MEERAH

07

by @oumfatima33

*MEERAH*

    *OUM FATIMA*
        ***

     *07*



        Na san halinsa sarai baya mai-maita tambaya, don haka na turo baki gaba sosai. Zuciya fal takaici na bashi amsa da cewa.

   "Daga gidan su Zeezee nake, wanda ya sauke ni kuma Class mate ɗina ne sunansa Haneef." Har yanzu idanunsa na kaina yana min kallon da nafi son duka da zai yi hakan, da ya fi min a kan kallon.

   Na fara ƙosa wa da wannan mulkin mallakar na Ya Ajmal, ji nake kamar na yi tafiya ta na barsa. Sai dai kuma ko giyar wake nasha ban isa aikata hakan ba, don duk tsanar da na masa dole nake bashi girmansa a matsayin Yayana, wannan ɗin tarbiyyar gidanmu ce.

   Sai da ya mula don kansa sannan yace.

    "Daga yau kar na ƙara gani ko jin kin kai magrib a waje, sannan na hana shiga motar koma waye. Understand?." Ya ƙare maganar yana riƙe kunnensa. Bani da zaɓin daya wuce na ɗaga masa kai, don na matsu ya sallame ni na tafi, kamar a kan ƙaya nake jina.

   Don haka na ɗaga masa kai ina cewa.

   "Yes."

      "Wuce ciki." Ya faɗa yana nuna min hanya, dama abinda nake jira kenan. Don haka har tuntuɓe nake yi na bar wurin. Wani irin zuzzurfan kallo Ajmal yabi bayanta dashi, sai da ta buɗe ƙofar ta shige sannan ya ɗauke idanunsa yana sakin ɓoyayyar ajiyar zuciya.

   Motarsa ya buɗe ya shiga ya tashe ta ya bar wurin zuwa inda ya fito da niyyar zuwa yaga mota ta tsaya a ƙofar gidan, yana ƙoƙarin shiga ciki ne kawai yaga wani yaro ya fito ya buɗe ƙofa. Ita kuma ta fito tana washe masa baki, har da masa godiya.

   Tsoki ya saki shi kaɗai yana dukan steering, yana mamakin rawar kan da take ji da shi a ƴan shekarunta da basu fi 15 ba.


******* Ban samu kowa a Palo ba don haka na haye sama kai tsaye na shige bedroom ɗina, na san Momy ita ma tana nata ɗakin tana gudanar da Sallah. Alwala na fara yi nayi sallar magriba, na ɗauki Alkur'ani nayi bitar karatun islamiyya na. Don duk rawar kaina bana wasa da karatu.

   Sai da aka kira isha na rufe na tashi na gabatar, bayan na kammala nayi addu'o'ina sannan na cire hijabin na fita. Kai tsaye bedroom ɗin Momy na nufa don sanar mata cewar na dawo tun ɗazu.

   A saman abin sallah na same ta tana lazumi, don haka na zauna a gefenta na shige cikin jikinta ina jiran ta kammala. Sai da ta kammala tayi addu'o'inta sannan ta lalle ni tace.

   "Me yasa kuka tsaya har magrib tayi baku dawo ba?." Ta tambaye ni da kulawa. Ƙara lafewa nayi a jikinta cike da shagwaɓa nace.

   "Momy Ya Aryan ne bai koma ya ɗauko niba, sai da naga dare zai yi ne na biyo motar su Haneef suka sauke ni. Shine da Ya Ajmal ya tare ni da muguntarsa a ƙofar gida!." Na ƙare maganar ina turo baki gaba. Gir-giza kai Momy ta yi tana cewa.

    "Ajmal ai shine maganinki a gidan nan Auta." Turo baki gaba na yi ina ƙara shagwaɓe fuska nace.

   "Haka ma zaki ce ko Momy, bayan kowa ya san shi kaɗai ke cin zalina a gidan nan." Na ƙare maganar cike da jin haushinsa. Murmushi tayi tace.

   "Ba cin zali bane Auta, so yake yaga rayuwarki na tafiya cikin tsari da tarbiyya mai kyau ne." Tura baki nayi kawai ba tare da nace komai ba, saboda hirar tasa ta ishe ni. Kum na san in dai a kansa ne Momy ba zata giya min baya ba.

