LULLUƁIN BIRI

68

by @halimahz

Yana ta kallon Fullo yana kuka sosai ya ce,"Na karɓi sadakin aurenki tuntuni. Na yi miki aure da mutumin da ban sani ba, amma ya ce ya sanki, kuma zai kasance tare da ke har mutuwa. Ban sani ba ko shi ɗin na gari ne, kuma ban sani ba ko nauyin auren kawai ya ɗora miki bai zo gareki ba. Kai Allah ya yi wadaran halina, Ya Afuwwu ka min afuwa."

Ya yi shiru, yana fama da numfashinsa.

"Sadakinki haƙƙinki ne. Dole na baki haƙƙinki. Ban karɓi sadakinki da niyyar na baki ba, na karɓa da niyyar na more rayuwata. Ya Allah..."

Ya haɗiye yawu da ƙyar.

"Motar da aka bayar a matsayin sadakinki, na siyar da ita da kuɗi mai yawa naira miliyan hamsin da biyar. Na so na gina kaina da kuɗin na fantama. Sai dai ikon Allah ban ma fara morarsu ba, Allah ya jarabceni da shiga wannan mawuyacin halin."

Ya kalli Fullo cikin wani irin nadama. Ya girgiza kai.

"Na san ƙwarai na zalunceku. Ba a taɓa samun mugun mutum irina ba wajen ƙuntata rayuwar iyalinsa. Ban baku ilimi ba. Ban baku tarbiyya ba. Ban kula da ku irin yadda Allah ya umarci uba ya kula da iyalinsa ba. Hasalima na ƙi karɓarku a matsayin ƴaƴan da na haifa. Kuma a ko'ina shegantaku na ke."

Muryarsa ta karye. Ya rufe idanuwansa.

"Na samu damar zama uba, amma ban zama uban na gari ba."

Ya ɗaga hannunsa cikin rauni.

"Don Allah ku yafe min. Ko na samu sassauci a ƙabarina. Ba na roƙonku saboda na cancanci yafiyarku. Ina roƙonku ne saboda na gane kurena."

Ya kamo hannun Abdulhamid.

"Haƙiƙa ban da tamkarka ɗana."

Murmushi mai rauni ya bayyana a fuskarsa.
"Allah Ubangiji Ya yi maka albarka. Allah Ya saka maka da mafificin alkhairi. Ya baka masu kyautata maka fiye da yadda ka kyautata min. Fiye da yadda ka dinga kare martabata da mutuncina. Ka so na zama uba na ƙwarai, ka so na zama uba na gari, amma duk na toje na ƙi baka haɗin kai."

Ya yi shiru na ɗan lokaci.

"Na san ba zan ƙara wani lokaci mai tsayi ba. Amma ka sani, Abdulhamid ɗawainiyar da ka yi da ni ba zan taɓa iya biyanka ba. Allah zai biyaka in sha Allahu."

Ya matse hannunsa.

"Matana da ƴaƴana duk sun guje ni saboda halina. Amma kai duk da mugun halina baka guje ni ba. Ka zauna tare da ni. Kana faɗa min gaskiya a lokacin da nake da damar gyarawa, amma na ƙi saurarenka. Allah ya sa ku gama da duniya lafiya."


Hawayen Abdulhamid da ya ke ta riƙewa suka zubo. Yana ci gaba da sauraran wasiyyar mahaifinsa.

"Don Allah idan ta Allah ta kasance na tafi, ka zama uba a wurin ƴan uwanka. Kar ka bari zumuncinku ya yanke. Ka nemi sauran Ƙannanka da Yayyenka, ka yi musu gatan da ni ban yi musu ba."

Ya ƙara matse hannunsa.

"Ka zama na gari Abdulhamid. Ka zama na gari. Mutum ba ya yin nadamar zama mutumin kirki har ya mutu. Amma idan ya zama mutumin da ake kuka da shi, zai yi danasani lokacin da ajalinsa ya zo, kuma nadamar ba za ta sake ba shi damar gyara kuskurensa ba, balle ya zama mutumin kirkin da za a yiwa kyakykyawar shaida bayan babu shi."

