ZALLAR SHA'AWA...

19-20

by @zahrasurbajo

Da suka iso, suka fara jajanta wa Aisha, kuma ganinta cikin yanayin rashin ƙarfi da kuma jaririya a hannunta ya sake tayar musu da ciwon mutuwar jameelu sukai ta kuka.

“Aisha, Allah Ya baki haƙuri,” Habu ya ce cikin murya mai cike da tausayi. “Mun san babu kalmar da za ta maye gurbin abin da kika rasa, amma Allah Ya fi mu sanin abin da Ya tsara.Da yasa ya kira jameelu adaidai lokacin da kikafi buƙatarsa”

Aisha ta fashe da kuka.Tace“Da kun zo da wuri da kun samu damar raka jameelu,haka aka kaishi ba tare da kowa nashiba tunda ni banida ikon binshi…”ta faɗi cikin kukan.

Musa ya sauke kansa kansa ƙasa yana hawaye yace“Mun yi iya ƙoƙarinmu, amma kuɗin hanya ya yi yawa, kuma ba mu samu damar zuwa da wuri ba sabida nisa,shine yasa amma bamuyi hakan dan bamu damu da jameeluba aisha.”

“Na fahimta,” Aisha ta ce,tana share hawayenta.

Habu da Musa haka suka je kabarin Jameelu, suka tsaya a kansa suna masa addu’a, suna roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya jiƙansa, Ya sanya kabarinsa ya zama ɗaya daga cikin lambunan Aljanna, sannan suka dawo gida suna ci gaba da zama tare da Aisha domin kada ta ji kamar an bar ta ita kaɗai cikin wannan lokaci mai wuya.

Bayan sun yi kwana biyar, sai suka fara shirye shiryen  komawa sudan,.

Aisha ta ji zuciyarta ta ƙara yimata zafi jin cewa zasu tafi.Tace cikin aunin murya"yanzu tafiya zakuyi ?"
Habu ya kalle ta.Cikin tausayawa yace
“Dole ne mu koma, Aisha, domin mun zo ne a matsayin wakilai, kuma sauran ’yan uwa suna can suna jiran labarinmu kinga ay bazamui ta zamaba tunda zaman namu baze dawo mana da jameeluba.”

Aisha ta kalli Musa, sannan ta ce, “zaku bar ni ni kaɗai kenan?”

Musa ya girgiza kai cikin tausayi.Yace
“Ba wai muna son mu bar ki bane,kawai de munga ke ma yanzu ba ki da cikakkiyar lafiya.Suan ba nan bace,shiyasa muke ganin gwara muje mu faɗa se asan yadda zaa tsara,azo atafi dake,inma mace zaa turo ta kula dake dole duka se munjene zaa san abunyi”
Ana hakane  Moneer ya shigo,inda kanshi tsaye ya shiga cikin maganar cikin nutsuwa.Yace"

“Abin da Musa ya faɗa gaskiya ne, Aisha har yanzu tana buƙatar kulawa, musamman saboda aikin CS ɗin da aka yi mata, don haka ba zai yiwu ta yi doguwar tafiya yanzu ba.”

Habu ya ce, “To bazamu iya tafiya da ita a hankaliba?”

Moneer ya girgiza kai sannan yace.
“Ba zan iya ba ku shawarar hakan ba, domin tafiyar hanya mai nisa a irin wannan yanayin na iya ƙara mata wahala, kuma jaririyar ma tayi ƙarama sosai.Da bin doguwar hanya irin haka”

Aisha ta yi shiru, domin a cikin zuciyarta ta san cewa jikinta ba zai iya ɗaukar irin wannan tafiyar ba, ko da kuwa zuciyarta tana son bin mutanen da suka zo daga dangin Jameelu dolene ita tayi haƙuri.
Moneer ne ya ci gaba da cewa, “Ku tafi ku kwantarwa da sauran ’yan uwa hankali, ku gaya musu cewa Aisha tana nan lafiya, kuma da zarar ta ƙara samun sauƙi, zan kawo ta da kaina,kuma munyi magana da wata tsohuwa zata zo ta zauna dasu ita da babyn”cewar mneer

Habu ya kalli Moneer na ɗan lokaci, sannan ya ce, “Allah Ya saka maka da alheri, Doctor, domin da ba dan kai ba da taimakon Allah,da ba mu san yadda lamarin zai kasance ba.”

Moneer ya amsa da, “Ba komai, wannan ay wajibi ne akan kowanne musulmi ya kula da ɗan uwansa.”

Musa ma ya yi masa godiya sosai, sannan suka yi wa Aisha addu’ar samun sauƙi, suka yi mata nasiha da ta riƙa kula da kanta da jaririyarta, kafin suka tattara kayansu suka shirya tafiya.

Lokacin da za su tafi, Aisha ta kasa ɓoye hawayenta tace.

“dan Allah da Kunje ku dawo ku tafi da ni,” ta ce cikin murya mai rauni.

Habu ya amsa, “Ba za mu manta da ke ba, Aisha, kina ɗauke da wani ɓangare na ɗan’uwanmu, kuma wannan yarinyar za ta kasance abin tunawa da Jameelu a gare mu har ƙarshen rayuwarmu dan haka zamu dawo.”

SAisha ta rungume jaririyar a kirjinta, hawayenta suka  ci gaba da zubowa.

Bayan sun yi mata bankwana, suka fita daga gidan, Aisha ta tsaya tana kallonsu har suka ɓace daga ganinnta
Ta koma cikin ɗaki a hankali, ta zauna a kan gado, ta kalli jaririyar da ke kwance kusa da ita, sannan ta ɗaga idanunta zuwa inda ta san Jameelu ya taɓa zama.Tace kamar tana ganinshi
“kaga Yanzu su ma sun tafi sun barni…”Ta faɗi hakan cikin raɗaɗi. hawayenta suka sake zubowa taci gaba da cewa.“Jameelu,ka tafi  ka bar ni da wannan yarinyar… ka bar ni da ita a duniyar da ban san yadda zan rayu a cikinta babu kai ba.”ta faɗi tana jin mutuwar na dawo mata sabuwa.
A wajen ƙofar ɗakin kuwa, Moneer ne ya tsaya yana kallonta ba tare da ta lura da shi ba.Ya ga yadda Aisha take rungume da jaririyar, yadda take kuka gwanin tausayi,duba  da ganin  yadda babu wanda ya rage mata daga cikin mutanen da suka zo mata ta'aziyya.ya sauke numfashi a hankali.Tausayinta da kuma farincikin cimma burinshi suka mamaye zuciyarshi alokaci guda.
***********
Bayan watanni biyu A wannan lokacin, gidan ya kasance na Aisha da jaririyarta ne kawai se tsohuwa ladi dake kulawa dasu.
Domin moneer beda mata kuma shima ba ɗan garin bane duk ƴan uwansa suna katsina shine kawai ke zaune anan shiyasa bakowa agidan se su.