   "Tashi kije ki duba idan an shirya table yanda ya kamata." Momy ta faɗa tana shafa kaina. 

   "Okay Momy." Na faɗa ina miƙewa na fice a ɗakin, addu'ar shirya Momy tabi ƴar tata dashi sannan ta miƙe tana ɗauke abin sallar ta shiga bayi.


****** Ƙarfe 8 da rabi muka yi zaman cin abincin dare, Sai a lokacin ne kuma Ya Aryan ya shigo gidan. Kai tsaye dining ɗin ya nufo yana amsa waya, bai kai ga zama ba Ya Sultan ya shigo shi ma Ya Ajmal ya biyo bayansa.

   Gaba ɗayan su dining ɗin suka ƙaraso kowa ya ja kujera ya zauna, duk gaishe da Momy suka yi ta amsa musu da kulawa. Ya Sultan na kalla wanda ya zauna kujerar kusa da ni, shi kuma Ya Ajmal ya zauna a kusa da shi muka saka shi tsakiya.

    "Sannu da dawowa My Yaya, ka sayo min chocolate ɗina dai ko?." Na faɗa ina tsats-tsare sa da ido don ma kar yace ya manta, murmushi yayi yace.

   "Kin fiye kwaɗayi yarinyar nan, to yau dai kam ban sayo ba sai dai ayi min afuwa."

   "Ai duk kai ne ka ɓata ta da kwaɗayin." Momy ta bashi amsa. Tura baki nayi gaba zan fara taɓara, muka haɗa ido da ya Ajmal da ya zuba min ido kawai yana min kallon dai dana tsana.

   Da sauri na duƙar da kai ƙasa a hankali na furta, don Allah ka ya sani idanunsa kayar min da gaba suke yi.

   "Good evening Yaya." Na faɗa a hankali, sai da ya mula don har na cire ran samu amsa wa sannan na tsinci muryarsa ya amsa min cike da basarwa.

   Maganar Momy ce ta katse shirun daya ratsa ta kalli Ya Aryan tace.

   "Me yasa baka dawo min da yarinya gida ba kamar yanda na faɗa maka?." Ɗagowa yayi zai bata amsa ya tsinci idanun Ya Ajmal suna bin sa da kallon tuhuma. Duƙar da kai yayi yana sosa ƙeya alamar rashin gaskiya.

   "Wai ba da kai ake magana bane Aryan?." Ya Sultan ya faɗa cikin kaushin murya.

   "I'm sorry Yaya, I'm sorry Mom Wallahi bayan na kai wa Mamy Safiya aikar ne, su Halifa suka jani muka fita. Shine bamu dawo da wuri ba. Wannan karon kam Ajmal ne yayi magana cikin ɓacin rai.

   "Kar ka ƙara mai-maita irin wannan kuskuren Aryan, taya za'a ce ka ɗauko yarinya amma ka tafi sha-shancin da ba'a aike ka ba. Ka manta da ita a can har ta gaji ta biyo wasu, idan wani abun kuma ya same ta fa?!." Ya ƙare maganar cike da tsawa yana kallon Aryan da idanunsa suka raina fata.

  I'm sorry Yaya in sha Allah ba zan ƙara ba." Aryan ya faɗa cike da girmamawa, yana duƙar da kai. Ɓoyayyar ajiyar zuciya Ajmal ya sauke sannan ya kalli Aryan yace.

   "Is okay, but you have to be very careful next time."

   "In sha Allah Yaya." Aryan ya faɗa yana duƙar da kai. A raina nake gulmar su biyun, 'masifaffe kawai, ayi mutum shi koda yaushe a fusace yake bashi da aiki sai yiwa mutane masifa?. shi kuma Ya Aryan ji yanda ya natsu yana ladabi da biyya tamkar wani Muminin gaske.'

    Muryar Momy ce ta dawo dani daga zancen zucin da nake yi ni kaɗai ina bin kowa da kallo.