Abdulhamid ya kasa cewa komai. Yana dai riƙe da hannun mahaifinsa yana hawaye.
Hayyo ya sake kallon Fullo. Sai ya ɗaga hannunsa ya taɓa gefen fuskarta a hankali.

"Fullo…"

Muryarsa ta karye yana ƙoƙarin yin murmushi cikin hawaye.

"Na gode…"

Sai ya kalli kofin da ke hannunta.

"Zan ƙara ruwan mai sunan Umminta."

Fullo ta ɗago kansa a hankali daga saman cinyarta, ta sake kai masa kofin ruwa bakinsa ya sha.

Kaka dai tana ta ƙara kiran wayar Dr Yusuf da tun a ɗazun ta kira ta nemi alfarmar ya zo da gaggawa. 
Hayyo ya dinga kallon fuskar Fullo. A fuskarsa akwai wani irin murmushi na ƙarfin hali, duk da yadda jikinsa ke ƙara tsananta da ciwon da bai taɓa ji ba.

"Ki tayani roƙon yafiyar mahaifiyarki…"

Ya dakata yana neman ƙarfin yin magana. Don kamar maganar tasa na gab da ɗaukewa gaba ɗaya.

"Ki faɗa mata ina sonta. Ina sonta fiye da yadda baki zai iya furtawa. Duk abubuwan da na yi mata harrin zuciya ne."

Ya ɗan lumshe idanu.

"Dan Allah ta yafe min ko na samu na ga haske a ƙabarina."

Yana faɗar haka wuyansa ya karye gefe ɗaya. Shaƙuwa mai tsanani ta kama shi. Ya dafe ƙirjinsa, yana jin wata azaba mai ƙarfi tana ratsawa cikinsa. Ya buɗe baki yana son yin magana, amma shaƙuwar ta hana shi.
Sai ga dunƙulen jini na fita daga bakinsa.

Gaba ɗayansu suka firgita suna kiran,"Abba." Kaka da Yami ma suka yo kansa suna jera masa sannu, kowacce fuska cike da tausayinsa da wanzuwar wani imani da tsoron Allah a zuƙatansu.

"Abdulhamid tashi mu tafi da shi asibiti, zaman da shi anan ba zai yiwu ba. Daure ka cicciɓe shi."

Ya yunƙura zai miƙe cikin kyarmar jiki, hawaye na ta ambaliya a fuskarsa. Idanuwan Hayyo a rufe ya damƙo hannun yaran nasa yana girgiza kansa, alamar babu buƙatar bashi taimakon asibiti.

Ya matse su cikin guntun ƙarfin da ya rage masa.

"Tawa ta zo ƙarshe ai. Karku wahalar da kanku."

Ya yi ta ƙoƙarin haɗa kalmomin.

"Ba zan ƙara wasu mintuna masu yawan da har za ku kai ni asibiti ba."

Ya yi ƙoƙarin ɗago kansa.

"Mutuwa zan yi Ƴaƴana."

Hawaye suka zubo masa.

"Bana so in tafi in bar ku a wannan lokacin. Amma ban isa in hana mutuwa ta ɗauke ni ba a lokacin da ubangiji ya tsara tafiyar tawa."

Ya yi ajiyar numfashi cikin wahala.
"Mutuwa ta zama dole a gare ni. Ko ba yanzu ba… Idan na mutu ku nema min gafarar Allah. Kar ku gushe face kuna neman min gafararsa a ko da yaushe."

Muryarsa ta ƙara yin rauni.

"Haƙiƙa ni ɗin mai tarin laifi ne a gare Shi…"

Ya yi shiru na ɗan lokaci, yana tattara sauran ƙarfinsa don ganin ya furzar da dukkan maganganun da suke saman harshensa.

"Mutuwa zan yi babu makawa."

Sai ya lumshe idanu ya sake buɗe su.

"Iyayena sun rasu tun ina saurayi…"

Murmushi mai ciwo ya bayyana a fuskarsa.

"Baƙin cikina shi ne ya zama ajalinsu. Ina da dangi ku nemesu, haƙiƙa ku ƴan dangi ne."

Ya matse hannun Abdulhamid.

