BABAN KAWATA

Chapter 39

by @smauta

Teddy duke yake saida ya dago kalleta da wani irin tsananin farin ciki a ransa teddy am your teddy bear?daga ta sama yayi ya juya sannan ya maidota kada my life ko menene ina tare dake...........




Tsantsar kaunar sa yake kallo acikin idanunta rugawa tayi da gudu toilet tana sakama kofar key 🗝️ bakin toilet din ya tsaya idan kin gama ina parlour zanje dakin ki nayi wankan nima bai jira ansar ta ba ya dauki kayanshi zuwa dakin ta,koda ta fito bata same shi a dakin ba kunyar fita takeyi daga ita towel dan tasan yana dakin nata da kyar ta dake sannan ta fito..........






A dakin nata ma bakowa kofar toilet ta tsaya ba alamun mutum dan tabe baki tayi kenan harya shirya wata atamfa cikin kayanta mai laushin gaske peach color ta dauka kwalliya ta zauna tayi light a mirror murmushi ta sakar ma kanta hannunta ta dora akan kirji yanzu ni manar matar aure ce Alhamdulillah Allah............





Khalil na zaune parlour sanye cikin farin kagani kamshinsa ya cika wajen koda ya hango ta daga sama tana saukowa ya mike tsaye kafe a kanta harta sauko gaban Ma Shaa Allah ya furta Matata tayi kyau kasa tayi da kanta tana murmushi, yazo ya kama hannunta ina mayafinki?jikinta ta kalla alamar mayafi kuma?.........






Zamuje restaurant muyi breakfast kin tafi da imani na dariya tayi a karo na ba adadi to bari nakoma na dauko bata dauki lokaci ba kuwa sai gata hannunta ya kama suka fito harabar gidan gaban motar shi suka isa kofar ya bude mata tashiga hannunta ya manna ma kiss sannan ya dawo hannun driver ya zauna har lokacin yana riƙe da hannunta............





A restaurant din ya ma VIP suka wuce wuri mai natsuwa manne take a jikinshi kamar za kwace mata shi,Shafa gefen fuskar ta yayi baby girl a hankali tace ummm nayi dacen mace tagari ke alkhairi ce gareni muddin abokin zama ya cuceka a sannu zakaga sakayya ina zaune Allah ya jefoki cikin rayuwata dan kizamar mani wani haske..........




Idonta ya cika da hawaye"Teddy ina sonka badan komai ba sai dan Allah ya matse hannunts nasani baby girl shiyasa zan baki duniya ta gaba daya suna cikin hira mai dadi wayar sa tayi kara alamun kira ya duba bai dauka ba dan bata fuska tayi murmushi yayi kasan rai baby girl s ranta tace lokaci yayi dazan zama matar ka teddy matar da zan mantar dakai duk wasu mata amma cikin ranta tana kara tambaya ta waye ya ke kiranshi da safe haka kuma yaki picking?????






Khalil ya mayar da wayar aljihu yayi murmushi yace bakowa ke kirana ba baby girl saki fuskar ki business ne,turo masa baki tayi hannunta dake kan nashi ta kalla ta matse shi a hankali yar kara ya saki kadan ouchh teddy mene haka kamar ba namiji da sauri yace indai ina gabanki jariri nake wani kallon so da kauna ya jefa mata har saida ta sauke kanta kasaaaaa............





Kafin tayi magana wayar da ta kara ringing dauka yayi ya tashi ya koma gefe Hello ina jinka okay zan kira daga baya duk abun nan tass taji shi a kunnenta ya dawo ya zauna yana kokarin murmushi sake daure fuska tayi, breakfast dinsu da aka kawo sukaci cikin natsuwa khalil na ciyar da ita da hannunshi kamar yarinya ita kuma tana cika tana batsewa har suka gama cin abincin tana kumbure kumburen fuska...........





Tambayoyi fal a ranta amma ta rasa ansoshin su bayan sun gama ya kama hannunta suka fito a mota ya jinginar da kansa ya rufe idanunsa nadan lokaci manar ta kalle shi hakanan taji tausayin shi ya kamata lokaci daya 🥺 teddy ka gaji? Ya bude idanu ya kamo hannunta ya sumbace ta bana tareda gajia indai kina gabana baby girl.............








Yawo yayita yi da ita har main office dinshi saida ya kaita ya gabatar da ita a wurin ma'aikatan shi yadda yake nuna mata tsantsar soyayya da kulawa ne yasa taji zuciyar ta na neman melting bayan ya dawo sallah azahar ne yace ta miko masa wayar sa cook dinshi ya kira oga barka da rana,barka mene time table na yau?brown spaghetti Bolognese and rice onion ya mutsa fuska yayi ka shirya lunch na mutum 10 inada baki around 5pm.........







Kina bukatar yayi maki wani abu?no kawai ta bashi ansa ka shirya lunch mai kyau kayima matata special girki tanada cin abinci sosai,manar ta harare shi teddy 🙄🙄niko??katse wayar yayi yana dariya eh mana kinada cin abinci kuma kina bukatar kuzari kar wurin nemanki na nemoki😜😜😜wayar sa ta karayin ringing a bugu na ukku wannan karen taga mai kiran kafin ya juyar da wayar JUDE gabanta ya yanke ya fadi rass kardai wani abun ya faru da kaka cikinta yayi wata kara.......





