3
https://www.arewapen.com/book?id=6a9287eff3eaa6dc8f153f72
BAYA TA HAIHU
Ummu Maher(Mrs SHU'AIBU)
Page 3
Mahaifiyar Habibu tana zaune a tsakar gida, tana aikin wankau ɗin da take yi Malam ya yi sallama ya shigo jikinsa a matuƙar sanyaye ya samu waje ya zauna, yana me kallon matarsa amma ya kasa magana saboda bai san ta inda zai ɓillo ba saboda ya san ya cutar da ita sosai. Ita ma kallonsa take tana mamakin mlm saboda tasan halinsa in har ya shigo to kazar gidan ma sai tasan da zuwansa, ga shi kusan kullum a make yake zuwa yana shigowa zai fara sakin amai ya ɓata ko ina ta gyara ta wanke ta fesa turare kamar dai babu komi a wajen, saboda haka sai ta ce" Mlm yau na ga ka shigo a wani irin yanayi Allah dai yasa ba mutuwa aka yi ba".
Cikin nadama ya fara hawaye, ya durƙusa a gabanta yana me neman afuwarta hannayensa suna riƙe da ƙafufuwanta ya ce" Don girman Allah ki yafe min laifina, wallahi tallahi ban taɓa tunanin wannan ranar za ta zo min ba saboda tun da na aure ki yau shekara talatin ina ƙunsa miki baƙin ciki don zatin Allah ki yafe mun".
Shiru ta yi mamaki ɗauke a kyakkyawar fuskarta, tana yi wa Allah godiya, saboda har ta cire rai da shiryuwar mlm saboda a haka ta aure shi tun yana saurayi.
Ruƙo hannayensa ta yi suka shiga ɗaki yana Binta tamkar raƙumi da akala, ta zaunar da shi a bakin gado bata san lokacin da ta rungume shi ba ta shigo kuka me cin zuciya saboda gani take kamar ba shi bane wani aka canja mata. Ranar dai haka suka wuni cikin farin ciki, ta fito ta cigaba da wankin yana taya ta suna hira tamkar dai ba gidan mlm Umaru ba, suna hira ne yake ce wa" wallahi na cuci yarana Lantana sam ban yi musu adalci ba, yanzu kina ganin Habibu saboda ni an hana shi aure shi dama yake namiji sannan a halin yanzu da Habibu ya ke da shekara 29 a duniya ba shi da sana'ar yi, kin ga kuwa ai na cuce shi bai taso ya ga ina sana'a ba sai dai zaman majalissar da ya saba".
Suna maganar ne Khaltume ta shigo ƙanwar Habibu, abin da ta gani ne ya sanya ta kasa yarda har sai da ta mutstsuka idonta ko dai mafarkin da ta saba yi ne, amma sai ta ga ba mafarki bane da sauri ta ce" Abba ka shiryu". Ta faɗi maganar ba tare da ta shirya ba, da sauri ya ɗaga mata kai tare da hawayen tausayinsu da sauri ta rungume shi tana kuka sosai. A ranar dai duka a halin gidan Mlm Umaru cikin murna da kwanciyar hankali suka kwanta suna mai godewa Allah.
***
Mahaifina matafiya ne yana zuwa su Legos da Abuja, shi yasa duk waɗannan abubuwan da suke faruwa bai san da su ga tashin hankalin dana tashi da shi ranar wai Ammi ta kira ƙanin Babanmu wai yazo za suyi magana.
Tun da ta kira na ji gabana ya yi mummunan bugawa a zuciyata ina cewa Allah yasa ba maganar Hammah Hamzah za ta yi masa ba, shiru na yi a ɗaki tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki.
Ina zaune Baffah Aminu ya shigo, Ammi ta sanya mishi ta barma ya zauna suka fara gaisawa ta ɗebo mishi ruwa ya sha, bayan ya sha ne ta fara magana " Baffah Aminu da ma magana ce akan ƴar wajenka Mero, to ta fito da miji ne ɗan wajen Hajiyar Damaturu to shi ne na ce bari na faɗa maka, kada kace baka sani ba saboda ka ga kune za ku karɓi dukiyar aure".