"Mayo Goi, Jalingo Local Government, Palace Road, Galadima Street, Gidan Galadiman Muri."

Ya ja numfashi da ƙyar.

"Nanne gidanmu… anan ahlina suke. Ku neme su kuɗin ƴan asali ne."

Hawayensa suka ƙara zuba.

"Allah ya yi muku albarka. Abdulhamid ka tayata neman Mijinta. Ka faɗa masa na basa amanarta, ya zame mata tamkar uba don Allah."

Ya sake kallon Fullo. Wadda yake jin yana tsananin buƙatar a ba shi damar da zai bata dukkan gatan da uba na gari zai bawa ƴarsa. Yana so ya jiyar da ita daɗin soyayyar uba.

"Don Allah ku ce da mahaifiyarku ta yafe min."

Sai muryarsa ta fara dusashewa.

"La ilaha illallahu… Muhammadu Rasulullahi… sallallahu alaihi wa sallam…"

Ɗif. Kamar ɗaukewar wuta, haka numfashinsa ya ɗauke. Hannunsa ya saki ya faɗi daga riƙon da ya yi wa ƴaƴansa. Shiru ya mamaye falon. Sai Kaka ta fashe da kuka tana faɗin.

"Shikenan Hayyo. Allah ya jiƙanka ya yi maka rahama, ya sa can ta fi nan."

Fullo ta ƙwala wata irin ƙara.

"A'a kaka! Abba nah!"

Ta kama shi tana jijjiga shi.

"Abba don Allah ka tashi."

Ta sake jijjiga shi, kuka yana shaƙe muryarta.

"Abba kar ka mutu. Abba kar ka tafi ka barmu muna buƙatarka. Wallahi mun yafe maka duk abin da ka yi mana. Don Allah ka tashi, Abba nah…"

Ta rungume shi.

"Muna sonka a yadda kake Abba. Ka tashi please."

Abdulhamid dai da yake namiji mai ƙarfin hali,  kukansa a hankali yake yi. Ya girgiza yama kasa cewa komai ba, a haka kamar mutuwar bata ɗimauta shi ba, but deep down his heart shi kaɗai ya san abin da yake ji a zuciyarsa. Kaka ta tashi ta fita domin kiran Ummi, fatanta Allah yasa bata yi nisa ba.

Sai dai tana ɗaga labulen parlo ta tarar da Ummi a tsaye tana goge hawaye da gefen mayafinta. Kaka ta tsaya gabanta tana kallonta yadda duk take a tsorace. Kuma da alama ta jima tsaye a wurin.

"Ya mutu ai."

Wasu sabbin hawaye suka sake zubo wa Ummi a fuska.
Kaka ma ta goge nata, sannan ta ce cikin sanyin murya,"Ki shigo ciki. A san abin yi kafin dare ya yi."

Ta ɗan yi shiru.

"Anan za a yi jana’izarsa ko sai mun koma can? Idan sai mun koma can, dole sai gobe za a kai shi, tunda kin ga dare zai yi."

Ta ƙara kallon Ummi, ita kanta Kakan a ɗimauce take da mutuwar.

"In kuma nan ɗin ne, to na shiga masallacin can na faɗa. Idan ya so ko bayan Magariba sai a kai shi."

Kukan da Ummi ta yi ta riƙewa ya kubce mata. Ta fashe da kuka sosai, ta shiga parlour jiki a mace ta nufi gawar Hayyo.
Tana isa gare shi sai ta tsaya tana kallonsa, kamar dai tana jiran ya buɗe idanunsa ya amsa mata. Kamar dai har yanzu mutumin da take gani a gabanta zai iya tashi ya ɗora rayuwarsa daga inda ya tsaya.

Sai ta durƙusa. Ta kifa kanta a ƙirjinsa, ta riƙe hannunsa cikin nata. Kuma zata iya cewa rabon da irin wannan kusancin ya kasance a tsakaninsu tun bata samu cikin Fullo ba. Rayuwa kenan! Yau ga ta a ƙirjinsa riƙe a hannayensa a lokacin da ba ya raye, lokacin da ba zai iya hantararta ko ya zageta ba, balle ya haramta mata jikin nasa.