   "Ki tashi kiyi serving mutane kika tsaya kina bin mutane da kallo kamar baki san su ba." 

   Miƙewa nayi na zuba wa kowa abinda na san yana so, koda nazo kan Ya Ajmal da na san baya cin abinci mai nauyi da dare. Haɗin salad da aka yi masa na zuba masa na tsiyaya masa Black tea ɗinsa na gado da na san yana sha.

   Ni kuwa Uwar kwaɗayi ɗanwaken fulawa na saka Bintu tayi min, na yanka dafaffen ƙwai, cabbage, albasa, da tumatir a ciki. Na kwarara uban man gyaɗa da yake ta ƙamshin albasa.

   Ajmal dake kallon duk abinda take yi don lokaci zuwa lokaci yake ɗagowa ya kalle ta.

   Ganin uban yajin data ɗebo zata zuba ya saka shi saurin riƙe hannun nata yana harararta. Cike da mamaki na ɗago ina kallonsa jin ya riƙe min hannu. Harara ya zabga min ƙasa-ƙasa ya furta.

  "Baki da hankali ne zaki zuba wannan gubar a abincin da zaki ci? Ko so kike ya saka ki rashin lafiya ne?." Ya yi maganar yana buɗe min girman idanunsa.Taɓe baki nayi cike da taɓarar dana saba yiwa su Yi Sultan nace.

   "Bafa guba bace Yaya, yaji ne fa abinci ake ci da shi kuma." Na bashi amsa ina buɗe masa nawa girman idanun nima. Harara ta ya ƙara yi sannan ya karɓe yajin ya mayar cikin bowl ɗin da aka zubo shi. 

    Tuni hawaye suka cika min ido, don har ga Allah ba zan iya cin ɗanwake babu yaji ba, saboda kwaɗayin yajin ma na saka aka yi min shi.

   Ya Sultan na kalla ina neman ɗauki daga gare sa, ya ɗaga min hannu alamar babu ruwansa, Momy na kalla ita ma ta ɗauke kai alamar kar ma na fara.

  Dama Ya Sultan da Momy kawai nake da hope a kansu su kuma sun ƙiya, don haka bani da zaɓin da ya wuce na fashe da kuka kawai har da turza ƙafafu. Dariya sosai su Ya Sultan suka saka cike da mamakin taɓarar Autar tasu, shi kansa Ajmal sai da ya yi ɓoyayyen murmushi.

   "Zo ki saka ɗan kaɗan to." Ya faɗa yana kallona, hawayen na share na miƙe jiki na rawa na ɗauka zan saka. Cokali na ciko zan saka ya maka min harara. Ba shiri na rage ina tura baki, zuciya fal abin faɗa babu dama.

   Fara ci nayi ina satar kallon kwanon yajin, don gaskiya bai min yanda nake so ba. Sai na kai hannu zan ɗauka sai mu haɗa ido, dole na haƙura na cisa a haka ba don ina so ba.

  Bayan kammala cin abinci zaman hira muka yi a Palo muna kallo, zuwa 9 kowa ya shige nasa ɓangaren.

★★★

    Washe gari muka tashi da murnar dawowar Dady, don baya ƙasar ya yi tafiya zuwa Egypt ne wasu harkokinsa. Yau zai dawo kuma a nan Kano zai sauka, hakan yasa tun da safe ake ta kai-kawo a gidanmu.

   Momy ta kasa zama da kanta ta shiga Kitchen ta girka masa kalolin abincin da ta san yana so, da taimako na dana masu aiki aka kammala da ɓangaren abinci. Gyaran gida kuwa tuni an kimtsa ko ina sai tashin ƙamshi yake.

   Ƙarfe biyu na rana jirginsu zai sauka, don haka zuwa ɗaya da rabi duk mun kammala shirya wa. Motoci uku muka fita dasu ɗaya nida Momy ne, Ya Ajmal ke driving da Ya Sultan a kusa da shi.

   Ɗaya kuma Ya Aryan da Ya Jawad ne, sai ɗayar kuma security ne. Ya Maheer da Ya Fadeel basa nan suna Kasar Cairo a can suke karatu.......