Sosai ya yi murna, ya sa albarka ya ce" Yaya Sani kuwa ya sani?
Tana murmushi ta ce" haba kai kuwa ai dole ma ya sani na faɗa mishi kuma shi da kan shi ma ya ce na kira ka".
Wani irin ihu na sanya ina ɗaki, Baffah Aminu ya ce, lafiyarki kuwa Mero"?. Ina kuka na fara magana "Wallahi ni kam bana sonsa idon kuka haɗa ni da shi komi zai iya faruwa". Na ta shi da sauri na koma ɗakina, Ammi ta bini da kallon jin haushi ta ce" ka ga ka da ka biye mata, yarinta ce kawai take damunta amma in sha Allah zan shawo kanta. Baffah Aminu me jiran ƙiris dama shima yana so ya haɗa ɗiyoyinsa da Hamzah ya ce" A a fa gaskiya babu hannuna ni kam, yanzu idan na sa baki aka yi auren nan idan aka zo aka samu matsala fa har dani, saboda haka babu ruwana ni kin ga tafiyata".
Ya ta shi ya tafi, yana me shi min albarka a cikin zuciyarsa saboda a cewarsa tsuntsu daga sama gasasshe.
Ammi ta kalle ni cike da takaici ta ce" kinsan Allah Mero idan har ba ki auri Hamzah ba wallahi babu ni babu ke, saboda baƙin ciki kowa yana haɗa jininsa da me arziƙi ni sai ki yi min baƙin ciki, to wallahi ki buɗe kunnenki da kyau ki ji in har kika sake kika cewa Abbanki bakya son Hamzah wallahi na lahira ma sai ya fiki jin daɗi".
Nan dai ta barni na cigaba da kuka na. Ba a fi kwana biyu ba Baffanmu ya dawo murna fal cikina saboda nasan ko ba komi zan samu sauƙin kyara da halin ko in kulan da Ammi take min. Tun da ya dawo ya rabawa kowa tsarabarsa ya kira ni da muryarsa me amo. "Mamana!Mamana!!". Da sauri na taso na tsugunna gabansa ya ƙare min kallo sannan ya ce"Mamana zo zauna kusa dani ki faɗa min abin da yake damunki saboda nasan ta inda zan ɓillowa lamarin".
Da sauri Ammi ta fito daga ɗakinta ta zo ta zauna, tana kyafta min ido alamar kar na ce komi sannan tana gaba min harara kamar za ta cinye ni. Bakina yana kakkarwa na ce "Baffah ba komi".
"Kin tabbatar ba komi Mamana?.
Na daga masa kai alamar eh.
Ya umarce ni dana tashi na tafi, jikina duk a sanyaye na tashi. Ina jin ta tana ba shi labarin Hammah Hamzah zai turo zuwa wani satin, shima albarka yasa amma ya ƙudurce wani abu a zuciyarshi wanda ba kowa ne ya sani ba.
Washe gari da sassafiya aka aiko kiran Baffanmu, jikina ya bani akwai wani abu saboda nasan hakan bai cika faruwa ba duk da ba halina bane laɓe sai na biyewa son zuciyata na tafi da sauri na laɓe saboda inji abin da yake faruwa, amma abin da na ji yasa na kusa daskarewa a wajen.
Ƙarar ƙarrawar gidan yarin muka jiyo, na tsaya da labarin Badawiyya ta ce" kash wallahi banso labarin nan na ki ya tsaya haka ba, duk da dai nasan za ki ƙarasa min ko".
Ina murmushi wanda yafi kuka ciwo na ce" to ai a cikin labarina ɗari wannan bai fi kashi ɗaya ba, saboda Wallahi idan kika ji cigaban labarin ke da kanki sai kwanyar kanki ta tsotse, saboda babu wanda zai yi tunanin irin hakan tana faruwa a wannan duniyar ta mu".