Kuka ne mai nauyi take yi, mai fitowa daga zurfin zuciya, ba tare da ta iya hana shi ba. Da ƙyar muryarta ta samu ta fito a cikin kukan kuma a kakkarye.

"Na yafe maka…"

Ta ƙara riƙe hannunsa.

"Allah ya yafe maka. Allah ya sa ka huta, Ubangiji ya lulluɓeka da rahamarsa. In sha Allahu ba zamu gushe ba wajen yi maka addu'a. Allah ya haskaka ƙabarinka ya yafe maka zunubanka. In sha Allahu Aljannah zaka zarce."

A take parlour ɗin ya cika da kukan uwa da ƴaƴanta. Kuka mai raunana zuciyar duk wani mai imani. Kukan mutanen da babu wanda ya san abin da ke cikin zuciyarsu sai su da kansu. Domin duk yadda mutum ya kasance da mummunan hali, ranar da mutuwa ta raba shi da duniya, sai rashin kasancewarsa ya taɓa zuciyar makusantansa.

Musamman mutuwa irin wannan. Da mutum kan ji ina ma da za mu iya dawo da shi. Ina ma mutuwa ba ta zo da wuri haka ba. Ina ma za mu sake samun damar zama tare.

Kuma ba wai don saboda sun manta da abin da ya yi ba a garesu. Face mutuwa tana da wani irin nauyi na rissunar da zuƙat. Kukan Fullo da Abdulhmid ya ƙara tsinkar da zuciyar Ummi.
Ta ƙara matsa jikinta kan Hayyo, tana kuka sosai. Babu wanda yake iya lallashin wani. Don kowa da nasa ciwon. A wannan lokacin ne Dr. Yusuf ya shigo parlour.

Yami ya fara cin karo da ita. Yana kallonta jikinsa a sanyaye, ya ce,"Lafiya Yami? Waye ba shi da lafiya? Ba dai jikin Ummi ne ya tashi ba?"

Yami ta share hawaye.

"A'a ba ita ba ce. Wanda ma aka kira ɗin ka zo ka duba shi, Allah ya karɓi abinsa."

Yusuf ya kalli wajen da Ummi da ƴaƴanta suka kewaye gawar, sannan ya dawo da kallonsa kan Yami.

"Ban gane ba Yami. Waye ya mutu?"

Yami ta amsa cikin sanyin murya.
"Baban Fullo ne ya zo. Kuma ashe ajali ne ya kawo shi."

Yusuf ya nufi wajen da sauri. Tsaye ya yi akansu yana ƙarewa gawar da kanta ke saman cinyar Ummi kallo. Tabbas mamacin ya sha jinya, sai dai duk da irin mawuciyar jinyar da ya sha fama da ita, ba ita zata hana wanda ya san fuskar ganeta ba. 

Don haka ganin fuskar na tsawon mintuna biyar ya matuƙar bawa Yusuf mamaki har ya razana ya ja da baya, ya kalla Ummi ya kalla su Abdulhamid tukunna ya ce,"Waye wannan ɗin?".   
  
Babu wanda ya iya basa amsa a cikinsu, ya dinƙa kallon Fullo da ke aikin girgiza Hayyo tana faɗin don Allah Abba ka tashi, ka tashi mun yafe maka kar ka mutu yanzu.  
  
Yusuf ya zube a wajen, hoton gawar Hayyo da hoton Kawunsa Muhammad da ya sani na haska masa a ido. 

A fili ya furta,"Kawu Muhammad".   

Kansa nema yake ya ɗaure, jikinsa na rawa ya saka hannu cikin aljihunsa, ya ɗauko wayarsa ya kira lambar Ammi. Wayar ta yi ta ringing har ta katse bata ɗaga ba.

Sai ya kira Aliyu. Yana jin ya ɗaga ya ce masa,"Aliyu ka kai wa Ammi waya."

Aliyu ya amsa to. Ya kashe kiran, bayan ɗan lokaci sai ga kiran ya shigo wayar Yusuf, yana ɗagawa ya ji muryar Ammi a daƙile.

"Ya aka yi?"

Yusuf ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce,"Ammi."

