15-16
Bayan an dawo da Aisha gida tare da gawar Jameelu, gidan wanda a baya yake cike da hayaniyar rayuwar ma’aurata ya koma wani wuri mai tsananin shiru, shiru irin wanda ba ya nufin babu mutane a ciki, sai dai yana nuna cewa farin cikin da ya taɓa cika bangayen gidan ya ja baya, ya bar wani gibi mai girma da ba a san abin da zai iya cike shi ba, domin duk inda Aisha ta kalla a gidan sai ta tuna da Jameelu, idan ta kalli kujerar da yake zama sai ta tuna da yadda yake komawa gida bayan ya taso gurin ayki, idan ta kalli ɗakin kwana kuma sai zuciyarta ta yi mata wani irin raɗaɗi saboda ta san mutumin da ya saba kwanciya kusa da ita ba zai sake buɗe ƙofar ya shigo ba bare har ya ɗebe mata kewa..
Moneer ne yazo ya zauna kusa da ita na ɗan lokaci, sannan cikin sanyin murya ya ce, “Aisha, ya kamata ki kira ’yan uwanki ki sanar da su cewa Jameelu ya rasu, domin akwai abubuwan da ake buƙatar shirya su cikin gaggawa, kuma tunda ba mu san tsawon lokacin da za su ɗauka kafin su samu damar zuwa ba, ya kamata su san abin da ya faru tun yanzu.”
Aisha batace komaiba ta ɗaga wayarta da hannayenta da suke rawa, ta duba lambobin da ke cikinta, amma kafin ta fara kiran kowa sai da hawaye suka sake cika mata idanu, domin kalmar da za ta faɗa musu ba ƙaramin nauyi ba ne da ita a gare taba; ta yadda za ta kira mutanen da suka san Jameelu a matsayin mijinta, sannan ta ce musu wannan mutumin ya mutu,,wannan baƙin saƙone da bazata mantaba,.
Daga ƙarshe ta kira ɗaya daga cikin ’yan uwansu, kuma da aka ɗaga wayar sai muryar Aisha ta karye ta fara kuka tace.
“yaya habu,Jameelune ya rasu.”
Daga can gefen habu ya yi shiru na wasu daƙiƙu, kamar wanda ya ji wani abu da ya kasa yarda da shi.
“Me kika ce?”ya tambaya cikin tsoro
Aisha ta fashe da kuka.Tace“Jameelu ya rasu… Allah Ya karɓi rayuwarsa.”
Daga ɗaya gefen muryar habu ta canza, kukansa ya bayyana, ya fara tambayarta yadda abin ya faru, amma Aisha ba ta iya ba da cikakken bayani ba saboda duk lokacin da ta fara magana sai hawayenta su katse ta, har Moneer ya karɓi wayar ya yi musu bayanin cewa Jameelu ya rasune bayan an kai shi asibiti cikin wani hali mai tsanani, sannan ya ce musu Aisha ma ba ta da cikakkiyar lafiya saboda aikin tiyatar da aka yi mata aka ciro mata yarinya.
Bayan sun ji labarin, ’yan uwansu sun yi kuka sosai, domin mutuwar Jameelu ta zo musu da baƙin ciki da mamaki, musamman ganin cewa ba su kasance a kusa ba a lokacin da yake fama da rashin lafiyar, kuma bayan sun yi shawara tsakaninsu sai suka yanke cewa ba za su iya zuwa nan take ba saboda nisan hanya da tsadar sufuri, don haka suka ba da umarnin a yi masa jana’iza ba tare da jiran zuwansu ba.
“Ku yi masa abin da ya kamata,” suka ce cikin kuka, “kar a jinkirta saboda mu, domin idan aka ce za a jira mu har mu samu hanyar zuwa, gawar na iya fara canzawa, musamman tunda an riga an fitar da ita daga ma’ajiyar gawa, kuma ba za mu so a bar shi yana jiran mu ba.”
Aisha dake zaune kusa da Moneer lokacin da aka gama wannan magana, kuma duk da cewa zuciyarta ta ƙi yarda da cewa Jameelu zai tafi ba tare da wani daga cikin danginsa ya zo ya yi masa bankwana ba, ita kanta ta fahimci cewa ba za ta iya tilasta wa mutane su yi tafiyar cikin gaggawa ba, musamman idan babu halin hakan tunda tasan ya rayuwar take.
Moneer kuwa, a zuciyarsa, ya ji wani irin sauƙi da ba zai iya bayyana wa kowa ba lokacin da ya ji cewa an ba da umarnin a binne Jameelu ba tare da jiran ’yan uwansa ba, domin duk abin da yake so shi ne a rufe wannan shafi cikin gaggawa kafin tambayoyi su fara yawa, kafin mutane su fara neman cikakken bayani, kafin Aisha ta samu damar zama cikin yanayin da za ta fara tambayar abubuwan da suka faru a asibiti.Amma a fuska bai nuna komai ba.
Sai ya sauke kansa ƙasa da yayi cikin jimami ya ce, “Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa.”
Nan take ya fara shirya mutanen da za su kula da jana’izar, ya tabbatar an shirya komai cikin mutunci, aka shirya ruwan wanka, aka samu mutanen da suka san yadda ake yi wa mamaci wanka, sannan aka yi wa Jameelu wanka cikin natsuwa da mutuntawa.