Saurin ta shi muka yi ganin Antin ɗakinmu ta nufo mu, da sauri muka tashi saboda idan ta zo ta fara dukan ka sai ta Allah saboda ba tada tausayi bare imani.
Tun daga bakin ƙofar ɗakin na muka tsaya, saboda jin irin warin tabar wiwi wanda kana jinta kasan tabbas wannan me shan bai san zafin jikinsa ba, ire-iren waɗannan abubuwan ne suke faruwa a ɗakin mu ko kuma wani lokacin ka ga ƴar uwarka mace tana nemanka, tabbas wannan ba ƙaramar masifa bace saboda a ɗakin daga Badawiyya sai Mero sune masu hankalin ɗakin sauran kuwa tun da aka kawo su gidan suka kuma kangarewa, har suke jin kansu ko ma menene za su iya yi.
Kamar kullum Badawiyya da Mero suka tashi cikin dare, suka gabatar da alwala da Sallah suna kai kukansu wajen Ubangiji saboda su aka cuta amma kuma aka kawo su gidan yari saboda ba su da gata, sau da yawan lokuta wasu ko tambayar su me ya faru ba a yi sai dai kawai ka ga an kawo mutun an watsar da shi a gidan yari, madadin yana me nutsuwa sai kaga mutum ya kangare saboda ya ga waɗan da sam basa tsoron Allah, karatun Alqur'ani muka yi sannan muka rufe da addu'a muka kwanta.
Mafarki sosai Mero ta yi, wai ga ta a kusa da Yaya Habibu da wuƙa zai kashe ta ai kuwa a matuƙar firgice ta tashi tana addu'ah, dafe da ƙirjinta tana jin adadin bugawar zuciyarta ta kalli gefenta da ɗaya ɓarin duk barci suke yi ita kuwa tashi ta yi ta zauna tana tunanin irin ƙarshen da ya gabata tsakaninta da su Yaya Habibu, yayarta Hafsah da kuma Habibu sai taji zuciyarta ta tsinki sosai sai ta fashe da kuka mai matuƙar ƙuna zuciyar me sauraro.
Badawiyya ta miƙe zaune tana mutstsuka idonta, ganin Mero a zaune yasa ta taso da sauri ta tsugunna tana share mata hawayenta, ganin ta ƙi yin shiru yasa ita ma ta fara kuka musamman da ta tuno Tata ƙaddarar wacce a duk ranar da ya tuno ta sai ta ji tamkar ta matse wuyanta ta mutu kowa ma ya huta da baƙin cikin da aka cusa mata a zuciyarta.
Ƴan cikin ɗakin duka suka ta shi, faɗa suke musu sosai wata daga cikinsu ya ce " aikin banza aikin wofi, da ba a san asalin balbela ba da sai ta ce da ga Misra take haba iskancin banza iskancin wofi kadan ba zamu haɗu muyi muku mugun duka ba, haba kun ishi mutane wallahi kusan kullum sai kun ishi mutane da kukan tsiya, da wani ne ya ce kuje ku aikata laifin yunƙurin kisa a kawo ku nan, ƴan iska kawai duk cikinmu nan babu wanda ya kai laifinku ni laifi na na tunawa matar babana asiri na ganta kwarto shike nan ta yi kutu kutu ta yi makirci ta kashe kwarton na ta tace ni ce, ni ban yi kuka ba sai ku har gidan Radio sai da aka yaɗa hotunanku to kuma meye na kukan, da kunsan za kuyi Ku zo kuna kuka ai da ba kuyi ba". Haka dai ta ƙara ci masifarka ta gama bamu dena kukan ba kuma ba muyi shiru ba, gajiya suka yi suka rufar mana da duka sai kace ɓara yi sai da suka yi mana lis sannan suka barmu.