"Na'am?"

Kamar ma a ruɗe yake lokacin da yake ce mata,"Kawu Muhammad."

Muryarta ta canja nan take.

"Me Kawu Muhammad ɗin ya yi? Ganinsa ka yi? Ka saba zuwa saudiya ka ce ka gansa kamar ka zautu."

Yusuf ya haɗiye yawu.

"Ammi ya mutu."

A matuƙar razane ta miƙe a inda take. Jikinta ya fara kyarma.

"Ya mutu?"

Ta ƙara maimaitawa kamar ba ta fahimci abin da ta ji ba.
"A ina ka gansa da zaka ce ya mutu? Yaushe rabonka da shi Yusuf? Wa ma ya san inda yake to?"

Yusuf ya yi saurin amsawa.

"To ban sani ba Ammi. Ko idona ne yake gane min ba daidai ba. Amma tabbas gani ga gawar Kawu Muhammad a gabana. Sanin da na yi masa a lokacin yarinta ba zai sa na kasa shaida shi ba, kuma karki manta fa hotonsa tamkar manne yake da idanuwanmu a kullum."

Ya ɗan yi shiru.

"Zan tura miki address. Ki zo yanzu ki gani ko shi ɗin ne. Amma ni na tabbata gawar Kawu Muhammad ce a gabana."

Ammi ta kasa magana. Wayar Aliyu ta zame daga hannunta.
Ta juya da sauri ta shiga ɗaki. Ta ɗauko mayafi jikinta na ta rawa ta sakko daga bene. Zuciyarta sai saƙa mata abubuwa take yi.

"Mu je, mu je Aliyu."

Ta fita tana faɗin.

"Duba wayarka. Yusuf zai turo da address."

Cikin mintunan da ba su haura ashirin ba, sai ga su Ammi sun iso gidan. Ta shiga parlour a rikice. Zuwa lokacin an riga an lulluɓe gawar.

Ta kalli Ummi. Ta kalli Fullo. Ta kalli Abdulhamid.

Babu abin da ke tashi a parlour ɗin sai gunjin kuka. Sai ta nufi gawar da sassarfa. Hannunta yana kyarma ta ɗaga zanin da aka rufe Hayyo da shi. Idanunta suka sauka kan fuskarsa.

Ta yi shiru na ɗan lokaci kamar wadda aka hana ta numfashi.
Kallon da take yi masa, kallo ne na son ta tabbatar da shi ɗin ne ko dai tsananin kamanni ne, duk da cewa shigowarta ta ga photocoy ɗin Hayyo a fuskar Abdulhamid. To amma ta san a duniya akwai halittun ubangiji da yawa masu kama ɗaya kuma mabanbanta jini. Duk da cewa kamannin sun ɓaci, amma a yanzun da ta tabbatar da gawar nan jininta ne, sai ta saki zanin nan take, ta zabura ta ja da baya.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un."

Ta fashe da kuka sosai.

"Ashe rabon ba zamu ƙara ganawa ba sai bayan ka mutu, Hammah kai nake gani da gaske?"

Ta kalli gawar, hawaye suna zubo mata ba ƙaƙƙautawa.

"Hammah ka yi magana ka tabbatar min kai ɗin ne."

Sai ta juya ta kalli Ummi. Ta yi shiru kafin ta tambaya cikin murya mai cike da mamaki da ɓoyayyan ciwo a cikinta.

"Mijinki ne da gaske?"

Ummi da mamaki take kallonta, ta ɗaga mata kai kawai, tana ƙoƙarin tantance abin da kunnenta ya ji Ammi ta faɗa da gawar mijinta da yake kwance a gabansu.

Ammi ta share hawayenta sannan ta ce,"Yayana ne. Uwarmu ɗaya, ubanmu ɗaya. Tunda ya zama ajalin iyayenmu, shikenan kuma ya kama gabansa, bai ƙara waiwayon kowa ba. Rabona da shi tun Yusuf bai fi shekara goma ba. Ya zo gidana sau ɗaya kawai, lokacin ma ko sauraronsa ban tsaya na yi ba, saboda ina fushi da shi."

