin Hali da kwarewa a harkar ya saka Wasila bata rai. "Kinga ki tafi gida za mu yi magana. Allah ne ya nufa ba da ke za a yi ba don haka bani son ki ja mini zagi idon jamaar unguwa suka iske ki a wurin nan kina kuka ai ni za a zaga"
Ba tare da tasan inda kafarta ke sauka ba haka ta nufi gida. Domin Mai napep dinsu tuni ya gaji da Jira ya yi gaba.
Inna dake duke tana cin danyar awarar data gama yankawa a rikice ta mike tsaye.
"Nadiya lafiya? Wa ya rasu na shiga uku?"
"Ka...Ka.. Kasim?"
"Me ya faru da Shi Kada ki CE mini mutuwa ya yi"
"Kasim da Wasila"
Dif numfashin Inna ya tsaya na wucin gadi.
"Sanar dani abinda ya faru kin barni a cikin duhu. Me ya faru da Kasim da Wasila?"
 "Kasim ya auri Wasila"
"Inna lillahi wa Inna lillahi rajiun! Jamila ki CE mini bacci nake in farka daga wannan mummunan mafarkin" 
Jamila dake tsaye ta kasa magana girgiza Kai ta hau yi tana Mai rike Inna dake kokarin faduwa. Ita dama ta san za a zo wannan ranar, saboda tuni ta San Kasim yana zuwa wurin Wasila bata so ta fada ne ta tsayar da wata husumar.
"Ku yi hakuri Inna, komai ya samu Bawa sai ya dauki kaddararsa ya godewa Allah. Tuni na sani Kasim ya koma wurin Wasila Amma sai na dauki haka a matsayin dama can Allah Bai rubuta zasu rayu tare ba Shi din ba alkhairi bane a tattaro da ita..."
Bangazar da Inna ta kaimata ce ta tilasta Mata yin shuru.
"Da a ce wani zai fada mini za ki iya yi mana haka tabbas zan karyata. Yanzu kinsan abinda ke faruwa Amma kika ja bakinki kika yi shuru. Inna lillahi wa Inna lillahi rajiun"
Kokarin fahimtar da Inna take Amma ina idanuwan Inna sun rufe bata ji bata gani haka ta ja Hannun Nadiya ba su zame KO ina ba sai gidan Malam Bawa.
Duk da duhun magriba Daya Fara gidansa akwai haske saboda Yana kunna fitulu saboda kwastomomin dare. 
Cikin kuka Inna ta Fara yi masa bayani. Dago Kansa ya yi ya kafe Nadiya da kallo. "Dago kanki ki kalleni"
Muryarsa ta daki don kunnen Nadiya, ba tare data shirya ba ta kafesa Ido. Wani irin Abu ta ji ya shigeta ta kasa Kau da idonta a Kansa.
Inna da ke kallon wannan ikon Allah ta zata duk cikin aikin da ake yi masu ne sai dai ba tare da sanin dalili ba ta ji gabanta ya Fadi.
Murmushi ta ga Nadiya ta yi tare da sauke kanta kasa tana wasa da yatsun hannuwanta.
"Yaya Malam, aiki ya yi ne so nake a daukar mana fansa mafi muni akan yarinyar nan ita da uwarta. Sannan Ka lalata auren ta yadda ba zasu taba haduwa a inuwa Daya ba. Ba don ina da sauran imani ba da sai in ce a kawar mini da Wasila daga doron duniyar nan. Amma ba zanyi haka ba so nake ayi komai a gaban idonta ta ga yadda gidan Kasim zai gagareta ita kuma ta kare a wulakamce a gida. A saka Mata warin jaba ta yadda ba zata tana auruwa ba hatta Kasim din yayi Mata saki uku"
Inna ta karasa maganar cikin zallar bacin rai.
"Inna ki daina fadar haka, ni a kaf duniyar nan babu Wanda nake so kamar Malam Bawa. Dama can shirme da kuruciya ce ta saka nake son Kasim Amma a yanzu nagane Malam Bawa shine rayuwata idan babu Shi mutuwa zanyi."
Tuntsurewa da dariya Malam Bawa yayi wawulon gibin dake cikin bakinsa ya bayyana. Hakoran nan sunyi jajur goro ya dafe su.
Inna kuwa mutuwar zaune tayi ilahirin jikinta idanuwanta ne kadai ke motsi...