Khalil ya dauki wayar yana ida shigewa balcony manar zuciyar ta na cigaba da bugawa kasa zama tayi ta mike kamar ta bishi amma ta kasa mintuna kadan yadawo ya sameta tana ta safa da marwa canza fuska yayi kadan lafiya? shiru tayi baby girl ya kamo hannunta suka zauna akwai wani abu ne ta kalle shi idonta cike da damuwa tace teddy naga mai kiranka akwai matsala ne da kaka karka boyeman,shafa goshin yayi ba wata matsala zan fadamaki dalilin kiran..............





Ya rungume ta ya dora kumatunshi a kumatunta babu wata matsala baby girl karki saka kanki a damuwa ki yarda dani babu wani abun tashin hankali dazai taso mana banyi maganinshi ba tun kafin ya iso gareki rungume shi tayi da karfi tanajin wani sanyi na ratsa ta kan wannan kalaman dayayi mata Allah ya tsare man kai amin baby girl ya cigaba da bata sakonni masu wuyar fassaruwa da kyar ta kwace a office muke fa,so what?????







Aikin shi ya cigaba dayi a office gajia tayi da zama ta kwanta akan kujera bata dade ba bacci ya kwashe ta murmushi kawai yayi yana cigaba da ayyukan shi sai dab magriba ya kammala iska taji ana hura mata a ido da sauri ta bude idonta teddy ne tsugunna gabanta yana mata daria daga jin AC sai bacci biya kudin bacci turo baki tayi gaba kamota yayi muje gida magriba na karatowa ba abinda ke tashi a motar sai karar AC da numfashin su hakanan gabanta ya tsananta faduwa innalillahi wainna ilaihir rajiun take maimaita kawai a ranta...............





Saida suka shigo gida ta bude idonta motoci biyu tagani wanda bata sansu ba kallonta yayi yana daga mata gira daya let's go kamar wacce aka zarema lakka haka ta fito itace a gaba yana biye da ita baya har gaban kofar parlour kyarma ta kwace mata a hannu da kyar ta iya murda kofar da sallama dauke a bakinta wacce ta makale a makoshinta sanadiyyar kiran sunan Kakaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaaa..............





Cimimiye kaka tayi kuka ta fashe dashi kaka yaushe kuka dawo dago kanta tayi ta gallama khalil harara da suke mata dariya tareda kawu labaran sai lokacin hankalin ta ya dawo kan duka yan parlour har yaran dede wai duk yaushe kukazo??kowa dariya yake mata kawu labaran yace nina taho dasu dan suga uwarsu yan bura'uban anzo abuja basu taba zuwa ba sai kauyanci sukeman abinci ko sunci ba adadi...........






Manar tace kai kawu to ai gida sukazo ja'ira diyata kinga yadda kika mulmul Alhaji Khalilu wallahi ka iya kiwo kai Allah saka da alheri yarinya daya ta jawomana kashin arziki dede na sallame sallah ta galla mashi harara to ya isa suda uban zance aifa ka iso baka barima ya huta, rungume dede manar tayi itama manaraaaaaaa yaude gani gaki ga kuma amanar ki ta kaka na maido kullum addu'a ta daya yadda muka tafi da kaka lafiya Allah yasa in dawo maku ita da ranta Allah ya anshi rokona ga ta na maido ta da kafar ta kai Allah abun godiya dole kuma na kara gode maka khalil kaine sila............






Dukka parlourn murna akeyi manar ta manta ma dawani Khalil part dinshi dake dayan gefen can suka tafi shida kawu labaran yanata rashin daraja dan bazai iya zama a cikinsu ba sai 9 na dare kawu labaran ya taho fagam fagam to ku tashi ai bamunzo nan muyi kwance gidan diya ba ya nuna dede data bararraje kin wani kware kai ai sai a tashi bake ba ba yaranki ba idan kika ga abun duniya idonki har ruwa yake😂😂😂😜😜1/0 kawu................







Kaidai Allah ya sawake maka wlh sai lokacin manar tace wai kawu ina zakuje wlh bansani ba yadai ce wani gidanshi ne can zamu zauna tunda a nan dinma za'a dinga duba kaka kafin mu koma suleja dede tace kai dawa za'a zauna ke dede karyar ki tasha karya billahillazi dani zaayi jiyyar abuja munahuka idan kinga nabar garin nan suleja muka koma kafata kafar ki ba dadin da zakici ina ƙauye gashinan har yan bura'uban yaranki na kwaso maki dan suci arziki kuma sai kin biya kudin mota dan ba'a banza na dauko su ba...........





Khalil ne ya shigo duk sukayi shiru kaka na zaune yazo gabanta magana sukayi kus kus bamai ji kaka ta mike to ku tashi muyi ta tafiya kwal kwal manar tayi da ido wai dagaske tafiya zakuyi nima zan biku dan Allah🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