Ta yi shiru. Idanunta suka koma kan gawar Hayyo, tana kallonsa na ɗan lokaci cikin wani irin kuka da tunani mai zurfi,"Allah ya jiƙanka Hammah. Yasa ka huta. Allah ya yafe maka zunubanka, ya haskaka maka ƙabarinka, Allah ya sada ka da Manzon Allah ﷺ."

Daga nan sai ta ɗauki wayarta, ta fara kiran ƴan'uwanta waɗanda suke uba ɗaya da Hayyo. Dama su biyu ne a wajen mahaifiyarsu, daga shi sai ita.
Duk irin fushin da aka yi da Hayyo, duk irin nisan da ya jefa a kansa tsakaninsa da ƴan'uwansa, har wasu daga cikinsu sun kai ga mantawa da shi ma, idan ba hira ce ta tashi ba. Amma mutuwa tana da wani irin iko na tada abin da mutum ya ɗauka ya mutu a cikin zuciyarsa da rayuwarsa.

Kan kace mene, waɗanda suke zaune a Gombe suka fara shigowa. Har sunata mamakin ashe ma duk wannan nisan zangon yana kusa da su.
Ba wai don sun manta da abin da Hayyo ya aikata ba. Ba wai don mutuwarsa ta share dukkan laifukansa a garesu ba. Sai dai don duk da komai na rashin daɗi da ya aikata, shi ɗin ɗan'uwansu ne, jininsu ne, sun yafe masa, saura tsakaninsa da ubangijinsa, kuma wannan ma suna da yaƙin Allah ya yafe masa domin ubangiji mai gafara ne ga bayinsa muddin sun roƙi gafararsa.

A lokacin da labari ya kai ga manyan Yayyansa da suke Taraba Jalingo, sai aka dakatar da kai gawar a daren ranar. Aka ce a bari sai washegari, domin a ba wa ƴan'uwansa damar zuwa su gan shi, a yi masa janaza cikin sutturar da ta dace.

Washegari da sassafe da misalin ƙarfe takwas, gidan ya cika maƙil. Maza da mata ƴan'uwan Hayyo daga wurare daban-daban, fuskoki cike da hawaye, wasu kuma sun kasa kukan, sun yi shiru kamar har yanzu hankalinsu ya ƙi yarda cewa mutumin da suka ɗauka ya ɓace tun shekaru masu yawa, yanzu shine kwance a gabansu babu rai. 

A haka har aka yi masa wanka aka haɗa shi. Abin da ake jira shi ne babban wan Hayyo ya iso domin ya jagoranci sallar jana'izarsa. Lokacin da aka ɗauko gawar Hayyo domin a fitar da ita daga parlon, sai wani irin shiru ya sauka na ɗan lokaci.
Sai motsin tasbihi da salati da kake ji daga bakunan ƴan zaman makoki.

Fullo tana can kusa da makarar, tana riƙe da ita gam. Aka zo za a ɗauki gawar sai ta riƙe ta da ƙarfi.

"Don Allah..."

Muryarta ta karye.

"Don Allah ku bar min Abbana kun ji."

Ta ƙara riƙewa, hawaye suna zubar mata babu ƙaƙƙautawa.

"Ku bar min shi don Allah. Abbana kada ku tafi da shi, bai mutu ba bacci yake yi."

Wasu daga cikin mutanen da tun lokacin da suka shigo ba su samu damar sakin kukan da ke maƙale a ƙirjinsu ba, a wannan lokacin sai suka fashe da kuka.

Ba wai saboda mutuwar ba kawai. Suna ganin yadda ɗiya take ƙoƙarin riƙe mahaifinta da ya mutu, wadda ke jin kamar har yanzu tana ganin akwai damar a dawo masa da ransa.

Kuka ya gauraye gidan. Ammi ta matso ta kama Fullo, amma inaa Fullo sai ta ƙara damƙe makarar.
"Don Allah Ammi ku bar min Abbana zai dawo fa."

"Ki daina wannan kukan mara amfani ki yi wa Abbanki addu'a kin ji. Duk mai imani ya shaida idan an mutu ba a dawo wa Halimatu."

