17-18
Aisha kuwa, tun daga lokacin da aka fara shirya gawar, kuka ya ƙaru mata, domin tun lokacin da aka ce za a kai Jameelu domin a yi masa wanka sai ta ji kamar ana ƙoƙarin kwace mata shi daga gare ta gaba ɗayane.
“Ku bar ni in gan shi,” ta riƙa faɗa cikin kuka, “ko da na ɗan lokaci ne kawai.”
Moneer yana ta ƙoƙarin rarrashinta, yana tunasar da ita cewa Jameelu ya riga ya koma ga Mahaliccinsa, kuma abin da ya fi amfani gare shi yanzu shi ne addu’a, amma Aisha ba ta iya sauraron nasiha yadda ya kamata ba, domin zuciyarta ta cika da ciwon mutuwa.
Da aka kammala wankansa aka yi masa sutura, aka sallaci jana’izarsa, aka ɗauke shi zuwa makabarta, Aisha ta tsaya a bakin ƙofar gidan tana kuka yayin da aka fita da shi, har ta ɗaga hannuwanta zuwa sama tana roƙon Allah.
“Ya Allah, ka gafarta masa… Ya Allah, ka jiƙansa… Ya Allah, ka san cewa na so shi, ka san cewa ban shirya rabuwa da shi ba.”ta faɗi gamida durƙushewa agurin tana kuka me tsuma zuciya
lokacin da aka kai Jameelu makabarta aka binne shi, Aisha tana can a gida tana kuka kamar ranta zai fita, tana jin kamar wani ɓangare na jikinta ne aka binne a ƙarƙashin ƙasa tare da shi.
Daga wannan rana ne gidan ya zama mata kamar kurkuku na tunani.
Takan zauna a inda suka saba zama tare, ta yi shiru na tsawon lokaci, wani lokaci har sai Moneer ya shigo ya same ta tana kallon wuri guda ba tare da ta san abin da take kallo ba, sannan idan ya tambaye ta abin da take tunani sai ta ce, “Ina tunanin yadda komai ya ƙare da sauri.”
Moneer ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin Aisha ba ta zauna cikin baƙin cikiba, yana tabbatar da an tanadar mata abinci, yana sa a kula da jaririyar, yana zama kusa da ita idan ta shiga damuwa, kuma duk lokacin da ta fara kuka yana ƙoƙarin tunasar da ita cewa yanzu tana da diya da take buƙatar kulawarta, domin rayuwa ba ta tsaya gaba ɗaya saboda mutuwar mutum guda ba.
“Ki kalli ’yarki, Aisha,” yake faɗa mata. “Wannan ita ce amanar da Allah Ya bar miki daga rayuwar Jameelu, kuma idan kika bar baƙin ciki ya rinjaye ki har kika kasa kula da ita, ba za ki taimaki kanki ba, kuma ba za ki taimake ta ba.”
Aisha ta kan ɗaga jaririyar ta matse ta a kirjinta, sannan ta yi shiru, domin duk lokacin da ta kalli fuskar yarinyar sai ta ga wani abu daga mahaifinta, abin da kan sa hawayenta su sake zarya a idanunta kenan, amma duk da haka kasancewar jaririyar a hannunta ya zama ɗaya daga cikin abubuwan da suke hana zuciyarta rushewa gaba ɗaya.
Kwana biyar suka wuce bayan binne Jameelu, kuma a wannan lokacin ’yan uwansa biyu, Habu da Musa, suka samu damar zuwa, domin sauran ’yan uwansu da suke Sudan ba su samu damar zuwa gaba ɗaya ba saboda tsadar kuɗin sufuri da kuma wahalar samun hanyar tafiya cikin gaggawa, don haka aka turo su biyu a matsayin wakilai.