Da ƙyar Ammi da Hajiya Madina da ta iso suka riƙe hannun Fullo, suka ƙwace shi daga kan makarar da ta yiwa mugun riƙo. Don ƙarfin ma kamar ba nata ba.

Fullo ta ƙara fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk wani mai imani, tana ƙoƙarin komawa kan makarar da aka riga aka ɗauka.

"Abbana..."

Hajiya Madina ta rungumota jikinta. A haka dai aka samu aka fitar da makarar daga parlon.
Sai dai suna fita daga parlon  Fullo ta ƙame ƙam. Idanunta suka bi makarar da kallo tana hasko mahaifinta kwance a ciki, kallon da take kamar tana son tantance wani abu.
Kuma kafin ta gama tantancewar take ta ƙwalla wata razananniyar ƙara.

"ABBANAAA!"

Ƙarar da ta yi amsakuwa a gidan gaba ɗaya. Nan take jikinta ya saki. Ta yanke jiki ta faɗi.

"Fullo!"

Hajiya Madina ta yi saurin cafko ta kafin kanta ya bugu da ƙasa. Kuka da ihu suka sake tashi a gidan. Wasu cikin ƴan uwan Hayyo mata suka isa zuwa gare ta da sauri.

A wannan ranar dai, Aljanun da ba a san Fullo da su ba suka tashi. Don farko ma ba a tabbatar da su ba ne. Sai da Ciroma ya zo kanta bayan dawowarsu daga kai Hayyo, tukunna ya tabbatar musu aljanu ne, tun da dama a family na su akwai wannan aljanun gadon kusan akan kowa. Zaka ga kamar mutum bai da su, amma daga lokacin da wani ya rasu a cikinsu, musamman mutuwar uwa ko ta uba, to zaka samu Ƴar wannan mamacin aljanun gadonta sun tashi.

*Mayo Goi, Jalingo Local Government, Palace Road, Galadima Street, Gidan Galadiman Muri.*

Tafkeken gida ne zubin gidan sarauta, sai dai ginin irin na zamanin da ne, ba irin na yanzu ba. An ɗan sabunta shi ne kawai, ba tare da an sauya ainihin fasalinsa sosai ba. Tsarinsa, faɗinsa da yadda aka raba shi zuwa sassa daban-daban duk suna ɗauke da irin tsohon salon gidajen babbar masarauta.

Ƙofar gidan marigayi tsohon Galadiman Muri ya cika da jama'a, sai ka ɗauka kamar ɗaurin auren wani babban mutum ake yi, ko kuma za a ƙara yin wani babban bikin naɗin sarauta ne.

A ƙarƙashin wata babbar rumfar tempol da aka kafa a gaban gidan, Maudo ne zaune a kan kujera, ya sha rawani, yana amsar gaisuwar ta'aziyya daga bakunan mutane da suke ta tururuwar zuwa gare shi.

Shi ne babban ɗa a wurin marigayi Galadiman Muri Alhaji Aminu Barkinɗo. Shi ne kuma wanda ya zauna a hannun mahaifiyar Hayyo tun tana raye, domin ita ce ta riƙe shi har rasuwarta. Bayan rasuwar mahaifin nasu kuma, Maudo ya maye gurbin kujerar Galadima ta mahaifinsa, ya ci gaba da riƙe ta har zuwa wannan ƙarni da muke ciki.

A cikin gidan, ɗumbin mutane ne ƴan ta'aziyya na ta shige da fice a cikin wannan ƙaton tsakar gidan da ya kusan cin fin filoti biyu. Idan ka tsaya kana kallon yadda aka raba gidan zuwa ɓangarori daban-daban, za ka fahimci nan ɗin ba gida ba ne kawai, family house ne babba ma kuwa, na manyan mutane, gida da aka gina don zuriyar da za ta zo, bayan zuriyar da ta gabata.

A cikin hayaniyar mutane, ana jin murya daga ɓangarori daban-daban, wasu suna miƙa ta'aziyya, wasu kuma suna karɓar ruwa ko abinci daga masu hidima. Abincin da zaka rantse bana gidan rasuwa ba ne, domin lafiyayyan abinci ne da yaji haɗi na musamman har da daƙwalan kaji akai.
A dai-dai lokacin ne wata farar tsohuwa tukuf ta fito daga wani sashe da yake daban a ƙawatuwa da duk sauran sashikan.

Tana dogara sandarta ne wadda aka yiwa kwalliyar sarauta a jiki, tana takawa a hankali cikin taku na ƙasaita, duk da irin tsufan da ya bayyana a jikinta amma ubangiji ya wadata da lafiya.

Tun fitowarta wata hadima ke biye da ita a baya. Hannunta riƙe da wata ƙwarya babba ta fura. Wannan tsohuwa ita kaɗai ta rage cikin matan Alhaji Aminu Barkinɗo, kuma ba zaka taɓa cewa ba ita ta haifi dukka tarin Ƴaƴan da Allah ya bawa Marigayi Galadiman Muri ba.
Daga cikin mata huɗun da ya aura, ita ce kaɗai Allah ya ƙaddara mata tsawon rai har zuwa wannan lokacin. Gata nan fess cikin ƙoshin lafiya sai dai bayyanar girma kawai, wanda dole ne duk yadda ka kai ga jin daɗi kuwa.

Suka ci gaba da tafiya har suka ƙaraso tsakiyar makeken tsakar gidan. Anan tsohuwar taja ta tsaya. Ta juya kai a hankali ta kalli matar da ke biye da ita. Idanunta suka sauka kan ƙwaryar furar da Hadimar ke riƙe da ita, kafin ta ɗaga ido ta kalle ta fuska da fuska.

Cikin yaren Fulatanci ta ce da hadimar,"Ki nemo Gaji ki ba shi furan ya kai wa Dottijo. Tun ɗazu ya aiko Manga, amma ba a samu an kai masa ba. Ƙila zai sha tare da baƙi ne. Yi maza dun Allah."

Hadimar ta amsa da kai, sannan ta wuce da sauri. Ta bi dogon soron da ya haɗa wannan ɓangaren gidan da wani babban fili, kafin daga nan a samu hanyar fita zuwa waje, bayan an wuce zauruka goma cif.

Daada ta tsaya a tsakiyar tsakar gidan tana kallon yadda jama'a ƴan ta'aziyya ke fitowa daga ɓangaren Ciroma.

Sai ta waiga, ta ƙwala kira,"Munyoɗo!"

Ba a amsa ba.

Ta sake kira a karo na biyu,

"Munyoɗo!"

Sai wata farar dattijuwa ta fito da sauri daga wani ɓangare na gidan, tana amsawa,"Daada! Tuba na ke ranki shi daɗe gani."

Ta ƙaraso gabanta, ta ɗan rissina, sannan ta ce,"Lafiya kika fito ke ɗaya? Kuma kin tsaya a rana. Me kike da buƙata? Ina Patel ɗin?"

Tana magana tana kama Daada a hankali, ta matsar da ita daga cikin hasken rana zuwa inda inuwa ta fi yawa.
Daada ta kalleta ta cikin gilashin idonta, sannan ta tambaya,"Ina wannan shike? Amm mata na wurin Hayyo?"

Munyoɗo ta ɗan tsaya, kamar ba ta fahimci wacce take nufi ba.
"Dukka Matan nasa ai sun samu isowa. Wacce daga ciki Daada?"

Daada ta ɗan ɓata fuska. Muryarta ta fita da yanayin ƙorafi.

"Wannan yaro dai Allah ya jiƙansa ya yafe masa kawai. Baka shiga tsakanin bawa da ubangijinsa ba. Ya je ya haɗo mata da yawa, in ka tashi neman ɗaya sai ka yi ta faman kwatance."

Ta yi tsaki a hankali, sannan ta sake duban Munyoɗo.
"Su nawa aka samu yanzu?"

"Su bakwai ne. Sauran huɗun an ce sun rasu. Suna babban parlo yanzu haka."

Daada ta girgiza kai a hankali, alamar Allah ya kyauta. Ta yi ɗan yi jim, tukunna ta ɗaga ido ta kalli Munyoɗo.

"To wannan Balarabiyar za ki kirawo min."

Munyoɗo ta ce,"Tom Daada bari na dubata".